Showing 198001 words to 201000 words out of 299981 words

Chapter 67 - Sarautar Mata By Makawa

04 Dec 2025

17638

k8n hakkura da,abinda ya faru a baya tsakani da ke bawai ki rike zancen haka ba,a ranki,
Wallahi, Kinji na,yi maki rantsuwar muslmi zankiye duk wani hakkin ki da bacin ranki da,ya rataya a kaina da yardan Allah,
Cikin dan daga murya da ban tabayi mai ba nake cewa bana bukatar rantsuwar ka don ni lafiyata yafi min ko a yanzu
Don ko cikin dagani har kai bawai mun san da zuwan shi bane don da na riga kowa kin yarda da,shigan shi a jikina tunda ba,a kaunar hada zuria dani a gidan nan,
Don haka wallahi ba zan saurareka ba don kuwa ni baka da abinda zaka fada min ,
Duk irin halarcin da nai a gidan nan a,rayuwata rana daya aka nuna min cewa niba yar mutunci bace a gurin ku,
Tun dana fara magana kan shi yana kasa sadde bai tankamin ba sai can naji ya sauke ajiyan zuciya tare da shafan kan shi a hankali,
Yadago jajayen idanuwan shi yana cewa mai yazafi haka Humaira dakike fadar wanan magana?
Na kara cewa a hasale rashin kaunar da ka iya,rufe idanuwan ka,kanuna min a fili shi ya jawo hakan,
Yace naji zan dai kyale ki ne don lalurar dake a jikin ki kawai amma in bashi ba,ai bakifi karfina,ba,wallahi,
Wani irin azaban radadin soyayyar Humaira yake jin yana taso mashi yana,sukar masa kahon zuciyar shi ,
Mikewa,yayi rai a bace komai duk ya rikice mashi a lokaci guda sai yake cewa, naji nasan yanzu baki bukata na,a,rayuwan ki ko kadan akan abinda ya faru a baya tsakanin mu
Wanda ke kin san cewa hakan bayina bane kawai akasine aka samu a tsakanin mu,
Wani irin kallon na,watsa mai mai nuna tsana a fili
Murmushi mai nuna takaici yayi cikin kada kan shi, yana tafiya yake cewa watarana zaki fahinci cewa ni ba makiyin ki bane ai,
Ya dan kai hannun shi da,wasa yana son ya lakatar min hancina cikin sauri na gwauce ina cewa wallahi kada ka fara na fada maka,
Yayi yar dariyar yake tare da cewa Allah ya kyauta yafita yabar dakin ran shi a bace,,
Ganin da nayi ya bar min dakin yasani rakashi da hararan takaici nace a fili je ka karata can da matar ka kunfi kusa ai,
Muddin ina tuna irin kuntata min da Hamza yayi a gidan banga ranan da zaiyi fari a,gareni ba
Da irin wanan tunanen ne har naji an soma kiran sallah magariba haka yasani mikewa zuwa yin alwala,
Shiko yana fita kofar gida ya koma ya zauna tare da soma tunanen duniya,
Sadiya ta,shigo gidan ahi ta,bata mashi zaman lafiya da matar shi mai kaunar shi a,rayuwa,

Alhamdullah don yanzu abubuwa sun dan daidaita a tsakani da maigidan amma babu zancen kasan cewa tare da maigida a tsakanin mu don ban bada fuskan yin haka ba
Saboda na fada mai ban daukan wanan akidar a tsakanin mu yanzu,
Duk iya irin wayyon su na maza yai min amma bai samu kaina ta wanan harkan ba,
Karshe ma,sai cewa yake wai ina gudun shine shiya kawo haka a tsakanin mu sai dai na nuna mai cewa saboda ciwon maran da ke samuna yasa likita ya fada min na,tsare kaina,
Hakan yasa ni samun sassauci akan bibiyata da yake yawan yi kan zance guda,

****** ********* ******
Natsuwa ta soma zuwa wa yaya Hamza don shawaran da na bashi na yadan fara buga buga shi yabi,
Matsalar sho gudane shine fitinar Sadiya gashi ba dama ya dauki wani mataki a kanta don tana da tsohon ciki a jikin ta,
Sai dai yanzu da cikin ta ya girma ta dan rage fitina sai dai sa ido daga zaune take yaba bakar magana ga kowa a gidan ,
Harkokina nake normal duk da ina cikin lalura amma ina dan sana,ana danakeyi don gujewa zaman banza,
Kamar yadda kowa ke fada min cewa naci faba da hakkuri hakan nakeyi,
Don al,amarin ubangji haka yake, wani lokacin sai yayi maka abinda zakaita bakin ciki akan shi saboda wauta da rashin hakkuri irin na mu na dan adam don rashin sanin abinda yake boye a,gurin Allah,
Sai daga baya sannu a hankali zakagane ai wanan abin shine alheri da a kullun kake roko gare ka ,
Don haka yanzu da na,samu natsuwar hankali a gida sai na fahinci cewa shigowan Sadiya a cikin mu wani hikima ne na ubangiji rashin ganewa ne yasani tayar da hankalina da farko a kan zaman ta,
Don ni kadai nasan irin zaman ukubar danayi tare dasu Umma da yaranta a baya,
Rayuwa nayi a gidan irin na bauta banda yancin kaina ko kadan a gurin umma,
Nakan ta rokon Allah da yakawo min agajin da zan samu sasauci akan zaman aurena a gidan Hamza na samu saukin al,amari,
Batare da wata fitina ko hayaniya tsakani na dasu ba ta jajibo wa kanta auren Sadiya agidan wanda yanzu shine sanadin samun saukin duk wani yawan fitinansu da,sa ido a kaina,
Sai gashi da yin auren ba,aje ko ina ba zaman yaki dadi a tsakan su ni kuma na samu nawa yancin ta sanadin hakan
Don haka duk halin da bawa ya,samu kanshi da mu tashi muna ta kishi irin na hauka a tsakani gara ki san yadda kika kama kanki ta hanyar hakkuri da dan basarwa har Allah ya kawo adadin abin,

****** ********* ******
Mun wayi gari da labarin haihuwan Zarah wanda kowa a gidan farin ciki yake,
Mama bata tsaya ba ta nufi gidan da yan komatsai irin wanda uwa take kaiwa yarta idan ta haihu,
Kamar su roban wanka na yaro da uwa sabulu wanda akewa hadin kamshi kala kala, da yan sauran tarkace irin na,al,ada,
Zan ita cewa tun bayan dawowana daga gida wanan ne karo na biyu dana fita daga gidan zuwa uguwa,
Na,shirya a cikin yar atamfana zani da riga masu ruwan grey color da farin zane,
Na kawo hijjab dina na dagwara a saman kayan tare da jawo kofan dakina ina kokarin kulle kofan ne Hamza ya shigo gidan,
Ranan yana dakin Sadiya ne don haka ban tsaya ga abinda nakeyi ba sai muryan shi da nakeji daga bayana yana fadin,
Zaki fita ke nan na dan juyo ina cewa eh ina son zuwa kafin rana yai min a hanya don da kafa nake son zuwa,saboda na mike kafana,
Kada ki rufe idon shi a kan kofana danake kokatin kullewa,yace ina son daukan wani abu a dakin,
Hakan yasani bude kofan tare da dan jaye jikina don ya shiga daga ciki,
Bayan shigan shi sai na dan bi bayan shi zuwa cikin dakin da ya shiga din, na samay shi a tsaye yana ce min
Kinyi matukar kyau Humaira cikin nan ya yi maki matukar kyau sosai a jikin ki,
Sai dai kassh ana min rowan na gana da dan tayina saboda wani hujja na likita wanda ba gaskiya bane hakan,
Anya Humaira baki tinanen cewa kina shiga hakkina da yawa a gidan nan,
Mutum da matarshi amma baida daman ya tabata ace mai zai aikata zunubi ne
Cikin natsuwa nace mai wanan ne dama abinda zaka dauka din ko kuwa,
Murmushi yayi tare da kokarin jawoni zuwa jikin shi,
Da sauri na dan gwauce daga rugumar da yai niyar yimin tare da cewa kada ka manta da cewa banice da hakkin kaba yau,
Koma nice din wanan abin bazai yi a tsakanin mu ba don ni lafiyata tafi min komai,
Yar murmushi ce ta subuce mai da sauri ya dan jaye min don bani hanya na fice daga dakin,
Tsaye na samu Sadiya kamar zakanya tana mai kallona cikin nazarin ko da,akwai abinda ya faru a tsakanin mu dashi,
Nakecewa yar wahala sai kitayi don kece da wahala ni wanan bai damayni ba yanzu,
Dakin Umma na nufa don nasallamayta cewa zan tafi a daidai lokacin da lokacin da ya fito da wani leda a hannun shi,
Kamar bai fahinci mai Sadiya take nufi a ranta ba, ya wani sha toka fuskan shi a daure babu annuri,
Ganin ya fita na koma na rufo kofa dakina a cikin zazzakar muryana mai tare da wani sanadarin dake sanya mai sauraron ta rudani,
Saina dawo zan tafi barka a gidan Zarah na ce mata batare dana tsaya jin mai zatace min ba
Sadiya tana jin abinda na fada ta wani dan tabe bakinta tana cewa wanan matsalar ki ce don baki zama kowa agurin su,
Tankar banji taba sai fitan danayi abina sai jin muryan ta nayi tanacewa Hamza dakai nake magana,
Nafita ina murmushi don nasan kaidin kishine kawai don kada mu fita tare dashi agidan tai wanan magana,

Tafiya nake a hankali har nakai gidan su zarah din dake cike da jama,a yan zuwa barka,
Na samu mama hafsi agidan itace mai kula da zarah da yaron ta,
Taimin sannu da zuwa tare da bani gurin zamana zauna alokavin zarah wace tafito daga bayi take cewa ,a,a maraba da matar yayana,
Cikin murnushi nake cewa matar yayan ku tana can gida zaune,
Ni yar uwarkuce don haka ku daina zolayata haka da,wanan sunan,
Dariya zarah dake kaiwa zaune takeyi tace rufa muna asiri da wanan bakar anobar matar
Ni ai Sadiya takai min ko ina agidan nan Aisha wallahi da ace ina da iko da zan fitar da ita aida yanzu zamanta da ta a cikin gidan mu, ya kare,
Ledar dake a hannuna na kayan jariri da zanin daukan yan barka na mika ma mama ina cewa asawa jariri ba yawa
Godiya sukeyi tare da kokarin warware ledan don ganin abinda ke a cikin ledan,
Nakarbi jariri daga hannun mama ina dan murmushi tare da cewa masha Allahu
Allah ya raya muna yasa dadin musulmi ne wanan baby haka maigirma zarah kinyi kokari wallahi,
Murmushi tayi tare dan dan zuba ruwan zafi a cijin wani cup ta kawo kunu mai zafi ta zuba kawai ta dan fara kurbawa a hankali,
Itace ke sha nice daga gefe nake dan rutse idanuwana a hankali don jjin zafin nakeji kamar nice mai shan ruwan,
A take naga ta wani hada gumi a fuskanta zuwa wuya nadan kalleta a cikin murmushi nace sannu,
Itama murmushin ta mayar tare da dan share zufan tana cewa aikema kina saman hanya Aisha,
Gidan an samu karuwa alokaci daya Umma dake ta cewa wai anki a haihu gashi da,Allah zai bayar sai yakawo muna duk a lokaci guda ,
Ikon Allah dama ai gajin hakkuri ne irin namu na dan adam ana sa Allah dole ne bai tashi ba
Yanzu bagashi gurin neman kiba an samo rama ba may auren Sadiya ya kawo wa yaya a rayuwanta banda zubar da mutunci a idon duniya,
Ina dadin ka zauna matar danka tana maka rashin mutinci a bainan jama a harda batin nakasa ta,
Lokacin danake fada mata illar abinda take kokarin jawowa kanta zuwa tayi tafadawa Sa,a suka zo gidan sukai min rashin mutunci shine har yau ba mu gaisawa da Sa,a ko mayawa goma zatayi gidan nan ba ruwana da ita,
Kin san tashin yarinyar nan kin san kuma halin uwar ta amma har ki yarda ki hada zuria da ita don rashi sanin ciwon kai,
Zarah tace ai yanzu yafita a tsakanin su nima kaina saida nai laifi a gurin Umma don nace kada tayi wanan hadin da take sonyi zai iya kawo masu matsalar amintakan su,
Amma Umma ta rufe ido tai min tas akan shi harda fushi tayi dani saida Alhaji yakaini na roketa gafara,
Yanzu gashi za,a hada zuria dasu kinga ai dole ayi hakkuri da zaman ta tunda ina zata,
Zarah ta,amsawa mama dacewa nima zancen da shi yaya Hamza yake min ke nan yace bazai iya rabuwa da mace mai ciki ba haka don shima yana gudun aiwa diyan shi ko kannen shi watarana,
Don na kawar da zancen don sam ban ma son naji zancen Sadiya da Hamza din sai cewa nayi amma a,asibiti kika haihu ko tace dolema Aisha ina zan iya haihuwan wanan yaro agida,
Nan muka nausa a hiran yadda ta sha wuya wurin haihuwa duk inajin tsoron hiran yafiye min jin zancen Sadiya da sukeyi,
Don ni kwata kwata ban son zancen ta a raina saboda irin wanan zancen yana bata min rai sosai,
Don gaskiya kishiya koda wace kuke zaman lafiya ce sa ita dole akwai wani abu a kasan ran abokiyar zaman ta,sai dai mutum yai ta kokarin boyewa don kada kafitar a fili sunan ka yafita,
Don duk wace nata,yafi zafi har ta baiyyana kishin ta a,fili sunan tane yakan yifice a,duniya koda kuwa itace ake cuta sai kiga gaskiyarta ya dushe an bata mata suna da zafin kishi ke gareta,
Allah ubangiji yasa mufi karfin zuciyar mu akan duk kishiyar da zamu zauna da ita aduniyan nan,
Ina gidan zarah har zuwa wani lokaci tare da ita da mama sai yan barka dake zuwa yi mata murnan samun karuwa,
Ina kallon irin yadda kishiyoyinta suke ta faman yin dawainiya da ita a gidan duk da nasan cewa ta kasa tana kasan zukatan su dannewa kawai sukayi,
Zakice ai babu wani zancen kishi a cikin ransu a kanta suna matukar farin ciki ne da haihuwan nata,
Wanda a gaskiya zancen ba haka yake ba don ko wacen su sai da ta nuna bacin ran irin yadda Alhaji Bala ke rawan kafan haihuwan zara a fili,
Amma a fili suna nuna sunfi kowa farin ciki da,wanan haihuwan kishi ke nan na tsanaki sai kin daure zaki iya hadewa,

Na is gida a gajiye saboda tafiyan kafa danayi daga gidan zarah zuwa namu gidan akwai dan tazara amma haka na daure nai wanan tafiyan don na san watsake jikina,
Bayan na dan huta sai na kwabe nafito nafara dan aiyukan dake a gabana,
Umma da tafito waje don tasha iska take tambayana yaya masu jegon su ke nadan tsaya a cikin fara,a nace,
Umma baki ga dan ba gudan babba dashi wallahi zaki ce ba zarah ce ta haifi wanan yaron ba don girma,
Tau ijin tana cin abinci tana kula da kanta nace Umma kin manta cewa mama na can ai mama bata yarda komai daya dace mama tanayi a gurin,
Allah sarki zarah yau tazama uwa itama kamar kowa yau,
Muryan Sadiya ce daga bayan mu take cewa ai dole ta haifi yaro babba tunda mahaifin shi yana kokarin ganin ya bata hakkin ta taci tasha mai kyau yadda ya kamata,,.
Azatona zancen arzikine sai najuya a dan murmushi nake cewa ai abin ke dai badaga nan ba baiwane kawai
Tace ijiki ba mutum ya kwana ya tashi babu wani cimakar kwarai da,zai sa jikin mutum yaginu, da kyau,
Sai anan nafahinci inda zacen ta ya dosa don haka nikan na juya na nufi gurin nawa harkan nabarta nan tana zuba tana cewa,
Irin wanan abinda aka dauko ko haihuwa mutum yayi ai saida gaske zai samu abinda zaici wa cikin shi balle wani dan abin maski da zai dora sama,
Mama tace tau Allah dai ya sauke kowan ku lafiya yan kuda na kwana mu shine fatan mu yanzu,
Umma ta gajar ce zancen Sadiya da fadin haka don tasan inda ta dosa ga maganar ta,
Ga haihuwa anyi sai dai babu abin kashin kuyan a hannu don haka duk sun shiga a cikin wani yanayi na damuwa don rashin sanin taka maimai abin yi,
Barci na nake irin na masu ciki hankali na,a kwancd saidai zuwa dare nakan dan tashi barci yadan gagareni har zuwa asuba sai kuma shedan yadan rudeni na koma da kyat nakan tashi nai sallah kada asuba ta,wuce ni,
A hankali yau ma na bude idanuwa na dake da nauyin barci a cikin su,
Muryan Hanza nake ji daga bayana kamar yana magana da wani, naji yana fadin
O Allah ga bawankanan Allah kaikasan halin danake ciki a wanan rayuwan
Ya Allah kada ka bari muyi kunya akan wanan al,amari Allah kai muna mafita ta hanyar alherin ka,
Shiru naji yayi duk d idanuwa biyu ban nu mashi alamar cewa idanuwa na biyu ba a lokacin,
Zan iya cewa yai barci amma faskiya a zahiri idanuwan shi biyu ne ba barci yakeyi ba,
Don ina jin lokacin da yakai kwance bayan yagama addu,oin shi idanuwan shi suka a kaina gurin da nake kwance yayin da yake karare min kallon cikin mamaki, irin halina don a sanaiyar dayai min ni mutum ce maihakuri da dauri ga kuma uwaba sanin ya kamat,
Amma gaba daya duk na canza mai tinanen shi a lokaci daya na,sake gaba daya duk da dai ba,wani rashin mutunci ko jittuwane babu a tsakanin mi ba,
Amma kuma bai taba tunanen cewa zan uya bijirewa bukatar shi har na tsawon lokaci irin haka ba batare da na tausaya mai ba,
Lalai mata abar su akan kishi don duk danace dokan likita nake bi yasan harda wani dalilina na,daban,
Sai faman juyi yake a saman gado shi daya yana jin kansa tankar wani dan maraya mara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login