Showing 201001 words to 204000 words out of 299981 words

Chapter 68 - Sarautar Mata By Makawa

04 Dec 2025

17702

galihu,
Idanuwan shi suna a kaina gurin da nake kwance a kasa saman ledan dakina daya sha guga sai kyali yakeyi don guga,
Bina da kallo yayi tun daga kafana har zuwa kai tare da sauke wani irin nufashi yana maigirgiza kai a hankali ya furta why Aisha why doing dis to me ?
Mikan da naji yayi da karfi tare da lankwsa hannayen shi saida sukai kara inajin su har inda nake ,
Cikin dakewa nake sauraren shi daga inda nake a kwance duk tausayin shi ya kamani ji nake kamar na tashi nasamay shi narugumi abina
Amma kuma sai na,karasa dauriya da dakewa a,cikin zuciyata batare dana mike na samay shi ba,
Har gari ya karasa waye muna a haka kowa da abinda ke acikin ranshi,

Ganin irin yadda al,amarin sunan zara yake batun bada ruwa a,gari yasani rufe ido batare dana tuna komaiba nafitar da buhu biyu daga cikin abinda ke aje a gurina na nace suyi sha,anin bukin dashi idan an samu sai abiyani,
Ranan nasha godiya a guri Umma fiye da tsanmanina don har dakina take tana min godiya,
Bayan an sayar akadan yi yan abubuwan da suka dace na suna dasu anyi buki lafiya an watse lafiya,
Yanzu kowa ya zaunu a gida don zarah ma tana gida andawo da ita wai shan ruwan zafi,
Duk da mijin baiso ta tafi ko ina ba amma umma ta matsa wai a dawo mata da diyar ta a gaban ta ta duba abinta,
Mama Hafsi ta nuna mata cewa zata iya zuwa safe da yamma ta duba lafiyan ta amma fir Umma taki yarda da,zancen ta,
Hakan yasa kowa gane cewa wani hikima ce ta son yaudaran mijinnata don akama ce mai kawo kawo,
Sam Umma ta manta da,zancen cewa a gidan ta,akwai masu ciki haihuwan fari dake shirin haihuwa, duk da,dai sadiya bana farko bane ta taba haihuwa a baya sai da cikin yakai wata biyar tai barin cikin, sanadiyar faduwar mashin da tayi tasamu miscarriage,
Sai kuma yanzu data samu ciki a gidan Hamza shine karo na biyu dayin cikin ta,
Dawowan Zarah gida ya kara tayar da,wani fitina don sadiya ta nuna ba yarda da irin yadda akewa Zarah tallen miyan ta daban a,matsayin ta na maijego wai tunda mijin ta ke sayo abin miyan wani lokaci,
Ni duk abinda sukeyi ba,bakona bane don haka ban daga kai na kalle su ba,sai dai nai ta abindake a gabana,

****** ********* ******
A cikin dare ina barci na dinga jin hayaniya yana dan tashi a gidan nabude idanuwa na dakyat don barci nake a lokacin mai dadi,
Dana,saurara dakyau sai nake jin muryan su mamane harda muryan mahaifiyar Sadiya a cikin su,
Da kyat na tashi na bude kofana sai nakejin muryoyinsu zancen na kuda naji sunayi,
Ganin na bude kofana shi kuma Hamza a lokacin naga ya shigo gida da saurin shi, yana ce masu ya tafi gurin makwabcin mu don asamu mota amma yace wai motar babu mai acikin ta,
Yanzu yaya za,ayi kenan ga yarinya tana ta,wahala haka tun karfe hudu na yamma bata haihu ba,
Abinda ba,asani ba na juya na koma dakina don nima dai nayi nauyi sosai a lokacin,
Ban kwantaba na zauna a saman kujera na ina iya tsiyakayo maganan su daga inda nake zaune,
Yadda nakejin nishinta har dakina sai tabani tausayi sosai, gani da abubuwan da ya kamata nai mata amma kuma kishiya ce ba halin na taimaka mata,
Nishin da naji yai yawa uwar na mata,fasa wai ta nisa kwarai tasa nafito nace mama ta daina mugun yunkurin nishi don kada ta samu matsala,
Sadiya tanajin muryana ta daga murya tana fadin Aisha don Allah kizo ki taimaka min kada na mutu ba,a,samu motan kaini asibiti ba,
Uwar tace baki da hankaline da zakice kishiya ta karban maki haihuwa,
Daki na koma abina don jin abinda uwarta tace min sai faman fada take mata wai ashe bata da,wayyo,
Sakata nasawa kofana,saidai gaskiya ban samu yin wani barcin kirki ba don tausayin ta, da nake ji,
Barci barawo nasamu ya dan daukeni zuwa asuba naji ana ta buga min kofa da karfi da sauri na budd kofa mahaifiyar sadiya ce da mama suke tsaye a kofana,
Mama take cewa don Allah nazo na duba,Sadiya tana a cikin wani hali,
Na,rasa yadda zan yi do gaskiya nace bazan taba taba don ina gudun abinda ka iya zuwa ya dawo,
Fita nayi zuwa kofan ta,wanda zance na mata yaushe rabon da naje dakin Sadiya koda kuwa kofan tane,
Kayane kamar dakin tsohuwa ko ina sai doyin tsamin dauda da dakin keyi,
Mama da mahaifiyar ta naiwa kwatancen yadda zasu taimaka mata na fake da cewa ni bazan iya ba don bana jin dadi,
Ina daga kofa nake basu directions ba adauki lokaci mai tsawo ba,sai tai wani nishi maikarfi sai ga da yafito,
Ikon Allah muna ta,wahala tun dazun ashe ga abu da saukia gida,
Gaba dayan su bazu kula da cewa yaron baiyi kukaba,sai faman cewa suke namiji ne gashi gudan babba dashi,
Nace mama ku yanke mai cibi don ya samu yadan huta ko,
Saboda yasha wuya kuma gashi baiyi kuka ba nan hankalin su gaba daya yadawo ga zance na rezan ma Sadiya bata dashi sai gurin Zarah aka,samu sabon reza,
Yaro yaki kuka har tsawon wani lokaci nace gaskiya su kaishi asibiti da sauri don a duba lafiyan shi,
Yaron yana hannun Umma, sai numfashi yake sama sama wani iri saboda wahalar da ya sha a ciki,
Ruwan wanka na,dora masu sai mamace tazo ta karbe ni tana cewa jeki huta kinji Aisha kema ai ba lafiyane dake ba,
Tunda,safe suka tafi asibiti sai gasu sundawo suna cewa wai anbasu gado saboda yaron baida lafiya



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,


Gaba daya hankalin kowa,a gidan a tashe yakd saboda wanan haihuwan da akayi,
Sai dai kuma,gashi an samu karuwa,amma kum,yaron baizo da lafiya ba a jikin shi,
Babu wanda ya zauna a gida don hankalin su ya na a gurin yaro mara lafiya, da uwar sa,
Ina zaune a kofan dakina na saman tabarman dana shimfida a kofar dakina don daki a kwai zafi sosai a cikin sa,
Kafafuwana da suka hau suka kumbura sunyi sutum sutum dasu,
Gyara zama nayi cikin kara jingina baya na da bangon da nake zaune a gefen shi,
Tausayin kaina ya kamani don ba bu wanda ya,damu da damuwana agidan kowa hankalin shi na kan haihuwan da akai masu sai farin ciki sukeyi, abinsu,
Ibrahim wanda tun safe ban gan shi ba,a gida ya,shigo da,alama bai kwana a gida ba dawowan shi ke nan a lokacin,
Har zai shiga dakin mahaifiyar su sai kuma yadan dawo baya yana dan kare min kallo ya ke cewa madam yaya akayi ne wai,?
Dan murmushi nayi tare da,gyara,zamana nasan har kullun duk cikin diyan Umma babu mai kaunana yadda Ibrahim yake matukar nuna,mi kullawan akoda yai she,
Cikin murmushi nake cewa sai yanzu aka,dawo kenan yace wallahi kin san aikin mu sai a cikin dare muke tashi mu fara kwaba flower don kada mu makara,
Yana shiga dakin shi sai ga Hamza ya shigo gidan da ganin fuskan shi kasan cewa yana a cikin matukar damuwa
Sannu da zuwa nai mashi tare da dan yunkurin mikewa,zaune da kyau nayi don na fuskan ce shi,.
Tambayan shi nayi cewa yaya jikin yaron sai yake ce min cikin dan canza fuska mai nuna damuwan mutum da cewan da,sauki a takaice,
Murya mai nuna damuwa a fili yadan ce a kasalance magani aka rubuta na,sayo na,samu na,sayo wasu wasu kuma ban samu sayan su ba tukun,
Shiru na dan yi zuwa wani dan lokaci ina zancen zuci don nasan yau duk inda zai shiga neman kudi a garin nan ya shiga don yai fari a gurin Sadiya in ba haka ba su sa kafan wando guda dashi da ita,
A sake na dan dago kaina nake cewa a zubo ma abinci ne kadan ci ko ? na nuna kamar ba abinda ya damay ni a zuciya na hakana,
Idon shibda suka dan kada sukai ja ya dago ya kara kallona yake cewa ashe kin samu girka abincin ne,
A,sake batare da na bashi amsa ba nake cewa na,asibiti ga ya can idan ka tashi sai a kai masu nasu don rana ya soma yi ko,
Na mike da kyat na zubo mai abinci a plate don nasan ba zama zaiyi ba balle na kawo mai a kulu,
Na tafi de bo mai ruwan sha ya kalli abincin ya,wani sauke ajiyan zuciya tare da godiya a ranshi don yasan cewa in badon Allah ya hada shi da nice ba yau da,bai san yadda zai yi ba,
Don inda Sadiya ce yadda bai bata, ko kwandala tayi girki ba,sai dai na,asibitin su mutum don baza tayi ba, wani bacin rai da,ahi kadai yasan dalilin shi yazo mai a rai abinda ya haddasa mai, bacin rai ya dan runtse idanuwan shi a hankali,
Har zuwa lokacin da nakawo mai ruwan idanuwan shi suna a lumshe bai bude su ba sai da yaji motsina ya dan bude lumsassun idanuwan shi da,suka kada sukai jawur,,
Ya sauke su a kaina cikin dan sake ajiyan zuciya, yake cewa wallahi duk abubuwan sun daure min gaba daya duk na zagaye garin nan amma ban samu wanda zai taima min ba da ko kwandala koda da sunan rance ne,
Allah ya kyauta nace tare da mikewa nabar gurin cikin dan tafiyana da nake yi da kyat, irin ta masu tsohon ciki,
Bin bayana yayi da kallon yadda yaga ina tafiya da kyat kuma a,hakan nayi muna girkin gida,
Ya shiga asibiti da kulla Sadiya tana hango shi ta,fara cewa ji shi dan Allah yanzu haka matar shi ce tai girkin don rufin asiri ya wani dauko ya nufo mutane dashi,
Tun dazun ance a,kawo magani amma,shiru kake ji ba,wani motsi tun safe sai yanzu ya,shigo wa mutane, da gadara aljihu babu ko kwabo,
Wata matar makwabatar su da tazo duba,su take cewa haba Sadiya mijinki ne fa na,sunna kikewa wanan zari haka gaskiya hakan baiyi ba,
Daidai lokacin ya iso gare su yana gaida su ya aje kayan abinci daga gefen su kadan
Gurin da yaron yake kwance yana mayar da numfashi sama sama ya,dan tsaya har tsowon wani lokaci yana kallon yaron , cikin tausaya mashi,
Muryan Sadiya ce tas shi juyowa tana fadin har yanzu ba,a,sayo maganin bane don nurse din ta,zo dazun tana tambayan mu ko an sayo,
Ledan da ya,aje gefe tare da,abinci ya,dauko yake cewa ga,wanda aka,samu,
Ke nan ba,a samu ba gaba daya ke nan gaakiya ni wanan al,amarin ya fa fara isata ace mutum kamar shi yafi kowa,shiga talauci komai mutim bai iya kata bus akan shi,
Tunda,abin ya,ishe ki ai sai kiyi maganin abi ko yafada cikin dan juyawa a,fusace ya fita daga dakin,
Yana fita daga,dakin ta jawo kulan abincin da yashigo dashi tana cewa bari naga yar sherin may ta,dafa muna ne wai,
Tana bude kulan tayi tozali da tuwon shimkafa da miyan taushe sai kifin da nai amfani da su a ciki,
Aka zuba mata tashiga ci tana ta,surutun tsiya kamar ba dantane a cikin wani hali ba na rashin lafiya irin haka,

Ban samu shiga gurin su ba,sai da akai sallah azahar na,shirya na tafi dubo su a lokaci Umma ta,dawo gida ita da zarah,
Tun daga nesa nake jiyo muryoyin su suna hira cikin dariya ita da matan uguwar su da,sukazo duban ta,
Tana hagone ta wani juyawa ta bada baya yayin da na karaso nai ma matan da ke zaune ina,wuni,
Sadiya bata juyo inda nake ba nake tambayan matan da na samu a dakin nake ya jikin yaron suka amsa min da,da sauki,
Idanuwana akan yaron ina kallon yadda yake mayar da numfashi da,sauri da,sauri,
Tausayin yaron ya kamani irin yadda naga yanayin shi nasan yaron yana jin jiki akwai abinda ke damun shi,
Tsayin lokaci idanuwa akan yaro ban san lokacin da tausayi yasa cewa ya kuwa samu yin kukan,
Har yanzu baiyi ba amma insha Allahu zai yi ai, tunda lafiya tana shigan shi a hankali muryan mama,Sa,a mahaifiyar Sadiya ke fadin haka,
Tsayin lokaci suna ta hiran su Sadiya tankar bata,san da tsayina a gurin ba,
Ina tsaye ina kallon wasu sun shigo ambasu yaron su dauka ni kuwa an hana min daukan shi don ina kishiya yar a,dawa,
Inan tsaye dai ba,a bani ko gurin zama ba, Sai ga,wata nurse tazo tana fadin don Allah su rage yawa a,dakin don sun cika mutane da surutu , da yawa,
Zan juya nima na fita Hamza ya shigo yana cewa ashe kin samu fitowa nazaci bazaki iya zuwa ba ai yadda na ganki dazun ai, yana kokarin mika ledan da ya,shigo dashi a hannun shi,
Murmushi nayi nake cewa na lalabo nazo na duba su na koma,ai ba,dadewa zanyi ba,
Wanan ai basu cika ba abinda aka ce guda shiddane zaka kawo kwali biyu kawai,
Su na samu kuma bazanyi sata ba don kiji dadi ko ?
Nurse ki duba min wanan maganin da ya,sayo don ba duka ya kawo ba sai nurse din takaraso tana dan duba maganin tace gaskiya sai ka,karo sauran zaifi don wanan kawai ai bazaiyi amfani ba,
Caraf nace ai duk antibiotics ne zasu iya amfana da amfara,shan su kafin sauran su zo don su fara yi mai aiki, sai na,fadi sauran maganin da,auka rage bai sayo ba,
Daga haka nasa kai zuwa waje nabarsu nan ita,da mahaifiyarta dashi da nurse din suna fafatawa inajin yana fadin shi duk ya buga bai samu kudi ba yaya zaiyi,
Ya,fitowa na bude post dina na ciro kudin da ke aciki wanda,suke nan min a,hannuna,danake dan amfani dasu na mika mai,
Yakarba tare da dan juyawa yana mamaki a lokacin ne wasu mata masu shiga gurin ta,suka,biyo zasu shiga dakin,
Ban so su gan mu ba don nasan zasu iya fada mata tasa wani fitina kuma ba abu mai wuya bane a gurin Sadiya,
Nurse din take tambayan Sadiya wanan da tafita wace ce ita Caraf Sadiya tace kishiyata ce ,
Tace amma dai tayi karatu ko don nnaga ta dan san aikinta gaakiya saboda itace ma kya gwada min inda,zan sa allura na,samu jijiya da sauri,
Karatun duba gari tayi a nan makarantar hanyar sokoto takare shine take yar burgar aiki dashi,
Nurse tace to ai tafi wanda yake zaune dip kuma wani hanyane na,samun kudi a gare ta,
Matan da suka shigo suka katse hiran su da nurse din matan ke cewa ai muga kishiyar ki a kofa tana ba mijin ki kudi,
Haba nan ta hau jinini saida uwarta ta kwaba ta tana cewa kada ki bari mutane su fahince ki dan Allah muji da zancen yaron da baida lafiya kawai,

****** ********* ******
Haka akaita faman kashin kudin asibiti yaron kwana biyu da haihuwa amma baiyi kuka ba,sai ma,shiga cikin wani irin yanayi da yayi
Wanda duk yaga yaron sai hankalin shi ya tashi don yana jin jiki,
Doctor yazo round duba marasa lafiya bayan ya,dan yi yan rubuce rubuce ya ke cewa yaron ku har yanzu bai yi kuka ba,
It's means akwai matsala a tare da shi ke nan duk yadda akayi akwai tashin hankali da cikin shi wanda yai ta hadiya bacin rai tun a cikin ciki,
Yana da wuya,yaron yayi rai yafadi kai tsaye cikin nuna tausayawa yake cewa don haka,sai dai muyi addu,a kawai,
Sai a wanan lokacin hankalin Sadiya ya daga jin abinda doctor ya fada masu akan yaron
Kuka Sadiya tafara yi sai kawar uwar ta ke cewa kinga ai irin abin da ake gudu idan kin fara abu akace ki bari baki bari kin fara fitina,sai rayuka sun kaiga baci,
Yanzu kinji abinda likita ce yawan bacin rai da ciki ko fitina ya kawo wa yaron dake cikin ciki hawanjini ko wani ciwo na,dabam,
Anfi son in mutum yana abu akace mai ya daina yayi hakkuri to kayi kabar wa Allah,
Amma ke idan kin fara fitina kin fara ke nan sai kowa ya gama ganin ki ana nunaki don iya masifa,
May ke cikin fitina ga diya mace wacce ke karkashin namiji sai yadda akayi da ita,
Yanzu ba gashi ba ke aka bari da tashin hankali don kece ke kwana da,yaron a,wahalce,
Kuka Sadiya takeyi a cikin tashin hankali don sai lokacin take jin wani iri a,ran ta jin cewa yaron za a iya rasa shi anytime, idan ba ayi da gaske ba,,
A lokacin surutai barkatai suka fara yaduwa wasu suce ai anyiwa yaron sammu ne wasu suce manya takama,shi, wasu suce ai bakine yai mai yawa wasu kuma,suce kawai ciwo ne daga Allah,
Sai a lokacin na fahinci dalilin hana min daukan yaron da akayi watau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login