Sarautar Mata

Chapter 69 of 94

agaji cikin su harda Hamza,
Innalillahi yake furtawa yana zuwa ja daya yai muna,saida muka watse gaba dayan mu har,su Asma,u dake kokarin raba tsakanin mu,
Sadiya har dakin ta kika biyo ta da masifa haka idon ta waje tasha wahalan shakan da nai mata,
Tace nabita may zakai min nan yafara kai mata duka sai da aka jashi yace wallahi yau sai tabar min gida,
Don ni wanan abin ya isheni wallahi, wallahi ko wa yai mata tsaye sai Sadiya tabar gidan nan,
Tace bazan bari ba indon kan wanan figagar matar taka ce sai dai ka kashe ni macuta kawai azzalumai wallahi sai ra fito da abinda ka,sayo mata jiya ,
Nace baza a fitar ba idan kin isa ki shigo ki dauka ki gani wallahi yau sai na gwada maki figaga nake a gidan nan,
Ke wallahi nagaji nagaji Sadiya shiru shiru wallahi ba tsoro bane,
Ai wallahi yau sai kin fane kin mare ni don sai na rama kowa yai maki tsaye saina rama marina a gidan nan,
Gida ya cika yacika da makwabata masu jira suji sai cewa mutane keyi yau abin ya ishi Aisha ne tunda kukaji tai magana dama mai hakkuri bai iya fada ba ai,
Asmau tace wallahi har daki tabita shine ya batawa Aisha din rai, daga gurin da Umma dake tsaye tace ke Asmau waya tambaye ki,
Nan mutane suka juya kan Umma wasu nacewa ai gaskiya ne idan bata bitaba may yakawo ta kofanta fada ,
Shigiya na tafi kofan ta din don wanan shigiyar diyar taki da kika haifa kowa bai so a gidan shine har kikewa mutane daukan kai wake kin haihu,
Wake son ta in bashi ba,da yazama, wagili bai san ciwon kan shi ba,diya haka,da,fari kamar zabaya,
Nace, koma,wace irice na godewa Allah na daya bani ita Allah yasa mata,albarka,
Ke tafi can shegiya yar iska wace saida ta tafi garin su gurin yawon iskan ci tadawo da ciki, anzo an nade shi ance nashine,
Kai matar nan ki rage shiri watan tafa uku gida tadawo da,wata daya da rabi ta haihu zaki ce mata haka wallahi kiji tsoron Allah kada Allah ya kamaki da laifin sheri,
Wata tsohuwa cikin makwabtan mu da suka shigo suke cewa haka sai gurin yadauka da cewa kai haba dai wanan kan kin yi karya wallahi don Aisha tun tashinta ba,a santa da,abin assha,ba,garin nan kuma da cikin ta tabar gidan nan kowa yasani,sai daiku,
Ko zaku shigan matane tajuya gurin matan cikin fitar da idanuwan ta kamar zata hausu da duka,
Sai dayan matar tace mi ina zamu shigar mata itama ai ta isheki don kin sha mari ai dama nadan iska ke nan ai sai baki babu karfi,

Hamza ya dawo yace wallahi sai tabar gidan kofan dakinta ya nufa da kwado a hannun shi ya kulle dakin,
Sai kuma ta juya a kanshi zai kara dukanta aka tare shi nan mutane suka in mata saida Asmau ta bata hijjab suka fitar da ita daga gida sai gidan su,
Kowa na tir da,Allah waddai akan ta muna jin muryan ta har waje tana,ashar,
A raina nace tir dake Sadiya ashe haka masifaffen mutum yake aduniya kai jama,a halin sadiya baiyi ba,wallahi,
Sai daga baya zancen Ummina ya fado min a,rai da tace fadan kishiya dama sheri ne da kake a cikin sa abinda ake son fada maka sai a fade shi acikin fadan kishi,
In badon Allah ya wankeni ba da yau ta zarga min masifan daba zan iya wanke kaina akan shi ba wai Jidda ba yar hamza bace yarinyar da take kamar shi yai kaki fari ne kawai ta kwaso nawa,
Tsohuwar nan tace amma dai gaskiya wanan yarinyar ba matar zama bace wanan ai masifa ce kuka daukowa kan ku agida ni tun da naji za ai wanan hadin nace may yakai Rabi yain wanan irin gagancin wa dan ta,
Dama nasan karshen amintakan ku ne yazo yarinyar da tashi cikin shiya kamar tambadadda shine har zakiyi sha,awan hada zuria da ita,
Tun shigowan wanan yarinyar cikin gidan nan babu zaman lafiya dakowa ko ke bata barki ba balle wanda take zaman shi kai may ake da irin wanan mugun auren haka,
Umma dai tana shiru daga inda take a zaune sai dayar matar tace yanzu aikin ji sheri inkina kama jiki ki rike sarakuwar ki da mutunci ki rike don kinga har tana batun sheganta maki jikan ki a bainan jamma,a ,
Badon mun san komai ba,ai sai mu yarda da sherinta, cikin da aka tafi dashi kusan wata bakwai shine take son zarga sheri irin na kishiya, don bakin ciki da takaici,
Dakina suka shigo lokacin ina daura zani don nacire kayan da mukai fada dashi dayar matar tace min maza ki fitar da,wanan kayan da kika cire a gidan nan don kada tsiya ya hau mijin ku,
Inaji ina gani taba wani yaro tace jeka konashi sai ya zama toka,
Kuma daga yau kada ki kara bari ku hada jiki da ita don ba karamin tsiya fadan kishiyoyi yake kawowa ba a gida dama ku kanku,
Bamu sanki da wanan hali ba Aisha tun tashinki a uguwar nan babu mai cewa ga abokin fada ki,
Don haka mun san kina da gaskiya amma kiyi hakkuri kibar biye mata kikyale ta da halinta
Dole ne koma,waye aka bishi har daki ko gidan shi ya ji zafi, a ran shi don hakan ba karamin raini bane,
Mama hafsi tana uguwa aka fada mata tadawo rai bace nan itama tashiga na ta fadan cikin bacin rai,

Ummina ranan da kanta tashigo gurina taimin fada har saida nai kuka ta kara jamin kunne
Akan cewa na fita harkan Sadiya dama namiji yana auro mace ba wai sai dole hali yazo guda ba ,
Koshi daya dauko ta wani dadi yaji gareta abu kullun masifa ba wani jin dadin zama kawai hakkuri yakeyi,
Ni fa ban son ace saboda ke tabar gidan nan gara nasu ya hadasu can tsakanin su da ace don, kuyi fada da itane har ya ce tabar mai gida,
Nace cikin share hawaye insha Allahu Ummi bazan kara yin haka ba yauma dai shedan ne ya zugani har nakai ga tanka mata
Ummi tace su ai anfada muna duk yadda kukayi su yaya sunce bazasu zo ba don in sunzo ba a mai kyau dasu,
Ni wallahi Aisha wanan auren yanzu yakai min ko ina,wallahi badon mijin ki yai min komai ba,sai don kawai irin rayuwan da kika tsuci kanki a ciki da kurciyar ki,
Gashi da andayi wani fitina sai munji shi an kafa yi min gori ke nan a gida har sai nagaji na tanka na basu amsa wai dawani mutum zaijine don Allah,
Yaya cewa take in dama anyi ne don taji kunya to irin abinda tagani nan ai taki yarda Kubura tashigo,
Don ai mata bakin ciki aka dauke ki aka bayar wai don kwadai,
Ni may hamza ya taba bani na kwadai da har zai tsone min ido na,daukeki na bayar,
In ma cin moriya ne ai sune sukaci moriyan shi a gidan don a lokaci babu abinda bai masu ,
Ummiinsha Allahu baxan kara yarda ajini da ita ba wanan din ma kaddarace kawai ya kawoshi,

Da yamma na,sa girki ranan nice zan yi girki don nayi arbain saboda haka ban tsaya jiran komai ba na dora girki,
Ibrahim ne ya,sayo muna kayan cefane ranan yace nai muna amfani dashi,
Kafin wani lokaci har na gama komai na,gyara kuma ko ina dazaran mutum zai shigo zaiji kamshin turaren wuta ko ina a gidan,
Jidda tana gurin Mama tun da tai mata wanka ta goyata a bayan ta hakanen yabani daman samu na aiwatar da,aiyukana,
Ana maggariba aka dawo da,Sadiya,sai dai Hamza din bai gida a lokacin sai suka koma zuwa tara na,dare ya,shigo gida da leda guda biyu a hannun shi dakin Umma ya kai guda dayan kuma ya,shigo dashi gurin mu,
Yakecewa yatafi wani kauye ne sayan wake don yana,son ya koma ya kaiwa mutumin dake son waken,
Yought, ne mai sanyi da naman kaza gassassa acikin leda yazo dashi sai laccacera,gora, shima mai sanyi,
Ruwan wanka nakai mashi kafin yafito daga wanka na dauko kullin kuka da madara na juye su a cup na zuba dan ruwa kadan na juya ban bari ya jika dayawa ba na,shaye da,sauri,
Mama Rahana ce tace nai hakan kafin na kwanta yau din tace kuka da madara magani yake sosai a jikin mace kuma yana maganin Ulcer idan kana dashi sai angwada za,a gane amfanin shi yar uwa,
Sallaman masu dawo da Sadiya ne mukaji again sunyi dai dai da ya fito daga bayin sun gaisa dashi suke bashi hakkuri anan inda yake tsaye yake cewa wallahi nayi rantsuea yau bata kwana a gidan nan don haka takoma sai ta kwana biyu a gida tukun,
Daga haka ya shige daki yabar su a gurin suns kokarin bashi hakkuri,
Ina jin matar nacewa ai kin faninidan zama gidan yana da dadi sai ki koma ki zauna aiga gidan nan gaki,
Kin samu Allah ya baki gurin zama amma fitinar ki yaki bari ki zauna lafiya dakowa ke bakibar mijinki baki bar mutanen gida ba da wani zaiji yau gashi kin kai ga yadda kikeso in kin fara abu bakijin bari,
Abinda yazo dashi na gabatar mai da shi a gaban shi tare da,abincin shi yadago kai yana ce min bazaki ci bane ke nake cewa na koshi,,
Don may bazakici ba nace don ina gudun inci yazama min abin fitina da matar ka,
Hammm kawai yace tare da dan furza iska daga bakin shi nace yau ace wullakancin Sadiya har yakai ta biyoni har daki da masifa wai don ka,sayo min abu,
Tunda bata son gani na da kai ka,sakeni mana ku zauna da matar ka lafiya tunda nice dai ba,a kaunan gani agidan,
Ke da bakinki Aisha kike cewa wai na,sake ki na fada maki babu zancen saki a tsakani dake har abada don ni wallahi baki min komai ba,
Ban saurari bayanin shiba na fashe da kuka ina cewa
Sau nawa kana,sayowa Sadiya abu agidan nan ina gani amma banyi magana ba sai ni da ta raina,zata zo hardakina don wullakanci,
Amma dai ai kinga na,dauki mataki akan hakan ko don nasan idan na kyale ta yadda kullun ake cewa nayi hakkuri abin wata rana zafi hakan ne,
Yanzu don Allah ace har da yarinyar da bata ko san tana duniya ba za,a yiwa kage don sheri,
Ai ba ita taiwa bani taimawa don diya tace kuma,wallahi bazan kyaleta ta ba akan zancen nan sai mun zauna da iyayyen ta
Da yaga ban saurare shi ba,sai kuka nake irin mai tsuma zuciya yana ta cin abincin shi hankali a kwance,
Sai da yagama sai ya shiga rarashina yana cewa ban son ace a kanki ne mukai fada da sadiya a gidan nan har na saketa Aisha,
Nafi son ace koma may zai faru ya faru a tsakanin ni da ita don wallahi Sadiya ta kai min ko ina a halin yanzu sai dai duk abinda Umma zatace tace amma ban iya zama da wanan yar cin mutunci,
Amma may zai saki ce wai na,sakeki akan wata,Sadiya can ni in baki sani ba,wallahi yau ki sani nafi kowa farin ciki da irin yadda akika nuna wa Umma da sauran yan uwa na Sadiya bata a gaban ki,
Kuma duk abinda take maki baki canza mu,amulan ki da kowa ba a gidan nan,
Abokaina awaje wallahi kullun yabon ki sukeyi akan hakkurin ki,
Akwai abinda yafi zafi da ciwo ace mahaifiyar ka bata damu da yar da aka haifa maba ta fari a gida,
Kawai ki barni akwai abin da nake jira dan lokaci kadan zako gani,
Na dago jajjayen idanuwa na kalle shi nace ni bance karabu da matar ka ba kawai dai kai warning din ta a zauna lafiya,
Da haka har ya,shawo kaina ranan mukai mu,amula irin na miji da mata sai fama samin albarka yakeyi don yace wai gaba daya yaji duk na canza mashi,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEEENABUIDDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON CIN AMANA NE HAKAN,,,,



Tafiyan Sadiya gida ya sa gidan mu ya koma shiru don ba kaji yawan sautin kidan da takan kur a MP dakin ta ko waya,
Ance mutum ko ya yake rahamace ta wani hanyan yau na fahinci hakan,
Don tafiya ya sa gidan mu ya koma tsit lokaci lokaci nakan ji yan gidan na zagin ta suna Allah yasa kada ta,dawo,
Har Umma takance wallahi dai badon dubaiyya ba da ba,abinda zai sa nabar wannan yarinyar ta dawo gidan nan wallahi,
Amma a gana zakaji Umma tana fadin yaron nan yai kokarin zuwa ya dawo da matar shi dakin ta tun duniya basu zageni ba,
Maimakon na daure fuskana yadda Umma take son gani sai nakan ce Sadiya ai tabawa kowa kewa a gidan nan don shi mutum rana gare shi,
A da can baya takance min sai Hamza ya kara aure don bazata yarda dan ta ya zauna da mace daya ba kamar laya agida,
Don ita tafi don taga gida ya cika da sarakai da kuma jikokin ta ta ko ina ta duba,
Idan Umma tafara yin wanan kalaman hankalina yakan yi matukar tashine wani lokaci har nakan shige daki nayi kuka,
Amma yanzu da na,zauna da kishiyar kuma masifaffa sai abin ya fice min akai nima na gane wasu abubuwa a cikin zaman duniya har ma da zama da Umma,
Tsayin Sati biyu ke nan ana ta kaikawo a tsakanin gidan su Sadiya da gidan Umma cewa a yi hakkuri Sadiya ta dawo dakin ta, hakanan,
Sun hana kowa sakat sai mutane suke turo wai aba Umma da Hamza din hakkuri,
Hakan yana nuna cewa tayi taushi dayawa yanzu don taga abinda bata taba zato ba,
Saboda bata taba tsanmanin zai iya rabuwa da ita ba kamar yadda kullun yake fadi,
Sai gashi yau kusan Satin ta biyu ke nan, zaune a gida tare da mahaifiyan ta da kannen ta,
Sai dai, har yanzu a ranta tasha alwashin cewa duk randa ta dawo gidan sai Aisha ta dan,dana kudan ta,,
Don ba karamin shiri sukeyi ba can acewan su wai zuwan da nayi garin mu naje nai mugun abu na birkita kan Hamza baki daya,
Yanzu baijin ko kallon kowa da gashi saini abinda naga dama naka aikatawa a gidan ba wanda ya isa ya hanani, duk nai asiri na shanye mutanen gidan gaba daya,
Tun sunayi a can har takai sun idar da,sakon zancen a gurin Umma aiko kamar jira takeyi sai ko ta hau ta zauna wai asiri na bankadowa hamza a garin shine yasa bai zaman lafiya da Sadiya,
Ya dawo daga kurmi inda yake kai sanaan shi, Umma ta tare shi da zancen cewa ya dawo da Sadiya hakana dakin shi,
Sai yake cewa Umma ko Sadiya zata dawo dakin ta ba yanzu ba don yanzu wallahi kinga hankalina yafi kwantawa sosai,
Don ko tafiya nayi banda wani farga ba akan komai hankalina akwance don nasan banu wani fitina a gida,
Umma tace ai dama hakana zakace tunda ai maka agumo kasha ka taune ka hade,
Bai fahinci may Umma take nufi da zancen ta ba sai yake cewa agumo kuma namay fa wayai min,
Tace yar lelen ka mana da,baka son ai zancen ta agidan nan Aisha ni dama wanan yarinyar tun farko ban yarda da ita ba,wallahi don nasan cewa duk irin sherin uwayen ta sai tafisu iya,
Dubi gidan malam mudi uwar ta, sai kaga kamar itace ake cuta nan kuwa itace ke cutan sauran,
Umma ina kuma wanan zancen yafito haka abakin ki babu ko dadin ji Aisha ce kuma zatai min wani asiri can,
Kai may kasani dama banda hauka ga abu afilin Allah ai ni ban damu da yarda ka ba tunda dama ba yardan zakayi ba,
Ina dai maka gargadi da kakausar murya kayi mazaka dawo da,Sadiya dakin ta zaman gidan ya isa hakana,
Idan kuma kaki wallahi za,ajimu a gidan nan da ksi don zan dauki mataki ta inda bakai tsanmani ba,
Cikin mamaki Hamza yace yanzu Umma akan nadawo da Sadiya har kike min wanan kalamin, ?
Sadiya fa dakika sani ce ba wata ba agidan nan tace eh ita din kuwa,
An susuta ka duk kawani birkice wa mutane, a lokaci guda akan wanan mai fari kamar zabaya din,
Wallahi Umma ina mamaki don ni har yanzu nakasa fahintar abinda Aisha take maki a gidan nan ,
Ai bazaka fahinta ba tunda ka makance a kanta sai kace wata yar gwal can,
Umma nifa sani da Aisha a gidan nan ban taba gani kojin cewa tai maki wani abin assha ba,
Mutane da yawa suna magana acikin abokaina cewa nai sa,ar mata don suna min korafin yadda matsaloli yake tasowa a tsakanin, gidajen su,
Musan man irin rikicin da ake samu tsakanin matan su da iyayyen su a lokacin ni nakan yi mamakin yadda matarka zata ta wa mahaifiyar ka,rashin mutunci,
Ashe nima hakan zai faru a kaina sai gashi shigowan Sadiya gidan nan duk abinda suke fadi akan iyalinsu nata yashanye nasu,
Koma dai may ye kadawo da ita dakin ta don itama matarka ce tana da hakki a kan ka ta karashe maganar gami da cewa nadai fada maka ranka zai baci idan kaki abinda na fada ma,
Maganan Umma bai sa shi dawo da,Sadiya ba a,wanan lokacin, sai da ta,kara kusan wasu sati biyun yai tafiya sau biyu a lokacin, ya dawo,

****** ********* ******
Ana gobe Sadiya zata dawo gidan ya ke ce gobe wanan zata dawo nake gani,
Kamar ban san wa yake nufi ba sai nake cewa wake nan fa,?
Yace Sadiya nake nufi nace Allah ya kai mu kawai a takaice,
Sai dai ina son idan ta,dawo kada ki biye mata kuna fitina duk da dai nasan cewa yanzu tashiga hankalin ta ai dan zaman da tayi a gida,
Sai kuma zancen gwagona ban son kina yawan wanan kunyan dakike yi a kan ta ya kamata ki saka

Download complete TXT · Novel page