Sarautar Mata

Chapter 70 of 94

ido akan ta ga kowa a gidan nan banda mama,
Maganan da ya,daure min kai ke nan don ya tafi ya barni da mamaki da tunane akan zancen,
Ke nan har Umma yake nufi na,sa ido akan ta kan jikanta jinin ta lalai akwai wani abu a kasa,
Hmmm ikon Allah wai Umma da kanta take zuba,ruwa a randan ruwan Sadiya ta share mata kofa da kayan ta aka,wanke,
Ni ko ajikina don duk da raina ya,baci amma ko a jiki ban nuna nawani damu ba don nasan muje zuwa mai hali baya barin halin sa,
Ta dawo da wani ladabi da wani dan yin wanka da gaye ni dama wanan bawai sai ranan da nake da girki ba nake abina kullun dagani har diyata tsab zaka samay mu a gidan,
Ba wani shiri har yanzu a tsakanin mu don kishiyace balle dani ta dawo a ranta sosai,
In har ina da matsala a zamana gidan yanzu to tsakani na da Umma ce da ta sakani a gaba da fada kamar karamar yarinya,
Kiri kiri take fitowa fili ta nuna bata so na ko kadan kuma Jidda tankar ba jikan ta ba,
Sai yarinyar taita kuka Umma naji ko Sadiya babu mai karban min ita idan ina aiki ga Jidda da,yawan kuka,
Umma kance wai yawan tsegumin uwarta ne duk tabiyo yarinya kamar gyare a guri kuwa,
Sai in mama Hafsi tana gida ne nakan dan samu sauki a gurinta ta karban min ita nai aiyukana hankali kwance,
Sunyi ta kokarin cusawa Hamza ra,ayi musgunawa a kaina amma sam bai taba dauka ba,,
An dan samu saukin fitina yanzu saboda irin sharuddan da Hamza din ya kidanya mata kafin ya,yarda ta dawo gidan,
Dole badon Allah ba ta sauya halin ta zuwa na zaman lumana da kowa har kusan wata,daya,ba wanda yaji muryan ta da kowa a gidan,
Wata rana bayan ya,dawo daga tafiyan shi da kwana biyu nice da girki na idar nai mashi komai yadda na,saba ya shigo don cin abinci yake ce min A
Aisha ya kamata na fara rage maki kudin ki tunda yanzu ina dan samun riba sosai a kai,
Nace haba dai yaya idan ka bani su yanzu may zanyi dasu tunda ba,wani sana,a nake mai kwari ba duk rushewa kudin zasuyi,
Kabarsu kawai a gurin ka kana juyawa zaifi na karbe su su lalace, a hannu ni ban sai komai ba kai baka more ba,
Nikan ai Alhamdullahi na more masu sosai wallahi don dasu na samu nawa, nace to Allah ya kara masu albarka yace amin uwar gidan Hamza
Dariya kalman ta bani wai uwargidan Hamza nace kalman taimin girma yar karama dani
Yace to Allah ya baki ko zaki ki karbane yanzu wata ta karbe ke sai ki koma matar Hamza ko don dai kuma ban yarda ace amaryan Hamza,
Abinda yasa mu dariya ke nan har akejin sautin muryan mu daga wajen tsakar gida,
Wanan abu ashe ya batawa Sadiya da Ummu dake waje zaune saman tabarma daya rai suka daga ido suka kalli junan su,
Umma tace ana can ana mashi karuwanci shiko sai kwasan dariya yakeyi yaga guri,
Sadiya ta,wani yamutse fuska tana cewa ai wanan yarinyar Umma ta iya makirci kamar karuwa,
Ni maganin su zanyi dukkan su don ban dukan shashanci a mayar min da yaro kamar rakumi da,akala,
Sadiya,ta,cije leben ta cikin jin zafi da kunan rai don ita in akwai abinta taki jini aduniya,bayan mutuwan to Aisha ce,
Daidai lokacin Hamza yafito dakina da murmushi a fuskan shi yana kokarin sa takalman shi dake kofan daki,
Wani wawan harara gaba daya,suka bishi dashi alokacin nima nafito da kayan da yaci abinci don a dauraye,
Cikin tsigar son fitina Sadiya tace aikin banza wai cusa kai inda ba,a kaunan ka,
Ban bi ta nasu ba nabi bayan shi ina cewa, kada ka manta da zancen sayen permpers din Jidda fa yaya,
Yace ai saboda shima zan fita yanzu don kada na manta ban sayo mata ba har dare yayi,
Ina wuta su sakani a lokacin kafin nagama wanke wanke ina jin dan kuskus din su koda zan shiga daki har su bar gurin kowa ya shige dakin shi,
Nace a raina Umma kan anyi girman atta wallahi da matar danki kuma kike gulman kishiya Allah ya kyauta,
Washegari da safe ya shiga dakin don ya gayar da Umma,sai take cewa babana yanzu dai naga kamar gaba daya baka fafin kan ka a gurin Aisha sai abinda tace,
Dan abinda zata,sayawa yarta don amfanin kanta shine sai kai za,a matsawa kasayo ita may ye amfanin sana,an nata datakeyi kullun a gidan nan,
Cikin mamaki yadago kai ya kallo Uwar yace yanzu Umma kuma banibda halin da zan saiwa "ya ta abu sai najira uwarta ta saya mata,
Ai na fahinci Aisha da "yarta kake wa nema duniyan nan don sune kawai a gaban ka bayan su baka damu da damuwar kowa ba,
Hmmm Umma ke nan yanzu abin dari da hamsi dana,sayowa Jidda shine kuma abin magana,
Hakkin waye sayan kanyan yarinyar banawa ba ko sai na barta Allah ya kamani da,alhakin su a kaina,
Aisha abinta bai rufe mata ido ba idan ma ban sayo ba nasan zata sayewa kanta,
Jekaita masu facali da kudin idan sun kare ai sai mu zauna mu zurawa kofa ido gaba,dayan mu,
Subbahanallahi Umma mai yai zafi haka har da zancen karewan kudi akan abin naira dari da hamsi,
Asalima fa kudin yariyar na na,gado na karba nake juyawa a hannuna ba,wanda yaji kuma kin sani amma baki magana ba a hakan sai don nai wa Gwagona lalura dashi don ta fito daga tsatsan Aisha zai zama abin magana,
Kai kada ka,fada min maganan banza don kaga wuyanka yai kauri ya isa yanka wallahi yanzu zan bata maka rai a gidan nan,
Allah ya huci zuciyar ki Umma amma gaskiya kuma bazan yarda hakkin yarinya ya hau kaina ba,
Idan kudin zai zama na gori ne ai sai ka mayar mata da abinta bashi ke nan ba,
Bai ce mata uffan ba sai dai ya mike cike da mamakin Umma a ranshi yafito ran shi bace daga dakin,
Hamza idan kafita ka,sayo min sabulun wanki da omo don zanyi wanki ne,
Ai ba ke ce ke sani saye ba idan na,tashi kuma ma yau kwana nawa da na,sayo maku sabulu ke ina naki suke,
Ta amsa a yatsune da cewa nayi wanki dashi mana ya kare inji Sadiya dake tsaye daga kofan ta cikin murde fuska
Dama halinta ne duk ranan da yake dakina fuskan ta babu annuri ko kadan kamar zatayi ihu,
Yace wanan ba gaskiya bane don kafin nai tafiya na,sayo su agidan nan,
Ai kaji irin ta yanzu ka sayo mata abu ka tsaya kana mata tambayoyi kamar tsohon dan sanda,
Amma da,wanine yace ka,sayo mai jikin ka har rawa yakeyi gurin sauri kada rai ya baci,
Daga inda nake ina jin su murmushi kawai nayi don nasan inda zancen su ya nufa,
Nace Allah gani gare ka kai min tsari acikin wanan mutanen daka hadani zama dasu,
Fita yayi batare da ya tsaya jin kalaman Umma ba don suna mashi zafi a rai sosai,
Har zuwa yamma bai dawo gidan ba sai bayan la,asar lis yashigo da alama ma daga kauye yake gurin sana,anshi,
Idan kagan shi bakacewa ma ya taba bako ko yasan biro don yai futu futu dashi already dama ruwan wankan shi yana saman murhu ina jiran yadawo yai wanka,
Da,sallaman shi ya shigo a lokacin duk kowa yana waje har da Umma da mama da ta dawo daga gurin neman kudin ta, ta baza kayan da ta sayo tana daurayewa, na gwanjo duk ta sayo sai ta zabawa Jidda masu kyau tace na saka mata,
Yana gaisawa da iyayyen nashi yake wasa da Jidda dake hannun mama,daga gefe daya,
Hamza ina Sabulun da nace ka sayo man din tun da safe nake jira ka kawo min,
Ban sayo ba yace mata a takaice,
Oho don ni ba mowar ka bace yasa baka,sayo min ba da,watace da yanzu ka,sawo ko tun dazun,
Ai kin gama zance tunda kince da,
Kai amma Sadiya baki da dabi a daga dawowan mutum babu ko sannu sai kice wai ya,ina,sakon ki halan kin aike shine,
Mama hafsi ke maganan nan cikin bacin rai don Allah ku dinga tausayawa mazajen ku mana ba a rayuwa haka gaskiya,
Mama ki kyale ni don ba maganan ki bane wanan ,
Idan baka,sayo min kabani kudina sai na,saye ko,
Ta tsiyan naki yau tashi ke nan dai Allah ya kyauta inji mama tamike tana kokari dauka yarinyar dage gefen ta,
Na fito dauke da,jug din ruwa a hannuna ina mika mashi Sadiya taci gaba dacewa sai a dinga yiwa mutum banbanci ana gani baza ai magana ba,
Haba ki bi sannu mana ai dole ya,sayo maki inji Umma take lalashinta,
Ruwan ya karba yakafa kai yasha sai da yai rabin jug din yamiko min tare da cewa,
Kai min ruwa na watsa kafin naci abinci duk a gajiye nake,
Har lokacin Sadiya tana bakar magana ya shiga daki zuwa can yafito da kudi a hannun shi yace,
Sadiya wai nawa ne kudin naki shin ?
Ai kafi kowa sani tace tana kallon hannun shi dake rike da kudi karbi nan gasu,
Ta karba tana kirgawa cikin cewa tafi nono fari yau Allah ya kwato min abina,
Kuma wallahi idan baka sayo min ba ni ban yafe ba tunda ina da hakki a kan ka ,
Ya juyo a hasale yace baki yafe may ba hakkin may kike dashi akaina,
A,a Sadiya tunda ya baki kudi ki kuma ina zancen baki yafe ba yafito ki daina ja mashi Allah ya isa haka mana,
Mijiki ne fa kina ja mashi Allah ya isa haka kuma ,
Wanda yaji haushi ya rama mashi mana a,a ni din kuma kike nufi na rama mashi ko wa Sadiya,
Umma in ma ke din ne ai dake nake tunda in ana magana dashi duk sai ku tare ni mafa ina da iyayyen nan ba shegiya nake ba,
Yanzu don nace ki bari shine kike fa damin magana haka nidai yanzu banyi da kowan ku ba magana na ne dashi amma duk kun bi kun shige ciki zance,
To ai sai ki tayi tundake in idon ki ya rufe kowa kina takawa ki hau,
Ai in hakane kowa ma yana da, dan bana a dakin shi bani kadai bace balle a saka min baki,
Ni wallahi ban yarda da wullakanci kowa ya,sa maka baki a hanaka magana kaman kowa ba haihuwan shi akayi ba,
Har yafito daga wanka ta,zaune ta zubawa su Umma da mama kwankwami akai Umma duk nauyi da kunya ya rufe, ta,
Yanzu dai din nai magana shine ya jawo wanan zancen haka ko tace to anyi dake ne kibar ni dashi muyi mana ai ban ce kowa ya,saka min baki ba,
Ke Sadiya yace cikin wani irin murya yafito da rigar da yai niyar sawa a hannun shi,
Idanuwar shi sun kada sun yi ja yace ki tafi gidan ku na,sake ki saki daya,
Fetur ke nan tace ahayye Umma sai ki zuba ruwa kasa kisha tun da kin kai ga yadda kike so yau zan bar maki gida ga dan naki nan susu sauran mace mijin tace na bar maki sai a daura maki aure dashi dama kishiyar yar agwai kike,
Innalillahi Sadiya kina da hankali kuwa kike furta wanan kalamin da bakin ki uwar nashi zai aura,
Yace mama ki barta duk abinda tayi ai Umma ce tajawa kanta don ita tasaye,
Wanan da ba mutum ba itace Umma ta rike wai mutum don kawai kiyayyan Aisha da take ji,
Indon kankane ai da kowa Umma tana fada ba Aisha ba kawai don gashi yau takai ga yadda take so,
May nagane dama ga,wanan auren tsiya na gidan ki ba ci ba sha ba sutura sai bakar masifan tsiya da,wahala,
Garama da Allah ya kashe dan da nasamu da ku da na hada zuria da irin ku irin tsiya da masifa,
Tallakawa karshe masu cin amanan mutane kawai wallahi ni ban dana sani da mutuwar wanan bakin auren wahalan,
Macuciya tsohuwa kawai dama don ki cuce ni ki bata mani lokaci kikaje dadin baki wai na,auri danki don na kwato maki dan ki ga halaka ,
Ashe kece macuciyar ban sani ba,wallahi dake da ummana kuka cuce ni banda bakar kwazaba idan dare yayi babu abin da na karu dashi a gidan ku,
Ke kuma Aisha gaki ga gidan in dai wanan gidan ne ina zaune zanji fitowan ki don wanan muguwa bazata barki ba ita da shegun diyan ta matsiyata yan banza kawai,
Tajawo kofanta ta rufe tana tafiya tana cewa kada Allah ya,kara hadani daku ko a lahira wallahi macutan banza kawai matsiyata,
Ke tafi karyan banza karyan wofi a kwasa akai ma,wani mugun abin kuma yau dai Hamza ya huta kuma,
Hamza ne ke fadin haka cikin binta da mugun kallo
Ba don komai ya kyaleta ba,sai don yai ma,su Baba alkawarin bai kara taba jikin ta,da sunan duka,
Hamza ya juya gurin Umma yace tau Umma kin gani kin ga abinda kika kwaso wa kanki zagi da tonon asiri dai yau munji shi ,
Mazan dake kofan gida suna ganin tafito suka sa mata dari suna cewa ke nan baki barin mugun halinki Hamza ma yai kokarin zama dake bakar annoba ki zageshi ki zagi uwar shi,
Ta juya gurin su tana cewa muna fukan banza muna fukan wofi ai da ku aka hada kai aka cuce ni ban yafe maku ba,
Ta samu uwar ta da kuka karya da gaskiya ta kwasa ta fada mata tanaji ance har da,saki ya,shiga tace dawa Allah ya hada ta,bada Umma ba nan suka yo gidan syka,dinga tonon asiri tdakanin su da Umma duniya tana jin su,,,


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABUIDDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON HAKA CIN AMANA NE,,,,

Alhamdullahi don yanzu abubuwa duk sun daidaita a,gidan mu an yiwa gidan kwasarima sosai ya koma kamar na,zamani,
Daga sana,an kai kaya company sai kums ya juya ga harkan noma ya raba hannun don dama shi ma,nomine baida da halin yi ne,
A yanzu noma Hamza keyi sosai ba kama hannun yaro dayake Allah ya albarka ci al,amarin shin tun noman farko sai alamarin ya daga sosai,
Yana noma masara dawa da,wake sai fadamun noman shimkafa da,su rake daya bude,
Nan ya fara,samun yaran aiki masu bin shi su ma su samu daga cikin su har Yahaya dan gidan mama Atika,,
Jidda,tana da, shekara daya na samu wani ciki a lokacin wanan cikin yazo min da,banbanci akan na Jidda din,,
Don ni kaina ban san dashi ba sai dai ina yawan alolayi kwanakin nan ga yawan tashin zuciyan dake damu na,sosai duk abinda naci sai na amaye shi tas mama ce tace dana ci na,saka dan namijin goro guntu a bakina ko ainihin goro ko dan dabino,
Ranan Hamza ya,dawo daga tafiya ya sayo kan sa yace a gyara da taimakon mama na,samu na kamala aikin naman, nai muna tuwon farar shimkafa, yai fari tas ga kamshin kayan yaji dake tashi daga cikin miyan,
Kowa yasan idan Hamza yai tafiya yadawo ba karamin dadi muke ci ba a gidan hakan yasa kowa dawowa gida a ranan,
Suna zaune kowa na kwasan gara agaban shi har shi uban aikin Hamza ya na gida tare da yan uwan shi ana hira, gwanin ban sha,awa, don Asmau zatayi aure badadewa ba, insha Allahu,
Ina tsaye sai aiyuka na nake ta faman yi ni ban zauna cin abincin ba tare dasu,
Gurin mama nazo ina cewa mama akwai sauran goron ne a wurin ki don ina son zan danci abinci,
Mama tace Eh akwai shi Aisha ai bazan yarda yanzu in rabu dashi ba duk da ni ina kokarin na daina cin shi sai gashi kuma watan cin shi ya kama a gidan mu,
Da sauri Umma ta dago kaina tana min kallon tantancewa don ta tabbatar da maganan mama,
Sukuma sauran basu fahinci may mama take nufi da zancen ta sai cewa Jibrin yayi a,a mama watan cin goro yakama mu kuma aini ban son goro sam wallahi,
Mamatace ai inkai baka son ci dan ka ko yar ka na so don in ba goron taci ba yanzu data sha ko ruwa ne zaka ga, sai ta amaye shi tas,
Sai lokacin suka fahinci zancen mama sai sukayo min ido caaa akaina lokacin ina kokari bude ledan goron da mama ta miko min,.
Ke madam kice min kin samu kujine har yafara gubda ruwa ban sani ba ni, inji Asmau take zolaya na,
Yar sheri kawai nace kema kwana,nawane kin gunda naki mu ga nashi kalan,
Hamza don jin dadi sai murmushi kawai yake daga inda yake zaune wani irin dadi ya kumay shi don shi sam bai kawo zazzabin daren da nakeyi wai ciki bane don cewa nake maleria ne ke damuna,
Kai wasu matan dai akwai su da bakar jaraban tsiya ace ko yaye yaro baka yi sai ka dauki wani ciki ka halaka dan ka da hannun ka,,
Take ran Hamza ya ba ci ya daure fuskan shi da da yake murmushi dashi don sam baiji dadin zancen Umma ba,
To ai haraban yana gurin dana shi da ya kasa barin ta ta yaye ya lalabata ya dura mata wani cikin batai yaye ba,
Ita Aisha maye nata aciki banda wahalan da take fama da ita ace ko ruwa kasha yana kasa,
Inajin haka na juya zuwa kofana don nasan yanzu zancen su zai iya rikidewa don fadin gaskiya,
Haba yaya wanan magana aibai dace aji shi a bakinki ba gaskiya abin farin ciki yasamu kuma zaki cewa yarinyar mutane jaraba ne da ita,
Da can baya da bata samu cikin da wuru ba ai gaba kuka sata da zuguba a gidan nan bata da shakat taki hauhuwa,
Yanzun kuma Allah ya kawo cikin da,wuri zakice wai tafaye jaraba dan adam dai ba,a iyashi wallahi mutum yakama girman shi mana wanan halin gaskiya ki sake

Download complete TXT · Novel page