Showing 210001 words to 213000 words out of 299981 words

Chapter 71 - Sarautar Mata By Makawa

04 Dec 2025

17620

wani jemay ta yankwamay kamar bata da lafiya,
Shi jego dakike gani ba komai bane dama jegon sai kici kisha mai lafiya ko ba,dadi dai cikin ki ya dauki zafi da yaji yanzu zakiga kina sheki saboda irin jinin da mata ke zubarwa yayin haihuwa idan kin ci abinci sosai kinsha ruwa gyambon ciki sai yai saurin warkewa,
Shiyasa nai dabaran cewa yabani kudi ni zan dinga maki miyar ki ta musan man yadda ba mai fahintar cewa shine ya bada har akai ga fitina,
Nidai ko Sadiya tasha giyar wake bata tambaya don may nake kyautata maki tundani ban samu ragowa ko matsayin uwa a gurin ta ba,
Ke kuwa duk inda na tsayar dake anan kike tsayawa kin san kimata,da,darajana Aisha dole duk abinda naga zai cuta maki nayi tsaye a kan shi ba,Sadiya ba har uwar taku nasan ranta yana baci a kaina bata dadai yadda zatayi danine kawai,
Murmushi naiwa mama don ni ba ma,abociyar magana bace dama sosai,
Haka tafita tana yaba min da bani shawaran na kara dagewa da hakkurin danakeyi don talauci bamai dorewa bane,
Duk abinda Allah ya hore maki a gurin mijinki ya baki karba da murna da farin ciki a bainar jama,a kada kiyarda ki nuna bacin ranki don kinfi kowa sanin baidashi yannzu,
Nace tau mama insha Allahu bazakiji wani abin assha daga garni ba ko yan uwana,
Don kishiyar ki ta hake cewa duk taga yai maki wani abinda bai mata ba,sai ta dauki mata ki sosai bazata yarda ba,
Jiya naji tana magana,dadare da matar wanta da,tashigo barka,

****** ********* ******
Karfe goma gida ya fara cika da yan buki yan uwa da abokan arziki nawa dana Hamza, harda ma,wasu makwabta da ake abin arziki dasu,
Sau daya nafito tsakar gida na kwashe kayan baby da aka shanya kada aiyawa sufadi a tattaka,su,
Sadiya tana kyalla ido ta hangoni a take fuskanta ya,sauya saboda tagane babban zani ne na,daura sai mamaki ya kamata ina na,samo shi ,
Daki takoma ta,sauya kayan jikin ta itama tare da gyara fuskanta,
Yan gidan mu mata dake aure sun min kara don gaba dayan su sunzo gurin sunan nawa kuma ni banyi zaton haka ba daga gare su,
Zaune muke sai faman yan gulmace gulmace akeyi ba wani girki mai yawa mutanen gidan mu sukeyi ba don haka,sai suke ga,duk mutanen dake gurin basu iya basu abincin da zasu sai nune da zunde sukeyi,
Suna cewa,wai abincin da zasu bayar gaskiya bazai isa ba dafo ba ni basu ga nai wani girki ba wanda zanbawa bakina,
Duk zancen su ba,a boye yake ba don haka muna jin su sai Kubura ce ke tambaya na ke Aisha dama bakiyi wani tanadi bane da zakibawa mutane nace akwaishi za,a kawo hakan yasa su kwantar da hankalin su da har suna zancen abinda ya kamata suyi,
Don a tsamanin yan dakina,saboda halin talaucin da muke a ciki babu abinda nake dashi da zasu ci,
Shigar wani shadda dan senegal nayi mai ruwan dark blue color kalan ya matukar karban jikina,sosai,
Daga safe zuwa wanan lokaci shiga kala uku nayi duk acikin yan dabaru irin na Anty Hindatu,
Ance zaman lafiya yafi zama dan sarki zuwa sha biyun rana daga gida su Anty Hinda mata suka shigo da manyan kulolin abinci da abin sha kala kala daga zobo kunun ayya, jinger da ruwa masu sanyi,
Nan guri ya kicimay da hayani Anty laurat yar kubura tace a,diban wa yan bangaren Hamza su san mu ba marowata bane ,
Shigana da yanayin abincin da aka,kawo shinkafa da miya da tuwon yarbawa, sai makaroni, dafa duka yaji cabeji da kayan ciki sai kamshi ke tashi,
Duk sai yasa jikin Sadiya da yan bangaren dagin miji sanyin jiki dole suka koma kallin mu,
Karfe biyu daidai sai ga yan walima da ita kanta gaiyyan aikin Anty hindatu data gaiyyato su nan aka,fara walima,
Malaman tai wa,azi ma ratsa jiki yayin da take nasiha akan hakkin a gurin iyayyen shi da kuma hakkin iyayye a gurin diyan su,
Sai wata matar da ta mike itama tai wa,azi akan Amana,
Wa,azin ya ratsa zukatan mutane sosai duk masu saurara anyi shiru jiki ya mutu nan aka shiga raba take away din da aka shigo dashi a buhu,
Sadiya tunda aka fara wa,azi tana daki kamar wacce aka tillastawa zaman daki ita da yan uwan ta,da,suka zo mata zaman daki,
Umma suna daga kofanta da farko suna dan hayani sai malaman tai magana akan ai shiru idan ana karanta sakon Allah don bada gagaresu bane sakon ,
Yar jaririyata tashs addua da fatan samun rayuwa mai albarka har mu iyayyenta an muna addu,an samun abin halak wanda zamu ciyar da ita,
Naji dadin wanan waliman don mun samu addu,a gwargwado a gidan mu wanda Allah kadai yasan bakin din amin da zai karba muna,
Mutane daya bayan daya aka,shiga watsewa acikin murna da farin ciki kowa kagani da yar ledan shi a hannu,
Don kayan snacks da masa wanda iyayyena,suka,sa akayi sune Anty tai take away nasu akabawa yan taron suna suka tafi dashi,
Na,yarda cewa duk abinda mutum yabarwa Allah zabin shi zaga abin mamaki don abin da akayi da,abinda na samu ban taba zaton hakan ba,a,rayuwa ta,
Nasamu kudi turamay da kayan baby ta inda ma banyi tsanmanin samun su ba,
Washegarin yan uwana suka koma gida inda mamana Rahana tazo gidan don nice na aika tazo,
Kamar ko yaushe itace na sa agaba da tayi min yadda ya dace tacirewa hindatu abubuwa da kanta takai mata har gida,
Bayan tafiyan mama gida na zauna ina ta faman tunane barkatai a,raina,
Yanzu yadda mama Rahana tace na fara sanar turamay how comes zan iya sayar da su a gida gaskiya akwai duba a maganan nan,
Sai dai kawai na kara dan duba abinda zanyi wanda zai fi karbuwa a gida
Maganan mama Rahana gaskiyane cewa haihuwa diyan mata daban yake don tun ranan da aka haifesu har auren su a cikin spending iyayye suke dole na samu dan abinda zan rika yi ina tallafawa rayuna dana diyata,
Ganin anyi suna komai ya kammala kuna ina kokari gurin kula da lafiya ns yasa mama hafsi fara fita zuwa harkokinta na neman kudi, kamar yaddacta saba tun da,safe kwarai take barin gida zuwa kai kaya yan kauyukan dake gefen gari,


****** ********* ******

Sabon matsalar da na fara fuskanta a gidan shi ne da,safe ranan da Mama tafara fita gurin sana,ar ta ina daki ina jiran naji Umma tace na kawo maijidda ai mata wanka,
Amma sai naji shiru can naji ta tana,wa dan gurin zarah wanka har da dan tawain ta,
Shiru shiru har rana sai na fito daga dakin na je har kofan dakin ta nake cewa Umma dama zancen wankan yarinyar nan ne naga har rana yayi, ba ai mata ba gashi mama tafita,
Ke bazaki iya mata wanka ba ne ko may shima wanan da kikaga ina mashi don kawai kada nabarta tayi ne ace dan mutane,
Zarah tanajin mu tace haba Umma Aisha ce kuma zataiwa yarta wanka gaki a gida, ai idan wani yagani sai ki ja muna abin fade,
Abin fade na may fa idan da bani gidan waye zai ma yarinyar wanka ai gara ta,fara koyo tun yanzu ta iya har wankan wanan yarinyar guda nawa yake,
Haba Umma gaskiya idan kince haka ko yayan mu bazaiji dadi ba gaskiya
Umma tace kada yaji mana ke na,fada maki bazan iya,ba ni wanka yaro wuya yake min,
Murmushi nayi na juya dauke da yarinyar a hannuna na kaita daki na shimfide sai na,debo ruwa nadawo daga kofar dakina nafara mata wanka sai dai ban iya ba
Ainace tashigo taga ina,wa yarinyar wanka tun kan ta karaso take cewa
Lah anty kece ke mata wanka,da kanki kuma yau i a su mama suka tafi, murmushi nayi naje nai magana yarinyar ta tashi sullube min,
Salati Aina ta saka daidai shigowan Ibrahim yake cewa kai idan baki iya ba baki ba manya,suyi mata wanan ai rashin hankali ne,
Murmushi nayi kawai tare da tsamay yarinyar daga cikin ruwa na,shige da ita cikin daki muna hira da Aina ina,shirya yarinyar,
Karban ta Aina tayi ta goya suka fita zuwa uguwa inda aka aike ta,
Aina tana zuwa gida ta kwashe tafadawa,su mama cewa ban iya wanka ba dana yar da yarinya a kasa,
Wanka kuma ita Aisha da kanta takewa yarta wanka gata da sarakai a cikin gidan, shine sai taimata wanka da kanta ,
Ranshin kunyafa inba,rashin kunyaba yaya za,ayi ace wai tayiwa yarta wanka ita,da kanta Ummina ce ke fadin haka a cikin zafin rai,
Mama Saude tace a,a ku dakata kun san fa Aisha ba mairigima bace ita duk yadda akayi akwai matsala akwai abinda ya faru amma zan shiga na ji koma may nene,
Da yamma ranan Aina tazo ta dauki yarinyar sai kawai naga andawo min da ita,an mata wanka,
Umma ina ce zancen zarah zaiyi tasiri a ranta amma sai taiwa,dangidan zarah wanka kawai ta kyalemu,
Da,dare su mama,Saude da maman Aina,sukazo dakina suka shiga muka gaisa nan suke tambayana dalilin da yasa nakewa yarinya wanka da kaina ga,sarakaina a gida,
Ban yi magana ba,sai kukan da na kamayi kawai don yadda nake jin zuciyana yana radadi a lokacin kamar zai tsage yafito don bacin rai,
Sun fahinci akwai matsala don haka,sukace natashi mu tafi dakin Umma din ,
Mun samay su ita da yar uwarta zaune suna hira ganin mu yasa gaba daya hankalin su dawo gare mu,
Sun gaisa dasu mama lafiya lafiya sai dan shiru da ya biyo dakin mama Saude ne tace Rabi gurin ki mukazo da Aisha,
Don bamu san laifin da tai maki ba,shine malam yace mu kawota ta roke ki gafara indan tai maki wani laifi ne da ba mu sani ba,
Sai shiru ya dan kara gauraye dakin a hankali na fara dan sheshekar kuka da na kasa controlling din shi daga idanuwa,
Mama Saude ta juya gurin da nake take cewa Aisha ki roki sarakuwar ki gafara indan kin mata laifi ne har ya,shafi yar da kika haifa tare da danta watau jikan ta,
A,a ni batai min komai ba,wanka ne dai nace ta koya taiwa yar ta don ban samun lokacin da zance kullun zan diga mata,
Assha Rabi wallahi ko kinci kafa bakiyarda ganye ba don yarinyar nan bata ci haka ba a gurin ku,
Dakata Saude kada kuzo ku sani gaba har dakina kuna son fada min maganan da,bashi ba
Wanan zancen nai maku bayani dalilina amma kuma kuke son juya maganar a,wata,tsiga ta,daban ina dai yarinya jikata ce ba ta,wani ba,
Kwarai kuwa jikan ki ce amma kuma baki dauketa a hakana ba nan zancen yaso ya juye masu a fitina,
Muryan su Hamzane suke cewa subbahanallahi may yai zafi haka may ke faruwa ne wai,
Suka ce min ta shi ki koma dakin ki tunda haka Allah ya nufe ki da,gani a rayuwa,
Wanan dai dama kunzo ne don ku fadi abindake a ranku kawai don abinda bai shafe ku bane,
Idan kuma ke munafuka kin fada masu cewa nai maki wani abune sai su zo su daukar maki fansa mugani,
Rabi kin ga tun farko matsalar da nai hange kenan na jaye halakata dake don na karanci ke ba mutumiyar da za a kama bane
Aikuwa nan abu ya kwabe aja mama aja Umma kowa na,fadawa wa dan uwa tsohon famin dake a tsakanin su dadewa,
Umma tace da kika hanamashi yar taki ai banga ta,auri wanda ya fishi ba indon wanan tsohon dan cacan da,aura ne har kike gadaran yar ki tayi aure inda yafi gidana,
Nan Mama tace macuciya don ban kawo ta kin gasta yadda kike gasa diyan mutane ki hanasu sakata da mijinsu,
Kinyi kane kane a tsakanin yara kina masu mulki da izza irin na,zzalumai,
Yanzu ai gashi kin daukowa kanki jarabar tsaye har nakasaki sai da akayi kuma kadan kika gani wallahi don wanda za,ai maki nan gaba sai, yafi wanan gurmanta da kike yi,
Duk diyan Umma suna tsaye a gaban su suna sauraren tonon asirin da sukeyiwa junan su,
Hamza yai ta hada su mama Saude da Allah akan suyi hakkuri su fita, subar zancen hakana,
Suna fita mama hafsi take tambayan may yafaru ne bayan fitan ta da,safe,
Zarah ce tafada masu duk abinda ya faru da akan Umma taiwa yarinya wanka amma taki,
Umma yarinyar nan dai jikanki ce amma,ba laifi wanan ba,Aisha kikai wa bani dai dana ke naki kika yiwa don duk abinda zai sami yarinyar nine dai ubanta ,
Ina,dashi Aliyun da ita,hauwau, duk jikokin ki daya,suke a gurin ki, sai dai kila,akwai wani abinda bamu sani bane da,yakawo haka,
Fita yayi cikin fushi yabar gidan sai su mamane suke ta mata magana,akan yadda tayi bata kyauta ba,

****** ********* ******
Wanan abinda Umma tai min ya,ba,Sadiya wani kafana,ta,raina ni da yar diya ta,sai dadi takeji tana annashuwa
Hamza hankalin shi ya,tashi sosai ya kasa fahintar abinda ke tsakanin mu haka ?
Yana son sanin ko mai yake kawo wanan matsalolin a tsakanin Aisha da ita,
Gaskiya shi yana son matar shi bazai yarda ace sanadiyar fitinar mahaifiyar shi ya rabu da matarshi ba,
Kwatakwata gaba daya haduwar Umma da mahifiyar Sadiya duk ta canza gabadaya,
Takoma irin su mafadaciya daga dan abu kadan ya hada ta dakai yanzu zata rufe ido tai maka tass,
Ina daki mama tashigo dakin ta,samay ni rakube gefe guda duk na,wani ramay lokaci guda,
Kallon tausayi taimin tare da kaiwa zaune tana cewa Aisha nasoki gane daga ina duk wanan abin yake fitowa,
Kin taba gani ko tunanen cewa Sadiya zata kwanta irin yadda ta lankwasa kanta a gidan nan yanzu,
Ko kin taba ganin mai abinkunya irin sadiya da ta buge uwar mijin ta tayi dana sani akan abinda ta,aiwatar a,baya,
Sai yanzu da suke da dalilin su shine suka hada kai da ita wai Sadiya ta roketa gafara shine take kokari faranta mata,rai ta hanyar kuntata maki,
Naji dadi da yanzu shi Hamza ya fahinci manufarsu yafito daga kaidin mata in ba haka da,har dashi zasu batawa lisafin shi su zugashi yai maki wullakanci ta boka ta malam,
Tun haihuwan ki da kwana biyu da,Sa,a ta,shigo barka,aka,fara wanan kule kulen wai ankai Sadiya gurinta ta roketa gafara,
Ni ban san irin halin yaya ba,wallahi mutanen nan kin san halinsu ba mutanen arziki bane amma sai ta biye masu, suyi ta tura ta,aikin dana sani,
Shi dai mijinki ya,fada mata cewa,wallahi yana,son matan shi in ma,suna ganin zasu tayar maki da hankali ne tau sau dai yabar gidan ya nema maki wani guri ku koma,
Shine ya tarya mata da hankali tahau borin kunya tana cewa wai an kwace mata,shi yanzu gaba daya ta,rasa gane kan shi kinje garinku an maki asiri zaki kashe mata da don bai ganin kowa da gashi in ba ke ba,
Murmushi nayi na takaici nace ai Allah shine shedu mama idan nai ma Hamza wani abu a garin mu,
Ke dai yanzu ki kara,dagewa,da,adduan Allah ya kara doraki a kan su kawai amma wa yan nan mutandn basu da kyau,
Magan ganun mama sun kara sani mayar da hankali ga,abinda ke gudana a gidan yanzu,
Na,fahinci yanzu tunda na haihu akwai shiri tsakani Sadiya da Umma sai wani, Ladabi takewa Umma,
Ita kuma umma duk dan abinda tafita,tasamo yanzu zakaji tace ina ya ta wai ni yar mama hafsi ba yar ta,ba tana take fakewa suna cutana kuma,



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,,,



Alhamdullahi zance don yanzu da hamza yai tsaye abubuwan sun yi dan sauki a kaina, sai dai a rufe akeko mai,
Sannu sannu Hamza yadan fara sana,a hankali ba wani sana na,azo a gani ba ko shi sai da ya,ari kudi guri wani dan uwan sana,an shi da can baya,
Shine ya dan fara barin gida yana dan shiga garuwa, yana yan kwanaki baya gida,
Hakan bai ma Sadiya dadi ba da ya tsiro da wanan tafiye tafiyen don ya hanata ta samu yadda take ita kaidai tunda ni ina jego,
Sannu a hankali likkafa ya fara ci gaba ga,sana,ar tashi don yanzu yakai yana dan iya kai kaya kurmi kadan kadan don ya dan kwarai da harkan,
Duk yadda akaso ya tsaya iyaka gida yai sanar don gudun abinda yafaru a baya yaki ya dauka cewa wancan kaddara ne haka Allah ya nufa,
Wanan zuwan da yayi wake yakai buhu goma sai Allah ya hadashi da,wani iyyamuri matashi shima yana sanar export ne daga kasa zuwa kasa yake kai abinci,
Wanan matumin yai matukar yabawa da,wanken da Hamza ya,shiga masu dashi sai yake cewa idan da zai samu wanan wake da yawa yana so ya,saya yakai waje,
Nan Hamza ya,dawo gida hankali a tashe don ga alheri ya hango amma ba hali, kamar yadda duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login