Showing 213001 words to 216000 words out of 299981 words

Chapter 72 - Sarautar Mata By Makawa

04 Dec 2025

17624

wani dan kasuwa yakan shiga halin yaya nakayi haka wanan bawan Allah shima ya shiga wanan yanayin fada can tashi can yana neman kudin da zai, karfafa kasuwan cin shi,
Duk yan uwan shi ya tunkare su akan su dan kara mai kudi ya gwada wanan sana,an amma fir suka ki,
Ya,samu Umma da,shawaran cewa ta bashi dama ya,dan sayar da filin su na baya gidan su amma fir umma taki yarda tace abin gado ne bata yarda ba,

Jego nakeyi bawai lalaine nasan tsananin halin da yake ciki ba a lokaci, ni dai nasan yana bukatar kudi amma ban sa kaina ba don bazan ma bayar ba,

Missali karfe daya da,wani abu na rana na dauraye yarinya kamar yadda na saba yi mata idan rana yayi
Powder nake shafa mata,sai watsalniya da kafafuwan ta takeyi irin na jarirai masu lafiya ni ka dai dagani sai ita adaki ina fadin ni dai tsaya na,sa maki leda don fitsari ki yai yawa wallahi,
Hamza naga ya shigo dakin mu kaina yana a duke nai mashi sannu da zuwa,
Hannun yarinyar ya dan rika a cikin nashi sai ta danke yatsan nashi a hankali yadan lakuci kumatun ta yace gwagona kinyi wayau fa sosai,
Zaune yakai da ita,a hannun shi yana mata wasa hakan yasani komawa bakin gado na zauna ina kallon su,
Hamza yai matukar ramaywa sosai ya fada sai kasunba da ya aje a fuskan shi,
Wasa yakewa Jidda yana hada goshin sa da nata gurin daya yana cewa gwagona Allah ya raya min ke na zama Baba nima azo a rusunna min,
Sai nai murmushi kawai,daga inda nake zaune yadago yana ce min duk yarinyar nan ke ta kwaso wallahi,
Nace kai yaya abakin ka kawsi naji haka cewa ake wai kamar kayi kakinta ne tafito don komai naka ta kwaso sai fari ne nawa,
Murmushi yayi yace ai dole jini yayi aikin shi a kowan mu,
Wayan shi tai kara abinda ya dakatar muna da hiran mu ke nan ya dauki wayan sai na fahinci maganace mai muhinmanci yake a,wayan yadda naga action din shi ya nuna,
Yana gama wayan sai naga ya dan tugumay yarinyar a jikin shi yana cewa,
Allah Allah kadubeni da idon rahamar ka ka bani falalar da zan samu nayi wanan business ne din kada ya,kubce min ,
Idanuwan shi a lumshe yana bubuga bayan yar baby dake a hannun shi yake cewa ace idan matsala ta sami mutum ya rasa gurin da zai dafa yaji sanyi,
Yau kusan sati uku ke nan ina yawon neman taimako aron kudi dazan da,sayi waken da,ake bukata nakai wani company,
Amma abu ya,faskara kowa ka tafi sai ya kawo ma lalurar duniya a kindayan maka,sune a,gaban shi,
Munan dai zaune muna ta zancen yadda mutane basu iya taimakawa na kasa gare,su,
Sai can nake cewa tau yanzu yaya zakayi gashi naji kamar mutumin yana cewa saura, sati biyu idan har ba,a,samu ba zai nemi wani ta,kawo mashi kayan,
Yace a,sanyaye haka dai yake ce min dole hakkura zan yi na,bari aba,wani tunda banda shi,
Sai dai idan kudin dake a hannuna zan hada na baka kafara saya,mashi dasu,
Da,sauri Hamza ya kalleni yana girgiza kan shi yana cewa, haba dai Humaira ai hankali hanjine,
Yai murmushi yace sau nawa ina karban kudi a,gurin ki ban taba biyannki su ba har yau ke kuma baki tambayeni su ba,
Wallahi har yanzu zancen nan da nakw maki kunya rashi biyan ki kudin ki da banyi nakeyi,
Yanzu kuma zaki fito da zancen na karbi wanda suke a,gurin ki kawai gwanda mu hakkura haka Allah ya nufa damu ,
Na ai bamu san inda alherin mu yake ba da kaita yawo babu mai baka,aro ai gara na mika,ma su ka juya,ko Allah zai sa muna albarka aciki mu gani,
Yace to shi ke nan amma,sai k8n shawarci iyayyen ki abinda,duk sukace dashi zamuyi amfani,
Na ce tau zan sa,akira min mama ko ummi nai shawara,dasu,
Wani irin ajiyan zuciya yayi don bai taba zaton za,a,iya,samun mace mai wanan hali ba azamanin nan da kowace mace idon ta ya bude da,son kudi,
Watau ita dai Humaira komai nata a cikin sauki take rayuwan ta bata,saka duniya a gaban ta ba balle ya damay ta kamar Sadiya,
Da wuya kaji Aisha tayi wani korafi akan asayo mata abu kaza ko tace kaza nake so bana son kaza,
Halin da maza da,yawa yake hada su fada da matayen su don namiji ya,tsani yakawo wa mace abu ta rai ko kuma kullunta kama fadin ba ba ba yana zubar da kimar mace a gurin mijin ta,
Gashi yanzu ba matan aure ba harda yan mata sun iya cewa yau kaza nake so gobe ma kaza nake so,
Ko kaiwa budurwa kyauta tun ba ai aure ba ta nuna ita kyautar bai mata ba don ba choice din ta bane
Iyayyen mu na,da duk abin da namiji yabasu hannu bibiyu mace zata karba tana zabga godiya da farin cikin ta,
Amma yanzu gashi duk yadda ya iya fita yai yawo a cikin rana in yadan samo abu ya kawo a,tsiwace Sadiya zata karba tana korafi akan shi,
Shiko ba haka Aisha ta,saba yi mashi ba a,baya duk abinda ya kawo sai dai tace mai sannu da dawowa takarba ta,gyara tabawa kowa kuma kowa ya,samu,gwargwado,
A haka muka bar zancen kan zan shawarci manya na muji may zasu ce, akai,,,
Sai dai shi har kasan zuciyar shi nauyi da kunya yake ji ace ya na karba dukiyar matar shi abu na lalacewa,

****** ********* ******
Bayan nagama fadawa mama da Ummi dana bukaci ganin su suka zo hankali a tashe don a zaton su wani matsalane tunda na bukaci suzo su biyu a lokaci guda,
Ummi tace yanzu akan wanan zance kikasamu taso Aisha ni wallahi na zaci wani matsalane keda mutanen gidan ku koda mijin ki,
Nace a,a dama ahine yace na,shawarce ku ai muji naku shawaran abinda zakuce,
Sai lokacin mama tai magana take cewa tau a gaskiya wani matsala ne kan babba don bai yuyuwa ki dauki abin hannun ki ki bashi ya akoda yaushe don namiji ba dan goyo bane,
Sai kin kwashi abin hannun ki kin mika mashi dayazo ya samu ta sanadin ki sai duk yasa kafa yatake komai yace wai ya manta, dake da akai wahalar samu tare da ke,
Mace ta zauna da kai da talauci tana hakkuri tana daurewa da,duk halin da kake ciki amma,da,zaran dadi yazo sai duk amanta da hakkuri ki, da dauriyan da kikayi a baya,
Sai a tafi zuwa neman matar da za,aci dadi da ita ke baki uya cin dadi ba sai wuya,
Ummi dake saurare tace ai shiyasa kkikaga,arzikin sai yazo da miskila,don baikaiwa ko ina,sai a bare, koda kuwa aiki kake yi kace kaidan cin amanane yanzu ko ina ba aikaiwa zaki ga matsaloli sun fara kuno kai iri iri,
Mama Rahana tace mijin ki uban yar ki ko ince diyan ki in ya cuce ki wallahi kan shi ya cuta don ke kin mai yadda,Allah yace a rufa dan uwa asiri kamar yadda zaka rufawa kan ka,
Imanin dayan ku baya kammala har sai yaso wa dan uwan shi abinda yake so wa kan sa,
Don haka ni dai bazan mu ce kada ki baahi ba don mijin ki ne kuma yana neman taimako gashi yayi hankalin cewa kifara,shawartar da magabatan ki tukun,,
Hakan yana da kyau don ni indai don shi yaron ne wallahi bazance baza,a bashi ba amma kin ga wanan makiran uwar tashi wallahi ina iya cewa kada a bashi don zata iya cewa nan gaba kada ma ya taimaka maki, inda hali,
Ai itama ta haifa ai gasunan a gaban ta sunki aure suna gwada sa,a da juna da ita a cikin gida akwai abinda yafi wanan ciwo ne,
Bafa karatu suke ba ba komai ba sai dai kawai ai wanka abi hanya ana laudi kawai,a hanya,
Shawara daya da zan kara baki shine ki kasa kudin uku ki bashi kashi biyu kashi daya ki rika,a hannun ki kina dan juyawa a hankali mu gani ai hanyar Allah yawa gare shi,
Sun kara jamin kune akan nayi hakuri na kawar da kaina ga,duk irin abubuwan da,ake gwada min agidan suna min ne don sunga cewa nafisu,
Inda ace kin zama abin tausayine da yanzu za,akama takaki yadda rai ke so suna cewa kece abin son su,
Wallahi ni yanzu na fahinci wanan bakar matar hassada da bakin ciki sune suke cin ta don taga kinfi duk diyan ta kuma baki damuwa da harkan su shine karin bakin cikin su a kan ki,
Don haka sai ki dage da,addu,a da kuma,sadaka koda dan kadan don sadaka rigakafin masifu ne ga bawa ,
A,sanyaye na amsa da,fadin tau mama na gode indan tadawo duk yadda mukayi zanfada maku,
Har sun kai kofa fita daga dakin sai mama Rahana ta,dakata take ce min kina nan kina amfani da ruwan dana aiko maki na tantabara ki hada da miski kina tsarki dashi kafin kiyi arba,in,
Nace ina yi mama cikin dan jin kunya ki dai tayin duk abubuwan dana fada maki don kinga kin haihu saboda mu mata daran mun fara haihuwa dole mu dan matsa da gyaran jikin mu,
Kwalban Alhaji Audun dana kawo maki kada kiyi wasa dashi Aisha don yana,da kyau sosai ga mace,
Kanumfari dai nasan cewa kina dashi har yanzu kuma kina amfani dashi,
Don ko shi ba baya ba saboda amfanin shi yana da matukar yawa ga dan adam sosai,,
Kwara uku ki tsugunna akoda yaushe a kanshi kiyi hayaki kasan ki dashi,
Inayi mama na bata amsa a takaice,
Bayan fitan su mama na zauna ina tunanen abinda ka je ya dawo akan wanan kasadan da nake son yi naba namiji kudina namijin dabani kadaice mallakin shi ba namijin da,yaje mijin mace hudu uban diya ba iyaka
Ke Aisha, rike kudin ki ke da diyan ki, sune naki bana mu duka ba, baban kowa,
Har na aje akan haka sai kuma wani tunane yazo min nace to amma kuma, idan ban taimaka mai ba may ye amfanin arzikin da nake fatan ni nayi mijina na,wahala akan son tara abin duniya zan bar mijina a cikin wahala,
Abina na shi ne haka abin shi namu ne don haka banji kyashin komai ba sai na yanke kawai na bashi kudin ya gwada sa,an shi ya gani ko za,a dace,
Bayan ya,shigo nai mashi bayanin komai sai ya dan yi shiru yana nazarin irin iyayyen da,Allah ya hore min bama su kyashi da,hassada ba,
Duk irin abinda yai min a baya basu duba akan shi har sun kara yarda na taimaka shi akaro na barkatai kuma again,

****** ********* ******
Alhamdullahi don dan kufin dana hada mashi wanda babana da sukazo suna suka kawo min kudin gonan su da,suka,sayar suka raba kudin shine aka kawo min na baba, bayan sun cire nasu kason a ciki,
Mutumin da Hamza yakaiwa kayan yaji matukar dadi don haka ya saye yadda ya,dace ya bashi kudin shi akan cewa ya dawo ya kara saya ya kai mashi,
Da Hamza zai dawo ya dan sayo wa Jidda yan rigunan yara mata kala biyu da permpers da,su man shafi na jarirai,
Ranan da ya dawo da yake ban yi arbain ba adakin Sadiya yake har yanzu don haka shigowan dare sukayi bai samu bamu kayan ba don ya samu munyi barci ko, don har na rufe dakina,
Ai Sadiya tana ganin kayan tafara mashi masifa kan cewa may yake nufi da zai sayo wa yar shi kaya haka ita kadai ita ko ta dawo hannu rabba bai sayo mata komai sai burodi kawai da manjan miya da,ya,sayo a gida,
Tun dare suka fara wanan jidalin saboda yana,da gajiya sai bai biye mata ba ya kwanta yai barci abin shi,
Tun da,asuba ya tashi zai tafi sallah ta farka da wanan fitinan nata haka ya tafi rai a bace,
Sai lokacin ne nasan cewa ya dawo daga tafiyan shi ashe cikin dare muna barci,
Ina jin ta tana fadawa Umma cewa wai tun yanzu zai fara nuna mata banbanci akan yar shi don ita Allah bai bar mata nata ba za, a dinga mata wanan cin fuska haka,
Yanzi don Allah ke Sadiya may ye cin fuska a ciki don ya saya wa yar shi kayan sawa shine kuma abin fitina haka,
Ina koke mai sayawa yarinyar nan kayan sawa ne in har kina dashi tunda kin a tare da uban ta,
Mama ni nafi son mutum ya tsaya yafadi gaskiya ba a goyi bayan karya ba,
Ke nan ni ba dolen shi bane da zaiyi tafiya ya,sayowa yar Aisha abu ni ina zaune ko dan kunne, ba zai riko min ba,
Tun da ina Sadiyan mahaukata bari abi ta,waban hanyar yarinya a cutata min ni ko sai na kyale shi ko wallahi bazan yarda ba,
Sai dai yasan nayi indai haka zai min don wallahi ni ba,wawiya nake ba,
Tunda bazaki yarda mama hafsi tace ai sai ki dauki mataki da kanki mu gani,
Wallahi dauka zanyi don bazan yarda da alabe a kaba a harbi barewa ba, watau ya,sayowa yar ta kaya don taji dadi niko da ban da da naji haushi,
Ina dani da Aisha din duk zaman shi muke a gidan nan ba zaman wani ba,
A lokaci ya,dawo daga massalaci yana jin yadda take fadawa iyayyen shi maganan banza,
Sadiya,wai may kike so ne da safen nan tun dare kike abu guda,na kyale ki yanzun kuma kin farka dashi zaki ta da makwabta daga barci da masifan ki haba, wallahi kin isheni bazan iya wanan irin rayuwan ba gaskiya,
Baki isa ki hanani yiwa gwagona sayyayan abinda rai nake son saya mata,ba don diyata
Sai ka dauki mataki tunda bazaka iya ba kamar yadda nima bazan yarda da cin amanan da kake son yi min ba ta hanyar diyar ka,
Wai ko Sadiya kina da hankali kuwa ?
Kai ka wuce inda zaka ban son wanan fitinan haka maza shige inda zaka,
Ya nufi hanyar dakin Sadiya don ya,dauko kayan da take masifa a kan su sai burodi da manjar miyar da ya,sayo kawai ya gani a dakin ta kwashe rigunan ta boye su duka biyu,
Daga labulen dakin yayi yana fadin zoki bani rugunan nan kafin ranki ya baci,
Yafito da bread din da manja ta,waje ya aje su ya koma cikin dakin nan tabishi da sauri ta samay shi yafara bude akwatin ta yana son ya,duba sai ta rike mai hannnu,
Nan su ka,fara kokuwa a tsakanin su karfin ba daya ba ya kwashe ta,sai saman gado tafada kuca ya bude akwatin kayan suna kasa ya kwaso su sai ta rike mai hannu,
Ya juyo ya dinga zabga mata mari gana uku da taji uwar bari ta sake kayan tafara kurma ihu yaje fita ta riko shi ta baya ya juyo cikin fushi yai mata dukan tsiya duk muna tsaye waje cirko, cirko muna kallon ikon Allah ,
Duk dukan da yake mata bakinta yaki mutuwa sai wayyo take fadi shege macuci azzalumi kawai,
Wallahi yau sai ka biyani kudina ban yarda duk abinda za,ayi sai ka bani kudina gidan nan macuci kawai azzalumi dan iska,
Ya ce kizo ki kwata inna karfine bazan bayar ba tace wallahi sai ka bani kudina yau bazan yarda,
Goya Jidda nayi a baya,na don naga masifar da yafi karfin gani na,yau gashi yana dukanta amma bakin Sadiya yaki mutuwa don tsaban bala,i,
Kai miko min rigunan nan don saboda,su ake wanan masifan dai ko ta kawo su na raba gardama,
A,a Umma ba gaskiya bane kuma Ibrahim wanda ke daga kofa yana kallon duk abinda ke wakana a gaban idon shi yaki rabawa,
Ita kanta Umma abinda ya faru a baya take wa tsoron zuwa ya,sake faruwa da ita gashi har yanzu bataji sauki ba tana dan dingisawa ne,
Ba hujja bane don wanan matar ace bazai sayawa yar shi komai ba don wai ana gudun zuciyar ta kafin Hamza ya mikowa Umma kaya ibrahim ya karbe su daga hannun dn uwan shi yanufi dakina dashi rai bace, ya aje a saman gado,
Wayyo Allah na,wallahi yau sai dai ka kasheni amma,sai ka bani kudina don bazan barka ba,wallahi,
Kai Hamza fito gidan nan mana hakana kabarta kada ka bi ta kanta ita mace ce kada ka jin mata ciwo,
Muryan Baba Mudi ne mijin Ummina da muke makwabtaka dasu ta gaban gidan mu yake magana cikin bacin rai ya,shigo daga cikin gidan ya tsaya daga kofa,
Hamza ya dago idanuwan shi da sukai ja yana mayar da numfashi daidaya yace cikin huci tau Baba ,
Zai fita Sadiya dake zaune tamike tasha gaban shi tana cewa wallahi yau sai ka bani kudina dubu goma sha biyu zanbarka kafita inba haka ba sai dai mu tafi tare wajen da zaka,
Baba ya,sake cewa kiyi hakkuri Sadiya insha Allahu zai baki kudin amma kibi sannu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login