Showing 246001 words to 249000 words out of 299981 words

Chapter 83 - Sarautar Mata By Makawa

04 Dec 2025

17626

turo ta furina neman wani abu kuma ta,dage ta sakani gaba harda kukan ta sai na taimaka masu,
Don haka ni Humaira bata da matsala a gurin yan uwana tunda itace mai bani shawara akan na taimaka masu,
Sa,ade badon ta na gina gidan nan ba ta kwashe yau din nan ta koma gida don ni banine zaune a gida ba wace ke gida kuma ba,gurin ta tazo ba,
Umma tace Uhum zaka kore mu dai ke nan a gidan naka ko?
Tun da kasan yin haka shine zai farauta ran Aishan naka ,
Kuma kasan in ina gidan nan dole ne Sa,a ta zauna cikin shi tunda bazata zauna inda bani ba, in dai kace Sa,a ta kwashe har dani zamu kwashe ke nan,
Yace shi ke nan Umma inkin ga hakan yafi maki sai ki bita ni dai nasan bance ke ba amm sa,a kan bata zama min a gida taja min magana a mutanen shiya zaman Sa,a ya isa haka tunda ba biyayya a gurin matan gidan,
Daga haka ya mike yabar dakin Umma tana ta faman fada tana fadin dama tasani sherina sai yakai ga narabashi da kowa nashi na zauna ni kadai da yaya na mata da yan uwana,
Su ma su Ibrahim fita daga dakin sukayi sukabar su su iya mata,
Zarah tace gaskiya Umma abinda Sa,a takeyi babu kyau koni wallahi Alhaji sai da yai min magana akanta yace mu dauki mataki akan sa,a tun bata jawo muna abin kunya ba don inda yake ganin ta a gari bai dace ba,
Ke rufe min baki aiduk kune shanyayyu baku son aga laifin yar gwal din ku ko kadan yadai ce mu bar mashi gidan mata shi ko tau yau din nan basai gobe ba zamu bar mai gidan shi,
Asamau tace Umma baifa ce da ke ba Sa,a dai da tayi laifi yake nufi kuma in ba ai mata fada ai abin baiyi ba wallahi don ba mai sin yaga nashi ya lalace,
A ranan Umma tasa a kwashe su a mayar dasu gida gaba dayan su sai da zata wuce ina tsaye daga gefe ta,waigo tana ce min mun bar maki gidan Aisha gurin ki ya cika,
Amma ki sani gidan nan bazaki zauna ke kadai ba sai wata wace zata shigo ta kwato min dana tashigo shi da yardan Allah,
Nace Umma Allah ya kawo ta lafiya, ai ba akaina zata zauna ba dai ko,.
Duk da,sun koma amma sai nayi girki na aika dashi can kaman kullun sai dai na samu sauki fiye da zaman su a gidan,
Tun ranan bai kara min magana akan zancen ba nima haka ban karayi mai wanan zancen ba ko da wasa,
Shima ne yai tan dan dari dari sai daga baya da yaga ban dauki maganan araina ba,sai ya,share,,
Amma na samu sauki sosai akan tsagwaman da suka dauko yin nacewa,wai na hana akai su makka wannan kuma yafaru ne a,ranan da,suka zo kabar tsaraban su agaban shi nake cewa Allah ya hore mai muma,ya kai mu makka a tare,
Suka ce wai da anga yawo a,gari da jibgo kayan gumama, nan mukai ta shamatar junan mu,
Suna fita Asamau ke cewa nifa wallahi na,fara zargin maganan nan ba gaskiya bane wai Aisha ta hana akai makka badi,
Inda gaskiya may zai satafadi hakan a gaban shi kuma gaban ke nan wallahi duk shirin Ummane fa,
Zarah tace ni tun farko na san hakan bai yiyuwa don idan ya tashi bata isa ta hana ya kaimu ba don shi yaya baida gwani gashi ranan da bakin shi ya fadi in muntura ta neman abu avurin shi ta kama binshi ke nan sai yai wa mutum abu,,
Ni gaskiya ban kara yadda da maganan da ba,a yi a gaban ido na ba sai nagani ko naji da kaina,
Niko a nawa bangaren gaba daya yanzu ban yarda dasu don na fahinci kan su suka sani kawai basu damu da damuwa na ba ko kadan,

****** ********* ******
Tun da ya dawo makka yanzu abin na Hamza kara bunkasa kawai yakeyi don ya,hadu da wani aboki a can wanda ya sashi a harkan sayar da motoci da mashin mashin na zamani,
Sosai wanan harkan ta,amshe shi baida issashen lokacin kan shi balle na wani, sai lokacin da na gan shi gida,
Hakalina a kwance yake nai kiba farina ya kara fitowa ina samun ci da sha da hutawa,
Ba wani zancen wata kishiya da nake ji balle ya tayar min da hankali gashi Umma tun zuwan ta gida dasukayi bada dain rai ba ta daina zuwa gidan mu da niyar kwana,sai dai tazo ta wuni takoma gida da dare ko shi sai tasan dan ta yana gari take zuwa, wai shi take zuwa dubawa bamu ba,
Satin shi Ukku baya gari wanan zuwan da yayi ne nake mashi maganan ina son zuwa naga gida,
Bai hana ni ba sai shirin tafiyan da yai muna inda yakaini da kanshi nayi tafiyan da mama hafsi da hussaina kaunata zamuyi sati daya acan,
Dalilin zuwa mama kuwa tare da mu tana son zuwa taima gwagona gaisuwan dan ta da yarasu ne shine tarakani,
Shi da kan shi ya kaimu inda yace idan zamu dawo zai turo wani yazo ya dauke mu,
Na samu kowa lafiya nakai masu tsarana masu yawa kwanana biyu da zuwa nashiga zagaya dangi da abokan arzikin da nai zaman lafiya dasu wancan zuwan da nayi,
Yan uwa sun tareni fiye da tsamani na don sai dadin ganina suke ji,
Yayan babana wanda yanzu shine ke limancin gari wani dare da na shiga gurin shi mu gaisa dashi,
Yake ce min wai kuwa Aisha ashe mahaifin ki ba yana da rai ba don inda duk nai istihara nakan ganshi kuma a cikin wadata zan gan shi,
Na dan limshe idanuwa na tare da sauke ajiyan zuciya nake cewa baba idan yana raye Allah ya baiyyanar muna dashi,
Sai naga yana dan kokarin jawo wani allon karfe daga gefen shi yana cewa bari na dan baki wani abinda zai taimaka maki a rayuwan ki, sai ya jawo tawada yafara rubutu ga allon nan ya wanke allon a gabana ya miko min yace na,shaye da bissimillah,
Ya jawo wani dan abu cikin wani takarda yace miko min hannun ki na mika mai sai yafara dan murza abin a hannu a hankali har na daina ganin abin yake ce min tsari ne daga duk wani fitina da za,a iya tura maki diyanki ma zan basu susha don tsari daga bakin mutane saboda kowa yagan su yana kaunan su sosai,baki zai iya kama makisu idan yai yawa,
Ki kuma dinga yawaita kama kan su kina masu addu,a safe da yamma ba adduan da ta wuce falaki da nas, da kulhuwallahu ga yaro,
Naiwa Baba godiya ina shirin mikewa yake cewa kikara hakkuri kinji Aisha hakkuri bai bar komai ba a duniya,
In Allah yaso ya yarda bazaki tabe ba a,duniya kuma duk mai binki da sheri a kan shi zai koma insha Allahu ke di kada kiwa wani mugunta a,rayuwan ki don bamu gaji yin hakana,a gidan m
Amma fa mu kuma duk wanda yace zai muna to karshen shi bata kyawo shiyasa kika gani har yau ban yarda wai wani ne yaima mahaifinki asiri ba yabar gari,
Kawai dai zuciya ce irin tamu ta fulani ya hau amma duk randa Allah yai dawowan shi gida kwatsam zamu ganshi ya dawo insha Allahu,
Jikina yai sanyi akan nasihan da Babana ke min, a lokacin nai mashi sallama na barshi a dakin shi tare da,yiwa matan shi saida safe,
Mun yi kwanakin da zamuyi ina ji kamar kada nadawo na bar su don kewan su da nake ji araina,
Mun ratse sokoto gurin mahaifan Ummi na suna ta min tsiya wai ni yanzu mahaifa na nasani nabar kowa,
Naba su hakkuri tare da aje masu tasu tsaraban danazo masu dashi mukai sallama muka kama hanya sai jega,
Jega babban gari garin da babu raggo sai bako, dan jega ba,a gane gidan ku, gida daya kofa goma,

Kamar yadda Hamza yace hakan ne yafaru kuwa don ko da muka dawo baya gida, yana kwatona gurin sarin motoci,
Na gyara ko ina nagidan ida nazo da,wata kaunata diyan Baba Liman na roka yabani ana cewa yarinyar Madina
Yarinyace karama batafi goma ga shekaru amma akwaita da kazar kazar din jiki bata jin nauyin jikin ta ko kadan,
Ba sai nace mata tai min abuba sai dai na,samu kawai tai min ita ma yarinyar farace sol kamana irin mu daya da ita don jini yana aikin shi,
Duk wanda ya ganta zaice muna kama da ita mun rabawa makwabata tsaraban da muka zo dashi sai suke shigowa yi min sannu da zuwa,
A daidai irin wanan lokacin da nake ganin kamar ban taba samun wata dama tajin dadin aurena ba da mallakan mijina na daga ni sai ahi da yan diyan mu agidan sai yadda ran mu yaso ba takura ko tsangwama ga kowa,
Hamza ya dawo daga tafiyan da yayi ya,dawo a gajiye cikin dare suka shigo da motocin su don irin yanayi tsaron dake hanya,
Da yake dare ne ban tsaya yin kwaliyan atamfa ko lace ba kwalliya ta kayan barci nai mashi,
Dan wani mini skirt nayi da,wata yar shirmamiyar shimi don nasan a lokacin su yafi bukata a ran shi,
Duk da yana da gajiya bai hana shi bina da wani irin kallo ba yanayi yana dan murmusawa tare da lumshe idanuwan shi, tamfar ya lashe ni tun a,falon,
Sai dai a lokaci yaran basuyi barci suna zaune a jikin shi sai shirmay suke zuba mai da jin dadin ganin shi madina tana daga gefe daya zaune a takure don bata saba da shi a lokacin,
Ganin suna da mun shi da surutu yafara dan ya mutsan fuska yasani cewa Madina oya Madina kwashe kuje ku kwanta dare yayi hakana,
Ta kwashe su zuwa daki ina ce mata gani nan zuwa nai masu addu,a idan sun kwanta,
Suna shiga yai murmushi yace kin kora min yara da,wayon manya ko,
Nace ai kane naga kamar kafara gajiya da hiran nasu shiyasa nace su barka ka huta yace aiko sun tafi uwar su bata barina na huta,
Nayi murmushi nace aidole nabarka ka huta don na hango gajiya a idanuwan ka,
Barin tafi na kashe masu wuta don suyi barci don naga yau basu son yin barci a idon su,
Na juya zanbi yaran yace look don Allah kada ki dade a gurin su, nace ai bazafi minti talatin ba
What ?
Gaskiya yai min yawa har minti talatin ina jiranki ki dai rage time din nace yayi na juya naji ya riko ni na fada a jikin shi ya ce Humaira wai ko kinga yadda kika koma zuwa gidan nan da kikayi may nene sirin ne wai haka dayawa,
Ko ban gani ba aikai kagani aikin gwagonane da take cikani da kayan dadi danaje,
Gaskiya gwago tayi kokari kin zama tamkar wata yar karamar yarinya kamar a shekarun da na aure ki,
Nayi dariya kawai ina cewa kai yayana kana dai zugani kawai dayawa naji kamar ba,wata bayan ni,
Ya kyalkyale da,dariya yace to ina watan take in bake ba a gidan nan nace agidan kawai ba azuciyar ka ban san iyakar mu ba,
Daga haka na wuce ban tsaya jin may zaifada min ba don nasan nabashi mamaki da amsa na,
Washe gari yace na,shirya har yaran muje gaida,su Umma yakuma yiwa Mama godiyan rakani gida da tayi,
Mun sha kwalliyar mu kamar ran sallah daga ni har sbi da yaran wasu shadda yasa ghalila mai tsada a jikin shi nikuma nasa wasu lace sky color dinkin shi mai dogon hannu, sai yaran da nasawa yan kati, madina tana saye da dinkunan da nai mata da tazo don nata basu fita a gari, dinkin kauyawa ne, sai kamshi ke tashi a jikin mu,
Mun shigo gidan suna waje dukkan su suna hira da murna mama ta tare mu tana muna yaya gajiyan tafiya,
Umma ko dan ta takecewa andawo lafiya Baba bakadai iya barin tafiyan dare ko ?
Ya zauna yana murmushi yana cewa Umma yanayin sana,an na mune hakana sai dai addu,a kawai,
Sai Umma ta dan fara kuka take kowa hankalinshi ya tashi a lokaci guda,
Kowa na tambayan ta Umma lafiya may kuma ya faru daga shigowan mu yamzu mun samay ku lafiya,
Nikan nasan cewa ganin mune ya sata wanan kukan duk wanda ya ganmu a lokacin sai ya yaba muna sai dai makiyin mu, kawai,
Hamza ko duk ya rude har da mikewa yayi yana fadin Umma wani abune ke maki ciwo ko may akai makine wai,
Mama tace ba abinda ke mata ciwo don tun safe lafiyan mu lau a gidan nan da ita,
Kara zama abin tausayi Umma tayi tana marairaice kukan ta duk hankalin su ya daga sai cewa Hamza keyi Umma idan nine nai maki laifi don Allah dai kiyi hakkuri ki yafe min,
Ganin da tayi duk ya kidimay har yana rokon ta gafara sai take cewa, cikin kuka,
Dole ne nai kuka Baba na ganin burina a kan ka ba zai cika ba har na mutu,
Subbahanallahi Umm may akayi kuma wanda ban cika maki burinki ba har zaki mutu baki gani ba,?
Duk gaba dayan mu munyi son muna sauraren burin da Umma ke dashi a kan dan nata da zata mutu bai cika mata shi ba,
Ina zaune sai shan jinin jikina danayi don ina Allah Allah in ba akaina ne gurin nata zai kare ba,
Duk munyi kasake muna kallon Umma wadda harda majina take fecewa don kukan da takeyi gasu Ibrahim duk sun shigo don ganin motanshi a gidan yazo,
Wai mama maynene ana tambayan kikin yi shiru sai sa zukatan mu cikin tashi hankali kikeyi, inji Jibrin dan zafi,
Hamza yakara tausa murya yana lalashi ta saida ta fece wani maji na tace, cikin sanyin murya irin na wanda ke kuka,
In ganka ka,shigo gaidani da matan ka biyu mana Babana kullun bawa idan ya samu ai ya,geadawa Allah yagode ga mata birjit agari kana da wadatan kara aure amma ka zauna da mata guda,
Tsaki suka ja banda hamza da ya dukar da kan shi din bai taba zaton wanan ne abinda mama takewa kuka ba haka,
Murmushi kawai na ita fuska na kakaro a fuskana nace araina Umma kin kai makira ta nan kuma kika bulo min ana zaune kalau,
Kowa na magana shi baiyi magana ba sai can naji ya bude baki cikin sanyin murya yake fadin kiyi hakkuri Umma in har lokacin yin hakan yayi ai zankara mata don ina da gurin yin haka bakiga gidana na mata biyu nayi ba,
Insha Allahu bazan barki har ki mutu ban cika maki gurinki ba nan badadewa ba zan kara mata ,
Kaiyya inji mama wai uwar diya mata ce ke irin wanan maganan haka da baki da diya mace ne sai ace baki san zafin abin ba,
Munzo da niyar yini mukazo amma wanan makircin da Umma ta azamin yasa duk jikina yai sanyi lokacin da yagama zai tafi nima namike ina cewa zamu tafi don tun da Umma tai magana sai ban kara magana ba da kowa, saboda wanan gurin na Umma ya sakar min da kasala ajikina
Gashi inba gyaran Allah ba kalaman da Hamza yaiwa Umma ya sha banban da wanda yasaba mata idan tai maganan yai min kishiya a baya hakan ya tabbatar min da yana gap dayin yanzu,
Ganin nima namike ina cewa yaran suzo mu tafi yasa shi cewa au kun fasa yinin da zakuyi a nan din ne,
Ummm kawai nace mashi tare da tattaro natsuwa na ina ce masu zamu tafi,
Ke Humaira baki fahince ni bane karin auren da nace yayi aiko ke amfanin ki ne ina kwanan baya ce min yayi aiki yai maki yawa a gidan yanzu idan ku biyu ne ai baxaki wahala haka na ba,
Yace hakane fa Umma itama saukin tane idan nakara din ai ba wani abu bane dama,shi aure bana kowa da kowa bane sai wanda yasan zaiyi adalci a kai,
Sai dai ina gudun nayi nazo ina zaluntar dayan ko a,taru a zalunce ta najawa kaina fitinan kabari shiyasa ni auren ma yafita min akai,
Amma tunda burin kike nan a kaina insha Allahu zan kara auren a zauna lafiya ni dake Umma,
Tace yyawa dan albarka haka nake son ka gurin biyayya yanzu da su biyu ne idan dayan bata zauna ba basai dayar ta zauna muna har daren ba,
Nai masu sallama naja yarana muka fita mamace kawai tai muna rakiya tana fadin Antina ina nan zuwa nai maku wuni yaya yace ai yanzu gwago gudun ki takeyi,
Muna hanya ba,wanda yaiwa wani magana abakin wani shagon sayar da kayan sanyi ya,tsaya yana cewa bari nai maku take away don naga rana yayi baku yi abinci ba,
Sai da ya dawo ya zauna amota

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login