Sarautar Mata

Chapter 84 of 94

shifa zama dakike gani na kishi zaman amana ne ita tana kokarin sauke nauyinta a kanki ke ko shedan yana rudinki,
Baki rasa ciba baki rasa shaba komai a kwaishi kuma mijinku bai rage ki da komai ba na zamantakewa don may zaki dagwarawa kanki wahala ita bata ko san kina yi ba ma,
Biba tace wallahi hakane gwago matsalana yanzu guda ne zuwa biyu uwar shi da yan uwan shi sune matsalata, a gidan,
Kinga inda zaki dosa ba inda bai dace dake ba kin kwaso shegen kishin iyayyen ki kin zo dashi har gidan miji,
Ko su uwafa uwace akanta wallahi inkin matsa sai ya saba maki, tace shima fa,taishe shi don halin fitinan ta yakai mashi ko ina,
Nan dai sukai ta zance akan yadda al,amarin gidanbmu yake dasu, sai da,suka gaji suka tafi don kan su,
Tun bayan dawon ta,gida naga ta rage wasu halayanta na sheri sosai don yanzu takan fito in muna falo a zauna adan yi hira da ita, ban damu da rashin girkin da batayi ba don nasan matsala ne na lalurar ciwo,
Sai dai ranan da Hamza ya dawo sai gata ta mike tana girki da kan ta da tagama kuma ta nade zazzabi ya tashi,
Sai na fahinci bata so idan tana da girki na kama mata don tana zaton zan mata babakere a kan aikin ta, don dan canjin da,ake samu daga gurin maigida,
Har wanan lokacin Biba bata fahinci ina da ciki a jikina ba don ban sake yadda ta sake ba,
Sai faman rawan kai take mutane na zuga ta suna ce mata wai maman yan biyu,
Nan ta dauko sallon da makirici a kan cikin yau tace kaza take so gobe ma tace wancan take so,
Tun yana biye mata ranan har yakai gacewa ke nagaji bake kadai bace nafara ganin ciki a gurin ki ba Allah yaba Aisha hakkuri,
Aisha kace niba Aish bace Biba ce ni yanayin cikin ta daban nawa daban kasani ko tunda ba haka takeyi ba ko ni cikin nawa namijine shiya sa,
Yace look Biba na fada maki ban son wanan rayuwan da kike shirin dauko min a gida ni dana miji da mace duk daya,na,dauke su tace haka dai kace amma ko a gurin Allah ba daya suke ba ai don an fifita su,
Rai a bace yafita yana mamakin irin halin rayuwan Biba bata dai bukatan a zauna lafiya, a gida duk abinda zai fitina a kan shi tasan yadda zatai magana sai anyi,
Nikaina yanzu har mamakin ir8n saukin kan da Allah yabani nakeyi dafarko na kance kodai nasihan Ummina ne dana hau yai min aiki haka,
Sai kuma daga baya nakan yi tuna ne koda sauki na,sama daga gurin Allah don nayi roko sosai dana je makka akan Allah ya yaye min kishi,
Allah kuma ya dorani akan duk wata mace da Hamza zai auro yakawo gidan shi daamsunan kishiya ina,rikon Allah ya fifita ta hal8n alheri a kan su,
Kan Umma mai nakan tsaya naita add,dua kan Allah ya dorani daga duk wani mugun nufi nata ina mai neman tsari dani da zuri,a na akan ta,
Saba,an da zan fara shima saida nai dawafi akan shi tare da yiwa diyana suma dawafin neman shiryuwa a gurin Allah tare da sa masu albarka arayuwan su,,
Gashi ko da,alaman Allah ya karbs min addua,a na don duk abinds na roka naga faidan shi a rayuwa na yanzu,
Abu daya ne shine baiyyanan mahaifina da har yanzu bai dawo ba kuma ko labarin shi babu,
Abin wani lokaci yana matukar damun zuciyana sosai saidai ba yadda zanyi dole nai hakkuri nabarwa Allah,

****** ********* ******
Kamar yadda Bibs ta kwalafa rai ga zancen zuwa makka shekara mai zuwa hakan bai samu ba don cikin dake jikin ta ance gwaunati ta hana mata masu ciki zuwa saudiya bana don matsalolin da ake samu acan da su,
Ba yadda batai masifa ba tana cewa ai ance in anbada cin hanci ana bari mace taje yace to shi bazai ba kowa cin hanci ba,
Tabari in Allah yasauke ta badi sai ta tafi inda rabon zuwa, case din har gurin mahaifinta takai karan Hamza amma yace wallahi bai biya sai bata da komai
Haka ya sata ido ga bado ido ga ruwa ga makka ga ciki tarasa wanda zata zaba daga ciki da kyat uwarta ta,taushe don da tace sai dai ta zubar da cijin taje makkan ta kawai intadawo tayi cikin ai,
Ina zaune ranan banjin dadin jikina sai gashi ya,shigo gidan yana,waya duk da,waya yake sai da nai mashi sannu da dawowa yavamsa min cikin lumshe idanuwan shi yazauna gab dani kadan,
A yadda na fahinci wayan da wani ma,aikacin hukumar alhazai yake wayan nashi,
Sai da ya kare yace wassh tare da shafan kanshi a hankali yace rangida may zan samu naci wallahi duk nagaji nace ga abinci ka can saman table kanakawo ma nan ne,
Yace da kin kyauta wallahi don yau duk nagaji gashi gobe kuma tunda safe zan kama hanya don wanan karon wani dajine da ake shigo da motoci ta saukin hanya muka samu can gaba da kwatano garin yake an hada mu da,wani mutum da,zai taimaka muna,
Allah ya taimaka nace mashi tare da mikewa zuwa dauko mashi abinci Biba tafito tana wani turo ciki a gaba ta canza tafiyan ta wai ga mai ciki,
Yakalle ta yai murmushi yace maiciki ke nan nadauka kina can kina sa,na,anki ai barci tace cikin dan zubar da miyau data tara a bakinta yanzu naji kamshin turaren ka nasan ka,shigo shine nafito ko kadan zo min da wani abin kwadai na dan sa,a bakina ,
Dariya mukai mata gaba dayan mu nace wanan cikin kan kila dan Baba muka samu tunda har yana jin kamshin turaren mahaifi shi ko a ina ne,
Dan Baba ai halinshi sai shi ni duk yabi ya jagwalgwalani wallahi sai faman kwadan dayake sani gashi kuma uban shi da shegen mako,
Yace yanzu duk abinda nake sayowa kici bai ishekiba sai kin ce min wai mai mako,
Allah yaba Aisha hakkuri da har yau batace min ga abinda cikin ta ke bukata ba tace bata da shine da tace ga abinda take so itama,
Murmushi yayi don ya fahinci haukan ta ya hana taga cikina da har yafito a cikin zani na yafan turo don yafi nata girma sosai,
Kitchen ta nufa tana fadi bari dai na nemi abinda naci tashige yana cewa sauniya kawai kanta kawai ta sani ita,
Yashige ya kwanta nima natafi waje don na wanke kayan yara da suka dawo dashi school,
Ibrahim yashigo gidan yana ta,sallama ya kawo mai wasu takardu daya aike shi dasu,
Biba tafito daga dakinta zata kitchen suka hade sama sama kamar kullun suka,gaisa dashi, yace ta sallamo mashi Hamza saicewa Biba,,
Bazan tashe shi ba don ya samu barci kaje idan ya tashi sai ka dawo anjima mamaki ya kama shi yace kamar ya bazaki fada mai gani nazo ba, yafa san da zuwana ,
Nace bazan tayar dashi ba ranshi ya baci yaduba dakina bani ciki yafita ranshi a,bace,
Sai gurin Umma yaje yana fada mata abinda yafaru tace yaje yai hakkuri ,
Saida yamma da yadawo yasamu dan uwan shi a falo yake fada mashi ce bata da wayyo nan yabashi hakkuri yace ba komai amma sai tagane kuren ta,
Inajin su don ina tsaye ina gyaran falon banyi magana ba don ba abinda ya shafeni bani bane inji yan conversations din sauratan mata sun min fada na rage shishigi kada su yi fushi dani,sunce na faye rawan kai😜
Zan shige naji muryan shi yana fadin zo mana humaira,
Juyowa nayi inda suke nazo na zauna a hankali saman daya daga cikin kujerun leather cushion din dake mamaye a,falon bakake,
Yace gobe idan Allah ya kaimu kije gurin Ummi kice suyi passport ita da Baba don ina ga tare dasu ne tafiyan bana,
Da sauri nadago kai na dube shi yace ko bakiji bane nace yaya makka zasu kake nufi yace shi nake nufi mana,
Ban san lokacin da na zube kasaba nace yaya nagode nagode kwarai da ,,,,,,
Hannu yadaga min yana cewa may nene haka Humaira don zanbiya wa uwata makka shine zakiyi min godiya may yasa dana biya wa Umma baki min godiya ba sai wanannan,
Murmushi nayi cikin murna nacewa Ibrahim yaya katayani godiya don Allah,
Saiga Biba bull tafito tace may yafaru ake godiya tana kallona ina rusunne a gaban maigida, da sauri naji Hamza yace ba maganan ki bane wanan,
Kallon tuhuma tafara yi muna gaba dayan mu yace wa Ibrahim kajirani mu fita tare akwai inda zamu dama,
Yashiga dakin shi yafito tare suka tafi batare da Biba taji abinda take son ji ba sai tuhumar mu takeyi,
Suna fita tace dama ai ba yau akafara cin amana ba a gidan nan koma mayye ai ji za a yi,
Azuci nace badai yanzu ba kan na kasa fahintar dalilun dayasa yaki fada a,gaban ta da,suka fita yake cewa Ibarahim ko Umm kada ka bari taji zancen nan sai in lokaci yayi,
Nima da dare da yashigo yimin saida safe yake ce min kada ki bari kowa yaji zancen nan sai in lokaci yayi,
Mun bar zance wa iya mu na tafi gurin Ummina munyi yadda yace muyi itada Baba nakawo mashi daga gidan mama Rahama ya kwashe su zuwa birnin kebbi yin E passport,
Salin alin aka gama komai na,tafiyan su batare da surutu yabi gari ba, muna jiran lokaci,
Umma ta shigo gidan mu akan zancen auren Sa,a datu sai dai bata san cewa yasamu yin tafiya don dama ya sallamay ta yace ko gobe ko jibi zaiyi tafiyan,
Sai gata,tazo bayan ya wuce a lokacin ban gida na shiga makwabtar mu yin barka an haihu kwana hudu yau ban shiga ba,
Don haka Biba ce kawai a gida sai Tv dake aiki shikadai a falo yara suna islamiya gaba dayan su,
Jin shirun da,tayi tana ta sallama sai ta leka dakina amma a,rufe yake don ban yarda nabar gida dakina a bude kamar yadda nakeyi a can baya, don itama haka naga tazo da sallon yi,
Dakin Biba ta nufa ta daga labule tana ciki zaune tana waya ta daga kai ta kalli Umma taci gaba da wayan ta, hankali a kwance,,
Habiba bakijin ina sallama ne tun dazun nashigo ba,wanda ya amsa min ,
Biba tace najiki ina waya ne da uwata sai tai sallama da wayan ta juyo gurin Umma dake cewa, eh lalai ashe kin kai can habiba,
Jinan Umma wallahi ni ban yarda ki shigo har dakina ina fama da kaina zaki aza min masifan ki,
Ni dai danki nake aure bake ba don haka wallahi ban yarda da zancen ace uwar miji tazo tana ciwa matar dan ta mutunci don ba ita ta haifeni ba,
Don Allah ki fita min daga daki kada kuma kice nai maki wani sheri ko,
Umma tace har korana kike a dakin ki yau Habiba don wuyanki yai kauri ya isa yanka ko,
Nan tafara tafa hannayen ta Umma nace ki fita,ban son fitina haka kawai don tsegumi da bani bani baki iya zama gidan ki kullun mutum yana yawa gidan sarakai babu ko kinya ni wallahi wanan abin ya isheni a gidan nan,
Uwarki ce mai yawan gidan sarakai ai nace uwarki ce mai kwadayi nikan wallahi ba uwata ba, sai dai uwar wa ke nan,.
Tace ni dai nace ba,uwana ba,wallahi abinda naji ke nan nace subbahanallahi Biba kanki daya kuwa tace da,akayi may fa,
Jinan maman Jidda kada kisa bakin ki cikin wanan magana kinji na fada maki,
Nace Amarya kibar wanan hakin don ba halin tarbiya bane kema fa watarana haihuwa zakiyi tace na haihu mana
Ko na haihu Allah yarabani da halin wanan kullun mutum yawo gidan dan shi yana aikin saka ido haka kawai za,a fado min daki ace wai nabar waya da uwata ,
Habiba yau ni kika zaga a gidan nan ba laifinki bane don ni najawa kaina hakan,
Tace inma kince nazage ki na zaga din don dai ni ba uwata ba, sai kawai umma ta fashe da kuka tana cewa Biba tai mata cin mutinci,
Da kyat na samu Biba ta shigd dakin ta tana fada tana cewa wallahi ita batayarda a zage ta ga banza,,
Umma tana kuka tana share hawaye da habar jibba din ta tana cewa kaman ni Habiba zata kalla tai min wanan zagin haka,
Babu komai bata da laifi nasan inda matsalan nan yafito nace Umma yi hakkuri, tace ai dole Aisha, ina yaron nan yake ne nace Umma bai fada maki cewa yau zai tafi ba tun safe suka bar garin nan, ai,
Tace yasamu wuce wa yau din ke nan ko nace eh Umma su tafi ko,
Allah ya,dawo muna dasu lafiya nace amin Umma take cewa bari ta koma gida tace dama nazo kan zancen Sa,a datu,
Nace Umm idan munyi waya dashi zan fada mashi cewa kinzo baki samay shi ba ai,
Tace tau nagode ni zan tafi sai dai in yadawo din zamu ga juna dashi don gidan mazan sunce suna son su san abinda,ake ciki,
Nace gaskiyane Umma yakamata su san abinda ake ciki hakana don su san matsayar su,
Nace Umma bari a kawo maki abinci tace barshi kawai zan koma ina ni ina zama gidan ku inci abinci ace kuma gotai,gotai dani nazo gidan ku na baje ina cin abinci,
Nace haba Umma ke da gidan ki tace gidan ku dai kudai keda gidan ku yanzu tunda har ankai ga korana,
Har kofan fita na kaita nai mata sai anjima tafita tana dan maganganun ta,

Sun safi matumin da,akatura su gurin shi a can kasar Ivory cost sun kuma gamsu da bayanin shi saidai abinda ya,daure masu kai mutumin ya iya hausan su sosai kamar ba dan kasar ba,
Yagane suna mamakin shi sai yace nima mutumin Nigeria ne ai zamane yakawo ni nan na zauna,
Amma ni dan kasarku ne sunji dadin zama gidan mutumin kuma sun sha daula a gidan sosai,
Yai masu hanya yadda ya dace su samu saukin kaya haka yasa su tunanen in har suka samu shigo da,motocin su ba karamin dagawa zasu yiba wanan karon kafin su dawo sunyi phouna sosai don sunji dadi bakunta a gidan mutumin,
Ya fada masu cewa zai shiga saudiya don aikin hajji saboda haka ba lalai ne su dawo su samay shi ba a garin,
Sai shima hamza ya ce shima yana ganin in yasamu hali yana son zuwa bana saudiyan don akwai business din da yake son yafara yi a can,
Duk process din da mutumin ya tsara,masu haka suka bi cikin ikon Allah sai ga motocin su da masusukan da suka,saro sun shigo Nigeria hankali kwance ba kamar yadd in zasu shigo da kaya suke shan wahala,ba,
Yai muna tsaraba masu kyau irin na mutanen kasar yazo muna dashi, kowa har yaran duk mun samu tsaraban shi,
Abinda ya,daurewa Biba kai yanzu shine duk kayan da take dasu a cikin kayan lefen ta,sai taga nima ina dasu abin sai ya daure mata kai tare da bata haushin haka,
Watau don son da yake min ma harda lefe ya hada min irin nata kenan, ko ranan da yadawo wani lace da take kuri dashi nata blue nawa light pink nasaka ajikina,
Ta hadiyi rai har tagaji gashi bata,san hakane ba duk ta mulke nata kayan ita, niko yanzun ne ma nafara,sawa,
Sai wanan dawowan Biba taga cikin dake jikina tai matukar yin shock sai dai bata yabbatar da,zargin taba sai lokacin da,taga yadan rugumoni zuwa jikin shi yana cewa ya kuke ya kuma girma,
Murmushi nayi kawai tare da karban jakar kayan shi na,shiga dashi daga ciki,
Inda take zaune tana dariyan yake ya nufa yana ce mata tare da riko hannun ta wai duk nauyin cikin ne ya hanaki taro na yau,
Tace ai kasamu taro gurin dayar mai cikin hmmm lalai ma ashe ko akwaita gidan nan ,
Daki ta shiga tafara kiran uwar ta hankali a tashe take fadin Mummy yanzin ashe makirar matar nan cikine a jikin ta amma ta boye min,
Uwar tace ta boye maki ko suka boye maki don ai mijin yasani amma bai taba fada maki ba,
Har da kukan ta,wai wani muna funcine nake shirin kulla mata in bashi ba yaya za,ayi nai ciki amma bata sani ba sai yau da Allah ya nuna mata,
Dakyat uwar ta shawo kanta tare da bata hakkuri akan haka din, cewa tafita batuna taji da zancen cikin ta kawai ta,samu Allah ya rabasu lafiya da cikin dakd jikin ta in diya ne bagashi zata,fara haihuwa dash ba to may zai damay ki tun da likita yafada maki namiji zaki haifa,,
Kin ga ita ko diya mata take ta zubawa ko yaushe sai fa in kin so ki tayar da hankalin ki,
Bayan kwana biyu kuma sai ga zance tafiyan su Ummi na saudiya ya bullo ranan kan hauka tai mashi yana daki kwance ta samay shi da kukan ta,wai yaci amanan ta yaya zaikai iyayyena makka ita yaki koda daukan uwarta yakai,
Yace ummmwumm ashe son kaki har ya kai can sadiya to ban biya ba,sai ki kaini kara duk inda zaki kaini, don ni fitinan ki wallahi ya,ishe ni Biba,
Tafada tai zage zags takiramu da macuta azzalumai mayaudara da dai sauran su harda fata tayi Allah yasa in su Ummi sun tafi can zu mutu,kada su dawo,
Agidan su Ummi ma sai bakin ciki da takaicine ya rufe su mama saude tafara tsegumi wai kilama asiri Ummi tai mata sukaki yarda ya auri kubura don Ummi ta bashi ni
Baba yacewa mama yaukuma saude dan maysiyanta da kukace a,wancan lokacin don kinga yanzun Allah yai ikon shi a kanshi shine zaki fadi hakan,
Umma kan tayi iya nata jidalin tagaji tai shiru kuma tasa shi sai yaiwa Sa,a duk abind ta lissafa ma shi ba bata lokaci sai da yasayo komai,da,ta,lissafa maShi yasayawa, Sa, datu din,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA

Download complete TXT · Novel page