Showing 30001 words to 33000 words out of 39684 words
Nuhu na saki matata Zainab saki uku in ta haihu ta sami miji tayi aure...." Wani murmushi me ciwo Dad yayi cikin tausayin ɗiyar tasa yace “Ai Shikenan muje gida Allah yasa hakan shine yafi alkhairi" jan motar yayi sukabar ƙofar gidan ta rushe da kuka me ciwo ta faɗa jikin Dad jikinta na rawa tace “shi...Shikenan Dad ya rabu dani... Wayyoh Allah na shiga uku meye yasa tun lokacin da bansoshi ba yaƙi rabuwa dani Saida ya koyamin soyayyarsa Dad waye zai mayemin gurbinsa?...."
Rufe mata baki yayi yace “Ki daina Mamana banason kukanki nasani kin tawaya a rayuwarki insha Allahu yanzu zaki samu gatan uba da kika rasa a baya Mamana ki yafemin wlh inasonki bansan dalilin da yasa na kasa janki a jikina ba" shiru yayi yana furzar da iska don ya lura bata da niyyar daina kukan shi kansa yasan kukan zai rage mata damuwa inya hanata ma baiyi mata adalci ba daga Rijiyar Zaki zuwa Sallari tafiya ce ba wata me shahararren nisa ba itakam batasan sunzo ba Saida taji ya buɗe mata kofa ya kamo hannunta suka shiga gidan duk da bata cikin nutsuwar tantance abubuwa tasan ba asalin gidan data sani bane.
Koda suka shiga wani ɓangare ya buɗe mata yace ta shiga ta tsaya tana kallon part ɗin komai akwai a cikinsa sosai ya haɗu nan ta zauna a bakin gado ya juya ya fice tare da cewa “Karkisa damuwar komai a ranki Mamana kiyi bacci kamar bakida wata matsala insha Allahu bazaki ƙara kuka ba"
Da wannan yaja mata ƙofa ita kuma ta kwanta badon tayi bacci ba saidon ta bawa zuciyarta dama tayi yawon ta yanda takeso.
Washegari da wuri ta tashi don dama ba baccin tayi ba ta fito a wanka kenan taji ana taɓa ƙofar tabada izinin shigowa wata mata ce da bazata wucce shekaru arba'in ba ta shigo da sallamarta da murmushinta tace “Jiya ina gurin aiki Daddynki ya kirani yake bani mummunan labari Zainab sai hƙr halin maza Bama ku sanya ƙafa ba nidai fatana karki sanya damuwa a ranki musamman da kike da tsohon cikin nan"
Sunkuyar da kanta tayi cikin ladabi ta gaishe da matar duk da batasanta a gidan mahaifin nata ba Hajiya Luba ta sani to ga kuma baƙuwar fuska wadda alamu yake nuna da bambanci tsakaninta da Hajiya Luba.
Kama hannunta Hajiya Sadiya tayi suka zauna tace “kina mamaki ko Ni baƙuwa ce shiyasa baki Sanni ba gabaɗaya satina biyu a gidan mahaifinki dama a satin nan nake cewa dashi ya kaini naga ƴata Zainab dayaketa bani labari tun kafin nazo to kuma Kwatsam wannan abu ya faru"
Zama Hajiya Sadiya tayi tanata kwantar mata da hankali Saida taga alamun ta ɗan saduda sannan ta barta tace zataje ta kwanta itama kwanciyar tayi zuwa takwas ne wayarta ta ɗauki ruri takai hannu ta duba sunan Deen ta gani gabanta ya faɗi idanunta ya ciko da hawaye wani ɓangare na zuciyarta na hanata ɗaga wayar wani na tunzurata ta ɗauka.
Ɗagawa tayi ta kara a kunnenta muryarsa a hautsine yace “Ina kike?" Mamaki tambayar tasa ta bata tace “Kak...kamar ya ina nake?" Cikin ƙaguwa yace “Wai meye yake faruwa ne na fito daga masallaci naje domin na duba ki saboda jiya na kwana ina mugayen mafarkai akanki na ishe bakinan na kira Umma tanamun wani zance dana kasa gane kansa please Zainab karku bugamin ƙwaƙwalwa don Allah meye yake faruwa wlh bansan komai ba"
Takaici ne da baƙin ciki yasata kashe wayar ta cillar da ita a gefe ta rushe da kuka me sauti cike da tunanin wannan salon rainin hankali na Deen.
Tana nan kwance mai aikin gidan tazo tace taje inji Dad ta miƙe ta fita tana daga hijjab ɗinta da bataso yake manne mata a ciki ta isa inda me aikin ta nuna mata ta tura ƙofar ta ishe Abba Umma da Ya Deen sai Dad da Hajiya Sadiya tunda ta shigo ya taso da sauri zaiyi mata magana Abba ya dakatar dashi ta hanyar daka masa tsawa dole ya nemi guri ya zauna.
Abba ne ya dubi Zainab yace “Uwar manya zo mana" cikin nauyin jiki isa gareshi ta shige jikinsa sai kuwa ta rushe da sabon kuka tace “Abba Ya Deen ya sakeni saki uku Abba me nayi masa ni bansani ba bansan laifina ba"...... Da mugun tashin hankali da kiɗima yace “Zainab! Ya isheki haka banason maganar banza ni mahaukacine da zan saki mace har saki uku kuma macen ma ke sannan da tsohon ciki.......
Please karki karanta in baki biya ba Nrml group 300 VIP 600 PC 1k acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko katin waya MTN ta WhatsApp number na 09013718241 ƴan Niger zaku turo kati Airtel
[10/21, 8:26 PM] AM OUM HAIRAN: *DH*
*_Paid page_*
Duk wanda yake gurin babu wanda bai kalleshi da yanayi na me taɓuwar ƙwaƙwalwa ba, Abba ne yace “Amma Shamsu kullum rainin hankalinka ƙaruwa yakeyi to idan bakai ka saki ba uban waye ya sakar maka ita talatainin dare harda rubutun takarda da zata zama shaida?"
Miƙawa Abba takardar Dad yayi shikuma ya miƙawa Deen jikinsa har rawa yake wajen karɓar takardar ya zubawa rubutun jikin takardar idanu hannunsa ya sake ta da sauri yanaja da baya yana girgiza kai cikin kaɗuwa yace “Wlh...." Katseshi Abba yayi da sauri yace “karka kuskura ka mayar damu ƙananun yara abokan wasanka idan Zainab tayi karya rubutu zaiyi ƙarya ne shi rubutu ai shaida ce saboda irin wannan abin da kakeson ka shigo mana dashi Shamsuddeen ka shiga cikin hayyacinka ka dawo nutsuwarka haihuwarka mukayi bai kyautu mu zama abokan wasanka ba saki ne ka saki Zainab da hannunka ka bata takarda kuma rubutunka ne saboda haka ta saku Allah yasa hakanne yafi zame mata alkhairi kaje kaikuma kayi abinda kakeso Shamsuddeen, tabbas ka bani mamaki kuma ka tozarta mu da tunanina yana bani ko dole mukayi maka ka auri Zainab zataci arziƙinmu ka raga mata ashe ba haka bane mun gode Deeni kwarai mun gode kaje ka rayu yanda kakeso"
Abba na gama faɗin haka ya fice Umma ta miƙe itama tabi bayansa wannan karon maganarta ta ƙare indai akan lamarin Deen ne, Dad ne ya dubi Zainab ya nuna mata hanya itama ta kama gabanta Hajiya Sadiya itama ta saita tata hanyar parlourn ya rage daga Daddy sai Deen to shima Dad tashi yayi da nufin barin parlourn don Allah ya sani matuƙa yaji ciwon sakin wulaƙancin da Deen yayima Zainab saidai yana tuna halaccin iyayensa gareta s lokacin da shi ya wofintar da ita ta rasa gatan uwa na uba ma ta rasa sune suka jata a jika suka gatantata har ta manta da duk wata nau'in damuwa a cikin rayuwa to shi meye zaisa saboda ƴar da iyayensa sukayiwa gata ya wulaƙanta musu nasu?
Da wannan yake tausar zuciyarsa tun ɗazu yakewa DEEN kallon rahma, yanzun ma Deen riƙe ƙafarsa yayi muryarsa na rawa yace “Daddy ka yarda dani wlh ban saki matata ba a tambayeta a nutse zata faɗi gsky wlh Dad indai Zainab bata faɗi gsky ba to dama shirya abinnan tayi amma Ni a jiya tun sallar Isha bamu sake haɗuwa ba sai yanzu a gidannan"
Murmushi Dad yayi ya dafa kansa yace “Ɗana taya rantsuwarka zatayi aiki bayan ka rubuta takarda ka bata kuma kaima ka karanta ka gani ko kuwa ba rubutunka bane a jiki ne?" Ɗagowa Deen yayi idanunsa ya kawo ruwa yace “Rubutu nane Dad amma ba hanuna ne yayi ba na rantse...." Rufe masa baki yayi yace “karka rantse Shamsu kaje kaci gaba da rayuwarka Zainab ƴar uwarka ce nafi kowa son naganka tare da ita saidai ita zanen ƙaddarar bawa so kulawa da gata basa canza shi Deeni aure shi kadai ne yake da siffar mutuwa ya dawo idan akwai sauran zama tsakaninku sai Ubangiji ya kawo sanadin daidaito ta hanya da kuma lokacin da ba'a zata ba"
Tsallakewa yayi ya fice daga parlourn da sauri ya koma part ɗinsa.
Deen kasa tashi yayi daga gurin cikin rashin sanin abinda ya dace yayi abu ɗaya ya riga ya sani kuma ya ƙudurce a ransa bai saki matarsa ba kuma babu wanda ya isa ya raba shi da matarsa.
Da wannan ya tashi daƙyar ya nufi gidansa part ɗin Zainab ya shiga ya fara birkitashi kamar zautacce kome yake nema oho haka ya gama hargitsa komai dake gidan kafin ya nemi guri ya zauna ya dafe kai yana huci yana furta “hasbunallahu wa ni'imal wakil" yanayi yana dukan kansa so yake ya tuna sanda ya shigo part ɗin da dare har yayi wannan aika²r ya kasa dole ya miƙe yana layi kamar wanda yasha giya ya isa part ɗin Nafisa da tun shigowarsa tagansa tana jiran taji wanne labari zaizo mata dashi duk da tasan komai amma tanajin tsoron kada aiki ta ya lalace kamar yanda ya saba lalacewa indai akan Zainab ne.
Yana shigowa ta tare shi tana cewa “Wani abu ya faru ne Shamsu naga alamun tashin hankali a tattare dakai?" Kallonta yayi idanunsa ya kaɗa yayi jawur zuciyarsa na neman faso ƙirjinsa yace “Na haukace ne Nafisa wai don Allah da gaske Ni mahaukacine haukacewa nayi?"
Da rashin fahimta take dubanshi tace “Ni don Allah kayimin bayani sai ninkeni kakeyi baibai" kama hannunta yayi yace “jiya da dare a ina na kwana ne?" Da zaƙuwa tace “a nan part ɗin mana wani abu ya faru ne?" Da daren Kinga na fita ne?" Ya sake jefa mata tambayar. Kasa bashi amsa tayi sai hilatarsa data fara ya dubeta yace.
Dana fita sallar asuba naga gidannan a bude nayi mamaki so bayan na dawo hankalina yaƙi kwanciya shine na shiga part ɗin Zainab shima na gansa a buɗe har ɗakinta batanan wannan tasani fita na nufi gidanmu batacan dukkanmu hankalinmu ya tashi muna tsaye zaman jiran tsammani Daddy mahaifin Zainab ya kira Abba yake sanar dashi jiya da dare wajen ɗaya yazo nan gidan ya tafi da Zainab sakamakon sakin da nayi mata Nafisa da yaushe naje ɓangaren Zainab har na saketa kuma yanzu na kasa tunawa?"
Da alamun mamaki tace “Amma dai Shamsu wannan lamari naka da mamaki to ai koni jiya bayan ka dawo dana tambaye ka ina kaje cemin kayi kaje ka saki Zainab ne har nake cewa dakai akan me zaka saki mace da tsohon ciki kaikuma kacemin ba damuwata bace na ƙyaleka don bansan abinda kakeji bane...."
Katseta yayi da cewa “Ƙarya kukeyi wlh bani bane Nafisa karkimin haka kinsani jiya tunda na kwanta sau ɗaya na farka don Allah kibada shaidar ban saki Zainab ba kar...." Dakatar dashi tayi da cewa “Aa fa Mal karka wani dameni da maganar wata sakakkiyar matarka kaine da kanka kace bai shafeni ba don haka na barshi a be shafeni ɗin ba" tafiya tayi ta barshi da sakakken baki ya zube a kujera yana cewa “Allah don Allah Allah ka tabbatar min da ban saki matata ba wlh bansan sanda na saki Zainab ba Nikam ko da gaske na haukace ne?" Daidai lokacin wayarsa ta shiga bugawa ya zarota da sauri ganin number Abba ya ɗaga yace “Abba kun bincika kun gano gsky ko? Zainab nasan tanasona bazata yarda na Cutu ba Abba bazamu jure...." Dakatar dashi Abba yayi da cewa “Muna Lugard Hospital Yanzu haka Zainab ta haife maka ɗanka namiji....
_Kuyi hkr da yanayin typing ɗin an very busy wlh_
Please karki karanta in baki biya ba Nrml group 300 VIP 600 PC 1k acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko katin waya MTN ta WhatsApp number na 09013718241 ƴan Niger zaku turo kati Airtel
[10/22, 8:48 PM] AM OUM HAIRAN: *DH*
*Paid page*
Miƙewa Deen yayi tare da sakin wayar cikin wani yanayi me kama da gushewar hankali yace “Hai...ta haihu kuna nufin ta haihu?" Nafisa dake fitowa dauke da cup na madara ta tsaya turus tace “Wace ta haihu?" Da sauri kamar wanda yake tunanin mafita a gareta yace “Zainab..."
Dafe ƙirji tayi tace “Na shiga uku ya akayi ta haihu...." Da sauri ta gimtse bakinta duk da kallon da taga Deen yana binta dashi sai kuma tayi saurin waskewa tace “Banso ta haihu yanzu ba naso ace sai komai ya daidaita Shamsu yanzu fa Shikenan ta haramta gareka tunda dama iddar me ciki haihuwa ce kuma ta haih...."
“Ya isa don Allah..." Ya faɗa tare da miƙewa yace “Duk da ina tuhumar kaina da hauka nasan cewa in har da gaske haukacewa nayi na samu gushewar hayyaci to babu alƙalami akaina saboda haka har yanzu inada igiyoyi uku na aure akan Zainab...." “Ta yaya meye yasa kakeson wahalar da kanka da iyayenku ne nifa inada tabbacin kaine da kanka ka saki matarka babu wani ja ko jayayya saboda haka abinda yafi sauƙi kazo muje muga Bby"
Wata uwar harara ya watsa mata ya juya ya fice yana duba agogon hannunsa ɗaya da rabi na rana asibitin da Abba ya sanar dashi can ya nufa bai sha wahala wajen gano ɗakin ba da Umma sukayi karo ta kwaso kayan da aka ɓata zataje ta wanke ta watsa masa harara tare da jan tsaki ta wucceshi duk sai jikinsa yayi sanyi yaja ƙafafunsa daƙyar ya nufi ɗakin Hajiya Sadiya dake fitowa tace “Aa Shamsu ashe sun sanar dakai yanzu nake shirin kiranka" shafa kansa yayi yace “Abba ya sanar dani"
Sake gaisawa sukayi sukayiwa juna Barka ya shiga ɗakin ita kuma ta nufi pharmacy domin siyo magani Allah ya taimake shi ɗakin sai Zainab ita kaɗai tana zaune ta haɗe kai da gwiwa sai sauke ajiyar zuciya takeyi, ya jima tsaye kanta bata sani ba har Saida yakai hannu zai ɗauki yaron sannan ta ɗago Idanunta ya shiga cikin nasa gabansu ya faɗi tare ta janye idanunta daga kansa ya sanya hannu ya ɗauki yaron da keta baccinsa hankali kwance buɗe masa fuska yayi yana kallonsa yaron masha Allah kyakkyawa dashi bai ɗauko komai na kamannin Zainab ba hatta haskensa na ubansa ne.
Sake sauke idanunsa yayi kan Zainab yace “Na gde ƙanwata" daga haka bai iya sake ce mata komai ba tsayin lkc har Umma ta shigo ɗakin ta tsaya turus tace “Aa ikon Allah Shamsu baka gama ganin ɗan naka bane?" Yasan Umma sarai bata ɗaukar abubuwa da wasa hakan yasashi yin ƙasa da kansa yace “Ku fahimceni Umma...." Dakatar dashi tayi da cewa “Dakata don Allah ba sai kace komai ba in ka gama kallonsa ka ajeshi ko kaje dashi ina buƙatar kaɗaici da Zainab"
Kora da hali Umma takeyi masa ya sani don haka ya aje bbyn ya fita Matsawa tayi ga Zainab tace “Meye yace Miki?" Girgiza kai tayi alamun baice mata komai ba ta sauke numfashi tace “Ki nutsu kisan inda ke Miki ciwo Zainab Ni na haifi Deeni amma bazan iya cewa komai game da halinsa ba, Zainab duk abinda kake tunanin bazai iyaba iyawa yakeyi kija darajarki ki zama me zuciya duk mutumin daya nuna baya son kasancewa tare dakai kaima ka janye jikinka daga gareshi Zainab rabuwarki da Deen bazai zama ƙarewar nasarar ki ba indai akan wannan ne kike zubar da hawayenki to ki daina"
Kalami ta rinƙa bata masu sanyaya zuciya har Saida taga ta saki ranta sukaci gaba da karɓar Barka wajajen yamma suka koma gida basu jima da komawa ba Deen ya shigo da kayansa niƙi² duk yanda yaso ganin Zainab bai samu ba kasancewar Umma ta kasa ta tsare Deen ya shiga damuwar da bai taɓa shiga ba a haka akaci gaba da tafiya har zuwa ranar suna akayi sunan babu wani armashi duk da ba ƙaramar bajinta Deen yayi ba a haihuwar amma rashin walwalarsu yasa kowa ma walwalarsa tayi ƙaranci.
Sai ranar suna sannan ya yarda ya kawo Nafisa tun daga get ɗin gidan ta raina kanta ta dubeshi tace “Shamsu inane nan ɗin?" ”Gidansu Zainab ne" ya faɗa batare da ya ko kalli inda take ba bare ya fuskanci mamakinta ya fice daga motar itama ta fito tana kallon gidan tana jinjina mamakinta wai ashe mahaifin Zainab attajiri ne lallai dole ta sake ɗaura ɗammara ashe ita da ƴar attajirai take kishi bata sani ba.
Da wannan tunanin suka shiga parlourn da Bahijjah ta fara haɗuwa Bahijjah tayi mata kallon mamaki tace “Sai yau akazo ganin ɗan kenan mugun ya hana" murmushi tayi tace “Me zanyiwa kuma bayan wanda ya haɗa ya raba" murmushi itama Bahijjah tayi ta kuma cewa “Ai fah dama dake kinsan zaren ba kalar yadin bane dama shigar sauri ce ta baku ba cancanta ba irinki kece kika dace da....."
Shigowar Deen ɗin ce tasata haɗiye maganarta da cewa “Abban Abdullah Barka da isowa" dafa kanta yayi yace “kyautarki ta musamman ne Bahy ina Zainab ɗin" kallon ƙofar ɓangaren Dad tayi tace “Kanta ke ciwo batason hayaniya shiyasa Dad yabada umarnin ta koma can kuma kar wanda ya shiga" jinjina kai yayi ya juya ya nufi part ɗin ya murɗa ƙofar ya shiga s parlour ya ishe Zainab ɗin kwance dafe da kanta Saida ya isa ya tsaya a kanta sannan ta ɗago ta sauke idanunta kansa yayi mata kyau sosai cikin shigar tasa ta yau, ta haɗiye wani abu me ciwo ta juya masa baya ya zauna tare da dafa cikinta yace “Meye ya kawo ciwon kan?" Tsaki tayi ta miƙe zata fice daga ɗakin ya cafko hannunta yana shirin magana ta gasa masa wani masifaffen mari daya sanyashi sakin hannunta tace.
“A farko kana cikin mutane masu daraja da nakeyi dansu dole kona bari donsu tsakiya ka zama me ragaggiyar daraja ƙarshe darajarka ta dawo arziƙin aure and end kuma nakejin cewa babu wata sauran alfarma ko ƙima da kake da ita a wajena Shamsuddeen ina me umartarka fita daga rayuwata ta lumana ko kuma ka fita don dole.........
Please karki karanta in baki biya ba Nrml group 300 VIP 600 PC 1k acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko katin waya MTN ta WhatsApp number na 09013718241 ƴan Niger zaku turo kati Airtel
[10/23, 11:24 AM] AM OUM HAIRAN: *DH*
*_Paid page_*
*_45-46_*
Bawai ciwon marin da tayi masa ne ya hanashi motsi ba a'a ciwon kalamanta lallai da gaske Zainab ta ɗauki wannan lamari, yana kallo har ta fice daga ɗakin taja ƙofar da karfi shima gwiwa a mace ya nufo parlourn Abba