[9/1, 9:49 AM] AM OUM HAIRAN: *DEEN HOUSE*
_(Romantic story)_
_Oum Hairan_
_Paid book_
Note: _Littafin DEEN HOUSE it's paid book kinsan bazaki jurewa abinda ke cikinsa ba kada ki siya bare ki faɗamin ba sukari, idan kuma zaki siya ne don ki fitarmin dashi duniya kijamin bankaɗe kaɗe to kema adana kudinki👌🏼._
_1-2_
Tsugunne jikin famfon wata matashiyar yarinya ce da a ƙiyasin shekarunta ta baya bazata wucce sha bakwai ba, wasa takeyi da kifin tarwaɗar da yaketa wutsil-wutsil a cikin ruwa tana Murmushi ji tayi an rufenta idanu ƙamshin turaren da ya ziyarci hancinta zuwa cikin kwanyarta shine ya alamta mata waye ne tayi dariya kyawawan haƙoranta suka bayyana tace “Yaya Zain ka shammacemu nasan ko umma batasan da zuwanka ba yau" sakar mata idanun yayi yace “Zainab bakida wayo kekam yayyafi fa akeyi ke dama gayyar Limoniya kika zauna kike wasa da kifi anan gurin jibi yanda duk kika jiƙe jikinki"
Umma dake fitowa tace “Yawwa gara da Allah ya kawo ka koda yake kai dama karkatacciyar kukarta ne me sauƙin hawa dama dai DEEN ne ƙila da tuni ta nemi gurin ɓuya, sannu ashe kana tafe amma baka sanar damu ba?" Murmushi yayi yana kama hannun Zainab zuwa gindin famfon ya zazzaga mata klin ya kunna ya fara cuɗa mata hannun yana cewa “yar tsohuwar Babata wlh gudowa nayi daga camp kewarku ta dameni musamman wannan ƙwailar ƙanwar tawa koda yake naga babu laifi ƙirjin ya fara abin arziƙi....."
Turo baki tayi ta zame hannunta tana dira ƙafa tana cewa “Allah! Allah nidai Yaya Zain ka bari zan daina kulaka kuma zan daina ma ce maka Yaya....." Cafka yakai