Showing 36001 words to 39000 words out of 39684 words
ba saidai koma yane na amince ki ɗauketa in har zuciyarki zata yarda inasonki matsayin mata ta biyu gareni Zainab don Allah karkice a'a ki bani dama zan maye miki gurbin mijinki har ma da abinda ya kasa ina me baki tabbacin bazaki taɓa yin nadamar amincewa dani matsayin miji ba"
Wata uwar harara ta zuba masa ta buɗe motar zata fita ya riƙo hannunta ta juyo ta kalleshi shima ita yake kallo yace “please Zainab don Allah..." Fusge hannunta tayi tace “Bana buƙata" daga haka bata ƙara ko kalma ɗaya ba ta fice masa a mota ta shige gida, Mama tana ganinta tasan da matsala ɗan uwanta baiyi kasuwa ba, to shima bai shiga gidan ba ya juya ya nufi gidansa yana zuwa ya zube a falo Hadiyyah dake zaune ta dubeshi tace.
Da matsala ne hero?" Numfashi ya sauke ya share zufa yace “Da nasan ƙaddarar shan wahala ce zata kaini gidan yaya Sadiya da bazan je ba Haddy..."
Cikin rashin fahimta tace “Ƙaddarar shan wahala kuma?" Jinjina mata kai yayi yace “Bayan ke bantaɓa jin zan iya son wata mace ba bare nayi sha'awar haɗaki da ita duk da tayin da kika dade kinayi min na ƙarin aure bantaɓa sha'awarsa ba sai yau da ƙaddara tasa nayi tozali da Zainab ƴar mijin Yaya Sadiya, Haddy daga kallon farko naji yarinyar ta kwanta min kuma zuciyata ta karɓe ta sannan naji a jikina bazan samu matsala daku ba domin itama iyayenta dattijai ne, saidai kash nayi rashin saa Zainab bata karɓeni ba tama cemin bata buƙata ta...."
Katse surutun yayi saboda dariyar da yaji Haddy nayi masa ya zubanta idanu da takaici Saida tayi me isarta sannan ta saita nutsuwarta tace “Allah Ali gadanga ƙusar yaƙi, anya kai da kazo a zamanin yakin zaka rinƙa fita kuwa wannan sarewa da wuri haka saikace ba gwarzo ba? Nikam don Allah karka karyamin da gwiwa wlh tunda kana sonta nima inasonta kaga yanzu muyi istihara mu nemi zaɓin ubangiji sannan muyi addu'a ta kasance alkhairinmu baki ɗaya insha Allahu zamu sami mafita"
Itako gwanar tun daga wannan rana bata ƙara bi takan Bature ba ko Mama ce keyi mata maganarsa tashi takeyi ta rasa masifar son da takewa Deen da duk lokacin da wani abu makamancin haka ya bijiro takejin idan ta amsa batayi masa adalci ba amma kuma a zahiri bata iya bashi cikakkiyar dama kota tattaunawa ce sau ba adadi kamar yanda ya taɓa yi mata tayi itama zuciyarta nayi mata wannan tayin na tayi auren kisan wuta ta komawa mijinta su buga sabon salo da Nafisa.
Saidai idan ta tuna haramcin hakan sai jikinta yakan yi sanyi, yau Litinin ce tun safe ta haɗe kayanta cikin jaka da niyyar yin ƙaura zuwa sheka tunda ya rage yanzu saura kwana huɗu su shiga hidimar bikin Bahijjah, haka kawai tunda Zain ya dawo taji bata kaunar zuwa Sheka musamman da Daddy ya kirata yake faɗa mata ya yanke hukuncin haɗa aurenta da Zaharaddeen tun ranar taji tsanarsa ta ɗarsu a zuciyarta amma ta danne to shima bai wani bawa maganar muhimmanci ba gudun kar abinda ya faru a baya ya kuma faruwa duk da yasan cewa a yanzu babu aure tsakanin Deen da Zainab amma yana tsoron dawo da ciwonsa sabo, bawai don bayason Zainab ba musanman ma da yaga Abba bai karɓi maganar ba.
Itakam ansata a zullumi haka tazo sukayita hidimar bikin dake sun shiryawa bikin ba ƙaramin kuɗi sukaci ba wajen gyaran jiki tayi wani kyau da bata taɓa yin irinsa ba abinka da Black beauty duk da ba bakace sosai ba tayi kyau na gaske har taso tafi amaryar ansha shagali matuƙa.
Abba ne ya hanasu dinner wai gayyar sheɗan ce basu so ba musamman Zainab tayi gayyar ƙawayenta sosai duk da ya hanasu Saida suka saci jiki suka kayi hayar wani ƙaramin hall sukayi ƙawatacciyar dinner ɗin su yasu mata suna tsaka da dinner ɗin ne aka aiko kiranta ta fito tana dariya yarinyar da tazo kiranta ta nuna mata wata aniyar mota ta isa cike da mamakin waye yake neman ta itadai tasan duk waɗanda ta gayyata sunzo, tsayawa tayi gaban motar wata matashiyar mace ta buɗe ta fito da ganinta kasan hutu ya hudata duk da kyawun skin irin na Zainab Saida matar ta zame mata abar kallo.
Isowa tayi gabanta tanayi mata murmushi ta miƙa mata hannu tace “Barka da wannan lokaci Mrs Aliyu Ni sunana Hadiyyah Aliyu Bature" mamaki bai ƙara kama Zainab ba saida taga Les ɗin dake jikinta shine a jikin matar ta kalleta sosai tare da kawar da mamakin tanaji a ranta ƙila arashi ne kawai itama ta siya tace.
“Allah sarki sannu da zuwa saidai ban ganeki ba" tana rufe bakinta yana fitowa a motar, Hadiyyah ta nuna shi tace “Amma kin gane wannan ko?" Murmushi Zainab tayi me cike da faɗuwar gaba tace “Lahhh ashe kene matar uncle Bature sannu da zuwa sis" rungume juna sukayi Zainab ta janye jikinta tace
“Amma kayimin bazata banzaci kana ƙasar nan ba" murmushi yayi yace “Tunda na dameki kin kulle Number na ai dama dole kiyi mamakin ganina Zainab" kunya ce tasata yin ƙasa da kanta tace mu shiga sister na kaikam saidai ka jiramu babu gurin maza"
Gyaɗa kai yayi yace “Zan jira daga gobe ne ai" dukkansu sukayi murmushi Zainab batasan meye yake going ba suka shiga ta cika Hadiyyah da kayan tarkacensu na biki sun jima suna taɓa hira harda Bahijjah duk da babu wani sabo dake Hadiyyah wayayyiya ce ta saki jiki dasu sosai ƙarshe Bature barinta yayi sai da zasu tashi ta kirashi yazo ya ɗauketa suka tafi gida tana tsokanar Zainab tana cewa “sai mun zo ɗaukar amarya gobe" murmushi tayi tace “angonki bazai barki ba Aunty Haddy Abuja fah za'a kaita" sosai Hadiyyah ta cika da mamaki jin yanda Zainab take magana ya tabbatar mata batasan komai ba.
Washegari asabar ƙarfe 11:00am ƙofar gidan ya cika da mutane bayan Daddy yayi waliccin Bahijjah an ɗaura aurenta kan sadaki dubu ɗari Abba ya dakatar da kowa yace yanada wani daurin auren kowa sai yayi sosoro lokacin da waliyyan Aliyu suka taso akayi siga akayi komai Abba ya ɗaurawa Aliyu aure da Zainab akan sadaki dubu ɗari biyu da hamsin shi kansa Daddy ƙamewa yayi saboda tunda suke da Abba baitaɓa yi masa wata alama da take nuna bazai bawa Zain Zainab ba haka taron daurin auren ya tashi Zain ne ya fara shiga gidan ya kwatsa musu abinda ke faruwa Zainab miƙewa tayi daga zaunen da take ta fasa ƙara tace “Na shiga uku na lalace Abba meye yasa kayi min haka wlh Deen shine nakeso please wlh bantaɓa son Aliyu ba....
A karon farko ma kinyi biyayya Zainab bare yanzu naji a raina bazaki bani kunya bane shiyasa na zaɓa Miki mijin daya dace dake, Zainab Shamsuddeen ni na haifeshi yayi amfani da damarsa ya aureki a farko a lokacin da kike tsara rayuwa da ƙaninsa Zaharaddeen munyi bakin ƙoƙari wajen tausarki kuma kinyi biyayya to yanzu ga Aliyu nan Zainab na yarda da son da Aliyu yakeyi Miki na roƙeki kiyi masa biyayya don girman Allah kuma ki ɗaukeshi a matsayin mijin da bazaki taɓa nadamar samu ba sannan ki cire jin cewa zakiyi aure don ki komawa Deen na isa daku dukkanku to na datse igiyar zumunci ko waya idan ta haɗaku kuji a ranku kun munafurceni kuma Allah yanaji yana gani ki tashi ku tafi yau zai koma ƙasar da yake aiki"
Rushewa Zainab ta kumayi da kuka ta faɗa jikin daddy da yake shigowa ya rungumeta hawaye shima ya zubo masa yasan abinda takeji duk da sun rabu da Deen tanajin babu aure tsakaninsu amma bata taɓa fidda tsammani irin na yau ba sarai yasan Zainab na masifar son mijinta kamar yanda ya sani Deen yanason Zainab to amma ya zasuyi wannan itace ƙaddararsu hƙr dole zai bata shima"
Shafa kanta yayi ya damƙo hannun Bature ya damƙa nata a ciki ya buɗe baki a hankali yace “Kiyi masa biyayya fiye da wacce zakiyimin kiyi koyi da ɗabi'un Nana Faɗima ɗiyar ma'aiki (S.A.W) a gidan aurenki don Allah kada kuncinsa yafi farin cikinsa yawa game dake Zainab sanda aka aurawa Mahaifiyarki ni bata sona amma bata gaza wajen yi min biyayya ba har Allah ya karɓi rayuwarta, kema karki gaza kinji"
Dunƙule hannunta tayi lokacin da Bature ya janye ta daga jikin Daddy ya haɗata da nasa ta rintse idanunta tanajin wata faɗuwar gaba karon farko a rayuwarta data haɗa jiki da wani namiji ba Ya Deen ba, janyewa takeson yi ya sake riƙe hannunta Daddy dakansa ya kaisu airport tanata rusa kukanta har suka isa acan suka tarar da Hadiyyah ita da Dad da Mama da Umma suketa aikin rarrashin Zainab shikam Aliyu gabaɗaya jikinsa yayi sanyi bai taɓa rasa wani abu da yaso a rayuwarsa ba amma Allah ya jarrabeshi da tausayin wanda ya rasa abinda yakeso musamman da yaga halin da Shamsu ya shiga lokacin da aka tabbatar da ɗaura aurensa da Zainab.
Har suka shiga jirgi jirginsu ya ɗaga zuwa Canada bai iya cewa da ita komai ba Hadiyyah ce keta faman bata hƙr tana share hawaye tausayin Zainab ɗin takeji sosai wannan wacce irin rayuwa ce taso Zaharaddeen a karon farko Allah ya bata Deen ta koyi sonsa ta yarda ta mutu dominsa kwatsam wata ƙaddarar ta raba su ta zaɓa mata Aliyu....
A raunane yakai hannunsa ya kama hannun Zainab ɗin dake kwance a kafaɗar Haddy ya buɗe baki muryarsa na rawa yace “Kiyi hƙr babu yanda zanyi ne bansan meye yasa na kasa haƙura dake ba Zainab ki bani dama insha Allahu bazakiyi nadamar shigowa rayuwarmu ba".......
[10/30, 9:17 PM] AM OUM HAIRAN: *DEEN HOUSE*
*END*
Sun sauka lafiya daga airport ɗin aka daukesu ita da Hadiyyah aka kaisu gida shi kuma ya tsaya wani uzuri tunda dama nan ne ma'aikatar sa, tunda sukaje gidan Hadiyyah ke dawainiyar rarrashinta daƙyar ta samu tayi shiru ta rakata ɓangarenta gidane ginin turawa falo babba a farko sai kitchen a cikinsa gefe corridor ne guda biyu suna kallon juna cikin corridor ɗin wani parlourn ne madaidaici sai dakuna guda biyu kowanne da bathroom dinsa sai kitchen a gefe shima ba babba bane sosai amma an ƙawatashi sosai ya haɗu ya ƙawatu.
Su kansu ɗakunan sun gaji da haɗuwa, bathroom Hadiyyah tajata suka shiga tace kiyi wanka ki canza kaya sai mu samu abinda za muci kafin hero ya shigo, ganin girman matar ne yasata amincewa abinda tace Hadiyyah tayi murmushi tace “komsnki ya rigaki zuwa da sati guda inada tabbacin babu abinda zaki nema ki rasa kiyiwa ango kwalliyar sumar da megida" Batace komai ba ta turo ƙofar tayi wankanta ta lalubi alƙibla a wayarta tayi sallolinta da aka biyota ta zame kan tiles ɗin ta kwanta baccin gajiya ya ɗauketa.
Sai wajen dare ya fara shiga taji an murɗa jamlock ɗin an shigo ƙamshin turarensa ya tabbatar mata da Aliyu ne wannan yasa wani malolon baƙin ciki ya taso mata, tanaji har ya iso gareta ya sunkuya yasa hannu ya shafa gefen fuskarta yace “Baccin gaske ya fita daban dana wasa My Zeey kiyiwa Allah ki cire abinda ke ranki ki duba maslaharmu ke daina kukan nan haka"
Ya jima yana rarrashinta sannan sukayi shiru ya kama hannunta yace “Ki fito kuci abinci" muryarta can ƙasa tace “Ni... Ni na ƙoshi..." “Wht?" Ya faɗa da ƙarfi yana juyowa sai kuma ya fice babu jimawa Hadiyyah ta shigo ɗauke da kayan abincin, Hadiyyah akwai naci ita kuma Zainab batason nacin magoya hakan yasata tashi ta rinƙa danna abincin kamar magani, shigowa yayi ya zauna yana shigowa Zainab ta aje cokalin Hadiyyah tace “Kaga hero kasa ta daina cin abincin ko?
Saukowa yayi ya zauna kusa da ita taja baya ya damƙota ya haɗe ta da jikinsa ya ɗauki cokalin ya fara bata abincin tana turjewa tana komi bai ƙyaleta ba itako Hadiyyah dariya kawai takeyi mata tace “Tunda Banida ƙarfin yi Miki ɗura ai ga masu gurin nan sunayi Miki, Ni zuwa ma zanyi na kwanta na gaji da yawa bacci nakeji"
Tana maganar tana tashi tayi musu sallama ta fice zuciyarta na suya wani abu na taso mata tana ƙoƙarin danne shi sarai tasan tanason mijinta kishinsa shine yake taso mata. Tana shiga dakin ta zube a ƙasa tana kuka tana rokon Allah ya danne zuciyarta kar yabata dama akanta ya haneta dayin abinda zaisa mijinta ya canza mata kallo.
Addu'a takeyi sosai kan Allah ya cire mata ciwon kishi a zuciyarta ya sanya fahimtar juna da salama tsakaninta da abokiyar zamanta, su kuwa a ɓangarensu tunda Hadiyyah ta fita Bature ya rasa gane kan Zainab rarrashi ban baki duk yayi amma a banza daga ƙarshe tashi yayi ya fice mata daga ɗakin sannan ne itama ta miƙe tayi shirin kwanciya ta haye kan gadon taja bargo bayan ta kashe glub na ɗakin ta fara karanta wasiƙar jaki ta jima sosai kafin bacci ya saceta cike da mafarkanta barkatai na Deen data saba.
Cikin dare ne baccinta yayi nisa taji ana taɓata tayi miƙa tare da salati ta sauke ajiyar zuciya tana ƙoƙarin buɗe idanunta taji an zura hannu cikin rigarta tuni firgici ya shigeta ta buɗe Idanunta kan Bature daya kwantar da kansa a jikinta yana girgiza mata kai ta kuwa yi saurin lumshe idanunta hawaye ya tsiraro mata yasa bakinsa ya lashe yace “Nayi Miki alƙawarin baki farin ciki gwargwadon iyawa ta har ƙarshen numfashi na Zainab Soyayyarki jarabta ce gareni bantaɓa son wata ya mace daga haɗuwa ɗaya ba kuma bantaɓa jin bazan moru ba idan ban samu wata ɗiya mace ba sai kanki Please ki duba girman Allah da darajar aure karki jani a ƙasa, indai bake kika bawa kanki matsala ba baki da matsala damu inada tabbacin zaki rayu cikin farin ciki"
Da kalamansa ya kashe mata jiki duk abinda bataso faruwarsa ba Saida ya faru sosai Bature ya susucewa Zainab ya rinƙa shayar da ita zumar ƙauna me saukar da kasala da sanya gaɓoɓi bukatuwa da abokin rayuwa sun raya daren yanda Bature yake tunaninsa shi kansa yasan da gaske ya angonce Zainab ta bashi a jikinsa.
Shi ba mutum ne me ƙulafucin sex ba amma akwai bata lokaci wajen tanɗe² da lashe² basu sukayi bacci ba sai bayan sallar asuba sannan suka kwanta tana manne a ƙirjinsa haka bacci ya ɗauke su goma agogon dake dakin ya buga ya buɗe idanunsa da sauri ya saukeshi akai tare da fara shafa bayanta hakan yasata buɗe idanunta takai dubanta ga agogo ya kama kunnenta ya tsotsa yace “kin makarar damu" lumshe idanunta tayi ta janye a jikinsa yayi murmushi tare da miƙewa ya fita, lokacin da yayi wanka ya shirya domin tafiya gurin aiki tuni Hadiyyah ta gama komai a babban parlour ya risketa ya zauna kusa da ita yayi kissing ɗinta yace.
“Na gaji da yawa shiyasa ban tashi da wuri ba kin tashi lfy" murmushi tayi tace “ango ai dole ya makara kayi ƙoƙari ma daka tashi yanzu ya kwanan ƴar uwata" shafa fuskarta yayi yace “tana fitowa yanzu itama ta tashi Ni zan fita" kallonsa tayi tace “break fah" agogo ya duba yace “Na makara over kuci komai da nawa Inna dawo sai kowa ta bani kaso na" dariya tayi ta kalli inda Zainab ke fitowa tace “Har nayi fushi kinsa Hero a set kin manta dani yunwa na neman kayar dani" sunkuyar dakai tayi tana Murmushi tace mata “ina kwana" amsawa tayi da kin tashi lfy ya kwanan ango" ƙasa ta kumayi da kanta Hadiyyah tayi murmushi tace “amma dai Ni kikejin kunya bashi ba ko?" Ɗagowa tayi suka haɗa idanu dashi yayi murmushi ya miƙe ya fice sukayi break sukaci gaba da harkokinsu.
Cikin yan kwanaki Zainab ta saki jiki da Hadiyya saboda Hadiyyah irin mutanen nan ne masu shiga rai tanada hƙr da kawaici duk wani abu da tasan in tayishi zai cutar da wani gudun aikata shi takeyi a haka har suka cinye sati biyun ta basu badon Zainab taso ba sai don bata isa ba tunda ba ita ta bawa ba mijinta tabawa kuma ya karɓa.
Aikam ta taɓa taji cikin kwanakin har rama tayi ta rasa meye yasa ita a rayuwarta ta kasa sabawa da namiji indai zai nemeta to zatakejin faduwar gaba, wanda inda zata saba yaci ace ta saba tun a Gidan Deen kasancewar ba irinsu ɗaya ba a halitta da Bature Deen mutum ne mabukaci sosai shikuwa Bature tsaka tsaki ne bai fiye takurawa wajen sex ba amma yakan gajiyar da mace da salon wasannin soyayyarsa me tsayawa a zuciya iyakar jarabar feeling ɗin da Bature zaiji idan yayi sex ɗaya ya wadatar dashi na tsohon yini wani lokacin ma harda kwana.
Haka rayuwar taci gaba da tafiya walwalar iyalin tafi komai burge Zainab amma ita a ɓangarenta ta kasa sakewa dasu musamman Bature kullum hankalinta na kan Deen so take ta ciresa a lissafinsa amma ta gagara cirewa musamman da ko yaushe sukayi waya da Dad abu ɗaya yake maimaitawa gareta ta taimakesu ta zauna da mijinta lafiya wannan kalmomi na iyayenta yasa ko tayi tunanin aikata wani abu takan fasa.
Zuciyar mace da kyautatawa cikin shekaru biyu ta sake da mutanen da Allah ya canza mata matsayin abokan rayuwa sukaci gaba da tafiyar da rayuwarsu me daɗi babu wata damuwa dake damunsu data wucce ta haihuwa Zainab bata wata damuwa tunda tanaji a ranta tana da Abdallah.
Shekaru suka yita tafiya kwanaki suna turawa rayuwa na ƙara sakankancewa shekaru har suka tafi bakwai a lokacin ne kuma kuma Hadiyyah ta rinƙa rashin lafiya kullum batada lfy suna zuwa asibiti akayi check nata result ɗin farko ya nuna tanada shigar ciki na sati Uku wayyoh zo kuga murna gurin wannan Ahli aka rinƙa tattalin cikin nan komai na aikin gida Zainab ta ɗauke mata duk da taƙi yarda ta zauna ɗin haka suke aiki Zainab na cewa “nikam aunty da kin zauna kin huta ki daina wahalar mana da Bby" takanyi dariya ta ƙyaleta.
Ba afi sati ba itama Zainab ta kama masassara
Kafiyarta yasa taji a jikinta duk yanda sukaso suje asibiti taƙi yarda Saida yaga