Showing 9001 words to 12000 words out of 39684 words

Chapter 4 - Deen House By Oum Hairan

15 Dec 2025

6066

tace “Aa Umma babu komai" numfashi Umma ta daidaita tace “ok to gobe da safe kizo gida tunda shi bashi da hankali bare mutunci zaman gidan nasa ma kin daina" wata ajiyar zuciya me ƙarfi Zainab ta saki cike da farin ciki tace “da wuri ma kuwa Umma" tana aje wayar ta fara haɗa kayanta ranta da zuciyarta wasai tace “Allah zai rabani da ƙaya"
Shi kuwa ya gama yanke hukunci da kansa yayi dressing gurin da taji masa ciwon ya kwanta da sassafe kuwa ya ɗauki hanyar Garko cikin Sa'a ya tarar da Mal Tsalha ƙanin kakansu a zaurensa da Almajirai yana ganinsa yace.





“Ikon Allah mutumin birni kaine a tafe haka babu zato" murmushi yayi ya zauna suka gaisa Mal Tsalha ya dubesa da kyau yace “Mutumin birni ina marainiyar Allah Zainabu Allah sarki rayuwa jiya na gama kukan rashin mahaifiyarta Ubaidah mutuniyar kirki shikuwa Ibrahim saidai fatan Allah ya ƙwatoshi hannun wannan azzalumar mata daya aura sun cutar da Ubaidah matuƙa" shafa sumarsa yayi yace “Wlh Mal abin sai addu'a wannan mata ina ganin tsafi takeyi yanzu fa baba Ibrahim ko gidanmu baya zuwa yama ce ya yafe ƴar tasa bayaso. am dama Mal akan maganar Zainab ɗin ne ta kawoni......" Nan ya zage ya rinƙa shiryashi da ƙarairayi abinka da mutumin ƙauye take ya hau ya zauna yanata salati yace “Yanzu yarinyar nan haka ta zama ashe kaico Ni Ɗalhatu ina ganin rayuwa aikuwa indai da gaske kanasonta bazaka bar garin nan ba Saida igiyar auren Zainabu a hannunka yaron nan kaidai Allah yayi maka albarka ka taimaki maraici kayi zumunci"......
[9/13, 6:23 PM] AM OUM HAIRAN: *DEEN HOUSE*


*OUM HAIRAN*




_Free Page_


_Sakamakon bina PC da aketayi ana roƙona nayi sauƙi to nayi maimakon 300 na nrml group yanzu 200 ne VIP 600 yanzu 500 ne PC 1k yanzu 700 ne acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank or 3184512451 Fauziyya Tasiu First bank ko katin waya MTN ta WhatsApp number 09013718241 ƴan Niger zaku turo kati Airtel ne._




Itako Zainab garin Allah na wayewa ta shirya barin gidan daƙyar Nafisa tabarta ta fita akan cewa zuwa zatayi ta dawo, tana samu ta fita ta ɗauki ɗan sahu sai gida da murnarta suka rungume juna bayan sun gama murnarsu suka zauna ta fara karyawa da dumamen tuwan shinkafa miyar zogale tanata zubawa Umma santi sunayi mata dariya.
A haka Abba ya fito ya ishesu yace “Aa Kakale dama gurin mahaifinki nake shirin zuwa akan maganar aurenki da ɗan uwanki Zaharaddeen"






Rufe idanunta tayi tana Murmushi sukayi dariya Umma tace “Ja'irai gara dai da kuka haɗa kanku Allah yasa yin na Allah ne" Bahijjah ce ta amsa suka tashi suka kama aiyukan gida Bahijjah na bawa Zainab labarin sabon saurayinta Zainab na dariya itama tana bata labarin yanda takejin Ya Zain a ranta, yini sukayi basu da zance saina samari su, ƙarfe uku saura Abba ya shigo suna baje a falo harda Ya Zain suna hira, yanayin shigowar Abban ne yasasu miƙewa dukkansu don alama ta zahiri ta bayyana ba lafiya ba hakanan Zainab ta tsinci kanta da faduwar gaba.
Umma ce ta katse shirun da cewa “Abbsnsu ya akayi ne munga yanayinka na bayyana tashin hankali" zama yayi a kujera yana furta “Innanillahi wa inna ilaihirraji'un" abinda ya ƙara ɗaga hankalin kowa dake gurin can ya ɗago yace “Anya Umma ba'a canza mana Shamsuddeen a asibiti ba?" Da sauri dukka suka kalleshi ya sharce gumi yace “Da yazo min da shirmensa naƙi aminta yanzu haka yaje garko ya shiryawa Baffa Tsalha ƙarya da gaskiya harma me afkuwa ta afku" da sauri duka suka sake dubansa tare da cewa meye ya afku Abba?" Cikin tsananin jimami yace “Baffa Tsalha baiyi bincike akan gskyr lamari ba ya yanke hukuncin ɗaura auren Shansu da Zainab yanzu Alh Aminu ya kirani yakemin Allah ya sanya alkhairi bansan ta mece ba na tambayesa yake cemin ɗana Shamsu mana da aka ɗaurawa aure a masallacin juma'a yanzu....."




Tashin hankali wanda baasa masa rana, jiri ne ya ɗebi Zain duhu ya mamaye gurbin hasken da yake gani a idanunsa yayi ƙasa luuuu cikin yanayi na ficewar hayyaci abinda ya janyo dukkansu sukayo kansa da mugun gudu Abba na jijjigashi Umma na sallallami Zainab kuwa da Bahijjah banda kuka da kiran sunansa babu wani abu da sukeyi.
Ganin babu alamar tashi a tare dashi yasa Abba fita waje ya gyara parking motarsa yazo suka cicciɓeshi suka sanyashi a mota sai asibiti, da azama likitan ya fara dubashi ya daɗe yana dubashi kafin ya ɗago ya dubi Abba yace “Meye yaja masa wannan bugawar zuciya na lokaci ɗaya?" Shidai Abba ya kasa magana sai girgiza kai kawai da yakeyi, haka sukaci gaba da kulawa dashi can babban likitan ya ɗago yace “Akwai yuwuwar ya samu sauƙi amma dole ya kasance idan wani abu yakeso kodai abashi abin ko kuma a nesanta shi da abin"




Da yanayin damuwa Abba ya girgiza kai lamarin ya cakar masa da kai baisan wani abu daya dace yayi ba a yanzu dole sai ya samu nutsuwa.
A ɓangaren Zainabu kuwa tunda wannan baƙin labarin a cewar ta yazo mata take aikin kuka wannan wacce irin kama karya ce a duniya bata taɓajin mutum mara hangen gaba da adalci kamar Ya Deen ba ta faɗa masa bata sonsa ba shine zaɓinta ba maimakon ya ƙyaleta shine yaje ya bi hanyoyin munafurci shima Mal Tsalha saboda lissafinsa bai dire ba ya yarda ya ɗaura masa aure da ita to waima shi meye nacinsa da ƙulafucinsa akanta ne? A hankali takejin ninkin tsanarsa na ƙaruwa a zuciyarta tunda take bata taɓaji da ganin mutum me son kansa kamar Ya Deen ba Shikenan yanzu ya rusa musu tsarinsu ita da masoyinta? Shikenan yanzu Ya Zain yafi ƙarfinta.......




Sake rushewa tayi da kuka tana nadamar zuwanta duniya a mara saa mara rabon farin ciki, da gaske ta sarewa farin ciki cikin rayuwarta domin Ya Zain shine takejin zatayi farin ciki tare dashi itakam da Abba zai taimaketa da ya tursasa Ya Deen ya sawwaƙe mata auren nan na masifa.
Wannan sune kalolin tunane²n Zainab wadda ta gama sarewa da tsammanin farin ciki a rayuwarta ba itaba hatta umma wannan al'amari ya tsumata tama kasa furta ko kalma ɗaya me sunan samun sauƙi ranta yakai ƙololuwar ɓaci da wannan tantirancin rashin albarka da DEEN ya aikatawa marainiyar Allah tabbas zata nuna masa kuskurensa domin baitaɓa fusata zuciyatta irin hakan ba.
To shima Abba matuƙa ya ɗauki zafi da DEEN tunanin irin matakin da zai ɗauka akansa kawai yakeyi da wannan damuwar duk suka yini babu me wata walwala ga Zain a kwance a asibiti cikin halin jinya, wannan yini babu wani wanda zai ɗorar da daɗinsa jiran zuwan Deen gidan kawai sukeyi, har dare bai leƙosu ba harma daga ƙarshe suka rufe gidansu.




Ko a daren da sukaje suka kwanta Zainab banda aikin kuka babu abinda take yi kukan daya sanya mata wani ciwon kai me masifar zafi daya haifar mata da saukar zazzaɓi, Bahijjah banda aikin rarrashinta babu abinda take yi amma kamar tana zugata sabuwar tsanar Deen na ratsa sassan jikinta ranta na ayya mata abubuwa da yawa.
Wajajen ƙarfe goma wayarta ta fara neman agaji Bahijjah ta dauko ganin number Ya Deen yasata kallon Zainab daketa jan ajiyar zuciya tace “Yaya Deen ne ke kiranki Zeey" wani uban dogon tsaki taja batare da tace komai ba, kiran nasa yana katsewa wani na shigowa Bahijjah tace “Ki ɗauka kiji meye zai faɗa miki" banza tayi mata dama wayar ta ishe ta ta karɓa ta dannata a airplane mode tayi jifa da ita Bahijjah dake zaune ta dubeta da sauri a fili tace “Lallai kin ɗauka da zafi Zainab Ni a haukana sai nake ganin kamar ki zubar da makaman yaƙinki ki karɓi ƙaddararki a yanda tazo miki Ni banga abin ƙi a Ya Deen ba inma kyau ne ai yafi Ya Zain kuma kin riga kinsan halin Ya Deen babu wani abu da zai rushe wannan aure sai ikon Allah.




Har Bahijjah ta gama surutunta babu kalma ɗaya da Zainab ta tofa saima bargo da taja ta lumshe Idanunta irin abubuwan da suke faruwa tsakaninta da Deen suna mata yawo tana matse hawaye haka baccin wahala ya ɗauketa zuciyarta cike da tunanin halin da abin ƙaunarta Zain yake ciki.
Washegari ma bai zo gidan ba sai yamma daya taso daga aiki yana tunanin irin masifar da zaije ya tarar agidan gashi fir Zeey taki ɗaga wayarsa da ita ya fara haɗuwa a tsakar gidan tana amai ya tsaya a kanta cike da faɗuwar gaba ganin ramar dake tattare da ita a iya jiya da yau kaɗai dabai ganta ba, taji shigowarsa kuma taji ƙamshin turarensa amma ko ɗagowa batayi ba ta miƙe jikinta a mace ta juya da niyyar tafiya tabar masa gurin taji hannunta cikin nasa ta tsaya cak idanunta a ƙasa wani malolon baƙin ciki ya turnuƙe mata zuciya daya haddasa ma idanunta cikowa da ruwa lkcn da ya Matso jikinta yace “meye ya saki rama da amai?" Ɗagowa tayi tayi masa kallon daya sanyashi sakinta daidai lokacin da Umma ke fitowa a falo ganinsa yasata ɗaure fuska ya rusuna a ladabce yace “Barka da yini Umma ya gidan?"




Harara ta watsa masa ta nufi kitchen ta zubo shinkafarta da miyar ƙwai da haɗin salat ɗinta ta koma parlourn, murmushi yayi dama yasan za'ayi haka ransa na raya masa yabi Zainab daki yaga halin da take ciki wata zuciyar ta haneshi ya nufi parlourn ganin Abba a zaune yasashi sallama tare da shafa kai Abba ya amsa tare da cewa “Aa Shamsuddeen dama kana gari" sake sosa kansa yayi yasan magana Abba ya fada masa yace “Wlh Abba na shiga busy ne jiya yau kuma na tashi da wani aikin gaggawa" murmushi Abba yayi yace “Hakane to ya aikin ince dai wanda aka fyeɗe ɗin ya tashi" yanda Abba keyi masa magana kamar ba komai ya bashi damar sakin jikinsa suka fara tattaunawa can ya shafa kai yace “Dama Abba inason idan zai yiwu a sanya ranar da za'ayi biki da abubuwan da ya kamata ayi mata game da lefe da sauran abubuwa in yaso sai abani list"




Zubansa idanu Abba yayi kamar bai fahimci komai ba yace “Wacce Zainab ɗin fah?" Sunkuyar dakai yayi yace “Kakale" murmushi Abba yayi yace “Au toto hakanne ai dake kasan Zaharaddeen ɗin bai samu aiki ba so nake na buɗe masa shago a kasuwa inyaso sai ayi maganar auren koda yake kaima kace wani abu za'ayi yanda kace...." A sanyaye Deen ya ɗago yace “Abba nayi tunanin Mal Tsalha ya kiraka jiya yayi maka bayanin yanda abubuwa suka juya wlh Abba nafi Zain buƙatar Zainab nafisa cancantar mallakarta shiyasa da naga kun kasa fahimtata naje na sameshi shi ya fahimci abinda naso ku fahimta harma yabani damar bada sadaki aka ɗaura aure na da ita"




_Alhmdllh ina gdy masoya da addu'a ido yayi sauƙi sosai sai gdyr Allah kuma na gode da uzurin da kukayimin musamman ƴan paid group._
[9/18, 8:08 PM] AM OUM HAIRAN: *DH*


_Paid page_



_15-16_



Murmushi Abba yayi yace “Toh aishe haka akayi ai bamu da masaniyar komai tirƙashi yanzu kuma gashi bakaine zaɓinmu kuma raayinmu sannan gwaninmu akan Zainab ba itama kuma ba kaine zaɓinta ba, ya kenan za'ayi?" Tunda Deen yaga yanayin da Abba yake magana dashi gumi ya soma karyo masa tabbas ya shiga uku har tara ma domin babu wata alama dake nuna Abba zai fahimceshi ɗagowa yayi yakai dubansa ga Umma dake zaune tana juya remote a hannunta yace.
“Umma...." Ɗaga masa hannu tayi Idanunta akan TV tace “Karka sani a lamarin da ban isa ba kayi yanda kakeso Shamsuddeen kaima Allah zai maka yadda ya dace gadai Zainab can kwance a ɗaki dalilinka ga kuma Zaharaddeen can a asibiti shima duk saboda kai"




Cikin kaɗuwa yace “What Umma wanne asibitin?" Kallonsa tayi ta kawar dakai tare da miƙewa tabar gurin ya jima zaune zuciyarsa na kai kawo sannan ya miƙe a saluɓe yace “Shikenan Abba bari naje na duba Zainab sainaje na gano Zaharaddeen ɗin" har yakai bakin ƙofa ya tsinkayo Muryar Abba yana cewa karka shiga ɗakin yaran nan sannan shima Zaharaddeen ɗin ka share ba sai kaje ba zaiji sauƙi" cak ya tsaya gabansa na faɗuwa da gaske su Abba sukeyi rausayar dakai yayi ya fice jikinsa a mace.
Yaji kamar zai fita yaji bazai iyaba ya koma ya buɗe ɗakin har yasa ƙafarsa ya jiyo Muryar Umma na cewa “karka shiga dakin nan ka ficemin a gidannan kafin ka fusata zuciyata"




Baiyi mata musu ba bare gardama ya fice a gidan ya jima zaune a mota daƙyar yaja motar ya nufi gidansa, yayi parking ya fito ya nufi cikin gidan baitar da kowa a parlourn ba hakan ya bashi damar nufar ɗakinsa yakai step ɗin ƙarshe Muryar Nafisa ta katseshi da cewa.
“Dama kai nake jira Deen ashe haka ne abin yake kaima duk sunanku ɗaya da sauran maza Deen Ni ka munafurta ashe dama daka kawomin Zainab ka kawota ne a matsayin kishiyata? Ka cutar dani kuma zaka tabbatar da ka cutar dani bashi kaci wlh, bazan hanaka Zainab ba amma fah ka jira zuwan da zowar" murmushi yayi ya juyo ya dubeta yace “Karki ɗaga hankalinki kisawa kanki wani ciwo Nafisa banyi Miki alƙawarin zan zauna dake ke ɗaya ba"
Bata bashi amsa ba ya banko ɗakinsa ta cije leɓe tare da yarfa hannu tace “Mu zuba mugani wlh kowa yayimin sai nayi masa"




Tunda ya shiga ɗakin yake kaiwa da komowa ya kira wayar Zainab tafi sau ɗari daga jiya zuwa yau bata ɗagawa abin ya fara girmewa tunaninsa zama yayi ya tsara mata test tana kwance tana zubar hawaye taji shigowar saƙon ta juya ta ɗauko wayar ta buɗe saƙon ganin number sa yasata jan tsaki ta sake lafewa a gadon zuciyarta na tafarfashi Zain kawai takeson gani gashi yafi ƙarfinta likitansa yace ba'a buƙatarta kusa dashi wannan abu nayi mata suya a zuciyarta inda tasan wata mafita da tabi don ganin muradinsu ya cika tunda itama Zain shine zaɓinta.
Ƙarar shigowar wani sakon ce tasata jan tsaki ta buɗe cikin ƙunar zuciya ta fara karanta sakon.
_“Nasani Ni me laifine a wajen ki ƙanwata saidai ina mai kwantar dakai domin baki hƙr ki karɓeni matsayin zaɓin da Allah yayi Miki ba wanda kika yiwa kanki ba Zainab kada ki wahalar dani inasonki da gaske wlh ba sha'awa bace kamar yanda kike tunani saidai inaji a raina kece zaki iya dani a yanzu da nasan kaina, Zainab ƙarfin feeling nawa ya zarce tunaninki kinsani tunda kin ɗan san wani abu game dani please ki bani dama don Allah ki manta da wani Zain"_



Wani mashin takaici taji ya caki zuciyarta batasan sanda ta ɗauki hannu ta rubuta masa _“Yafika cancanta azzalumi me son kansa"_ duk da ba kalma mai daɗi ta faɗa masa ba Saida yaji sanyi a zuciyarsa yaja numfashi tare da rungume wayar a ƙirjinsa yanajin ƙamshin turaren challenge da Zainab tafi amfani dashi yana ziyartar hancinsa har wani lumshe idanu yakeyi saboda shauƙin son kasancewa da ita.
Wannan dare baiyi bacci me daɗi ba Nafisa kishi ya hanata zuwa gareshi Zainab kuma dama ita yasan sai yayi aiki akanta sauƙinsa ɗaya dake tana zuwa b.u.k zai samu damar ganinta in yaso.




Washegari Zainab ta sake tashi jikinta yayi tsanani don ko tsakar gida bata fito ba wajajen ƙarfe 10:00am ya shigo gidan cikin Sa'a kuwa babu kowa sai Zainab da Bahijjah a ɗaki hakan ya bashi damar shiga ɗakin da sauri, ganin yasa Bahijjah miƙewa tana gaisheshi ta fice yaja ajiyar zuciya ya matsa ga Zainab dake kwance tana numfarfashi ya janye hijjab ɗin data ƙudundune da sauri ya birkitota yana cewa “Subhanallahi zazzaɓi me zafi haka Little meye kikasa a ranki haka?"
Baisan ta farka ba Saida yaji tana ƙoƙarin janyewa ya ƙara ƙanƙameta yace “Please ki bari meye yake damunki mijinki likita ne fah...." ,“Ubanka ke damunta Shamsu kaji ko nace harda uwarka duk suna damunta zaka tashi ka fice ko saina rotsa maka kai da muciya...." Tana maganar tana ƙarasa shigowa ɗakin ganin tabarya a hannunta baisa ya firgita ba saima ƙara riƙe Zainab daketa ƙoƙarin ƙwacewa da yayi yana shirin yin magana batare da yayi aune ba yaji ta kwantsama masa a ka aikuwa jini yayi tsartuwa ya fallatsa jikin Zainab wadda ta miƙe da sauri tace “Kay Umma meye haka...." Faɗuwarsa ce ta janyo Bahijjah dake shigowa ta saki ihu tace “shikenan Abba shigo kaga Umma ta kashe Ya Deen mukam mun shiga uku mun lalace...."



_Kuyi hƙr gwaji ne inason tantance yanayin ƙarfin idon ne🤗_
[9/20, 9:17 PM] AM OUM HAIRAN: *DH*


_Paid page_


_17-18_




Da gudu Abba ya ƙaraso ɗakin ya faɗi gaban Deen yana cewa “Ya subhanallah Amina garin yaya zaki bugeshi aka haka?" Itadai Umma saboda yanda take mugun jin haushin Deen juyawa tayi ta fice Abba ya kinkimesa ya fice cikin tashin hankali suka nufi asibitin da yake aiki ganin babban likitan nasu cikin critical condition yasa likitoci rufuwa akansa suka fara dubashi tare dayi masa bakin ƙoƙarin wajen ganin matsalar bata girmama ba.
Har dare wajen takwas sannan ya farka ya ɗauki hannunsa ya ɗora akansa jinsa a daure yasashi tuno da abinda ya haddasa masa ciwon ya cije leɓe zuciyarsa cike da ƙunci to shi meye aibinsa don ya cikawa zuciyarsa burinta?" Motsin da yaji yasashi buɗe idanunsa ganin Abba ne yasashi kafeshi da manyan idanunsa ya tako fuskarsa babu yabo babu fallasa yace “Ya jikin?" A sanyaye ya amsa da cewa “Da sauƙi Abba" shiru taci gaba da gudana can ya kawar da shirun da cewa “kuyi hƙr Abba ku daina fushi dani akan Zainab wlh zanbata rayuwa me inganci fiye da wacce kukeyi mata tunani a gurin ɗan'uwana.....





Zubansa Idanu Abba yayi yana dariyarsu ta manya ya juya yace “tunda ka samu bakin magana Ni zan tafi gida mu kwana lafiya" Abba bai jira cewarsa ba yayi ficewarsa" ya furzar da iska ya yunƙura ya miƙe jiri na dibansa ya fice daga ɗakin nurse ɗin da sauran ma'aikata sunata yi masa sannu baya iya amsawa saboda zuciyarsa ba daidai take ba, a napep yaje gidansa koda shigarsa baiga kowa a parlourn ba kai tsaye ya wucce ɗakinsa ya kwanta ransa dukka a jagule yarasa gaɓar laifinsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login