Showing 24001 words to 27000 words out of 39684 words

Chapter 9 - Deen House By Oum Hairan

15 Dec 2025

6068

yini to kwana fah tunda kinsan bake ɗaya ke gareni ba?"




Narkar dakai tayi tace “Shikenan na hƙr amma inajin tsoron Allah Ya Deen" kamo hannunta yayi yace bari na cire Miki tsoron" ta ƙwace da sauri tana girgiza masa kai tace “aa zanma daina ji basai ka ciremin...." Numfashinta ne yayi sama saboda rufe bakin bazatar da yayi mata da nasa suka zube a kujerar ya nutsa hannunsa cikin sumarta ya lumshe idanunsa yana hautsinata tare da tsotsar lips ɗinta da salon da dole ta sakar masa jiki idanunta a lumshe taji bakinsa saman ƙirjinta taja wata ajiyar zuciya me ƙarfi ta tallafe kansa tace.
“Ahhh wash.... Ya Deen...." Janye bakinsa yayi ya ƙara sa zuge zip na rigar ya zubawa luntsuma²n nononta idanu sun ƙara cika sai ɗaukar idanu sukeyi, hannu yakai yana mulmula saman nipples ɗinta wani daɗi yana shigarta yanayin yana saukar mata da wani ni'imtaccen sinadari me kashe jiki, abin mace da miji sai Allah tuni Zainab ta manta da komai ta sakewa Deen jiki suka farantawa junansu duk da cewar iyakar sonta data jurewa Deen sosai yafi ƙarfinta wahala takesha a hannunsa kafin ya samu gamsuwar da yake buƙata yakan ɗauki dogon lokaci yana sukuwa kafin ya biya bukatarsa ita kam batada dogon zango da wannan takeyi laƙwas idan wani abu ya shiga tsakaninsu.




Bayan komai ya kammala ne sukayi wanka suka kwanta bacci sukayi me daɗin gaske da yamma yayi shirin tafiya gidan Nafisa ran Zainab baiso ba haka ta rakashi har wajen motarsa yayi kissing nata ya dubeta yana murmushi yace “Ki kula da kanki" murmushi tayi tace “kaima ka kula da kanka" dariya yayi yace “Zan kula dake fiye da yanda zan kula da kaina" langwaɓe kai tayi tace “are you sure Ya Deen?" Ɗaganta gira yayi ya shiga motar ya tayar ya jima yana kallonta sannan yaja motar ya fita suna ɗagawa juna hannu har ya fice daga get ɗin ta rufe ta koma ciki tana Murmushi zuciyarta wasai ko ba komai kalma me daɗi ma sadaka ce.
Gyara gidan tayi tsaf sannan ta nufi ɗakinta ta sake wanka ta ɗauro alwala ta tayar da sallar la'asar koda ta idar bata tashi a gurin ba ta ɗauki littafin Bulugul maram tana dubawa bayan ta duba abinda zata duba ta ɗauki hisnul muslum ta fara duba addu'o'i masu ƙarfin bawa jiki kariya tana cikin dubawar ne taji ana kwaɗa sallama a parlourn gabanta yayi wata muguwar faɗuwa tayi kasaƙe can bayan kamar wuccewar 2 minutes ta kuma tsinkayo Muryar mace ta kuma kwaɗa sallama tare da cewa ko babu kowa ne?"




Miƙewa Zainab tayi cikin firgici take tambayar kanta to waye ya buɗe gidan bayan tasan tayi masa key ta kulle ko ina? Sake kwaɗa sallamar da akayi ne yasata buɗe ƙofar dakin tana amsawa da Muryar tsoro ta nufi parlour gabanta na faɗuwa zubawa matar dake tsaye a parlourn idanu tayi tana ƙare mata kallo ta baya tsoronta na ƙaruwa ganinta sanye da baƙar doguwar riga har ƙasa ko ƙafarta ba'a gani kanta da hijjab shima baƙi, cikin in'ina Zainab tace “Sas...sannu..." Juyowa matar tayi abin mamaki sai taga matashiyar budurwa fara kyakkyawa tayi mata murmushi tace.
“Yawwa sannu kina lfy?" Ajiyar zuciya Zainab ta sauke tace “Zauna mana" guri ta samu ta zauna itama ta zauna suka gaisa ta miƙe tace “ina zuwa" kitchen ta shiga bata jima ba ta dawo ɗauke da lemuka da cincin da nama a tire ta ajiye mata ta koma ta zubo mata abinci ta kuma janyo Center table ta ajiye ta zauna tana Murmushi duk da har yanzu a tsorace take tace “Saidai ban ganeki ba ashe a buɗe nabar ƙofar wlh nayi tunanin na rufe shi yasa da naji sallamar na kasa amsawa saboda tsoro"........
[10/14, 8:35 PM] AM OUM HAIRAN: *DH*




AW



Tunda tafara magana wannan mata take kallonta har Saida ta rufe bakinta sannan tayi murmushi ta ɗauki inibi takai bakinta ta lumshe Idanunta tare da cewa “Ni sunana Shamsiyya ina zaune anan bayanku dani da duka dangina ina fatan banzo Miki da yanayi na firgitarwa ba" ajiyar zuciya Zainab ta sauke tace “aa kawai dai nayi mamakin yanda akayi kika shigo gidan tare da zaɓata ki kawomin ziyara a wannan lokacin"
Murmushi Shamsiyya tayi tace “Gidanki a buɗe yake ta ƙofa na shigo ziyara kuma kinsan yammata sunason su samu abokiyar shawara matar aure saboda su karu da juna kafin nasu lokacin yayi" jinjina kai Zainab tayi itadai har yanzu bata gasƙata cewa ƙofar gidanta a buɗe take ba hakanan sukaci gaba da hira da Shamsiyya har Zainab ta saki jiki da ita ba ita ta shirya barin gidan ba sai goma da rabi shima gani tayi Zainab tana hamma ta miƙe tace “to ƙawata zan tafi amma kafin na tafi gobe zakije makaranta da safe idan kin dawo zaki tarar da anyi Miki ɓarna a gidanki kada ki damu da ɓarnar zaayita ne domin janye hankalinki ki faɗa tarko Zainab akwai tarin maƙiya a cikin rayuwarki na farko kin sansu Matar mahaifinki itace ta saka rayuwarki gaba na yanzu ne baki sani ba wanda yanayi da lokaci bazai bani damar faɗa Miki su ba a yanzu, Zainab Ni ba mutum bace kamarki kamar yanda na faɗa Miki sunana Shamsiyya ina tare da mahaifiyarki kafin mutuwarta nayi ƙoƙarin bata kariya saidai ƙarfina baikai ba ajali bashida magani saboda haka nake baki shawarar ki nutsu ki kula da gabanki"




Tsoro ne ya sake ziyartar Zainab jin Shamsiyya tace ita ba mutum bace taja baya da sauri abinda yasa Shamsiyya murmushi ta buɗe hannunta takai hannu ta kama hannun Zainab inda aka huda ta barbaɗa mata wani magani ta saki hannun tayiwa Zainab murmushi ta ɓace ɓat abinda yasa Zainab razana da ƙara ja da baya da sauri tana dube² babu alamun wani mutum ya taɓa wanzuwa a gurin bayan ita aikuwa tsabar tsoro batasan sanda fitsari ya kwace mata ba tun da canma ubangiji yayita da mugun tsoro bare yanzu da abubuwa suketa zuwar mata saɓanin tunaninta.
Tafi awa tsaye ta kasa motsawa daga inda take tsaye har Saida taji wayarta tana ring sannan kamar me fasasshen ƙwai a ciki ta matsa ta ɗauka ganin number Ya Deen yasata sauke ajiyar zuciya ta kara a kunnenta amma sai ta kasa magana sai shine yace “Sarkin tsoro nayi tunanin kinyi bacci" numfashi ta sauke batare data iya cewa komai ba itakam batasan ta inda zatayi masa bayani ba saima mutum yaga kamar ƙarya kakeyi.
“Zainab ƙalau kike kuwa?" Ya faɗa lokacin da yaji maganarsa tayi tsayi babu amsa" sake aje fasali tayi tace “yanzu sai jibi zaka dawo gidannan Ya Deen Nikam wlh inajin tsoron kar wani abu ya sameni..."




Katseta yayi da cewa “To ya akayi wani abu ya faru ne bayan tahowata?" Ta buɗe baki zatayi masa bayani kawai taga haske ya keto ta window na parlourn ya nufota aikuwa ta saki ƙara ganin fuskar zaki cikin wannan haske ta kwasa da gudu ta fice daga parlourn maimakon hasken ya barta sai taga yanata binta tana gudu yana gudu abin mamaki tana zuwa ta ishe ƙofar gidan a buɗe batayi wata² ba ta fice daga gidan tanacin uban gudu dama ga unguwar sabuwa.
DEEN kuwa yanajin ta saki ƙarar ya miƙe da sauri ya fito Nafisa tana kiran shi amma bai ko juya ba sai cewa da yayi mata “Zainab ce take tsorata..." Taɓe baki tayi ta koma ta zauna taci gaba da kallonta a ranta tana cewa “tukunna ma" gudu yakeyi sosai saboda ransa ya faɗa masa zata iya ficewa aikuwa kamar yanda ya zata tun daga nesa ya hango mace tanacin uban gudu tana waiwaye a titin unguwar hakan yasashi rage gudun da yakeyi cikin tashin hankali yayi parking ya fito ya tareta ya rungumeta ta zube a jikinsa cikin gushewar hayyaci abinda ya janyo ɗaiɗaikun mutanen dake gurin suka taru ya sunkuceta ya sata a mota ɗaya cikin mutanen yace “Ya daga ganin baiwar Allah zaka sanyata a mota kanada alaƙa da itane?" Ajiyar zuciya yayi ba burinsa tsayawa ɓata lokaci ba saidai bai isa yabar gurin nan ba indai baiyi musu bayani ba hakanne yasa ya zuge clock na agogonsa ya nuna musu wani ƙaramin hotonsa da ita dake jikin agogon yace “Ƙanwata ce kuma matata gidanmu yana nan ƙasa kaɗan ina tunanin shaiɗanu ne suka shafeta ko kuma firgitata akayi a gidan shiyasa ta fito"




Yan son ganin ƙwaƙwaf saida suka ƙarewa hoton kallo sannan suka kalli Zainab suka tabbatar da itace sannan sukayi masa fatan samun sauƙi wani dattijo a gurin yace “Indai shafar shaiɗanu ce ka kaita gurin Mal me Alfadari insha Allahu kona ture kona maita ko ƴan iskan gari masu burin wahalar da bil'adama dukkan nau'in wata iska dai saita barta da yardar Allah"
Deen bai bawa maganar wannan mutumin muhimmanci ba yayi masa gdy tare da karɓar number wayarsa yaja motar suka tafi, bai nufi gidanta da itaba gidan Umma ya wucce da ita su Umma har sun rufe gidansu sukaji ana bugawa Abba ya taso ya tambaya waye Deen yace “Abba buɗe Shamsu ne" buɗewa Abba yayi ganinsa rungume da Zainab yasa Abba cewa “Ya subhanallah babu lfy?" Saida ya kwantar da ita yace “wlh Abba tunda na dawo taketa firgici nan ya kwashe komai ya faɗa musu, sosai Abba yayi mamaki ya kuwa rinƙa yi masa faɗa shidai baice komai ba nan Abba yace “Kaje kawai ita ka barta anan zuwa safiya muga abinda ya dace ayi mata"



Ya rasa meye yasa indai akan Zainab ne baya yarda da maganar su, yanzun ma sosa kansa yayi yace “Da nayi tunanin idan kaɗaici ne yake sanyata firgicin na gyara ɗayan part ɗin na gidan da Nafisa ke zaune saina haɗasu guri ɗaya" da sauri Umma tace “Aa Bama zai yiwu ba Deeni wannan matar taka baƙin kishinta yayi yawa bazan yarda ka haɗata da wannan sakaliyar yarinyar ta nakasata ba" cikin rashin kuzari yace “Amma Umma bawai ina musa Miki bane sai nake ga kamar idan suna taren zasu cuɗi juna kuma yau da gobe zatasa kowa ta haƙura...."
Katseshi Abba yayi da cewa “kaje nace Sarkin gardama zaka tsaya kuna tattakawa" miƙewa yayi ya dubi Zainab dake kwance yace “Ai bata farfaɗo ba Abba...." Kallon da Abba ya jefesa dashi shine yasashi jan kafafunsa ya fice. Abba ya tashi ya matsa kanta ya riƙe kanta ya fara tofa mata addu'a zuwa wani lokaci ta sauke ajiyar zuciya ta miƙe zumbur tana waige² ya kamo hannunta yace “Kakale ina zaki zauna mana" ajiyar zuciya ta sauke a karo na biyu ta zauna tare da ɗora kanta saman cinyar Umma ta rushe da kuka tace “Wlh Umma tsoratani akeyi a gidan Ni bazan koma ba"




Shafa kanta Umma tayi tace “Yanzu inane keyi Miki ciwo?" Kallon Umma tayi tace “Ni kaina ne kawai yake juyawa" sannu sukayi mata Abba yace “tashi kije ki kwanta" bata gardame ba ta nufi ɗakinsu na da ta kwanta kusa da Bahijjah yau tayi bacci me daɗi duk da cikin baccin tana ɗan firgita amma ba kamar kwana biyun can ba.
Da sassafe kuwa Deen yazo gidan lokacin Abba ya fita suka gaisa da Umma ya shiga dakin da Zainab ke kwance ya ishe ta baccinta takeyi hani'an murmushi yayi ya zauna kusa da ita ya fara jagwalgwala tayi ajiyar zuciya tare da miƙa yaja numfashi da ƙarfi daidai lokacin data buɗe ido sukayi 4 eyes ta sauke fasali tare da tashi zaune tanajan mayafin rufar zuwa ƙirjinta tace “Ina kwana" lumshe Lulu eyes ɗinsa yayi ya kwanto jikinta yace “Ke kika kwana ƙalau Ni da ciwon feeling naki na kwana zaro ido tayi tare da dariya tace “saikace ya kwana shi kaɗai naga akwai Aunty Nafisa a kusa dakai" tayi maganar da Muryar shagwaɓa.




Harararta yayi da sigar wasa yace “Ke ɗin nake muradi ita mun daɗe tare" rausayar dakai tayi tace “ai sai kaci ɗin...." Dira tayi a gadon da sauri tayi waje yayi dariya yace “Zamu haɗu ne zakiyimin bayani kinsan yanda haɗuwarmu take kasancewa ai"




Yana maganar yana fitowa daga ɗakin daidai lokacin Abba ya shigo suka gaisa yace “In anjima kazo ka ɗauki matarka nasa za'a kawo mata magunguna" tanajin haka zuciyarta ta karye tace “Allah Abba...." Rufe mata baki Abba yayi yace “Babu abinda zai faru insha Allahu kuma kada zuciya ta zargar Miki kowa kiyi imani da Allah da cewa babu abinda zai sameki sai abinda Allah ya ƙadarta zai sameki"
da waɗannan kalamai Abba ya kashe bakinta tayi shiru amma duk jikinta a mace yake saboda sosai ta firgita da gidan nata tun bayan dawowar shi ganin yanayinta ne yasashi fita batare da yace mata komai ba hakanan ta yini sukuku jikinta babu ƙwari ana kiran magrib ya shigo gidan a kwance ya ishe ta har yanzu bata da kuzari shima sai jikinsa yayi sanyi ya dubi Bahijjah yace.
“Tashi muje" cikin murna Zainab tace “Yawwa Ya Deen Allah dama Ni banason zama Ni kaɗai" murmushi yayi yace “ai masani kuyi sauri ina jiran ku a mota"
Hijjab ta ɗauka tasa Umma nayi mata dariya kunya ta kamata yanda Umma keyi mata tsiya tace “Da ance baaso jibi yanda take neman yin tuntuɓe" murmushi tayi tace




“Allah Umma ba haka bane Bama a gidana zai kwana ba Ni dama tsoro nakeji" bata ƙara kulata ba sukayi mata sallama suka fito yaja suka ɗauki hanya dake ɗan neman magana ne ba gidanta ya nufa ba gidan Nafisa suka nufa ta kalleshi da sauri tace “Ya Deen ina zamu?" Zan kaiki ku gaisa da ƴar'uwarki ne" ya faɗa batare daya kalleta ba itama bata sake cewa komai ba har sukayi parking a gaban gidan suka fito yana gaba suna binsa a baya yakai hannu ya cafko hannunta a haka yasa key ya buɗe gidan suka shiga banda kaurin turaren magani babu abinda harabar gidan takeyi itako Zainab banda ras-ras babu abinda ƙirjinta yakeyi a fili ta furta A'uzubillahi minasshaiɗanur rajim bismillahir rahamanu rahim Innanillahi wa inna ilaihirraji'un" ba Deen ba hatta Bahijjah Saida ta juyo ta kalleta, da sauri ta waske da cewa “Ya Deen gabana faɗuwa yakeyi" harararta yayi yace “ke kin samu matsala" da haka suka nufi ƙofar parlourn tana taka step na farko na shiga parlourn mararta tayi wani irin murɗawa data sata durƙushewa ta damƙe hannunsa da ƙarfi jikinta ya ɗauki ɓari ta sake damƙe hannunsa tuni ya ruɗe ya durƙushe shima yana tambayarta menene?..." Bata iya bashi amsa ba saboda jinin da taga ya fara malala a gurin cikin tashin hankali da yanayi na gushewar hayyaci tace “Ya... De..en ji...ni..."



_Paid book ne karki karanta in baki biya ba Nrml 200 VIP 400 PC 600 daganan zuwa 19 ga watan Rabi'ul Auwal in ya wucce zai koma kudinsa na asali biya ta nan acct details 0255526235 ko katin waya MTN ta WhatsApp number na 09013718241 ƴan Niger zaku turo kati Airtel_
[10/16, 8:12 PM] AM OUM HAIRAN: *DH*




Aml



_Paid book ne karki karanta in baki biya ba Nrml 200 VIP 400 PC 600 daganan zuwa 19 ga watan Rabi'ul Auwal in ya wucce zai koma kudinsa na asali biya ta nan acct details 0255526235 ko katin waya MTN ta WhatsApp number na 09013718241 ƴan Niger zaku turo kati Airtel_


Saboda dukan da kalmarta tayi masa bsisan sanda ya saki wata gigitacciyar ƙara me amo yace “Wht Zainab jini a ina....." Bai ida ƙarasawa ba saboda shi da kansa yaga jinin aikuwa zube ƙafafunsa yayi cikin gigita yace “Shikenan ya zube Zainab ya akayi haka...."
“Meye ya zube?" Yaji an faɗa ta bayansa ya juya idanunsa na kawo ruwa yace “Nafisa cikin Shikenan yanzu ɗan dana sanya ran samu nan da yan kwanaki yabi rariya, Innanillahi wa inna ilaihirraji'un..." Wani murmushi tayi tare da taɓe baki tace “Au haba to Allah ya kyauta yanzu akan ɗan tayin ciki zai zube kake wannan abin dubi don Allah abin kunya harda hawaye"




Bahijjah ce ta dubeta tace “Eh shi ai raguwa yayi kece kika ƙaru saboda baki samu ba shine bazaki iya ɓoye hassadarki ba asararriya kawai...." Mari ta ɗauke Bahijjah dashi ta ɗaga hannu zata rama Deen ya riƙe hannun yace “ba wannan ba Bahijjah muje a taimakawa wannan baiwar Allan in yaso in mun dawo sai kuci kanku"
Cije leɓe Bahijjah tayi tabi bayansa suka koma mota yaja a guje sai asibiti iya ƙoƙari sunyi don ganin cikin bai salwanta ba amma ina ƙaddara tariga fata yanaji yana gani cikin ya fita wata biyar abinsa ya girma sosai, da kansa yayi mata wankin ciki yana hawaye sosai yaji ciwon fitar cikin matuƙa saidai ba yanda ya iya.
Bahijjah ce ta sanar dasu Umma abinda ke faruwa Umma ta rinƙa faɗan ubanme yasa da yakaita gidan bai wuce da ita gidanta ba, Bahijjah tayi ƙasa da murya tace “To ai Umma bashima da niyyar maida ta gidan nata don naga anyiwa ɗayan ɓangaren gyara kuma dama naji yana cewa idan ya haɗe su hankalinsa zaifi kwanciya"




Takaici ne yasa Umma kashe wayarta tasan dama ba fasawa zaiyi ba tunda yayi niyya amma fah ita tana hango matsala zaman Zainab da Nafisa Zainab batada abin zafi komanta da sanyi take tafiyar dashi saɓanin Nafisa da dukkan alamu suka nuna komai zata iya aikatawa akan kishi.
Asibitin Umma ta nufa Deen yayi mamakin ganinta tunda shi yasan bai faɗa mata ba dake dare bai wani yi sosai ba ranar Umma ita ta kwana da Zainab washegari dole gidan iyayensu aka wucce da Zainab Umma ta rinƙa kula da ita a cewar ta wata biyar ai haihuwa ce, Deen baiso komawarta gida ba saidai shima yasan ya tsaya jayayya ɓatawa kansa lokaci zaiyi.
Sannu sannu Saida tayi wata guda a gida dake lfy ta samu tayi ƙiba tayi wani kyau na musamman Umma kuwa sai gyara yarta takeyi tare da nema mata tsarin jikinta a cewar ta kishiya baku tare ma ta jefeka balle duk motsinka akan idanunta.



Ranar data cika wata guda da dare yazo tana kitchen tana haɗa kunun gyaɗa ya shigo batasan yazo ba Saida taji Abba yana kiranta ta fito da cup a hannunta tana cewa “Naam Abba" shiga ɗakin Abba tayi da sallama Idanunta suka shiga cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login