Showing 84001 words to 87000 words out of 178785 words

Chapter 29 - Babu So Complete Hausa Novel

05 Feb 2025

32853

farkawarta kunnenta ya jiye mata wasu maganganun da harta ɗan fahimci abinda ke faruwa da akema jidalin tana wajen. Sai dai kuka take har muryarta bata fita, dan kunnenta ya jiye mata wasu manya-manyan zagi da Gwaggo Halima ta dinga jifan iyayenta da su. Gashi kuma Mamie na kuka ita da Aunty Mimi da babban yaron Aunty Mimi ɗin da Amrah. Tsabar kukan da take har amai tayi dan ji take kamarma ta mutu itakam ta huta, sai dai taci alwashin bazata taɓa zaman aure da Shareff ba itama.....
        Yayan Mommy da suke kira da Baba Ibrahim ne ya gama ƙarema kowa kallo, ganin babu Shareff a wajen ya tambaya. Anan ne Abbah ya mike ya nufi ƙofar bedroom ɗin Daddy. Zaune yake a kan sallaya hanunsa dafe da kansa dake matuƙar sara masa kamar zai faɗi, sallarma da ƙyar ya iya tashi yayita ganin lokaci zai shige dan har magtib ya haɗa. Jin muryar Abba ta sashi miƙewa da ƙyar ya nufi ƙofar ya buɗe, Abba dake kallonsa cike da tausayawa ya ɗan riƙo kafaɗarsa.
       “Yaya dai Babana kanne ke ciwo?”.
   A hankali ya iya jinjin kan nasa da ɗago idanunsa da sukai jazur ya ɗan kalli Abban. Murmushin ƙarfin hali yay ya maida kansa ƙasa ya risinar. Sannu Abban yay masa cikin tausayawa da riƙosa suka fito, kusan kowa sai da ya zuba masa ido a falon, shi kam bai yarda ya kalla kowa ba ya zauna kusa da ƙafafun Abba.
       Baba Ibrahim ya buɗe taro da addu'a, kafin ya fara magana cikin nasiha dajan hankalinsu akan muhimmancin zuminci a musulunci da zamantakewar rayuwa. Ya ɗora da faɗin, “Wannan aure a ganina abin alfaharine a gareku dan koba komai ya dunƙuleku ne waje ɗaya a matsayinku na jini guda. Fatan alkairi da ƙarfafa gwiwa kawai ya rage kuyi ga shi Shareffuddeen da nauyin ya rataya a kansa, amma ba wannan shirmen ba, gaba ɗaya yaran nan fa a ƙarƙashin ikonku suke, bazakuyi fatan bijirewar waninsu gareku ba in har kunada hangen nesa. Amma ke Nafisa minene naki na tada jijiyar wuya yaro ya saki matarsa??”.
       Mommy dake cike fam da nasihar Yayan nata ta saki kuka, “Wlhy ni dai Yaya bana buƙatar wannan haɗin, inhar nice na haifi Shareff to ina umartarsa ya saki yarinyar nan hakan zaifi mana zaman lafiya a gidan nan bana buƙatar wannan kwamacalar. Taya yana auren ƴar wajen Halima kuma ace ya auri wannan ai an haɗa husumane dan kishi ba wasa bane, babu wani zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya da hakan zai kawo sai ma wata sabuwar musibar. Kuma wannan ai munafunci ne, inba munafunci ba miyasa zasu ɗaura auren bada sanin kowa ba....”
      “ALLAH ya rabamu da ita. Ban san hujjarki na kawo wannan misalan ba, ba kuma na buƙatar sani, sai dai zan miki adalci ɗaya, shine jin ta bakin shi Shareff da ayanzu ikon zartarwa ke hanunsa akan matarsa, dan nasan su dai su Muhammadu da yardarsu da son su sukai wannan haɗin alkairi, kuma basu ɓoye dan munafuntarku ba sai dan kawo masalaha saboda sanin halinku. Dani kuma aka ɗaura auren tun waccan ranar kafin a ɗaura na ita ɗiyar halima da kike magana, domin kuwa da safe muka ɗaura na ita Juwairiyya iya mu kaɗai batare da sanin ko shi kansa Shareffuddeen ba, kafin a ɗaura na ita wannan yarinya Fadwa bayan sallar juma'a......”
  Baki ta buɗe zatai magana ya ɗaga mata hannu, dole tai shiru dan tana bala'in shakkarsa. Kallonsa ya maida ga Shareff da kansa ke ƙasa har yanzu bai ɗago ya kalli kowa ba, sai dai komai na shiga cikin kunensa kamar kowa, yayinda jawabin na Baba Ibrahim ke shigarsa tamkar almara, taya ya kasa gane an ɗaura masa aure da Anaam? Miyasa kuma aka zaɓi ɓoye masa shima?...... “Shareffuddeen!”. Ya kirayi sunansa cike da kulawa.
      Bai ɗago ba, sai dai ya amsa da “Na'am Baba”. Cikin dasashshiyar muryarsa dake tabbatar da baida lafiya. “Nasan kanajin komai basai na ƙara maimaici ba, iyayenka sun baka mata domin ƙoƙarin ƙara ƙarfafa zuminci a tsakaninsu da ku da suka haifa, shin kai ka amince da hakan a matsayinka na ɗa a garesu ko kuwa kanada ja tamkar mahaifiyarka?”.
      Tsitt falon yayi kowa ya zubama Shareff ido musamman Fadwa, Mommy da Gwaggo da Gwaggo Halima.........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[11/3, 7:19 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*




*_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718


*_36_*


.........Burin Mommy kawai ya kalleta amma yaƙiyin hakan. Tsahon minti guda baice komai ba yana satar kallon fuskokinsu ta gefen idanu. Tabbas ya hango tashin hankali kala-kala musamman a fuskar Mommy da Gwaggo da Gwaggo Halima da Fadwa, ya haɗiye busashen yawu da ƙyar tare da tattaro dukan ƙwarin gwiwarsa da jarumtarsa. Cikin dakewa ya ce, “Baba bani da ja akan hukuncinku”.
       “Kan ubanka Al-Mustapha!!”.
  Mommy ta faɗa cikin suɓutar baki, Murmushi Abba da Abie suka saki kusan a tare, hakama aunty Mimi da Mom da aunty Amarya sai da sukai kananun murmushi. Ɗayan yayanta da suke cema Yaya Kamil ya harareta, a kausashe yace, “Nafisa! Dama kina buƙatar ya bijirema iyayensa ne? A matsayinsu na mahaifa a garesa su zartar da hukunci ki nunama duniya k baki bama ɗanki tarbiyya ba saboda wani banzan tunaninki da hujjojinki? Karna sake jin bakinki a wajen nan, in ba hakaba ranki zaifi haka ɓaci billahillazi!!”.
        Dole tai shiru saboda a maganar Yaya Kamil ɗin babu wasa sam. Baba Ibrahim ya sake maida hankalinsa ga Shareff. “Ka bamu amsa ne a dunƙule Shareff, kana nufin ka amsa auren kenan?”.
       Sai da ya ɗan saci kallon Mommy ta gefen ido, tako zuba masa ido cikin matsanancin ɓacin rai, janye idanunsa yayi ya maida kan Daddy shima ya tsume kamar fuskar tasa zatai aman wuta.
     “Shareff kai muke saurare, in har a ranka kanajin auren nan cutuwane a gareku ka saki yarinyar nan tun yanzu anan karka saka ku a wani halin da zai wargaza zuminci”.
     A hankali ya girgiza kansa dake rissine a ƙasa. “Baba ku gafarceni bazan iya sakinta ba tunda an ɗaura....”
      Kukan da Anaam ta fashe da shi ya hana Gwaggo data ɗauki sallami tana tafa hannaye ƙarasawa, hakama Mommy da Gwaggo Halima da suka zaburo. Fadwa ma kuka ta saki mai ƙarfi yayin da Aunty Mimi da Mom da Abba suka saki wata nannauyar ajiyar zuciya, Abie ko murmushi ya saki, shi ko Daddy ya ɗan lumshe idanu. Mamie dai kanta a ƙasa yake babu mai iya gane yanayinta. Albarka su Baba Ibrahim suka shiga sanya masa da suma murmushin ya ziyarci fuskokin su, hakan ya ƙara tunzura kukan Anam da Fadwa....
      “Nidai bana Son sa baba, akwai wanda naima alƙawari zan aura nima, kuma shi nake so!!”. Furucin Anam cikin matsanancin kuka ya daki kunnuwan kowa dake a falon. Cikin sauri da zaburowa Mommy tace, “Shima ai ba son naki yake ba, shegiyar yarinya mai kama da ifiratan aljanu. Yaya ai kaga abinda nake gudun masa tun farko, mizaiyi da wannan mara tarbiyyar yarinyar har tana wani iƙirarin ba son sa take ba fitsararriya.....”
     Hayaniyace ta nema sake kaurewa a falon, yayinda Anam ke rusa uban kuka ita akwai wanda take so. Tsawar da Abie ya daka mata ce ta saka gaba ɗaya hayaniyar kukan Fadwa da Hargowar Mommy data Gwaggo yin tsitt. Anam ta maƙure jikin Aunty Mimi tana sake fashewa da kuka. Baba Ibrahim ne ya kalla Abie cikin murmushi, kansa ya girgiza masa cikin dattako. “Ayi haƙuri Usmanu abita a hankali sai a samu masalaha sahihiya. Tsanani baya kai kowa ga hanyar nasara. Juwairiyya zonan kinji”.
       Da taimakon aunty Mimi ta mike taje gabansa, kusa da ƙafafunsa ya nuna mata, ta zauna tana shashshekar kuka da sharɓar hawaye da gyalen data rufe har fuskarta. Cikin lallashi yace, “Kukan ya isa haka to, maza share hawayrnki”.  Da ƙyar ta iya danne kukan, sai dai hawayen basu bar zirara ba.
Cikin lallashi yace, “Faɗa min wa kike so?”.
Kai tsaye tace, “Muzaffar!”.
“Miyasa shi Shareffuddeen baƙya son shi?”.
Shiru tai ta kasa magana, ya ƙara maimaita mata tambayar.
“Kawai Baba”.
“Ai shi mutum ba'a ƙinsa kawai Juwairiyya. Amma zan baki wata dama da kuma alfarma kin yarda?”.
Cikin share hawaye ta jinjina masa kanta. Yay murmushi irin nasu na manya masu basira.
“Ina so kimin alfarmar yarda a kaiki gidan Shareffuddeen. Daga nan zuwa wata uku in har baki samu wani farin cikin zama da shi ba, kizo ki sanar min, ni kuma na miki alƙawarin da kaina zan saka shi ya sallama miki”.
Karon farko ta ɗago ta kallesa. Cike da tabbatarwa ya jinjina mata kansa yana murmushi. Ta kai dubanta ga Shareff, cikin sa'a kuwa suka haɗa ido. Wani shegen kallo da taima fassara dana tsana ta hango cikin idanun nasa, sai taji ƙwarin gwiwar cin nasarar shawarar baba ibrahim, dan kuwa ta tabbatar babu wani farin ciki da zata samu daga Shareff ɗin musamman idan ta auna irin tsanar da yay mata a rayuwa. Idan haka ne gara ta amince kodan goge laifinta da su Abie zasu iya gani, cikar wata uku kuma dai-dai da kammala Serves ɗinta kenan......
“Baki ce komai ba”.
Baba ibrahim ya katse mata tunani.
“Baba na amince”.
Murmushi ya saki mai ƙayatarwa, hakama abie da Abbah da Daddy duk sai da suka saki ajiyar zuciya. Yayinda Mommy tai ƙwafa sai dai babu damar cewa wani abu.. Baba Ibrahim ya sake ƙara musu nasiha baki ɗaya musamman Gwaggo dake a matsayin uwa garesu su duka a wajen. Hakama Mommy data hau dokin zuciya da yasan bazata taɓa tanƙwasuwa ta sauƙi ba. Itama dai Fadwa da Gwaggo Halima sun sami nasu rabon musamman ma Fadwa da yaketa lallashi dan yasan an mata laifi. Suma dai su Daddyn ya musu nasihar ya kuma ƙara bama kowa haƙuri da fatan komai ya wuce sannan yay addu'a taron ya tashi dan dare ya farayi.....

          ★★Washe gari an tashi ne mafi yawan rayuwuka a ɓace, ga amaryar Maheer ta iso tun daren jiya, tana a sashen Mom kamar yanda Daddy ya sharɗanta. Aunty Halima dai tun daren jiya tabar gidan tare da Fadwa, acewarta dai su Daddy basa ƙaunarta babu ita babu su, Fadwa ma tabar gidan Shareff kenan sai dai ya biyota da takardarta. Komai babu wanda yace mata a cikinsu, sai Gwaggo dake faman matsar ƙwalla tana faɗar maganganu. A haka dai babu daɗin rai akai walima washe gari dan dama ango Maheer shi bai yarda da wani event ko ɗaya ba, butsutsunsa yasa Mommy haƙura duk da taso a sha shagali tamkar bikin Shareff da Fadwa.
       Shareff ma dai tun a daren ya koma can gidansa tare da Khaleel da Maheer ɗin da suka kwana da shi a can saboda yanayin jikinsa daba gama daidaita yay ba. Itama dai Anam bata kwana da lafiya ba dan tunda sassafe ma sai da Abie ya kaita asibiti da kansa aka bata gado. Dan haka har yamma tana can tare da Aunty Mimi da Abie ɗin, sai su Mom da su Daddy da sukaje daga baya dubata. Wannan ya kawo ƙaracin armashin buɗar kai da akai na amaryar Maheer, bayan sallar la'asar danginta da wasu a dangin Mom sukai mata rakkiya gidan mijinta. Gida yayi ƙyau dan Maheer ma yayi ƙoƙari sai sambarka. Sannan iyayen amarya ma sunyi nasu ƙoƙarin dan kun san dai Mom dama duk inda take na masu manda ne. (Tana bala'in son huɗɗa da masu kuɗi a gidan sanyi🤣).
         Tun a ranar mafi yawan baƙi suka kauce dan uwar bikin a birkice take. Tako'ina Mommy ɗin ta birkicema kowa. Gida yayi lafiya, baƙin da suka rage kalilanne, Hakan yasa koda aka sallamo su Anam daga asibiti sanda suka shigo gidan tsitt yake.

      Washe garin data kasance lahadi sai ga mahaifin Fadwa har gida ya maido Fadwa, babu ragi yay mata tatas a gaban su Daddy ita da Mommy. Fafir kuma yaƙi sauraren zantukan Gwaggo duk da uwa take a garesa. Wannan dattako daya nuna ya matuƙar faranta ran kowa a gidan ciki harda Shareff da aka sashi zuwa gidan. Daga ƙarshe kuma ya bisu da nasihar zaman haƙuri dana riƙe junansu domin samun kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya. Bayan wucewarsa su Daddy suka sake zama da Shareff, sun basa umarnin ƙarasa abinda ya rage masa dan nan da sati ɗaya amarya zata tare ɗakinta. Yaso yace suɗan ƙara masa amma baiga wannan damar a fuskokinsu ba dan umarni suka bashi ba shawara ba. Daddy kuma ya turkesa a wajen yace ya biyasa kuɗin sadaki dan shine ya ranta aka biya a waccan ranar. Dole yayma Daddy transfer ɗin kuɗinsa take a wajen sannan ya barsa ya tafi.
       Ƙin shiga wajen Mommy yayi dan wasan ɓuya yake da ita tun ranar, ya aika Aysha ta kira masa Fadwa tazo su wuce. Amma sai Mommy tace a faɗa masa Fadwan ta ƙarfi ce idan yanada ƙarfin yazo ya ƙwata. Murmushi kawai yayi sanda Aysha ta zo masa da amsa, batare da yace komaiba ya shiga motarsa ya fice a gidan dan gwara wannan wasan ɓera da magen da yake da Mommy ɗin akan tunkararta face to face a yanzun.

         ★ Kamar wasa ciwo ya kwantar da Anam sai da aka kwasheta aka koma da ita asibiti a daren yau. Dawowar su Amrah cikin gida yasa su Mom suka sani, dan daga Mamie har Abie da Aunty Mimi duk suna acan asibitin. Duk da dare ya farayi haka Abbah da Daddy suka fita, Khaleel ne ya jasu a motar bayan sun kira Abie sunji asibitin da suke.
        Lokacin da suka iso har an bama Anam ɗin gado amma saka mata ruwa barci ya ɗauketa. Ta rame sosai dayin wani irin fayau da ita, suna cikin jajantama juna Shareff ya shigo, Khaleel ne ya  tura masa sms ya sanar masa sanda zasu taho, dan haka ganin nasa ya bama kowa mamaki har Abie ya kasa haƙuri yay magana.
     “Babana waya saka fitowa a wannan daren haka? Ga anguwarku da nisa?”.
    Ƙaramin Murmushi yay idonsa na satar kalllo Anaam dake barci duk ta koɗe tayi fayau da ita abin tausayi..........✍


_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[11/3, 7:19 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*




*_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718


*_37_*

.........Kiran sallar farko ya farka, dama ba wani barcin kirki yayi ba, dan bai baro asibiti ba a daren jiya sai kusan ƙarfe ɗaya, shima sai da Abie ya korashi dan suma duk lokacin suka wuce aka bar aunty Mimi kawai da Anam dake barci. Sai da ya watsa ruwa kozai samu ƙarfi sannan yay alwala ya fita massallaci, gari ya ɗanyi shaa ya shigo gidan, ya ɗan ja tsaki dan gaba ɗaya gidan yay masa wani irin girma, yayi niyyar sakama Fadwa ido yaga iya gudun ruwanta amma a yau yaji bazai iya hakan ba, dan ya kula sai ya fito mata ta inda bata zato sannan zasu samu dai-daito. Wayarsa ya ɗauka yana zama bakin gado dayin ƙaramar ƙwafa, aunty Mimi ya kira, bugu biyu kuwa ta ɗauka suka gaisa, ya tambayi yamai jiki tace da sauƙi amma bata tashiba har yanzun dai.
     “Masha ALLAH, nima zan shirya yanzu zan shigo, ko kuna buƙatar wani abu ne shiyyasa na kira?”.
    Aunty Mimi ta amsa da “To ALLAH ya kawoka lafiya. Bama buƙatar komai tunda bata tashiba balle aji ko ita tana son wani abu ɗin”.
        “Okay to sai nazo”.
Ya faɗa yana yanke wayar. Bai wani jima ba ya kammala shiryawa ya fice, sai da ya shiga mota ya fara kiran number Fadwa, harta tsinke ba'a ɗagaba, ya sake tsuke fuska ransa na ƙara ƙuna dan ya tsani raini a rayuwarsa. Wayar ya jefa kujerar gefansa yay ma motar key ya fice.

        Gama wayar aunty Mimi babu jimawa ta farka, da taimakonta taje toilet dake a cikin ɗakin, jikinta sam babu ƙarfi, hakan yasa Aunty Mimi taimaka mata ta ɗan watsa ruwa mai ɗumi sosai sannan tai alwala suka fito. Murya a karye irin ta mara lafiya tace, “Ummie bazan iya salla a tsaye ba ina ganin jiri”. Taimaka mata aunty Mimi tai ta zauna kan sallaya, dai-dai nan masu gyara ɗakin suka shigo tare da wata nurse. Su dukansu suka gaida Aunty Mimi da tambayar mai jiki, ta amsa musu da fara'a.
        Gyaran gado mai sharar ta fara, yayinda Nurse ɗin ke tsaye tana jiran Anam ta idar. Sai da tai addu'a Nurse ɗin ta taimaka mata ta koma saman gado, kwancia ta ƙarayi dan gaba ɗaya batajin ƙarfin jikinta. Harta lumshe ido sallamarsa ta sakata buɗewa, kallo ɗaya tai masa ta maida ta rufe abunta fuskarta na sake tsukewa. Gaisheshi Nurse ɗin tai hakama mai sharar, ya amsa sama-sama yana ƙarasawa gaban aunty Mimi ya ajiye ledojin hanunsa. Aunty Mimi dake dubansa da murmushi tace,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login