Showing 87001 words to 90000 words out of 178785 words

Chapter 30 - Babu So Complete Hausa Novel

05 Feb 2025

32830

“Babana mun hanaka barci ko?”.
      Murmushi ya ɗanyi da kaiwa zaune a ɗayan gadon dake ɗakin, ya rissina yana gaisheta kafin ya bata amsa da “Ko badan kuba dole na fito ai yau akwai office”.
        “Tofa ango guda da zuwa office”.
   Idanunsa ya sauke akan Anaam batare daya ce komai ba, cikin son basar da zancen yace, “Har yanzu bata tashi ba?”. Kallon Anaam aunty Mimi tayi, ganin tayi luff kamar bata jinsu tai ƴar dariya. “Yanzun nan tai salla ma, tana komawa saman gadon kana shigowa. Sallamar Doctor ta hanashi cewa komai, tare yake da nurse ɗin ɗazun, ya miƙa masa hannu suka gaisa yana tambayar yamai jiki. Da aunty Mimi ma suka gaisa sannan ya ƙarasa gaban gadon.
       Cikin tsokana yace, “My patient barcine ko likimo?”. Duk da ta jisa bata motsa ba, sai dai taɗan buɗe idonta ta kallesa ta maida ta rufe. Murmushi yayi da sake faɗin, “Alhmdllh ALLAH ya ƙara lafiya. Sister Rabi taimaka mata ta tashi”.
     Da taimakon Nurse daya kira sister Rabi ta tashi, sai langaɓewa take kamar zata saki kuka, cikin lallashi doctor yake mata ƴan tambayoyi akan yanayin jikinta tana bashi amsa, ko sau ɗaya taƙi yarda ta kalli sashen da Shareff yake. Bayan doctor ya kammala ya bada umarnin a bata abinci ko kaɗan taci zai aiko a sake saka mata ruwa da allurai uku, dan suna buƙatar ta samu barci sosai da alamu suka nuna kwana biyu bata samu. Koda ya fice shi da Nurse ɗin bata yarda ta kalli inda yaken ba, saima ƙoƙarin kwanciya da taso yi aunty Mimi ta dakatar da ita. Idanunta ta ɗago cikin marairaicewa ta kalli aunty Mimi, har ƙwalla sun taru dan ma gilashin idonta ya ɗan ɓoyesu duk da fari ne tas, karaf suka haɗa ido, ta sake yin kicin-kicin da ɗauke kanta tamkar bata gansa ba. Shiko ya kafeta da nasa idanun sai dai shima tashi fuskar tsamm take babu wasa.
    “Ummie jiri”.  
Ta faɗa a hankali.
“Na sani mamana ki daure kici abinci kamar yanda doctor yace sai ki kwanta ɗin. Bata iya musu ba, dan haka tai shiru. Aunty Mimi ta bubbuɗe ledojin da Shareff ya shigo dasu, kayan tea ne a leda ɗaya, ɗayar kuma abincine dai-dai cin mara lafiya kuma abinda Anam ɗin take matuƙar so. Amma da yake daru takeji sai tace ita bata son shi, aunty Mimi sai lallashinta take amma ta kafe ita bata sonsa a kira Mamie ta kawo mata wani.
     Sarai yana jinsu amma bai tanka ba, sai danna wayarsa yake kai kace hankalinsa baya kansu sam. Ana cikin badaƙalar Khaleel ya iso. Cikin shirin office yake, ya gaida aunty Mimi da Shareff ɗin yana ajiye basket na abinci da Mom ta aikosa ya kawo. Kafin ya karasa gaban gadon yana kallon Anaam da ƴar sakin fuska dan shi murmushi ma kakan daɗe baka gani ba tare da shi. “A jiki yayi sauƙi granny tunda gaki zaune, jiya har mun fara ƴar ƙwalla da murnar cin gummba”.
    Murmushi ta saki tana kallon Khaleel ɗin kamar ba ita ke bori ba. “Kai Yaya Khaleel, kai ashe soma kake na mutu?”.
     Murmushi yayi shima a karon farko, “To Granny na sani ko lokaci yayi jikin tsufa”.
          Ta ɗan hararesa tana ɗauke kanta, dariya yayi nan ma. A ɗan shagwaɓe tace, “Yaya mika kawo min?”.
   “Breakfast ne Mom tace a kawo miki kafin su ƙaraso”.
   “Na gode”.
Ta faɗa tana maida dubanta ga Aunty Mimi da ke kallon Shareff daya miƙe fuskarsa kicin-kicin kamar zaiyi aman wuta. “Ummie zanci”. Da ga shi har Aunty mimi kallonta sukai, yay mata wani mugun kallo ya ɗauke kansa. Itama harara ta balla masa ta ɗauke nata idon. Sarai yaga harar dan haka ransa ya ƙara ɓaci, batare da yayima kowa sallama ba ya fice abinsa.
     Daga aunty Mimi har Khaleel da kallo suka bisa.....

        ★Yini guda ƴan dubiya nata leƙowa jefi-jefi, sai dai babu Gwaggo babu Mummy, Aysha ma satar hanya tai ta biyo su Mom da zasu zo tazo ta duba Anam ɗin. Dan Mommy ta hana yaran ɗakinta duka. Shareff dai bai sake leƙowa ba sai kusan takwas na dare, da alama daya tashi aiki sai da yaje gida sannan ya dawo nan dan jallabiya ce a jikinsa. Yanzu ma Anaam yitai kamar bata san ALLAH yayi ruwansa ba, shima kuma daga gaisuwa da yay da Aunty Mimi da wata ƴar uwar Mamie data zo duba Anaam ɗin yaja bakinsa ya tsuƙe. Aumty Mimi suka fita zataima baƙuwar rakkiya aka barsu su biyu. Shiru ɗakin ya ɗauka kamar babu masu rai, sai ƙarar iskar fanka kawai kakeji, taƙi yarda ko sau ɗaya ta kallesa sai faman cin apple ɗinta take da aunty mimi ta yanka mata hankali kwance. Idanu ya ɗan tsura mata amma duk da haka ta ƙi ta nuna tasan da zamansa....
      “A tunaninki wannan rashin kunyar taki zaisa ki samu biyan buƙatar taki?”.
    Shiru babu alamar tama jisa tanata dai cin apple ɗinta, ransa ya ƙara ɓaci, cikin jin zafi da ɗacin da muryarsa ta kasa ɓoyewa yace, “Oh ga mahaukaci na magana ko? K! Ki shiga hankalinki wlhy, inba hakaba zakisha baƙar wahala a banza stupid kawai”.
        Babu ko ɗar a cikin idanunta ta ɗago ta zuba masa su duk da suna cikin gilashi, “Yaya Shareff ALLAH bazai baka damar bani wahalar ba kuwa, dan hanyar jirgi daban ta mota daban. Aure ne dai nace bana so kuma komi za'amun bazan so ba dan inada wanda nake s......”
    Ji kake “bumm!” akan bakinta, sam batama lura da sanda har ya taso ya iso gareta ba. Ya ture hanunta da take ƙoƙarin ɗaurawa saman lips ɗinta ya maye gurbinsa da nasa yatsun biyu, cike da baƙar mugunta ya shiga murzasu. Duk da dukan da take kaima hanun nasa bai janye ba sai da ya tabbatar ya murjesu san ransa sannan ya saki. “Karki fasa rashin kunya, nima bazan fasa ɗaukar mataki akanki ba”. Ya ƙare maganar gab da fuskarta har yana busa mata numfashinsa da iskar bakinsa dake ƙamshin mouth freshener na banana.
      Kuka ke son taho mata amma tanata ƙoƙarin dannesa dan taci alwashin bazata sake barin hawaye akan fuskartaba game da wannan auren, zata ƙwaci kanta da ƙarfinta kuma duk abinda za'ai mata sai dai ai mata bazata zauna zaman aure da shi ba. Shima baibi takanta ba dan harya fice ma abinsa rai ɓace. Taja wani shegen tsaki da ɗaga gilashinta ta share ƙwallar da suka taru a fatar idon dan ta danne sauran ta hanasu tasiri. Koda aunty Mimi ta dawo bata tambayeta ina Shareff ɗin ba, da alama dai sun haɗu a waje ne.
      Daga ita har shi haka suka kwana rai a ɓace. Washe gari ma shine ya fara zuwa asibitin, sai da yaje wajen doctor ya biya komai ya basu sallana sannan ya iso ɗakin. Da aunty Mimi kawai yau ma ya gaisa, ƴar darun tasa na kwance ta juyama ƙofa baya baima san idonta biyu ko barci take ba. Shine ya sanar ma aunty Mimi an sallamesu, tai godiya ga ALLAH sannan ta miƙe ta fara haɗa kayansu. Ya ɗauki kayan ya fita da su, ita kuma ta tada Anaam da dama idonta biyu ta taimaka mata ta shirya sannan suka fito bayan doctor ya shigo sunyi sallama. Tsaye suka samesa a jikin motarsa yana waya da alama a cikin su Daddy ne. Ƙin yarda tai ta kallesa duk da shi tana jin nasa idon a kanta. Aunty mimi zata sakata gaba ta tirje akan ita dai baya take so, kokuma subi napep.
       Faɗa aunty Mimi ta fara mata dan ta kaita wuya kuma, shiko kamarma bai san sunai ba ya shige motar abinsa bayan ya gama wayar tasa. Dole dai ta shiga gaban bisa tursasawar aunty Mimi........✍🏻


_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[11/4, 12:31 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*




*_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718


*_39_*


.........Alhmdllhi amarya ta iso gidanta lafiya, ta kuma samu tarba daga wajen dangin mahaifiyar su Daddy da suma sukazo suka taru anan domin nuna gata gasu daddy ɗin, duk da tun zuwan nasu ƙawayen aunty Halima dake gidan zagaye da Fadwa suka kirata suka sanar mata. Babu ko kara na tuna cewa dangin mahaifiyarta ne ta kirasu tai musu tas a waya da tabbatar musu zata iya da makircin kowa daya nuna goyon bayansa akan aima ƴarta Fadwa kishiya, kishiyarma ɗiyar ƴar uba. Inna Suwaiba! Wadda ta kasance ɗiyar wan maman su daddyn ce ta amshi waya tai mata tas itama dan in masifa ce ta fita iyawa, ai ko babu shiri ta yanke wayar tana zage-zage.

Kowa ya yaba sashen amarya tare da jinjinama ƙoƙarin iyayenta, dan tabbas kam sun nunama duniya ita ɗin ɗaya ce tilo a garesu kuma ƴar gata. Cikin raɗa Mom da Hajiyar sudan suka sake yima Anam da keta sauke ajiyar zuciya nasiha. Rungume Mom tayi, muryarta a ɗashe alamar taci kuka mai yawan gaske tace, “Mom ni bana son sa dan ALLAH, Mom karku barni anan zan iya mutuwa”. Mom dake rungume da ita tana shafa kanta tai murmushi. “To kiyi haƙuri, zan samu Abbanku nai masa bayani yanda zai fahimceni, yanzu dai ki kwantarmin da hankalinki kinji”.
Da sauri ta fiddo fuskarta dake cikin mayafi tana kallon Mom da jajayen idanunta da suka kumbura matuƙa saboda kuka. “Mom dan ALLAH da gaske?”. Hajiyar Sudan Da Mom suka haɗa ido, murmushi sukayi, kafin Mom ta jinjina mata kanta “Da gaske mana. ba Baba ibrahim ma yace nanda wata uku indai da wata matsala zai ɗauki mataki ba”. Sake rungumeta tai tana jinjina kanta fuskarta na bayyanar da murmushin da tunda aka fara badaƙalar auren nan ba'aga irinsaba a fuskarta. Cikin dabara hajiyar Sudan ta fita a ɗakin, dan dama su kaɗaine suka rage mutane duk sun fice kowa na tsoron ya rasa mota. Lallashinta Mom ta ƙarayi, kafin itama ta miƙe cikin dabara da plan ɗin da suka haɗa da hajiyar sudan.
Hajiyar Sudan ɗin ce ta leƙo tai kiranta wai tazo taga wani abu, miƙewa Mom ɗin tai tana gyarama Anam zama. “Kinga zauna ina zuwa”. Ji Anam tai kamar dabara zasu mata, sai dai kafin tai wani yunƙuri Mom ɗin har ta fice a ɗakin, tun tana irga seconds harta koma minutes, ganinfa alamar mintuna kusan goma sun cika babu alamar motsi ma ya sakata miƙewa da sauri hawaye na ciko mata ido. Tabbas babu kowa a falon, hakama sauran ɗakunan zuwa kitchen, wasu irin zafafan hawaye ne suka silalo mata, ta dafe kujera saboda jiri dake neman ɗibarta, da ƙyar ta iya maida kanta bedroom ɗin da suka barta, ta zube a kan gadon hawayen na cigaba da sauka a guje dan bata da ƙarfin yin kuka mai sauti.....

Gida ya koma tsitt, duk da sashen Fadwa har yanzu akwai wasu ƴan uwan babanta uku na hanun damar Gwaggo halima da su Mommy basu da alamar barin gidan, sun zagaye Fadwa dake kuka suna ƙara mata fanfo dan ba'ace nasiha ba. A kallo ɗaya zaka tabbatar da taci kuka itama har ta godema ALLAH, dan hatta da muryarta ma ta dishe. Gaba ɗaya ji take Shareff ɗin ma ta gama tsanarsa, ko ganinsa bata sonyi shi da duk wanda ya shafesa. Tsoron mahaifintane kawai ya taka mata birki akan ƙudirinta na barin gidan, amma batajin zata iya cigaba da rayuwa da Shareff ƙarƙashin inuwa guda da maƙiyarta, yarinyar datai matuƙar tsana a rayuwarta ace a yau itace kishiyarta, kishiyarta da zata iya shearing da mijinta abin sonta. Kai ina wannan ma maganar tatsuniyace, za kuma ta tabbatarma duniya cewar tatsuniyar ce...

Duk wannan hidima da akeyi ango Shareff na can gidansu gurfane gaban su Daddy suna sake masa nasiha da jaddada amanar matan nasa a hanunsa domin a yanzu matsayi guda suke amsawa a wajensa. Kuma su dukansu ƴan uwansa ne na jini da basa fatan zuminci ya samu wani nakasu ko rauni a dalilin aurensu. Basu barsa ya baro gidan ba sai da ƴan rakiyar amarya suka koma. Yay musu sallama ya fito. Babu sashen daya shiga, dan shima yasan baida wannan damar a yanzu. Ga kuma kansa na masa matuƙar ciwo ma na hayaniyar da aka sha ga kuma jikinsa da bawai ya gama dawowa dai-dai bane shima dama. Dauriyace kawai da ƙarfin zuciya irin ta maza.
Duk yanda abokansa suka so masa rakkiya kamar auren Fadwa ƙi yay, dole suka haƙura suka gudu sai Fharhan ne kawai dazai jasa a mota dan shi bama zai iya driving ɗin ba. Da farko tsokanarsa ya dingayi, sai da yaga baya cikin good mood ne ya koma nasiha a garesa, dan kuwa dai shi ɗin shaidane akan abinda Shareff yake ɓoyewa a zuciyarsa tsahon shekaru, sai dai ko'a yanzun ma bai nuna masa yama fahimcesa ba yadai bashi shawarwari kawai. Har suka iso bai dai ce komai ba, sai da zai fita ne yace masa “Thanks” a taƙaice. Da kallo kawai Fharhan ya bisa, sai kuma ya girgiza kansa yana murmushi.

Kai tsaye sashensa ya wuce duk da yanada tabbacin zuwa yanzu babu kowa a gidan, ya zube cikin kujera yana furzar da huci mai zafi lokacin da yake kai bayansa ga kujerar. Ya lumshe idanunsa da yake jin sun masa matuƙar nauyi. Kusan mintuna goma ya ɗauka a wajen yana kokawa da abinda zuciyarsa ke saƙa masa, kafin ya miƙe ya nufi bedroom ɗinsa. Wanka ne a ransa, dan haka bai zauna ba ya zame kayan jikinsa ya shige bathroom. Koda ya fito jikinsa kawai ya tsane ya zura jallabiya yasa turare kaɗan. Hakkinsa ne ya duba kowaccensu, duk da kuwa tunda Fadwa ta dawo gidan taƙi yarda su haɗu. Sashenta ya fara zuwa batare da tunanin zai samu kowa ba. Turus ya ɗanyi da mamaki, hatta fuskarsa sai da ta nuna dan bai zaton samun kowa ba. Fadwa da ke kwance ta ɗora kanta saman cinyar aunty Malika tai masa kallo ɗaya ta kauda kanta tana jan siririn tsaki ciki-ciki yanda bazaiji ba. Kallonta yake amma taƙi yarda su haɗa ido, ya ɗan girgiza kansa kawai. Komai baice ba ya fito a falon dan ko sallamarsa babu wanda ya amsa a cikinsu, sai kuma binsa suke da kallon banza....
“Lallai wannan mijin naki ya cika ɗan iska Fadwa. Yanzu muna amtsayin ƴan uwan uwarsa amma yay mana wannan kallon banzar babu ko gaisuwa ya fice”.
“Ke ko ya zai gaishemu kansa na hayaƙin asiri Safarah. Ai bayin kansa bane, dole fa su Aunty Nafi (Mommy) sai sun tashi tsaye dan Shareff ya shiga kaidun waɗannan mutanen wlhy”.
Kuka Fadwa ta sake rushewa da shi tana kiran ta shiga uku. Cikin zafin rai wadda batace komaiba tun ɗazun ta daka mata tsawa. “A gidan ubanwa kika shiga ukun? Idan taƙamarsu asiri da tsubbu gaban iyayen gidansu sukazo. Har miye su? Mi akai akayi wannan ƴar yarinyar da bata wuce ki fetota a hancinki da makirci kawai ba. Danni banga abin ɓata lokaci agareta ba balle kuɗi na neman asiri. Wannan yaƙin da kanki zakiyisa in har kin cika ke ɗin jinin baba yalwa ce (Kakarsu data haifi mahaigiyar Mommy, Gwaggo, mahaifin Fadwa, mahaifiyar Bibah).
“Aunty Lawusa dolene nai kuka, wlhy shima na tsanesa, bana son ganinsa munafiki ne”.
Yanda take maganar tana kuka yasa Aunty Malika sake jawota jikinta ta rungumeta. Kuka ta sake fashewa da shi. “Aunty yanzu fa zuwa zai ya kwana da ita, shike nan sun rabani da mijina.....”
“Basu isa rabaki da mijinki ba, ki kuma kwantar da hankalinki shi bai isa kusantarta ba, bama a yau ba har abada, yanda ta shigo haka zata bar miki gida sai dai ta koma ta cigaba da rabama abokan shashancin nata a ƙasar data fito”.
Ɗagowa Fadwa tai tana girgiza kai, “Aunty baki san waye Shareff bane, wlhy sam baida haƙuri akan mace, ko faɗa yay da ita zai iya neman biyan buƙatarsa shi babu ruwansa”.
Dariya aunty Lawusa tayi sai kuma ta haɗe fuska. “Malama ki mana shiru haka, idan shi hrj ne ƙarshen dai maitar mace kenan ko? To bai isa tarayya da yarinyar can ba har abada tunda ya taka abun can da ƙafafunsa”.
Sosai Fadwa ta zaro idanu “Aunty wane abu wai?”. A tare suka sanya mata dariya, aunty Malika ta fiddo ƴar kwalba a jikkarta har guda 2. Ba kinga nayi turaren wannan ba ɗazun? Na kuma barbaɗe ƙofar falonki da wannan yanzun?”. Kanta ta jinjina mata. Ta dafa kafaɗarta tana murmushi, to wannan da kike gani sunansu *ɗan kaɗafi da ni kaɗai ce mace* mu dukanmu nan babu wacce bata aiki da shi a gidanta, kuma munga biyan buƙata shiyyasa kema muka amso miki, dan haka ki kwantar da hankalinki indai wannan yarinyar ce da ƙafafunta zata bar miki gidanki, ko zasu kwana manne da juna wani abu bazai taɓa shiga tsakaninsu ba”.
“Ni wlhy ko gadon ma bana ƙaunar su haɗa aunty, kai ko hanunta bana son ya taɓa riƙewa a gidan nan”.
“Wannan duk mai sauƙi ne, kedai kawai ki saki bakin aljihu, dan yanzu babu boka babu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login