Showing 90001 words to 93000 words out of 178785 words

Chapter 31 - Babu So Complete Hausa Novel

05 Feb 2025

32847

malam maganin mata sune ke ƙwatar mace, shiyyasa mukayo miki haɗinsu gasu nan na musamman yanzu haka ma Hajarah zata taho miki da wasu daga Niger, Fadwa sai kin koma juya Al-Mustapha inda kike so, balle ke ma da kika gama morewa da samun mabuƙaci, ta wannan hanyar zaki banbance masa tsakanin aya da tsakkuwa ki kuma damƙe abunki dan dama naki ne shi kaɗai. Tun farko su Aunty (gwagg halima da Mommy) sunyi sakaci ai da basu haɗaki da haɗi na musamman ba kafin aure da Shareff bai taɓa kallon wata mace ba, kai auren nan ma da bai sai sun wahal da kansu ba da kansa zai bijire wlhy. Amma ko yanzu bata ɓaci ba muna tsaye kanki”.
Fuskar Fadwa ta washe da murmushi, ta rungume auntys ɗin nata cike da farin ciki, jitai gaba ɗaya duk wata damuwarta tama gushe, dan tayi imani da duk abinda suka faɗa tunda ita ɗin shaidace akan yanda suke juya gidansu da mazajensu duk da sunada kishiya, aunty Malika ma su uku ne amma idan kaga yanda mijinsu ke rawar kai a kanta saika ɗauka ita ɗaya garesa ko kuma amarya, sai dai itace ta tsakkiya........✍🏻




_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[11/4, 12:31 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*




*_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718


*_40_*



...........Ya jima tsaye a ƙofar sashen tamkar mai nazari, kafin ya ɗaura hanunsa akan handle ɗin ya murɗa a hankali. Ƙamshi dai da aka sani da sashen kowace amarya ne ya fara tarbarsa, ya shiga da sallama kan lips ɗinsa idonsa na zagayawa kan komai na falon. Ya turo numfashi mai ɗan ƙarfi ta hancinsa, cikin tafiya kamar mai irga steps ya nufi bedroom ɗin da yake saka ran samunta, dama 3bedrooms ne a sashen iri ɗaya dana Fadwa ne, sai kitchen, store, falo, bedrooms biyu suna facing juna a corridor guda, ɗaya na a can gefe kusa da dining alamar dai na baƙine. Nan ɗin ma dai sai da yay ɗan jimm sannan ya tura ƙofar, babu kowa, sai dai shima yasha kaya tsaff. Maidawa yay ya rufe, ɗayan ya buɗe.
Kwance take ta dunƙule waje ɗaya, tare da lulluɓe duka jikinta da bargo. Hawaye take sosai ga rawar sanyi alamar zazzaɓine a jikinta. Ya ɗau tsahon minti uku yana kallonta duk da ba fuskarta ce a buɗe ba kafin ya cigaba da takawa cikin ɗakin sosai fuskarsa a tsume har yanzu da takaicin su aunty Lawusa, dan ma baiji abinda suke shiryama Fadwan ba kenan..
Isowarsa gab da gadon ya bashi damar jin yanda take sauke ajiyar zuciya a jajjere har tanayi kamar zata shiɗe. Sai kuma rawar sanyin da takeyi har yana iya ganin kaɗawar jikinta duk da a lulluɓe take. Hannu ya kai ya yaye bargon baki ɗaya, hucin zafi sosai ya bugesa.....
“Shiii!! wayyo sanyi-sanyi....” ta faɗa tana ƙoƙarin riƙo bargon da ya janye ɗin, bai bata damar yin hakan ba, ya kai hanunsa na dama saman goshinta. Sosai kan nata ma ya ɗauki zafi. Zumbur ta miƙe, dan sai yanzune ƙamshin turarensa ya kai ga hancinta, gaba ɗaya tama shafa'a da inda take. Tai saurin gyara glass ɗinta da ya sirranta kumbiri da jaan da idonta sukai tana ja da baya...
“Kina tunanin hakan da kika zaɓama kanki shine maslaha? Duba yanda jikinki yay zafi, idanunki suka kumbura saboda kukan da bazai miki amfani ba bayan kin san hakan a gareki matsala ce babba. Garama ki nutsu domin kukanki da borinki bazai canja komai ba”.
Wani irin kuka ne ya kufce mata na takaici da ƙara jin zafinsa. Yaja siririn tsaki da juyawa ya fice a ɗakin. Fillo ta ɗauka ta wurgama bayansa duk da ya riga ya fita sai ya samu ƙofa, ta ƙara ɗaukar wani ta jefa. Sai da ta jefa uku sannan ta zame ta kwanta tana cigaba da kukanta da ita kanta ta gaji da yinsa. Kusan mintuna bakwai ya dawo, akan fillos ɗin data wuwwulo ya fara sauke idanunsa, ya ɗan girgiza kansa kawai ya tsallakesu. Cup ɗin da ɗauke da tea ya ajiye tare da magani, batare da yace mata komai ba ya sake fita, bai jimaba ya dawo da goran ruwa.
“Tashi zaune” ya faɗa cikin bada umarni, dan yasan idan yay mata laku-laku bayin yanda yake so zatai ba. A yanzu ɗin ma duk da a yanda yay maganar sai da ya sake maimaita mata a ɗan tsawace sannan ta tashi. Da kansa ya gyara mata filo jikin fuskar gadon ya kuma taimaka mata ta jingina da ƙyau. Kusa da ita ya zauna yana mai kallonta tamkar mai nazari. Ita dai taƙi yarda ko sau ɗaya ta kallesa. Numfashi ya ɗan furzar da ɗakko kofin shayin ya miƙa mata. Cikin ɗashewar muryarta tace, “Ni na ƙoshi”.
A karon farko ya saki guntun murmushi dan shi dariya ma take bashi, yana dannewa ne kawai. Ya ɗan rufe idonsa ya sake buɗewa a kanta. “Shi borin naki ya shafi har cikinki da lafiyarki kenan?”. Ya faɗa cikin sauƙaƙa muryarsa har yanzu da murmushi akan fuskarsa. Baki ta tura gaba da ƙoƙarin zamewa zata sake kwanciya ya riƙota. Son zame jikinta take amma ya hana hakan, sai ma jawota da yay gaba ɗaya ta dawo jikinsa. Tsuma jikinta ya farayi, murya na rawa tace, “Nidai ka sakeni bana so”.
“An gaya miki nima ina so ne?”.
Yay maganar a hankali cikin kunenta. Da sauri taso janye jikinta amma ya hana hakan, murmushin dake son sake kufce masa ya danne, ya ɗakko cup ɗin shayin ya sake miƙa mata, ɗago idanunta da suka cika da ƙwalla tai ta kallesa, ganin ganda yay kicin-kicin da fuska ta maidasu ƙasa. “Bacci nake ji gashi kina ɓata min lokaci”.
So take ya fita ya barta dan haka ta amsa, ya ringa ya gama wucewa, dan haka ta kafa kofin a baki tai masa shan ruwa. Shi da kallonta kawai yake, ta miƙa masa kofin zata sake zamewa ta kwanta ya riƙota. Zatai magana ya harareta, baki ta murguɗa masa a kaikaice sai dai sarai ya ganta, baibi takanta ba ya ɓalla magani da ruwa ya bata. Tana gama sha bata yarda ta kallesa ba tai wuf ta kwanta tare da jan bargo ta rufe har saman kanta. Shima baice mata komai ba ya ɗauka wayarsa yana dubawa. Sai da ya tabbatar barcinta yayi nisa sannan ya ɗauka kofin data sha tea ɗin ya fito bayan ya kashe mata wuta....
A hankali ta sauke ajiyar zuciya dan likimo dama tayi ba barcin take ba. Ta ɗanji ƙarfin jikinta dama akwai yunwa tare da ita, sai dai duk da hakan jiri na ɗan ɗibarta kaɗan-kaɗan. Ƙofar ta tashi ta sakama key sannan ta cire kayan jikinta ta saka masu sauƙin nauyi, toilet ta shiga tayo alwalar kwanciya ta dawo ta haye gadon dajan bargon ta ƙudundune dan har yanzu sanyin bai gama sakinta ba.

Daga shi har ita makara sallar asuba sukai, haka ya sashi yin salla a gida, yana kuma idarwa ya koma ya kwanta kamar yanda itama a nata ɓangaren kwanciyar ta sakeyi. Barcine cike da idonta, da alama maganin daya bata yana saka barci.
Ƙarfe kusan sha ɗaya ta farka. Alhmdllhi babu zazzaɓin hakama ciwon kan. Sai dai jikinta babu ƙarfi kamar yanda zuciyarta babu daɗi. Ɗakin ta gama ƙarema kallo da yaba ƙoƙarin iyayenta duk da batajin zatai tsahon zangon zama a wannan gidan. Ta wuce toilet tana sake tabbatarma kanta taƙaitaccen zama zatai. Da ruwa mai ɗumi sosai tai wanka, koda ta fito har ta gama shiryawa babu motsin kowa, taci alwashin bazata ƙuntata kanta ba, ba kuma zata sake yarda tayi kuka ba zatai yaƙin barin gidanne da ƙarfin zuciya dana ƙwanji, dan haka ta gyara gadonta sannan ta fito falo. Anan ɗin ma komai ya mata ƙyau dan an saka kalar da tafi so ne a rayuwarta. Tai ɗan murmushi tausayin iyayenta na ratsata, da sun sani basu wahal da kansu ba ma. Kitchen ta shiga shima ta ƙare masa kallo har store dake cike da kayan abinci na gara. Ta shiga ɗayan bedroom ɗin nan ma komai abin birgewa. Tunawa da wayarta data baro bedroom ya sata komawa, ta ɗakko ta fito ta tuna bata shiga ɗayan ɗakin dake facing nata ba. Kanta tsaye ta shiga kamar ko'ina, tai turus da ganin wanda batai zaton gani ba a ciki. Zaune yake a bakin gadon da alama yanzu ma ya tashi a barci, buɗe ƙofar ya sashi ɗago idanunsa. Ita ta fara janye nata cike da basarwa taja baya da nufin maida ƙofar ta rufe tana ɗan tsuke fuska da faɗin “Good morning”.
Bai amsa mata ba, bai kuma janye idanun nasa a kanta ba harta maida ƙofar ta rufe. Cikin ɗan ƙunƙunini da murguɗa baki tabar wajen. Falo ta koma tai zamanta ƙafa ɗaya kan ɗaya tana kunna wayarta.
Agogon dake ɗakin ya kalla, ganin har goma da rabi tayi ya sashi miƙewa ya fito a ɗakin, harya nufi hanyar falo sai ya tsaya cak, da baya ya dawo ya buɗe ɗakin data kwana ya shiga. Bai damu da rashin samunta a ciki ba ya shige toilet ɗinta, wanka yayi tare da ɗaukar cikin sabbin brush ɗinta ya buɗe ɗaya yay amfani da shi. Towel ɗinta ya ɗauro, ya riƙo wani a hannu yana goge jikinsa. Gaban mirror ɗinta ya ƙarasa yana bin kayan kwaliyyar dake kansa da kallo ɗaya bayan ɗaya, iska ya ɗan furzar daga bakinsa, sai kuma ya nufi ƙofa, kaɗan ya leƙa kansa duk da yasan bawai zai iya hangota bane....
Har yanzu tana falon zaune abinta tana buga game hankali kwance, kai kace ba ita bace ta gama bori da rusar kuka ba jiya da sauran kwanakin da suka gabata. Jin kamar ana kiran sunanta ya sata ɗagowa takai dubanta ga hanyar corridor ɗin. Baki ta murguɗa jin ya ƙara kiranta cikin ɗan daga murya, cikin magana ƙasa-ƙasa da ba'ajin mi take faɗi ta miƙe. Harta nufi hanyar ɗakin data barsa ɗazun ta dakata sakamakon jin gyaran muryarsa a nata ɗakin, idanu ta zaro da riƙe ƙugu tana duban ƙofar, ta cije lip ɗinta na ƙasa cikin takun fusata da tsaurin ido ta nufi ɗakin tana wani ɗaure fuska ita a dole bazata masa ta sauƙi ba........✍



_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/23, 10:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*




*_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718


*_41_*


..........Gaba ɗaya tsiwar dake bakin nata ta maƙale akan harshenta, ta juya baya da sauri tana rumtse idanu ƙirjinta na bugawa da karfi. Duk abinda takeyi yana kallonta ta cikin mirror, cigaba yay da goge sumarsa kamar bai ganta ɗin ba, keys ɗin dake ajiye saman mirrorn ya ɗauka ya miƙa mata. “Je ɗakina ki samomin kaya....”
    Kafinma ya rufe baki tai gaba har tana neman yin tuntuɓe. “Da haƙwaranki zaki buɗe ƙofar?”. Ya faɗa cikin katse mata hanzari. Jitai kamar ta fasa ihu, amma sai ta daure idanu a rufe ta juyo tare da miƙa masa hannunta. Kansa ya ɗan girgiza ya ajiye keys ɗin ya cigaba da abinda yake yi. Kaɗan ta buɗe idanunta, tana tura baki gaba ta ɗauka batare data yarda ta kalli inda yake ba ta fice da hanzari. Haka kawai abin nata ya bashi dariya, amma sai ya haɗiye baiyi ba.
        Baki ta shiga taɓewa tana bin ko'ina na sashen da kallo. Babu dai tarkace babu kuma mugun datti, amma yana buƙatar gyara dan da alama shi yake aikin gyara da kansa tunda taji ance Fadwa na gida sai jiya aka dawo da ita. Bakinta dai bai furta komai ba ta buɗe wadrobe nashi. Anan kam komai a tsare yake, ga kuma ƙamshi kayan nayi. Taja wasu mintuna tana bin kayan da kallo daki-daki kafin dai ta zaɓi wanda suka kwanta mata a rai, cikin ɗan taɓe baki take faɗin, “Ko basu makaba dole ka saka, ko kunyar zama da towel a gabana baiji ba tirr” sai kuma ta taɓe baki, “Mutumin nan fa Sassaƙeƙen ƙato ne fa yasin” tai ƴar dariya da kai hannu ta buge bakinta.
     Tafiyarta take hankali kwance batare data lura da su ba, daga aunty Malika har aunty Safarah, Fadwa aunty Suwaiba sun saki baki suna binta da kallo harta wucesu, baya Fadwa tai kamar wadda jiri ke neman kwasa ALLAH ya sota akwai bango bayanta “Aunty kenan wajenta ya kwana fa?”. Ta faɗa hawaye na rigegen sakkowa. Su duka kallonta sukai, a ɗan hasale aunty Malika ke faɗin, “To ke kam dai lallai takaicin kishiya zai karki idan baki nutsu ba, kuma in har kika bari ta gano lagonki wlhy kin mutu. Mi kwanan nasa wajenta ya amfana masa tunda gata nan tsaye kan ƙafafunta babu alamar tanada daraja na mace a wajensa. Ashema kina kokwanto akan maganin nan?”.
    “Aunty ki fa......”
Cikin katseta Aunty Safarah tace, “K washe garin da aka kawoki gidan nan a haka kika kasance?”. Wata wawiyar ajiyar zuciya Fadwa ta sauke mai ƙarfi saboda tuno wahalar data sha a hanunsa a daren da aka kawota, washe gari kam komai bata iya hasalama kanta ba sai da taimakonsa, dan ko tafiya sai da taita cin azaba kafin ta dai-daita bayan kwanaki biyu, ta share hawayenta tana murmushi, tabbas ta yarda mijinta bai taɓa yarinyar nan ba, dan babu macen da zataje hanun mijinta a karon farko a ganta a haka, shi ɗin namiji ne, idan tace namiji, tana nufin namijin gaske... (🤕dama akwai mazan ƙarya? Ƴar uwa kisa a ranki kema mijinki namijin gaske ne😚😉).

          Anam da batasan sunai ba koda ta isa sashen nata bayan tayi sallama a ƙofar ɗakin cogewa tai taƙi shiga, sai ƙofar data buɗe ɗan kaɗan ta zira hanunta da kayan a kai. Yana zaune a bakin gadonta yana waya ya hango hanunta, ɗauke kansa yay kamar bai gani ba ya cigaba da wayarsa. Jitai hanunta yana neman sandarewa, ta harari ƙofar tamkar tana ganinsa, cikin tunzura baki ta shiga ɗakin, da baya-baya ta dinga tafiya a hankali harta iso gaban mirror, ido suka haɗa da shi ta ciki daga inda yake zaune dan ya gama wayar, da sauri ta kauda kanta ta ajiye kayan a kujerar mirror ɗin tai gaba. “singlet da boxer kuma fa?”.
     “Yayaaaa!”
Ta faɗa da sauri dajan sunan cikin salon kai bakajin kunya tana juyowa. Suna haɗa ido tai saurin sake juya baya “Ni dai babu ruwana”. Jin motsin tashinsa tsaye ta fice da sauri. Sai da ta gama yima ƙofar harara kala-kala sai kace wata ƴar yarinya sannan ta wuce ɗakko masa. Shima daga can ƙaramin tsaki yaja da faɗin, “Girma ba wayo”.
     Yanzu kam bata kai ɗazu daɗewa ba ta dawo, cikin dakiya da ɗaure fuska ta shigo ɗakin kanta tsaye, har gabansa taje ta ajiye ta juya ta fita batare data yarda ta kallesa ba. Da kallo kawai ya bita a ransa yana raya (anya yarinyar nan bata da aljanu ma kuwa?) rashin mai basa amsa ya sashi sake jan wani tsakin ya ɗauka kayan ya saka. Tana zaune a falon ta wani tsume kamar sarauniya a kujerar mulki ya fito, da farko tayi kamar bata gansa ba, sai da ya ƙara matsowa sosai taji ƙamshin turarenta a jikinsa. “Yaya satar turare ka koma kuma?”. Ta faɗa tana tsatstsaresa da idanu. Shi rasama mizaice mata yayi, zata ƙara magana akai knocking. Ɗauke idonsa yay daga kallonta ya nufi ƙofar ya buɗe. Cikin girmamawa Mubarak ya risina ya gaidashi. Kai ya jinjina masa yana amsawa.
     “Yaya dama breakfast ne akace a kawo”.
    “Okay ya mutanen gidan?”.
“Kowa lafiya yake”.
Komai bai sake cewa ba ya matsama Mubarak ɗin ya shiga, shi kuma ya nufi sashen Fadwa. Taso sharesa amma kwarjininsa da cikar haibarsa ta kasancewar sa namijin tsayayye da bazai ɗauka raini ba ya sata nutsuwa, idanunta a ƙasa tace masa ina kwana. Falon yake ɗan bi da kallo batare daya amsa mata ba, sake gaisheshin tayi a ɗarare, sai dai bai amsa ba yanzun ma, saima tambaya daya jeho mata...
     “Masu zugakin sun tafi kenan?”.
Saurin ɗagowa tai ta kallesa, ganin ya tsatstsareta da idanunsa masu kaifi ga fuskarsa a tsume matuƙa ya sata saurin maida idanun nata ƙasa sai dai ta kasa cewa komai. Ya furzar da numfashi mai zafi da zurfi. “Daga yau na haramta musu zuwamin gida, idan kuma sukai kuskuren sake zuwa ɗin zan ɗauka kowane irin mataki a kansu. Kema bazance karki ɗauka huɗubarsu ba, amma ki sani idan naci karo da wani hali a gareki saɓanin wanda na sanki da shi kamar jiya zakisha mamaki na”.
      “Humm” kawai tace a ƙasan maƙoshi, dan ta ɗauka zantukan nasa da suna borin kunya irin mazan da sukaci amanar matansu wajen ƙara aure. Sai dai kamar yanda su aunty Malika sukai mata huɗuba bazatace da shi komai ba, zatabi komai a sannu harta cimma nasara akansa daga shi har amaryar tasa. Humm ɗin tata ta matuƙar zafarsa da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login