*Sadaukarwa ga Ahalin Sharoo Gambo Yako,mazan su da matansu,alherin Allah yakai muku a duk inda kuke,nayi tawassali ga Annabi Muhammadu (SAW),Allah kai ruƙo da hannayena dan alfarmar ahalin manzon Allah (SAW)*
_Bissimillahirrahmanir raheem_
_wannan littafin nawa ƙirƙirarsa nayi banyishi dan wani ko wata ba,duk abinda kaga yayi dede da rayuwarka arashine_
_wannan daban yake da sauran,salonsa na dabanne,akwai abun dariya,zazzafar soyayya,tausayi,ƙiyayya,da ɗumbin danasani,karku bari abaku labari,kubishi sannu a hankali dan kwashe darasin dayake tafe dashi_
_surbajon ce de har yanzu,salo da basirar duk nata ne,nice da kaina ba saƙo ba,ga me_
*Ummu Aymana*
*Surbajo*
*Kano to jiddah*
*Karen bana*
*Sanadin kidnapping*
*Ɗan karuwa*
*Cin Amana Ko Fansa*
*Giɗaɗo ba Shege Bane*
*Allah Gatan Bawa*
*Ƴar Bautar Ƙasa*
*Aure Da Haihuwa*
Da de sauransu.ku kasance da wannan banufiya domin ci gaba da samun nishaɗi.😍
*1*
"Zahra'u ya kamata ki fito haka fa kizo ku wuce,tun ɗazu su hanne ke tsaye suna jiranki,bana son sakarcin banza fa"cewar wata dattijuya dake zaune kan kujerar zaman tsakar gida tana ɗaure nono a ledar siga.
Daga can cikin bukkar dake kusa da dattijuwar wacce aka kira da Zahra'u tace "Inna do Allah Do Annabijjo,ki barni in sa jambakina cikin kwanciyar hankali,ke bakisan in bakayi kwalliya ba ko kallonka ba'a yi?"
"aykin kawai,yo tun bara kike sa jambakin amma har yanzu ba mashinshini,se asarar kuɗin siya miki da nike yi"cewar inna daga wajen da take zaune.