About this Novel

 

Story Preview

THE WIFE'S SECRET

Bance ki karanta min littafi dole ba, wanda suka san me littafin ya ƙunsa sunsan amfaninsa, bazaku tsaya ku bibiyi labari ba sai ku fara tsegumi akai😂Ah to nidai na gaya muku
Page 1-2

Cikin ƙwarewa yake sarrafa sitiyarin motar, fuskarsa na cike da tsananin ɓacin rai, tsaki yake ja lokaci zuwa lokaci, har ya iso katafaren gidansu dake Maitama, cikin garin Abuja, wani mahaukacin horn ya danna mai ƙarfi, yayinda mai gadi ya buɗe masa get cike da girmamawa yana a durƙushe har motar Ab ta wuce inda ake parking, a tsakiyar jerin gwanon motocin da aka yi parking ɗinsu wanda a ƙalla zasu kai biyar, tasa ce ta shida, cikin takun isa da izza ya fito, kyakkyawan matashi ne wanda a shekaru zai yi 36yrs a duniya, dogo ne fari sol kamar balarabe, yanada ƙirirar jiki mai kyau bazamu kirasa sirri ba, saboda damatsen hannayensa a murɗe suke, hatta ƙirjinsa ma a buɗe yake ma'ana yanada faffaɗan ƙirji, sanye yake da wani lallausan yadi mai ruwan ƙasa, ɗinkin rigar iya guwaiwarsa, yayinda wandon ya kasance bashi da wani faɗi ya matse shi ba sosai ba, hannunsa riƙe da key care da wayarsa ƙirar Apple, kyakkyawan hannunsa da ya kasance da gashi luf-luf yana ɗaure da agogo ƙirar Samsung Galaxy watch mai kyau, kai tsaye ya fara tafiya har ya isa ƙofar da zata sada shi da babban parlor, da sallama ya ƙarisa ciki tare da neman guri ya zauna, kasancewar babu kowa a parlorn bakajin ƙarar komai sai na Ac da TV, wata mata ce ta fito zuwa parlor, matar fara ce tass suna kama da Ab sosai kamar tasu ma ta ɓaci, sai dai tanada ƙiba, sannan a shekaru zatakai 60yrs, faɗaɗa fara'art

Continue reading →

Reader Reviews

Login to leave a review.

No reviews yet — be the first.

Da Bazarmu Team

More Novels You May Like