Innallihi wa'inna alaihir raju'on, Farida waye ya take ki da mota har hannunki ya k'arya haka?"
Kuka Farida kawai keyi mai cike da tsananin rad'ad'in zuci da azabar da hannunta ke mata.
Kwance take akan gadon marassa lafiya, irin na asibitin. Hannunta ta kalla ganin yadda ya kunbura har yayi fushi da waya, wani miyau mai zafi ta had'e a mak'oshinta tana kallon abokiyar zaman Mahaifiyarta wacce duk ita ce silar shigarta cikin wannan wahalar, domin da baccin bata d'ora mata tallar da bata so ba, da duk hakan bata faru ba.
"Inna Zubaida wani ne a mota ya bige ni, kuma bai tsaya ba, yayi tafiyarsa, sai wasu Mutane k'alilan ne suka kawo ni asibitin nan"
"Dalla can rufe min baki, ai ni wallahi ni ce kika jama asara, yanzu ubanwa zaije wajan aikin ki? Kin kuma san inda kike aikin nan bafa mutumci ne dasu ba, kuma na rantse bazaki ja min salalan tsiya ba, domin idan aka kore ki daga gidan Alhaji Sammani B Radda Mai Naira ai na shiga uku na, dan haka yanzun nan kima tashi ki kama hanya mu wuce, dama tallar baifi ta wuni d'aya kike zuwa min ba, shine yanzu kinje kin shige ma titi kinja masu hannu da shuni sun bige ki kin barni da aiki".
Wata doctor ce da tun maganar Inna Zubaida ta farko take kallonta cike da mamaki, ta kasa hakuri ta kalleta ta ce.
"Baiwar Allah amma da alama bake ce kika haifi wannan yarinyar ba ko?. Domin da ki ce kika haifeta bazaki fara mata zancen rashin zuwanta wajan aiki da zatai na y'an kwanaki ba. Ke burinki kawai ta kawo miki kud'i kawai, baki gudun ma ace yau anje wani ya lalata mata rayuwa gaba d'aya?, miye zan.......
"Ke Kinga baiwar Allah, babu ruwanki a cikin sha'ninmu, ina ruwanki? Ke ke rik'eta ko ni? Ko kuwa ke ke d'aukar cinta ko shanta?. Kinga Malama ki sallame mu ma mu wuce gida".
Inna Zubaida ta k'are maganar tana hararar likitar kamar idonta zasu fad'u.
Girgiza kanta kawai likitar tayi tana sake duban Inna Zubaida ta ce.
"A sallame ku ai bai taso ba, saita samu sauk'i tukunna".
Rai a b'ace cike da da harguwa Inna Zubaida ta fara cewa.
"Ai ko kun samu mai biya mata magani, domin na rantse da Allah ko sisina bazatai ciwon kai ba, yawwa, gara ma ku sallame mu wuce a'ato, idan ma baku bamu sallama ba, yanzun nan zamu wuce sai naga ubanda ya isa ya hanamu tafiyar".
Likitar zata sake magana aka bud'e k'ofar d'akin aka shigo.
Shuru tayi tana kallon wacce ta shigo d'in.