Showing 189001 words to 190481 words out of 190481 words

Chapter 64 - Munafikin Namiji Complete Hausa Novel

Ya ɗaga labulan ɗakin yana daga bakin ƙofa ya dinga kallon yarinyar da kuma mahaifin nasu dake kwance ga Hanne dake kuka hannunsa ɗaya zube cikin aljihu ya ce "Ya akai?"

Nan take Hanne ta yi masa bayanin komai sai kawai ya saki labulan ya fita, ba jimawa ya dawo da bulalar darbejiya ya rufe ta da duka ya yi mata jahilin duka tas kana ya yar da bulalar ya ɗauki Giɗaɗo dake cikin kwance daman yunwa dukta cinye shi, ya nufi mota da shi yana zuwa ya samu abokinsa wanda tare daman suka zo ya buɗe motar suka saka shi a ciki, Muwab ya koma ɗaya gefen YAA B ya ja motar da wani irin sauri yabar unguwar. Bayan sun sauka Kano ya kai shi asibitin Aminu Kano teaching hospital, aka kammala komai tare da kwantar da shi ya nufo gida Muwab ya tafi gida shima. A main parlour ya samu Sadauki zaune shi ɗaya har ya yi sallama Sadauki bai ji ba, ya lula duniyar tunani Noor da suka baro a Japan suka dawo gida hutu, tun daga makaranta primary irin soyayyar nan ta ƙuruciya da wawta a ciki amma abin ya girmana komai yake Noor yake tunani.

"Kai da ubanka ba magana nake ba" sai a lokacin Sadauki ya ɗago kai yana haɗe fuska sosai ya ce "Ban ji ba"

"Tunani uban me kake da har nake magana baka ji ba"

"A'a yaya kawai ban ji ba" daidai nan Al'hussan ya shigo da kayan ball a jikinsa, Al'hussan kuma ya fito daga direction ɗin kitchen hannunsa riƙe da plate ɗin indomie, sai lemo a tare suka ce "Wlcm yaya"
Sadauki ya miƙe ya bar wajan abinsa yana shiga bedroom ɗinsu ya ɗauki jitarsa ya zaga zuwa lambu, Ridayya ta fito hannunta riƙe da farar riga irin ta likitoci ta saka glasses a idanunta, dake bayan su Al'hussan cikin data samu ta sake haifar tagwaye duka masa aka saka musu Jaheed da Junaid, ya sake samun wani cikin ta haifi namiji still aka kuma saka masa suna Talba, gabaɗaya yaran data haifa maza ne ake cewa mata uwar iyaye maza, Abbiey da har yanzu yake ɓoye shekarunsa ta hanyar kyakkyawan shiga da cima mai kyau da kwanciyar hankali shima ya fito daman sallama suka gama da Ridayya zata ta fi asibiti night duty gare ta, amma zata fara zuwa ta gaida Dada kakarta ta ƙara duba jikinta, kai tsaye Abbiey ya ƙarasa kusa da Alhaji ƙarami ya ɗora hannunsa a kafaɗarsa yana cikin tattausan jallabiya mai kyau da laushi hasken nan nasa har ɗaukan idanu yake, ya ɗaure sumarsa da ribbon ta sauka baya a hankali ya ce "Aboka nai ya kake?" Al'hussan ya yi murmushi ya ce "Abbiey ya zan tara gashi irin naka da YAA B kalle ku kamar wa da ƙani" Alhaji ƙarami dai bai magana ba sai kame fuska yake, Ridayya ta ce "Suma ina dawowa duk yanke shi zan yi ai musu kwalkwabo" a tare Abbiey da YAA B suka shafa kansu ta ce "And wannan fuskar taka ta yi kyau da yawa idan zaka fita shafa baƙi ai na ji labarin ƴan mata sun fara rushing akan ka, da kai da Sadauki kuna feeling kan ku wai ku samari ko? Karka fara saka ƴanmata suna mini sunturi a gida" ta juya ta kalli Al'hussan ta ce "And you too ba zan ɗauki ɗabi'ar ta ball ba zan bi duka na yayyaga kayan ball ɗin, karku manta nan gidan Ustaz ne ba gidan Professor ba. Ta juya ta kalli Al'hassan ta ce "Kai ba mace ba kai kenan a kitchen, ya kamata ka fara ɗaura zani ai da gayya daga yanzu azumin Alhamis da Litinin zaka fara" su dai duka kallon ta suke ta ce "Ina Sadauki?" "Ya shige bedroom" ta riƙe haɓa ta ce "Shi ban ma san layin daya ɗauka ba, banda nunƙufarci babu abinda ya iya ba zan ɗauki ba duk ranar da naga ƴan'uwansa a parlon ya shige bedroom zai San bashi da wayo" Abbiey ya ce "Saura ni" ta juya ta harare shi ya ce "kin haɗe kan yarana kin musu tas saura ni kawai, Kodayake ai an ce za a mini aski" ta yi murmushi sai a lokacin Alhaji ƙarami ya ce "Father is on the hospital" ya faɗa da fuska a dame duk sun fahimci wa yake magana akai, uba uba ne dole ya damu da mahaifinsa.

Burin Ridayya na zama cikakkiyar likita musamman a ɓangaren mata ya cika, bata da sauran damuwa komai ya zama tarihi idan ba magana akai ba sam ita ta mance farinciki da walwala kawai take da mijinta, idan suna Japan a can asibitin take aiki, daman yaranta duk a can suke karatu, idan sun samu hutu su dawo Naija a ziyarci ƴan uwa. Zainura ta haifi kyakkyawar yarinya mace Burhan ya saka mata Zainura saboda soyayya matar Junaid kusan tare suka haiho da matar Tajj, rayuwa ta yi daɗi sosai har yanzu kuma Yaya Zuhura bata samu mijin aure ba, hakan ya fara damunta duk ta zama wata kala. Hajja Azizat ta yi wa Bilal ƙanwa aka saka mata Rusul ta zama ƴar shalele sosai kuma Abbiey ke son Rusul kamar rai.

Gabaɗaya suna zaune a parlour suna jin labaran da yake trending a lokacin cewa ana neman wani TAHHB SCORPIO babu asalin photon fuskarsa sai wani da iya idanunsa ne sukai fito farare tas dasu "Allah ya shirya masa zuri'a, wannan ai abin tsoro ne shi a cikin al'umma" Sadauki ya ce "Kamar na san shi" Ridayya ta zare idanu ta ce "Wannan ɗan daban?" Ya sha kunu kamar shi ya yi magana ba can ya ce "MUTALLAB sunan shi...." Daidai nan Abbiey ya shigo ya tsaya ya ce "Mimi come" yana faɗa ya yi waje duk suka bisa zuwa compound, wata dalleliyyar baƙa ce a tsakiyar compound ɗin, ga decorations alamar na gift ne ta zaro idanu ya miƙa mata key ya ce "For me?" Ya ɗaga mata gira ya yi murmushi, ta yi sauri ta rungume shi Sadauki sai murmushi yake YAA B ma yana can tsaye yana musu bidiyo a hankali Abbiey ya ce "Today is our anniversary day, take this as a gift Mimi" tai ta masa godiya Sadauki ya ƙarasu ya ce "Mimi muga key" ta miƙa masa ya shiga motar ya fara gwadawa "I love you" ta ce "Na gode sosai man ban san me zan ce" kawai ta fashe da kuka ya rungume ta ya ce "Say Allahamdulilah" tana murmushi idanunta akan yaranta gata kusa da mijinta a hankali ta ce "Allahamdulilah!....."

End

Komai ya yi farko yana da ƙarshe babu wata ƙaddara da take tabbata, babu wata ƙaddara da bata da lokaci idan mutum ya yi haƙuri. Haƙuri yana da ribar kamar yadda Ridayya taga ribar shi a yanzu, duk baƙin cikin mutum hassadar shi idan Allah ya ce zai ka kai to tabbas zaka kasance, ku yi haƙuri da gidan mazajenku watarana sai labari mai haƙuri ya kan dafa dutse ya sa roman shi, a daina baibaita yara ƴaƴan kishiya ƴaƴa ne, baka san wanda zai jikan ka ba, da yara da dukiya daban suke a kuma daina aibata halittar Ubangiji domin yin hakan kana nuna Ubangiji bai iya halitta ba. Nan na kawo ƙarshen littafin MUNAFUKIN MIJI

Domin yin gyara ku sharshi ƙofa a buɗe take 08164069385

Wattpad ina godiya da haɗin kan da kuka bani ina jiran last comments ɗinku😍

WhatsApp Arewabooks Facebook duka ina godiya ina jiran jin sharhi, a yi haƙuri a bisa rashin posting an samu matsala ne kuma hakan bai taɓa faruwa dani ba kuma daga wannan ba za a kuma ba in sha Allah.



BRIGHT PENS
na godiya da jimirin bibiyar littafanmu a karo na farko CUTARWA, YI WA KAI, MUNAFUKIN MIJI, ƘUDIRAR ALLAH. ku jira mu a second batch in sha Allah.

Zan dawo cikin littafin *MUTALLAB* labarin Mutallab daban yake zan so ko wacce uwa ta karanta, zan so ko wacce budurwa ta karanta, zan su ko wanne namiji ya karanta. Bani da tabbacin zai yi daidai da ra'ayoyinku amma ina da yaƙinin kuka fara karantawa ba zaku daina ba, rubutun zanen ƙaddara a nan nafi ƙarfi da saka idanu zubar da hawaye. Amma wannan salon na musamman ne ban taɓa yin irin shi ba kawai ku biyo ni a labarin MUTALLAB ma'ana dai MUTALLAB TAHHB SCORPIO.
************* Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels



Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login