Showing 162001 words to 165000 words out of 190481 words

Chapter 55 - Munafikin Namiji Complete Hausa Novel

na farko kuma kusan na biyu.

Murmushi ya suɓuce masa dukda cewa idanunsa a rine suke tana iya hango yadda ƙirjinsa ke ɗagawa. Kallon Ridayya kawai yake irin kallon dake nuna, I love you so much, the kind of crazy love that even in Ustaz's eyes she has never seen that. Har ya juya sai kuma ya sake tsayawa irin me ya sa zan tafi? Why should i do that? Ridayya ce fa? Ba zata taɓa cin amanar shi ba, ya aminta da ita aminta mai yawa amintar da har zuciya da gangar jikinsa sai da suka shaida hakan, murmushi ya dinga yi shi kansa bai san dalilin faruwar murmushin nasa ba.

"Wow! U look so beautiful shanshan kin sauya a idanuna sosai" yana magana yana ɗan hargitsa sumar kansa alamar ya fara fita daga yanayin da yake na Hamza zuwa na Sadauki.

Ya zubawa cikin Ridayya idanu domin tabbatar da abinda zuciyarsa ke ayyana masa, idan cikin gaske ne mene haɗin budurwar da zai aure da cikin haihuwa? What bring her here? Me ta ke yi a Japan?

Ƙara matsawa ya yi wajanta ta girgiza masa kai irin ya dakata ɗin nan, he just trying to get more close to her a gigice Ridayya ta ce "Stop it, Stop it Stop it Sadauki" jikinta duka rawa yake tsoro da fargabar yanayin Sadauki ya saka mararta riƙe wa, idan ta tuna cewa Abbiey na hanya kamar yadda ya ce sai ta ji kamar abinda ke rayuwa a cikinta zai fito zuwa duniya ne, bata san hawaye ke fita daga cikin idanunta sai da ta ji saukar yatsar Sadauki manuniya ya sharce hawayen ta ɗago ta kalle shi ya mata murmushin a hankali nunfashinsa na sauka da kyar a fuskarta ya ce

"Wai Shanshan wannan sabon yanayin fa? Bai dace dani ba na miki wani abu ne?" A taushahe ya yi maganar Ridayya ta kasa cewa komai bata san haɗa idanu da shi tsananin tausayinsa ke addabar zuciyarta, ta san ta masa laifi kuma laifi mai girma "Sadauki ka fahimta mana!" Ta furta a fusge tana ja baya ya bita ya ce "Me zan fahimta bayan abinda na fahimta yanzu? Ki barni kin wofintar dani saboda muradin ki yi karatu? Tunaninki ba zan bari ki yi karatu ba ko mene? And wannan guje-gujen na mene eh?"

"I am sorry very very sorry Sadauki "

"Sorry for what? Zan jira ki zan dinga dakon soyayyar ki a nan ɗina" ya nuna tsakiyar ƙirjinsa da hannunsa ya ce "Har zuwa ƙarshen numfashina, bani nake son ki ba Ridha ruhi da zuciya da gangar jikina ke ƙaunar ki, bana son komai sai rayuwa dake kawai so nake ki riƙe hannuna mu yi rayuwa tare.....,"

"I am sorry Sadauki ka yi haƙuri don Allah...," matse kafaɗunta ya yi idanunsa a rine ya ce "What wrong with Shanshan? Hakurin mene na miki uzuri na fahimci cimma muradinki zan jira da gaske zan jira ki, so halitta ne kuma jarrabwa ce na jarabtu akan ki Shanshan kawai ni ina son ki"

"Ciki gare ni Sadauki ciki ne dani haihuwa zan yi, na haramta a gare ciki gare ni Hamza Sadauki "

Ba kansa ne kawai ya harba ba hatta zuciyarsa sai data girgiza tana neman rabewa biyu a tsakiyar ƙirjinsa, kalmar CIKI kawai yake masa yawo komai nasa yana warware ƙirjinsa na matse masa guri guda, murmushi ya yi mai kama dana masu jin tatsuniya a fusge ya ce "Ciki? Wasan banza kenan" Ta girgiza kai ta ce "Da gaske nake"

Ya tausasa murya ya ce "How? A gida an sani? A ina kika same shi? Kin san uban cikin?"

Ta yi shiru kawai domin tana da yaƙinin Sadauki ba zai fahimce ta ba, tana kuma shakkar faɗa masa cewa ta yi aure ne, cikin sunna ne maƙale a mararta. Sadauki yana da naci da taurin kai kafin ta gama yanke shawarar abin yi ta ji ya damƙo hannunta ya ce "Ciki Ridayya? Abinda ya kawo ki makaranta kenan?" "Ba zaka gane ba Sadauki Please let go of me kar ka saka na shiga fushin Ubangiji"

"Fushin Ubangiji na nawa Ridayya? Kin san me kika aikata zina? Har da cikin shega" a gigice ta ce
"Ba cikin shege bane Sadauki, i am a married woman, am married and live with my husband in this country, ba abinda kake tunani bane wannan dalilin yasa nake baka haƙuri"

Sakin ta ya yi a karo na farka na rayuwarsa a gaban mace idanunsa suka zubar da hawayen da bai shirya zubar su ba, yin kansu kawai sukai ba kuma iya idanunta ke hawayen ba hatta idanun zuciyarsa kuka take ya dafe kai ya shiga kaiwa da kawowa ganin tunaninsa ya yi hijira ya saka Ridayya ɗaga ƙafafuwanta da ƙyar ta bar wajan tsakanin gittawar mintuna ya juyo yana cewa "stop kidding me dear kina son zuciyata ta buga da gaske na san ba za ki iya karya alƙawarin da kikai mini ba, idan na yi magana ne ki yi yafe mini na tuba na bi Allah na biki Ridayya....,"
Shiru! Shi kaɗai yake kiɗan shi da rawarsa babi ita babu ko inuwarta da sauri ya rufa mata baya domin yasan wasa take masa.

Bata ko ganin gabanta a haka take tafiya hannunta duka biyun riƙe cikinta hawayen tausayin Sadauki yaƙi tsaya mata, sama sama take jin ƙarar horn a bayanta a hankali kuma motar ke tafiya tana bin sahun ƙafafuwanta jin haka ya saka Ridayya matsawa gefe domin bawa motar hanya itama motar tsayawa ta yi a gefe. Bai jira an buɗe masa ba ya buɗe da kansa ya fito, jikinsa sanye brown ɗin suit mai kyau ya fito da ƙafarsa ya fito hannu ya ɗagawa wani ya dakata slowly yake tafiya har ya cimmata. Ƙamshin turarensa ta ji ta tsaya ba dai ta juyo ba sai da ya ƙara su ya ɗan taɓa kafaɗarta da sauri ta juya tana goge hawayen fuskarta ta ce "Abbiey"

Ya ɗaga mata gira biyu idanunsa nutse a kanta da ƙyar ta yi yaƙi da zuciyarta wajan dakatar da kukan ta ƙirƙiri murmushi ta aza a fuskarta tana matsawa wajan kusa MB USTAZ ganin a gaban jama'a tana neman shige masa ya yi saurin kama hannunta yana bata side hug tare da tafiya da ita a hankali har zuwa wajan mota key ɗin dake hannun John ya amsa yana basa umarnin neman abin hawa ya buɗewa Ridayya gaban motar ta shiga kana shi ma ya shiga bakinsa ɗauke da addu'a ya fara driving zuwa direction da zai kai su gidan da suke a nan Japan ɗin. "Ni fa ban ɗauka da gaske yau zaka dawo ba Abbiey" bai ce mata komai ba ya dai juya ya kalleta ganin yau halin ya motsa ya saka ta yi shiru can ta ce "Ya hanya ka dawo lafiya? Ya su Umma, Mami, Baba ƙarami da Baffa?" Bai amsa ba sai sautin karatun ban daya ƙaro yana lumshe idanunsa a hankali yake kuma tuna yadda ya ruski Sadauki da Ridayya domin ya gane Sadauki sosai tun a gidan su Tajj da yadda ya riƙe mata hannu da ƙoƙarin rungume ta da ya yi ya cije lips underneath his breath ya ce "Allah ya yafe miki Ustaza"

Sadauki ikon Allah ne kawai ya kai shi hotel ɗin da yake zaune ko wajan abokinsa Riyad su yake ya auna maganar Ridayya a ma'auni na hankali amma sam yaƙi samun gamsuwa da maganar ya ji yaƙi yarda dole ne ya sake ganin Ridayya domin this time around ƙafarsa ƙafar Ridayya zuwa Naija zuciyarsa gabadaya ciwo take masa, he feels like uwa wani abu ke shirin faruwa dashi. Wayarsa ya dauka shiga duba picture ɗinta a hankali yake bin baƙar fuskarta da kallon fararen idanunta masu kyau da tsari ga wasu irin abubuwa na musamman a cikinsu ya yi murmushi yana manne wayar a ƙirjinsa a hankali ya ce "Rest of my life" ya sake lumshe idanunsa underneath his breath ya ce "Shanshan my love" Number hajiya Azizat ya kira ta jima kafin ta ɗaga ya yi shiru itama ta yi shiru can Sadauki ya ce "Are you still crying mother?" Ta cikin wayar ta ce "Kuka kuma? Do i look like a baby to u Hamza?" Zai yi magana ta ce "Ya isa now tell me ya Japan yaushe zaka dawo kuma" Ya cije lips "guess what?"

"No idea son"

"I meet Ridayya"

Da sauri kuma cikin ɗaga murya Hajiya Azizat ta ce "What! Ka yi mata magana a can kuma Japan ɗin?" Cikin rashin fahimta Sadauki ya ce "Me ya sa ba zan mata ba? Bayan da tunaninta kullum nake kwana da tashi, i meet her i talk to her ta sauya sosai na ji kuma na ƙara son ta fiye da ko wacce rana data shuɗe"

"Innalillahi wa'inna illahir raji'un!"

"Wannan salatin fa?" A kasalance ta ce "Stay away from her"

Shuuuuu! Ya ji abu ta cikin kunnensa yana shigewa ya kasa cewa komai sai kawai ya kashe wayar gabadaya ya kasa yin wani ƙwaƙƙwarar tunani. Riyad ya kira ya ji yaushe zai shiga makarantar su Ridayya ya faɗa masa sai basa wani secret abu yana buƙatar information akan haka.

Ridayya na zaune hannunta riƙe da honey ɗin da maid ɗinta Ilhas ta haɗa mata, matar ta jima a gidan MB USTAZ ne da kansa ya saka aka nemo masa mace mai hankali wacce zata kula da Ridayya da abinda yake cikinta, shi kansa da yake namiji bai taɓa ganin ciki mai girman na Ridayya ba, ga tafiya ta saka shi gaba kuma yana tsananin tsoron barinta ita ɗaya, komai yake hankalinsa yana kanta. Mai aikin ta ce "Madam kina huta sosai ƙafafuwanki sun kumbura ga ƙirjinki yana yawan ɗagawa kamar mai matsalar numfashi, cikin ya yi girma dukda da bai shiga matakin haihuwa ba" Ridayya ta ja ajjiyar zuciya tana shafa cikin har yanzu Sadauki ne ke yawo a zuciyarta cikin sauri jima take yin Assatagafirullah! A gajarce ta ce "In sha Allah zan kula"

"Me za a tafa muku naga Alhaji ya shigo"

"No; kar ki damu da abinda za mu ci zan kula da wannan ki yi abinda kike so kawai" Ilhas ta jinjina kai domin bata jin daɗin jikin nata amma tabbas Ridayya na buƙatar kulawa ta musamman. Fita ta yi domin iyaka cin ta ƙaramin parlon gidan ganin hakan ya saka Ridayya miƙewa bayan ta kammala shan zumar ta nufi shashin da ta san gwarzonta na ciki, ƴar ƙaramar riga ce a jikinta silver mai sauƙin nauyi domin zafi jikinta ke yi mata dukda weather na ƙasar, rigar iya cinya jikinta duk a bayyane ga cikinta a gaba sumar kanta a tufke har baya gwanin sha'awa. Tura ƙofar ta yi sallama ta yi cikin siririyar muryarta mai cike da nutsuwa da tarin rauni tana shiga yana fitowa daga wanka murmushi ta yi ta ƙarasa bakin gado ta zauna tana miƙe ƙafa ta ce "Yau me ya samu Yaa Bilal ne?" Showel ɗin hannunsu ya miƙa mata ta gane me yake nufi ta maƙale kafaɗa ta ce

"Ni ma na ga ji fa"

"To tasar mini a ɗaki" Ta dinga dariya tana kallonsa ganin yadda ya kame fuska sam bata san fushin me yake ba, dukda bai nuna ba amma ta san dole akwai wani abu a ƙasa tana kallonsa ya gama shirya wa tas sai baza ƙamshi yake ya fito a cikakken mutum mai cikar zati gwarzon Ridayya mijin Ridayya yayan Ridayya jigon Ridayya ta ko wacce fuska, kusurwa ko wanne sashe. Jallabiya ya ɗakko zai saka yana sane ta yi saurin miƙe fuska a shagwaɓe ta ce "Abbiey Please na" Tana taɓa shi ya yi saurin damƙo hannunta ya haɗa ta da jikin wardrobe ta fara zazzare ido ya dinga kallonta ya ce

"Wana kama?"

"Ni ni.... A a bani ba"

Yanayinsa ya bayyana tuni shiyasa ko magana baya son yi ya sauke mata numfashi a ƙirjin "Ke kina tura mini stickers da emojis na kisses, a hall meeting"

"I am sorry"

"Nooo!!"

Magana za ta yi kawai ya kashe hasken ɗakin bisa sunna ya nufi bedroom....... Ƙafarta yake danna mata a hankali kumburin na sauka tana kwance gefensa karatun kur'ani suke saurara duka suna bi a hankali wayarta a hannunta ta shiga X tana rubutu can ta ji ya kashe karatun ya rungume ta very tight a jikinsa zuciyarsa na bugawa sun jima kana ta zuba masa ruwa mai sanyi ya kalli ruwan ya saka hannu ya amsa ya ajjiye ta ce "Kasha mana" "ban so"

"Me kake so"

"You!" Ta zuba masa ido yana ƙara riƙe ta a jikinsa "You Ustaza i want you Ridherh, I need u jaririya i want u always to be by my side I love you, I really really loves u Nisful hayaat" ya sumbaci kuncinta bayan ya gama maganar.

Gaban Ridayya ya faɗi akwai abubuwa da Abbiey ya kamata a ce ya sani amma ba zata taɓa iya faɗa masa ba, ba zata iya ba ita haka ƙaddararta take zama da MUNAFUKIN MIJI ya rusa dukkan wani jin ɗaɗinta ya taɓa career ta. Kallon juna sukai ta ce "About yesterday a makaranta" ya yi shiru ta ce "Sadauki Abbiey..." Ya yi saurin rufe mata baki da yatsu biyu ya ce "It's ok"

"Ya zo wajena....," ya watsa mata wani kallo jikinta ya yi sanyi calmly ya ce "I trust you ok"

Ta jinjina kai tana komawa jikinsa ta kwanta “I love you” da sauri ta miƙe tunawa da zata ɗora girki ga dare na yi ta kusa faɗuwa ya riƙe ta ya ce "Zauna"

"Abinci zan yi fa baka ci komai ba"

"Na sani, akwai maid za ta yi" ta maƙale kafaɗa ta ce "Bana son mai aiki ta yi maka salon ta barbaɗa wani abu"

"Kina tsoran snitching"

Gwalo ta yi masa har ta tafi ta dawo kamar zata ɗauki wani abu ta yi masa kiss ya girgiza kai kawai yana lumshe idanunsa. Ridayya taƙi komawa makaranta saboda tsoron gaminta da Sadauki sosai take jinsa a zuciyarta da shakkar haɗuwa da shi. Soyayya suke mai cike da kwanciyar hankali da fahimtar juna gashi kullum sai Ustaz ya bata magani ya kuma yi mata addu'a wani lokaci kuma ya sauya mata hira don ya fahimci aikin maganin, ya gujewa zuwa Nigeria yana buƙatar zama kusa da iyalinsa da bata kulawar daya dace ita da abinda ke cikinta. Suna da fahimtar juna amma hakan baya hana su samun saɓani wani lokacin Ridayya ta dinga kuka tana ita gida kawai zata koma shi kuma ya birus da ita idan ya gaji da jin kuka ya dafe kumatu ya ce "Oh ni mijin kwaila naga ta kaina, wanne zunubi ne wannan Ustaza?" bata yin komai sai girka musu abinci da wanke kayan Abbiey na sirri domin ta ce gajerun wandonansa sirrinta ne. MB USTAZ a zuciyarsa yake tsananin haɗuwa da Ubangiji akan hakkin Mardiyya ya kasa sauke nauyinta dake kansa har zuciyarsa kuma babu saki a tsarin rayuwarsa yana jin da zarar Ridayya ta sauka za su koma ya daidaita kan matansa ya yi addu'ar Allah ya bashi ikon kamanta adalci a tsakaninsu gashi daman an ɗaga zaɓe sai zuwa watanni bakwai masu zuwa...

Umma na zaune a parlour look so worries tunanin inda za taga Babban mutum kawai take ta ji a ranta fushi ya yi saboda ta saka ya saki shegiyar yarinyar can wacce bata san wacce duniya take ciki ba, gashi abubuwan hannunta na neman gazawa ta yi siyayyar haihuwar Mardiyya gashi da sauran rina a kaba Diyya ta ce kayan fitar suna kala ashirin take buƙata, filin da ya yi saura wajan Umma ta mallakawa cikin Diyya ta saka sunan Mardiyya har da shaidu abin duniya ya fara yi mata zafi ita hakan duk bai dame ta ba ɗanta kawai take son gani, gashi har mujiyar yarinyar ba labarin su ta kalli Baba ƙarami ta ce "Ka yi wa Allah ka faɗa mini inda yarona yake ina so na ganshi ga matarsa na dab da haihuwa duk wasu responsibility nata yana kansa ka ji tsoron hakki Abba" "Responsibility?" Baba ƙarami ya maimaita ta ce "E, hakkina na uwa dana matata dana cikin dake jikinta nasan kasan inda yake duk duniya bashi da wacce ta fini wallahi"

"Hajiya Hadiza kenan ashe kin san ya sauke hakkinki na uwa ke kuma ba ki san ki sauke nasa ba ko? Ko a naki tauhidin babu haka halan? Ke da kan ki kika saka ya saki matarsa dukda kin fi kowa sanin irin son da yake mata, kika zana masa kashaidin zama da wacce kike ganin ta dace da shi, while ya miki abinda kike so shi ma soyayya ta saka ya yi abinda yake ganin daidai ne 50/50. Bari ki ji duk abinda ya faru ki kuka da kanki babu wanda ya ja miki sai ke, kin ɗauki son zuciya ki sawa ranki ki kasa yadda da ƙaddarar Ubangiji ki kasa tunanin dukkan abinda ya faru muƙaddari ne daga Indallahi, wallahi tallahi sai Allah ya tambaye ki hakƙin Muhammad domin raya kiwo ne a gare mu"

Cikin fusata ta ce "Na gaji Alhaji Tahir na gaji ni duk ba kaga irin baƙin cikin dana haɗiya ba? Wacce uwa ce zata zuba idanu ɗanta yana wahala akan abinda nake tunanin yafi ƙarfinsa? Ka duba ƙaunar daya nuna mata ya sadaukar da farincikinsa samartakarsa just because of her? Who is she in the whole world? Ƙiri-ƙiri ta kalli tsabar idanunsa ta ce masa Allah ya isa ta tsane shi saboda mijinta Zameer ta kalli idanunsa ta kira shi da sunan da ko ni shaƙar faɗa masa nake, tun tana zanin goyo yake ɗawainiyya da ita komai ya samu ita, sai yanzu da komai ya ƙare mata zata dawo wajansa don taka bashi da zuciya a kanta, to wallahi tallahi ba a haifi wacce zata wulaƙanta mini yaro ɗaya tal a duniya ba, kuma ina kan bakata bana son Ridayya bana ƙaunarta gwara da Allah ya raba su balle baƙin cikinta ya kar ni"

"Idan baƙin cikinta bai kashe ki ba, rabo zai kashe ki"

"Me kake nufi what do you mean by that eh?"

Ya miƙe tsaye ya ce "Kin ji ai, ki raba kanki da rabo ki ji tsoron rabo tun wuri ki amshi ƙaddara, daga ƙarshe ƙofar da kika saka a ɗakin babban mutum sam bai bata dace da ɗakin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login