HAJAR

Chapter 54 of 85

abinci..", Nurain couldn't help it but to smile lightly, she's so childish, tsuke fuska yayi kamar ba shi ya gama murmushi ba yace "Au kina zaune a gidansu zaki ringa musu rashin kunya, idan suka miki wani abun ke kika jiyo... c'mon get up ki nemi wani abin ki dafa kici, ko babu abinci ne a store..?", ta dena kukan tana shessheƙa tace "Ni spaghetti na nake so bxn iya dafa wani ba..", ta ɗora kanta kan cabinet don ynxu strength din mganar ma babu, she start be coming more weak than before, Nurain ya buɗe fridge ya ciro ƙatuwar bottle din sweetened fresh milk, cupboard ya buɗe ya ɗakko glass cup ya wankesa a sink, tini ya ɓalle murfin bottle din saida ya kusan cika glass cup din da fresh milk snn ya mayar da bottle din fridge, ya duƙa gabanta ya ajiye glass cup din madaran, ta ɗan kallesa sai kuma ta dubi cup din madaran, miƙewa yayi yana jan rigarsa ya nufi ƙofa ya buɗe ya fita, after few seconds Hajar ta ɗauki cup din madaran tana turo baki, lokaci guda abinda ya faɗa akan Aljanu yayi hitting brain dinta, sai kace muzuru a lefe haka tabi kitchen din da idanu, ba tasan lokacin da wani ƙarfi yaxo mata ba ta miƙe bayan ta suri cup din madaran ta fita da sauri, still a palour ta gansa kan doguwar kujera yana latsa wayarsa TV da ya kunna tana aikinta ita kaɗai, Hajar dai ta rakuɓe ta zauna gefe guda ta kafa kofin madaran a baki, saida ta kwankwaɗe tass snn ta diri cup din, after 10mins bayan madaran ya faɗa mata ta miƙe ta shiga kitchen, a buɗe ta bar ƙofar ta ajiye cup din a sink ta fito da sauri, walking like a chameleon ta nufi stairs, Nurain ya bita da kallon wutsiyar ido har ta ɓacewa ganinsa, tashi yayi ya zura slippers dinsa tare da jan rigarsa ya kashe kayan kallon da duk wasu kayan wuta na palourn, da haka ya haura sama yana brushing sumarsa with his hand, yana haure stairs ya ganta tsaye bakin ɗakinta jingine da bango, har ya wuceta yaji tace "Ai a kitchen kawai suke ko..?", ya zuba both hands dinsa a pocket ya juyo yace "Su wa..?", tace "Aljanun..", har zai ce mata Eh sai kuma ya fasa don so yake yayi teasing dinta yace "No daman a waje biyu suke a gidan nan, da kitchen da kuma nan" yayi pointing ƙofar ɗakinta, zaro lulu eyes dinta tayi kamar zasu faɗo ta kalli ƙofar ɗakin, da sauri ya sunkuyar da kansa ganin yadda ta zaro ido sai kuma ya ɗago bayan ya haɗe gira, Hajar ta yarfe hannu tace "na shiga uku..", yace "A'a baki shiga uku ba tinda kin iya rashin kunya, don haka saiki zama ready kiga abinda zasu miki tinda kin yiwa ƴan uwansu rashin kunya..", wani irin zaro ido tayi tana girgiza kai tace "wllh ban musu rashin kunya ba, a ina na musu rashin kunya, kawai fa cewa nayi sai sun biyani abuna, kai kaji lokacin da na musu rashin kunyar..?", ya ɗaga shoulder yana taɓe baki, yadda ta wani gigice tana zaro ido ne yake basa dariya, daman gashi tubarkallah akwai idanun bare ta zarosu, tace "kuma ni yanxu ma na yafe musu na bar musu abincin halak malak..", yace "kin bar musu knn..?", ta gyaɗa kai sai kace lizard tace "Eh halak malak", yace "Alright shiga ki kwanta..", ta juya tana kallon ƙofar ɗakin sai kuma ta juyo tace "babu abinda za suyi min ko..?", yace "may be", har ta kai hannu zata buɗe ƙofar sai kuma ta fasa ta juya tace "dan Allah baza suyi min komai ba...", tsaki yayi ya buɗe ɗakin ya shiga yace "kin fi kowa iya rashin kunya da tsiwa amma ga tsoro sai kace me, c'mon malama shigo ki kwanta..", ba musu sum sum ta shiga ɗakin ta nufi gado, ya bita da kallo ganin yadda hijab dinta ke jan ƙasa kamar zai harɗeta yace "ba dai da wnn blanket dake jikinki zaki kwanta ba...?", nan ma ba musu ta kware hijab din ta ajiye ta wuce ta haye gado, saida ya tabbatar ta kwanta ta rufe legs dinta zuwa neck da duvet snn ya nufi switch din ɗakin, kashe hasken yayi ya bar mata dim, kawai sai Hajar taga kamar gaba ɗaya ya kashe wutan don duhu ta gani dunɗum, afujajan ta yaye rufar tayi kneeling kan gadon ta tsala ihu, bai san lokacin da ya bar bakin switch ba ya hau kan gadon ya toshe mata baki, tana jin present dinsa daf da ita ga kuma ƙamshinsa tayi sauri ta faɗa ƙirjinsa ta sakar masa kuka, ba wai a tsaye yake ba bare yace ƙafarsa ne ya shanye ji yayi kamar an zare masa spine gami da caka masa wani allura a ƙwaƙwalwa, bai san lokacin da ya tafi luu ya faɗa kan gadon da bayansa ba ita kuma ta faɗa ƙirjinsa fiye da da, ta wani lafe a jikinsa harda gyara kwanciya don wani secure take jinta a nan ɗin, gani take ba wani harm da zai zo gareta a jikinsa don haka tayi lakur abinta, after a while ba tasan ta yaya ba kawai taji hannunsa cikin rigarta, da sauri ta buɗe idonta da ta lumshe ta fara shirin ɗagasa, yayi saurin mirginasu ta koma ƙasansa, pillow ya janyo ya ɗora kanta a kai ya koma gefe ya zauna zuciyarsa na racing, ta ja duvet ta lulluɓe jikinta don gaba ɗaya rigar baccin ta kwaye, shi dai bai sake kallonta ba yana yaƙi da abinda yake ji, can dai ya juya ya kalleta ganin yadda take sauke numfashi ya rage murya yace "Hajar", sau uku yana kiran sunanta amma no response, ya tashi a hankali ya nufi ƙofa don har lokacin bai dawo normal ba.

★Umma na zaune tsakar gida tana tsince waken alale, Sabra ce kusa da ita da uniform tana cin wainar gero da ƙuli ƙuli da Umma ta bata kuɗi ta siyo, Umma tace "marmaza ki cinye ki tafi karki makara auta", Sabrah tace "toh Umma" sai kuma ta dauki rabin wainar da ta rage ta lunƙuma a baki, ta tashi ta wanke hannunta daga nan ta shiga ɗaki ta ɗakko jakar makaranta, saida ta shiga wajen Baba ta gaishesa ta amso kuɗin makaranta kafin ta wuce makarantar, Umma ta koma bakin rariya tana wanke gwangwanaye, Sa'adatu ce ta fito sai soshe soshe take sbd cixon sauro da kuɗin cizon da ta sha, ta ɗauki buta ta zuba ruwa tana gyatsine, tsaye tayi kan Umma ta riƙe ƙugu tace "malama ban hanya zan wuce", ko kallonta Umma ba tayi ba ta cigaba da abinda take, idan ba iskanci ba ga isasshiyar hanya nan da zata wuce ta shiga banɗakin amma sbd rashin mutunci wai sai ta inda Umma ke zaune zata wuce, har wani girgije girgije take tace "wllh ko a matsamin ko na bi tako ina ma, mutum da gidan ubansa anzo an baza shirgi ta ko ina, can an zube wake nan kuma an baza gwangwanaye, a matsa min ko in taka in wuce..", da sauri Sa'adatu ta waiga jin ana buɗe sakatar ɗaki, Naseer ya fito daga ɗakinsu fuskarsa a haɗe yace "waye yake mgana a tsakar gidan nan?", simi simi Sa'adatu ta kewaye Umma ta wuce toilet tana ƙunƙuni, Naseer ya koma ɗakinsu yana ƙwafa, don aikinsa na kwana ne wllh da sai ya gyarawa marasa kunyar yaran nan zama, tin jiya ma yaso tafiya amma bai tafin ba sbd Baba yace ya jira yau masu neman auren Nabilah zasu zo, Umma ta ajiye soson hannunta zuciyarta na mata zafi, ya za ai yarinya ƙarama ta giggilla mata wnn rashin kunyar, kawai sai Hajar ta faɗo mata, tabbas da Hajar na nan Sa'adatu bazata ci bulus ba saita mayar mata da martani, ynxu tinda babu Hajar akanta za suyi durango knn, daman Maimuna ta fara addabar Sabrah da ƙeta da mugunta. Da yamma Naseer ya shigo gida yana kallon Umma yace "Umma ki bada tabarma inji Baba", Umma dake tankaɗe tace "tom" ta tashi tana kaɗe hannunta ta shiga ɗaki, babu jimawa ta fito da tabarma ta basa, Maama da ta fito daga kewaye ta bi Naseer da kallo har ya fita, After like 20mins Baba ya shigo gidan tare da Naseer, Naseer ya miƙawa Umma tabarma yace "gashi Umma", amsa tayi ta shiga da ita ciki, Baba ya dubi ƙofar ɗakin Maama yace "ina uwar Nabilah", fitowa Maama tayi tana riƙe da labule tace "gani..", Baba yace "Alhmdllh an kawo kuɗin auren Nabilah gasu nan aljihu na..", Maama tayi kasaƙe don bata taɓa tunanin kuɗin ƴarta aka kawo ba amma aka zauna a tabarmar Umma, Maama tace "Amma an yimin adalci knn a matsayina na wacca ta haifi Nabilah", Baba yace "toh ko ke zaki fita ki amso kuɗin auren ne...?", a fusace Maama ta koma ɗakinta zuciyarta na zafi, Baba ya sanar da Umma abinda ya faru ita kuma tayi masa Allah ya sanya alheri. Maama ta kalli Nabilah da take linke kayanta tana jerawa cikin wardrobe tace "ba dai wnn matsolon bane ya kawo kuɗin aure...?", Nabilah ta saukar da kanta ba tace komai ba, Maama ta hangame baki jikinta har ya fara rawa tace "mgana nake miki kika wani sunkuyar da kai sai kace munafuka..", Maimuna tace "Maama dama kin dena ɓaɓatu don wllh shine, Tanimu mai pachi ba", Maama tace "kar dai kice min Tanimu da yake zaune bakin titi mai pachin tayar motoci", Maimuna ta tuntsire da dariya tace "shi fa", a fusace Nabilah tace "Eh shi ɗin zan aura ina ruwanki, ke zaki zauna min dashi iye, bana son shisshigi da kwala kai a faranti", Maama ta shiga tafe hannaye tace "Annabilatuwa ashe ba ki da hankali da tunani, ni kuka kai juyayi kika jajiɓowa kanki, ke mahaukaciyar inace..?", Nabilah ta zumburi baki tace "nidae ina sonsa a haka.. ai gwara ma ni an san sa kuma yana zuwa gida, itafa Maimuna ko layin gidan nan bai taɓa zuwa ba...", Maama ta katseta da faɗin "kin hau fel waya kin diro, shi wnda yake son Maimuna ba mai kuɗi bane, uban me zai haɗasa da layin nan ya shaƙi ɗoyin kwata da maƙaƙin hammatar su Iliya mai awo..", Nabilah ta ajiye kayan hannunta ta bar ɗakin da sauri, Maama ta cigaba da jaraba ita lallai Nabilah ba zata auri Tanimu ba, Sa'adatu kam ko ta tafasa sauke ba tace ba don ba shiri suke da Nabilah ba.

★Murɗa handle din ƙofar office din tayi kafin ta shiga da sallama tana tafiya like a cat, ya ɗaga kansa ya kalleta sai kuma ya haɗe gira, daga lokacin da yazo zuwa ynxu ta shigo office dinsa a karo na uku knn, kuma duk shigowar da zatay saita fesa different turare don haka da different ƙamshi ta shigo a ynxun ma, fuskarta a sake sai kace za tayi murmushi ta ƙaraso ciki ta ajiye file din hannunta kan table, a fakaice Nurain ya kalli file din yace "my secretary will do that", Ruqayyah ta dubi mug din coffee da ta ajiye masa tin shigowarta na farko, ta leƙa mug din tace "Amm baka sha Coffeen ba ai, alright sai mu canza brand tinda dearest baya son wnn..", tana gama faɗin haka ta ɗauki mug din ta nufi ƙofa tana tafiya kamar tarwaɗa, sai 3 Nurain ya bar hospital din kuma daga nan fita sukay da Farooq, ba shi ya koma gida ba sai takwas na dare, direct sama ya haura ya wuce part dinsa, after yayi refreshing kansa wajen ƙarfe sha ɗaya ya sauka ƙasa ya shiga kitchen ya haɗa Coffee, daidai inda ta jingina da cabinet jiya ya ringa kallo, to ko yau ya akay da Aljanu tinda yaga alamar ta shigo kitchen din, yana gama haɗa coffee din ya fita, bayan ya haura sama ya tsaya yana kallon ƙofar room dinta, har ya kai hannu zai murɗa handle sai kuma ya fasa, shi kaɗai yasan yadda yayi controlling kansa jiya, so solution dinsa ɗaya kuma shine to stay away from her, da wnn tunanin ya wuce room dinsa. haka nan kam acikin kwanaki uku bai saka Silly girl a idonsa ba, deep down his mind he want to see her amma action dinta kaɗai ma sosai suke jefasa a halin da bai san inda zai nemo solution ba, ranar Asabar da daddare suka tafi Airport tare da Farooq zasu taho dasu Hajiya da jirginsu yake daf da sauka, sai ƙarfe tara jirginsu Hajiya yayi landing, Hajiya na ganin Nurain abinda ta fara tmbyarsa shine ina matarsa, a takaice ya bata amsa yace tana gida, wajen parent dinsa ya wuce yana musu sannu da zuwan da Hajiya ta hanasa da tmbyar Hajar saida ya bata amsa snn ta barsa, bayan an gama musu checking suka wuce, already Abba part dinsa ya wuce Mami ma haka bayan sun isa gida, Hajiya kam branching tayi a main palour, daman Farooq bai shigo ba suna zuwa ya tafi gida, Hajiya ta daga kai ta kalli Nurain da ya fito daga part din Mami bayan ya shigar mata da kayanta, Hajiya tace "ina matar taka ne Usuman..?", Nurain yace "ohh Hajiya nace miki tana gida fa", Hajiya tace "Auho aini da kace tana gida na sha nan kake nufi, sai kace min gidanta ba wai gida ba..", Nurain yace "toh tana can", Noor ce ta shigo da ƙaramar jakar kayanta, Nurain yace "kayan sun ƙare Noor..?", Noor tace "Eh Yaya", da haka ta nufi hanyar ɗakinta, Hajiya tace "gobe da sassafe ka kawo min ita nan ta amshi tsarabarta don duk rabin kayan da na siyo ita na siyowa, sbd itace ta taimaka min na sakata na wala a kujerar jirgi, da bata shafamin man zafin nan ba ai bazan iya zaman kujera har na daɗe ba, shiyasa da naje Saudiyyar ma duk kayan da na gani ita nake tunawa, gashi nan kam na lafto mata kaya kuma babu wnda zan bawa sai ita, Noor ce ta tayani zaɓa tinda ta fini sanin birni..", Nurain yace "Ai kam saidai su raba dasu Aysha..", katsesa tayi da faɗin "wace kuma Aishan kake nufi wai Shatu..?", Nurain yace "Eh", Hajiya ta tsuke fuska tana kallonsa ta ƙasan glasses dinta tace "ba da wanda zasu raba, idan ta Shatu zan biye da tuni ƙafata ta daɗe da ruɓewa, sam sam wnn ɗiyar ta Ummi bata temaka min wajen shafa man zafi", Nurain ya kalli tsadadden agogon dake wrist dinsa, ganin dare yayi ya tashi ya miƙawa Hajiya hannunsa yace "muje na rakaki ɓangarenki kema ki huta", Hajiya ta kama hannunsa ta miƙe snn ta riƙe sandarta da other hand din tace "Eh gsky rakani nima na yada kwankwasona karka tafi ka barni ni kaɗai nayi ƙuƙi sai kace mayya tinda kowa ya ɗaɗe, su basu yi bacci ba a jirgin ni kuma na ɗan gyangyaɗa..", yana riƙe da hannunta har saida ya kaita ɓangarenta snn ya fito, ya yiwa Maminsa sallama Abba kam tinda ya shiga part dinsa ya kwanta, ƙarfe sha ɗaya da ƴan mintina Nurain ya bar gidansu zuwa gidansa....✍️
💛 HAJAR 💛

{68..}
Washe gari ƙarfe tara da rabi Hajar ta fito daga wanka ɗaure da towel, a hankali ta zauna kan stool tana rubbing lotion, wata doguwar riga armless ta saka bayan ta gama shafe shafenta, ta fesa perfumes masu sanyin ƙamshi, a hankali ta buɗe ƙofar room dinta ta fita tana ƙarewa corridor kallo, after few seconds ta ƙarasa fita ba tare da ta rufe door ba don ba ta so tayi ƙara, walking slowly cikin sanɗa har ta kai bakin door din ɓangarensa, ko takalmi bbu a ƙafarta wai don kar aji footsteps, tafi minti biyu a tsaye kafin ta kai hannu da nufin sliding door din sai kuma ta fasa, ta ciji lower lip dinta painlessly ta kara kunne a jikin ƙofar, wani irin turo baki tayi don ba taji motsi ba, ta juya ta koma room dinta still tana turo baki, toh ko dai ita kaɗai ce a gidan ynxu ne, three days fa ba ta gansa ba ko sau ɗaya, tana barin bakin ɓangaren nasa ya buɗe ƙofa, ya ringa surveying corridorn da idanunsa amma bai ga kowa ba, shi dai he is not mistaking tabbas yaga silhouette din mutum, har ya juya zai koma ciki sai kuma ya fasa ya cigaba da kallon wajen, pointed nose dinsa ya ja don sosai ya shaƙi sassanyan ƙamshin da ya karaɗe corridor din, after a while ya juya ya shiga ciki. Hajar ta zauna kan stool dake gaban mirror tana kallon kanta, toh wai yana ina ne, tsaki tayi a fili tace "ina ruwana ya tafi space ma", hular da ta rufe gashinta ta cire ta warware jelar gashin da ta naɗe, oil hair spray da Maysha matar Hammad ta bata ta ɗauka ta feshe hair dinta dashi, after that ta jiƙa kan da hair butter snn ta fara combing dinsa a hankali, jin an buɗe ƙofa tayi sauri ta ɗaga kanta, ido huɗu sukay dashi hannunsa daya cikin pocket din sweat pant dake jikinsa, miƙewa tayi still tana kallonsa sai kuma ta koma ta zauna, kallonta yake without blinking ya wani tattare thick eyebrows dinsa, Hajar ta saukar da kanta sai kuma ta ajiye comb din hannunta kan mirror, sosai ta masa kama da baby doll sbd armless gown da ta saka da kuma black coiled hair dinta dake a warware, da sauri ya ɗauke kansa speaking with a repartee yace "idan kin gama abinda kike ki shirya zan ajiyeki can wajen Hajiya...", ba tare da ta ɗago ba tana twisting slim fingers dinta ta gyaɗa kai tace "toh", yace "idan kin shirya sai kiyi yadda na koya miki a can garin da wayar da na ara miki..", nan ma tace "toh", bai ko ƙara 1sec ba ya juya ya fita ya rufe mata ƙofar, lumshe idonsa yayi yana sauke ajiyar zuciya sai kuma ya shiga ɓangarensa, saida Hajar ta gama combing din gashinta snn ta sauka downstairs ta

Download complete TXT · Novel page