HAJAR
Chapter 69 of 85
saida ya tabbatar nauyin zuciyarta ya ragu, tana jin bbu wanda ya mata rarrashin da ya shigeta kamar na mijinta, surely ta rarrasu don more than 60 percent na raɗaɗin da take ji ya ragu, ya kai soft palm dinsa ya goge mata ragowar tears din yace "please stop crying Allah ya jiƙan Abba..", sai wajen takwas da rabi Hajar ta shiga gida da bag din kayanta da ya taho mata dasu, other hand din nata kuma ledar kayan ciye ciye ce. Washe gari akay sadakar uku tinda kwanan keso Baba yayi, wajen sha daya na safe sai ga su Mami harda Hajjaju Hajiya da Noor da kuma Umminsu Farooq da Aysha, suka zo da uban abinci kala kala na sadaka, Anty da Umma ba ƙaramin mamaki suka sha ba ganin yacca surkan Hajar suke sonta, ga Iron Lady da suka ga tana mata wni tarairaya na musamman, Umma har cikin ranta take jin daɗi da Allah ya kai ƴarta gidan da ake sonta, yoh toh so mna idan dangin miji basa yi da kai ta ina zasu ringa maka irin wnn mutuncin, bayan 20mins da zuwansu Mami Anty Zulaihah ma tazo don tasan gidan tinda tare da ita aka zo ɗaukan Hajar, Khausar dake biye da mahaifiyarta ta ringa bin gidan da kallo tana yamutse fuska, tinda taji cewa gidansu Hajar Anty Zulaihah zata zo shine tace itama zata zo, Hajar ta duƙa ta gaida Anty Zulaihah wcca ta amsa mata da sakakkiyar fuska snn ta mata ta'aziyya, Khausar dai bata ko kalli Hajar ba bare ta mata gaisuwa, Hajar na lura da yacca ta ɗauke kai da ta ganta, ita kam bata damu ba don duk wnda ya wanko ƙafa yaxo gidansu sbd mutuwar Babanta ya gama mata komai, Hajar na kallon Khausar tace "Sannu Khausar", Khausar ta ɗan kalleta tace "Ya ƙarin haƙuri, Allah ya jiƙansa..", Hajar tace "Ameen..", ko 10mins su Anty Zulaihah basu ƙara ba suka tashi zasu tafi, zuwa lokacin har Khausar ta fara fifita da handbag dinta tana yamutsa fuska, kafin sallar Azahar su Mami ma suka tafi. Da yamma lokacin jama'a sun rage tururuwar zuwa Mu'azzam ya shigo gidan, kwaraɓaɓɓen kitchen din gidan da basa amfani dashi duk ya mutu sai uban shirgi ya buɗe, girgiza kai yayi ya bar bakin kitchen din, ɗakin Baba ya buɗe ya shiga bayan wni lokaci ya fito, wajen Naseer dake tsaye bakin titi tare da Huzaifa ya wuce, Mu'azzam na kallon Naseer yace "Yaya saidai a ajiye a ɗakin Baba a ynxu dai kafin a gyara kitchen din", Naseer yace "Tom.. ku shiga dasu", tini Huzaifa da Mu'azzam suka ringa ɗaukar Foodstuffs din da suke shaƙure a ƴar ƙurƙura suna shiga gida dasu, bayan sun gama kwashe uban kayan Abincin tare da ƴan tayi Naseer ya bisu gidan shima, duba yadda suka ajiye kayan yayi snn ya rufe ɗakin Baban ya bawa Sabrah muƙullin yace ta kaiwa Umma, Maama da akan idonta aka ringa jibgi Foodstuffs din don tana tsakar gida ta dubi Naseer da wni irin yanayi bayan taga ya bawa Sabrah key yace ta kaiwa Umma, Maama tace "Nasiru..", Naseer ya dubeta a karo na farko tin shigowarsa gidan, tace "Zo nan ina son ganinka" da haka ta tashi ta shiga ɗakinta tana ɗingishi, har ynxu ƙashin cinyarta ciwo yake sbd bugun da ta sha a hannun police, Naseer da zuciyarsa take zafi don har cikin ransa ya tsani halin mahaifiyarsa, da ƙyar ya tausashi kansa ya bita ɗakin, kallo ɗaya ya yiwa Maimuna dake malelekuwa a ƙasan leda tana murƙususun ciwon ciki, Sa'adatu ta cusa wayarta da take dannawa ƙarƙashin pillow ta hau baccin ƙarya, haɗe fuska yayi don ya lura da ita, ya duƙa gaban Maama yace "Gani..", Maama ta ringa kallonsa jin yacca yayi mgnar a daƙile, ta girgiza kai tace "Nasiru na lura kai da Huzaifa da Nabilah kun ƙullaceni a cikin ranku, kar ku manta dai ni uwarku ce ko da kuwa tsince tsince nake a bola..", Naseer ya sauke numfashi yace "ba hka bane Maama..", tace "Ai ni ba mahaukaciya bace da za kace min ba hka bane Nasiru, toh ba dai a canzawa tuwo suna, idan ma gani kuke ni na kashe mahaifinku toh wllh ba ruwana, lokacinsa ne yyi snn kuma dukkanku na fiku sonsa don tare kuka ganni dashi..", shi dai Naseer yayi shiru baice komai ba, Maama ta gyaɗa kai tace "Wccan Uban kayan abincin tuli guda a ina ku ka samosa..?", yace "Abokin Baba ne ya kawo..", Maama ta micincina ido tace "Abokin Baba kuma...?, ina mal yaga Aboki mai arziƙin da zai nannago uban kayan abincin nan ya bamu..?", Naseer yace "Alhj Muktar fa", nan ma Maama ta ƙanƙance ido tace "waye hka..?", yace "Surkin Hajar", saida zuciyar Maama ta koma ciki tsabar ruɗu amma bata nuna ba ta rausayar da kai tace "ba shakka shiyasa ai ka damƙa mukulli hannun masu abincin", Naseer ya shafa kansa yace "zan koma soro kar azo ana nemana..", bai jira cewarta ba ya tashi ya fita with speed, takaici ma bazai barsa ya gaya mata sauran Alkhairyn da Abba ya musu ba, ga kuɗi masu yawa ya bayar yace su riƙe a hannunsu snn yace duk abinda ake buƙata a gidan Naseer yaje ya samesa ya gaya masa, a wnn lokacin ai da wuya a samu mutum irin Abba wnda zai waiwayi iyalan Abokinsa bayan rasuwa, kowa ta kansa yake nafsi nafsi. Hajar ta raka Zainab da tazo mata gaisuwa har soro, Hajar tace "Ngd sosai Zainab..", Zainab tayi murmushi tace "ba komai Hajar, Please karki manta ki kirani anjima sai nayi saving number dinki tinda bakya amfani da wncan..", Hajar tace "insha Allah.. ngd sosai Zainab ki gaida Ummi dan Allah..", Zainab tace "zata ji". Hajar na gida har saida akai bakwai, kullum Nurain sai yaxo to check on her, gashi kuma suna waya frequently, yau ne akay sadakar bakwai, da yamma bayan gida ya watse bbu kowa don da yawan mutane sunxo sunyi gaisuwarsu, Anty ce tare da Umma a ɗaki, tin ranar uku Anty ta tafi gidanta sai ranar biyar da ta kuma zuwa sai kuma yau bakwai da tazo, Anty tace "Yau gashi har Baba yayi kwana bakwai a ƙasa, Allah ya jiƙansa ya gafarta masa yasa aljanna ce makomarsa..", Umma da Hajar suka amsa da Ameen, Anty tace "Addah saidai wni hanzari ba gudu ba, zaman gidan nan a gsky ba naki bane ya kamata mu fara tunanin inda zaki koma, baza ki cigaba da zama da waccar matar mai zuciyar kafurai ba..", Umma ta numfasa tace "gskyr ki Jamilah, tabbas bazan cigaba da zama da Rabi ba a gidan nan, zanyi tunani akan hakan..", Anty tace "Yauwa kar ki ja tunanin nan ya daɗe don ni ko sati biyu bana so ki ƙara nan gaba wllh, wccar matar abin tsoro ce tsakani ga Allah", Umma tayi shiru ba tace komai ba, Anty tace "idan gidan Iya zaki koma toh..", Umma tayi saurin girgiza kai tace "A'a bazan koma gidan Iya ba gwara na tafi Yola kawai..", Anty ta zaro ido tace "Yola kuma Addah, wajen wa zaki a Yola..?", Umma tayi murmushi tace "haba Jamilah ya kike mgana sai kace wasu marasa dangi, wajen Gwaggo Habiba zan tafi..", Anty ta sauke ajiyar zuciya tace "haka ne Addah, wllh Gwaggo Habiba tana son mu kuma na tabbata bazata ƙi zama dake ba, lalurar da take da itace ma tasa bata zirga zirga wajen zuwa inda muke wllh", Umma tace "zan dai yi tunani Jamilah", Anty tace "Toh", tini idanun Hajar suka ciko da ruwa jin Ummanta za tayi nesa da ita, Anty ta kalli Hajar tace "ke kuma yaushe zaki koma gidanki..?", Umma tace "Ni nasha ma yau zata koma wllh..", Hajar ta saukar da kanta ba tace komai ba, Anty tace "Ya kamata dai ki tafi tinda anyi bakwai kar kuma a shiga haƙƙin aure..", Hajar bata iya cewa komai ba sai gyaɗa kai, Anty tace "Hajar na jinjina miki Allah ya miki Albarka, yadda naga dangin mijinki na tarairayarki suna ji dake nasan cewa kinyi riƙo da tarbiyyan da mahaifanki suka baki, Allah yasa ki cigaba da ɗorewa a haka kuma kar kiyi sagegeduwar da soyayyar nan da suke nuna miki zata ƙare..", Hajar tace "Insha Allah..", Daf da magrib Hajar na zaune kan kujera gaban rariya tana alwala don ynxu she's clean jiya tayi wankanta, Nabilah tazo ta ɗebi ruwa a buta ta durƙusa nan kusa da Hajar itama za tayi alwalan, Hajar dai bata ko kalli inda take ba ta cigaba da alwalanta a hankali, a hankali Nabilah tace "Hajara..", Hajar ta ɗaga kai ta kalleta sai kuma ta cigaba da alwalanta, Nabilah ta sake kiran sunanta a karo a biyu, da mamaki Hajar ta kalleta sai kuma tace "Na'am..", Nabilah da idonta ya ciko da ruwa tace "ya haƙurin mahaifinmu..", Hajar tace "Mun gode Allah..", Nabilah ta ɗanyi jimm sai kuma tace "Toh ayi haƙuri da duk wni abu da ya faru a baya, irin saɓanin da muka samu a matsayinmu na ƴan uwa, dan Allah kiyi haƙuri komai ya wuce Hajara..", Hajar tace "Ni kam a cikinku bbu wnda na riƙe a raina Nabilah, nice ƙarama acikinku amma kuka nuna bakwa sona a koda yaushe cikin kyarata kuke, snn kuka ringa haɗemin kai samm ba kwa nuna cewa ni ƴar uwarku ce..." sai kuma tayi shiru kafin tace "bazan manta ba shegiya kuke kirana duk da cewa ubanmu ɗaya, bbu damuwa komai ya wuce ni bbu wnda na riƙe a cikinku Nabilah..", Nabilah ta goge hawayen da ya zubo mata tace "haƙiƙa ba mu yiwa mahaifinmu adalci ba, ke kam bbu ruwanki sbd mu muke fara janyo duk wata fitina, duk wata matsala mu muke janyota wllh, dan Allah Hajara kiyi haƙuri mu manta da komai ko don mahaifinmu..", Hajar tace "ba komai kema kiyi haƙuri don ƙarfe ɗaya baya amo" tana gama fadin haka ta wanke ƙafarta ta tashi ta shiga ɗaki. Washe gari Umma tace da Hajar ta shirya ta tafi da wuri ido na ganin ido ba sai dare ba, haka nan Hajar ta hau shirya ƴan kayanta a jaka jiki a sanyaye, wajen sha biyu Abdallah ya kawo saƙo yace inji Anty kuma saƙon na Hajar ne, ai kam Umma bata buɗe ledar ba haka ta miƙawa mai ita, ita dai Hajar ta amshi ledar tana tunanin mene ne a ciki, Abdallah ko zama beyi ba yace zai wuce don kasuwa zai tafi Anty ta bashi saƙon ya kawo, bbu jimawa da tafiyar Abdallah kiran Anty ya shigo wayar Hajar, bayan sun gaisa Anty tace "Abdallah ya kawo miki sako ko..?", Hajar tace "Eh..", Anty tace "Ohk.. akwai paper acikin ko wanne wcca aka rubuta ydda ake amfani dashi..", Hajar tace "Toh ngd Anty" duk da bata san mene ne abinda Anty take mgana akai ba, Anty tace "Yau din zaki tafi..?", Hajar tace "Eh insha Allah da yamma..", da haka sukay sallama. Hajar ta saka hijab dinta a hankali, duƙawa tayi ta saka wayarta cikin bag din kayanta, idanunta cike taff da ruwa ta juya ta kalli Umma, da sauri ta tafi ta faɗa jikin Umma ta fashe da kuka tace "Umma dan girman Allah karki tafi Yola ki barni..", Umma ta daure tace "A'a bazan tafi ba Hajara..", Hajar ta ringa rusa kuka don mikin mutuwar ne ya wani taso mata, ynxu shknn bazata sake ganin Babanta ba, indai tazo gida bazata ga Baba ba, Mu'azzam ne ya shigo ɗakin ya tsaya yana kallonsu, sai kuma yace "kin fa bar mutum yana jira Hajar..", Hajar ta zame jikinta daga na Umma tana jan zuciya, Mu'azzam ya ɗauki jakar kayanta ya fita da ita yana cewa "ki fito hka nan..", haka nan Hajar ta fito tsakar gida da ledar kayan da Anty ta bata a hannu, Umma na biye da ita tace "Allah ya kaiku gida lfy..", Hajar ta kalli Nabilah dake zaune a ƙasa bbu ko tabarma ta zabga uban tagumi sai kace me fama da cutar depression, walking gently Hajar ta isa inda take ta duƙa gabanta tace "Nabilah..", Nabilah tayi firgigit don tayi nisa a tunanin da take, Hajar tace "Ni zan tafi sai na sake zuwa kuma..", Nabilah ta numfasa tace "Toh Allah ya kaiki gida lfy, zan amshi lambarki a wajen Umma sai mu ringa gaisawa..", Hajar ta gyaɗa kai da haka ta miƙe, hannun Umma ta riƙe tace "Umma na tafi..", Umma tace "Allah ya miki albarka Hajara ya kaiku gida lfy..", Hajar tace "Ameen Ummanmu..", Nabilah ta ringa kallonsu tana jin dama ta ta uwar ce a hka. Har bakin mota Mu'azzam ya raka sister dinsa, sai a lokacin Nurain ya amshi bag din kayan daga hannun Mu'azzam ya saka a booth, kafin ma ya gama saka jakar tini Mu'azzam ya juya ya shige lungunsu, Nurain ya zagayo side din da Hajar ta tsaya, ta ɗan kallesa sukay ido huɗu, murmushi ya sakar mata sai kuma ya kai hannu ya buɗe mata front seat, saida ta shiga ya rufe snn ya zaga driver seat ya buɗe ya shiga, ya rufe murfin motar sai kuma yayi stretching kansa sosai yace "Alhmdllh..", bai kunna motar ba ya juya yana kallonta, sosai ya lura da kumburin da idanunta sukay, ya sauki wni boyayyen ajiyar zuciya, Calmly ya kamo hannunta yace "Baby wife..", ta kallesa a takaice tace "Ina yini..", yayi pecking hannun nata yace "Ni har ynxu ba nida suna", ta saukar da kanta ba tace komai ba, ya sake pecking hannun nata na almost 10secs har saida ta ɗago ta kallesa, yace "Uhmm ba nida suna a wajen matana har ynxu..", ta kalli hannunta dake cikin nasa, yasa other hand dinsa ya riƙe haɓarta ya ɗago kanta, kallon eye balls din juna kawai suke, ya lumshe idonsa ya sake buɗasu a kanta, kashe mata ido daya yayi yace "A taimaka min da suna..", yacca ya kashe idon sai kace wni abu ne ya faɗa masa da kuma yacca yayi mganar ne ya bata dariya, bata san lokacin da wni murmushi ya kufce mata ba, ta ɗora forehead dinta kan hannunsu dake maƙale tare still tana murmushi, yaushe rabonta da wni abu wai shi murmushi, shima murmushin yayi ya ɗago kanta ya haɗe forehead dinsu waje guda yana murza hannunta yace "I like it when you smile"......✍️
💛 HAJAR 💛
{83..}
Good 4 days Nurain ya dauka yana cheering Baby wife dinsa up, sam baya barinta ta zauna jigum bare ta shiga damuwa, a kullum yana tare da ita though yana fita aikinsa amma baya daɗewa aikin 3hours kawai yake ya dawo, daga nan zai zauna da ita a gida har sai yamma snn yaje gidansu ya gaida parent dinsa, a gida yake sallar magarib da isha'i ma, bayan nan kuma sai ya ɗauketa su fita su zaga gari, hka nan suke dawowa gida da uban kayan maƙulashe da ya siya mata, kullum da Asuba kam tare suke yiwa Baba Addu'a, sosai Hajar ta sake raɗaɗin zuciyarta ya ragu saidai kuma ciwone da bazai taɓa warkewa ba a zuciyarta har itama ta koma ga mahaliccinta, Addu'a ba kama ƙafar yaro take yiwa Babanta cikin duka kamsu salawat da take gabatarwa. walking gently Hajar ta fito daga bathroom da towel ɗaure ribs dinta ta yafa wni a shoulder dinta, lulu eyes dinta ta sauke akan gadonta sai kuma tayi murmushi ganin har ynxu yana kwance a nan din bai tashi ba, tin Asuba da ya shigo nan din ya kwanta, A ɗakinsa suka kwanta itama da asuba ne ta taho nan, gashi dai har ta sauka downstairs ta kimtsa komai, har part dinsa ma ta gyara ta gama breakfast amma bai farka ba, a tunaninta kafin ta fito dga wnka zata tarar ya tashi sai kuma ta tarar bccin yke har ynxu, gaban mirror ta zauna ta shiga rubbing lotion, tana shafe shafenta tana kallon gado ta cikin mirror, da hka dai ta gama ta bar gaban mirrorn wni sassanyan ƙamshi na tashi a jikinta, a hankali ta buɗe wardrobe without making any sound ta ɗauki kayanta, tana gama saka kayan ta kalli agogo, ƙarfe tara da rabi ta gani, ta zaro ido toh ko dai yau bazai fita bane, ita dai bazata tashesa ba gsky, kallon gadon tayi lokaci guda ta isa gaban gadon, ta sauke idanunta a kan fuskarsa, kallonsa ta ringa yi without blinking, zama tayi gefen gadon a hankali ta sunkuya daidai fuskarsa tana kallonsa, wnn shine karo na farko da ta masa irin wnn kallon, dman haka mijinta yake, words can't express handsomeness of her husband, kawai ganin idonta tayi a cikin nasa, wani irin bugu zuciyarta tayi, ya subhanallah kar dai ya kamata tana kallonsa, wayyoh Allah ta shiga uku, tini ta ɗaga kanta tana inda inda, sai kuma ta ɗan kallesa, kallonta taga yanayi with his sleepy eyes, ta kalli gefe da murya ƙinƙina tace "Amm... daman.. naga.. lokaci..", murmushi yayi ya mirgino ya ɗora kansa kan cinyarta, yana kallonta da kyau yace "daman me Baby wife...?", ta ringa kallon thick eyebrows dinsa sai kuma ta girgiza kai tace "ba komai..", pink lips dinta ya kalla da tayi mganar yace "ban yarda ba", ita dai bata kalli cikin idonsa ba kawai thick eyebrows dinsa take kallo, ta girgiza kai ba tace komai ba, shiru ne ya gifta for some seconds, slowly ya riƙo hannunta ya ɗora kan forehead dinsa, ta ɗan yi tsam kamar zata janye hannun daga goshinsa sai kuma ta fasa, ya gyara kansa sosai a laps dinta yace "Toh gashi dai na kama wata yarinya tana kallona, So ynxu sai a bani suna..", juya lulu eyes dinta tayi tace "A mafarki ko..", ya tattare girarsa yace "Nope in reality mna..", ba ta san lokacin da tasa finger ta fara shafa eyebrows dinsa ba tana bin zanenta, lumshe ido yayi yana jin ydda take yawo da slim finger dinta a girarsa, after a while ya buɗe idon yana kallonta, wni abu yaji yana sukar masa zuciya ya kasa dena kallonta, ta turo baki ganin kallon da yake mata sai kuma ta rufe masa idanu da palm