Showing 240001 words to 243000 words out of 252835 words

Chapter 81 - HAJAR COMPLETE NOVEL DOCUMENT

Before 12noon su Nurain suka isa Airport bayan sun baro gidan Hammad, bayan sun gama bin duk wata procedure suka shiga jirgi, seats din kusa da window suka zauna don dman business class ne, Nurain yasa flight attendant ta kawo musu bassinet sbd Nanerh, ana fara announcement jirgi zai tashi Nurain ya amshi Nanerh, Hajar tayi fastening seat belt dinta gami da runtse ido tana karanto duk addu'ar da tazo mata baki, har yau tana jin tsoron tashi da saukar jirgi, bayan jirgi ya keta hazo ya gama leveling a sararin samaniya Nurain ya kwantar da Nanerh a bassinet din da aka basu, Hajar ta cire seat belt dinta ta gyara zamanta sosai, bbu jimawa bacci ya ɗauketa don dman shi take ji, throughout yester night ba tayi wni baccin kirki ba sbd zumuɗi, a shoulder din Nurain ta kwantar da kanta, shi kam headphone ya saka a kunnensa ya kunna karatun Alkur'ani ya lumshe ido, saida aka fara raba abinci snn Hajar ta farka, ta kalli Nurain dake side dinta, ya cire headphone din yace "kin tashi", ta gyaɗa kai sai kuma ta kalli bassinet din gabansu, wayam ta gani bbu Nanerh, ta zaro manyan idanunta waje ta zaburo sai kace mai shiri miƙewa tsaye tace "My baby", Nurain yayi tapping dinta sai kuma ya nuna mata mutumin da ke gabansu jar fata, a hannun mutumin ta hango Nanerh, saida ta leƙa fuskarsa taga fari ne sosai, ta rage murya tace "kamar ɗan China", Nurain yace "yhap shine". After the journey of 8hours suka isa Hong Kong, lokacin ƙarfe 4 na dare, suna fitowa daga filin jirgi Nurain ya tsare musu Cab, wayarsa ya kunna ya shiga language translator App, da Language translator App din sukay communicating da drivern Cab din tinda shi dai bai iya Chinese ba su kuma basa jin turanci, hotel mai cab din ya kaisu kamar yacca sukay da Nurain, bayan Nurain yyi amfani da currency dinsu da ya taho dasu a hannu ya biya kuɗin transport din suka shiga hotel din, Suit room sukay lodging, wanka Hajar ta shiga bayan ta fito ta yiwa Nanerh ma, daga nan ta jero sallalolin da suka wuceta snn tayi ta asuba da ta ƙarato ynxu, Nurain ya musu order din abinci room service, nan Hajar ta kasa cin abincin, snacks din kawai ta iya ci ta haɗa da drink, bayan sun gama cin abincin Nurain ya fita, Hajar da Nanerh kuma baccinsu sukay sosai, sai sha biyu da wni abun Hajar ta farka, ganin da sauran lokacin sallah bai ƙarato ba ta wuce bathroom ta wanko fuskarta ta fito, a hankali ta isa gaban the wall to wall glass windows that viewed the skyscrapers of Hong Kong city, ɗan buɗa baki tayi in an excited way tana kallonta perfect view din da bata taɓa gani ba a rayuwarta, sosai ta shagala da kallon city din tana jin daɗi, ba ta ma ji ƙarar buɗe ƙofar da akay ba, Nurain ya tsaya yana kallonta ganin duk sallamar da yake batama ji ba, ya ƙarasa inda take yace "me ake gani..?", ta juya ta ɗan kallesa tace "birni nake gani", yace "you like the view from here", tace "Sure.. daman haka China take", yace "All the same amma nan Hong Kong ne", ta tattare gira tace "Ohh", yace "Nanerh ba ta tashi ba..?", tace "Eh", Lunch ma a nan cikin hotel din ya musu order, sai da daddare yasa ta shirya zasu fita yin dinner snn suga gari, tini Hajar ta shirya snn ta shirya Nanerh cikin baby jeans carpenter masu kyau, Hutong restaurant suka je one of the top traditional restaurant in Hong Kong, traditional food and modern one akay seving dinsu, Nurain yasa aka kawo musu seafood, spicy lamb ribs Hajar ta fara taɓawa, bon appetit the food is so yummy saidai seasoning din basu ratsa taste dinta ba, ai kam ta ciro guzirin maggi da tayi ta ringa barbaɗawa tana cin abincin, bayan sun gama yin dinner a Hutong restaurant ba hotel suka koma ba, babban Disneyland of Hong Kong ya kaita, daman wajen yafi daɗin zuwa da daddare, ita Hajar yadda taga mutane garin sunfi hulɗa da daddare ne yafi bata mamaki, sai kace wasu ƙannen aljanu, sosai Hajar taji daɗin Disneyland din, ta zaga ko ina tana shan cotton candy da Nurain ya saya musu, sai 12 na dare da wni abun suka koma hotel. Washe gari kuma da wuri suka fita ya kaita Victoria peak da kuma Ocean park, a Ocean park ne suka hau speed boat suka zaga farkon ruwan wajen, A washe gari kuma bbu inda suka je hutawa akay sai next day suka je Wong Tai Sin, shi kuma wajen kawai natural abubuwa ne suke tsawa and it is a top tourist spot, a ranar nan din kawai suka je sbd wajen nada girma da ɓangarori daban daban, Lantau Island ne ƙarshen wajen da suka je a Hong Kong, daga nan kuma ya kaita malls yace su sayi kayan tsaraba.........✍️
💛 HAJAR 💛

{95..}
Satinsu ɗaya a Hong Kong suka wuce China, A Beijing suka sauka kuma anan ne Nurain ya gabatar da ɗayan shirin nasa na zuwa China, kullum sai ya fita sun haɗu da Mr Lee, idan ya dawo da daddare ko yamma su fita da Hajar, A cikin sati biyu ya gama abinda zai yi, a washe garin da ya gama aikin suka shirya zuwa Shanghai City, Shanghai shima babban birni ne a ƙasar China snn akwai wajajen buɗa ido a garin, by train suka tafi Shanghai din tinda miƙaƙƙiyar tafiya ce daga Beijing, Woah a Shanghai city ma sun zaga ba ƙarya, Hajar ta buɗa ido iya buɗawa, duk wni guri da baƙi suke zuwa saida suka je, Yu Garden suka fara zuwa, anan Hajar taga ƴaƴan itatuwan da bata taɓa gani ba, fruits da vegetables ba a cewa komai, har watermelon mai purple flesh ta gani, da tayi tasting taji zaƙi zau kamar zuma, next inda suka je shine The Bund, shi kuma historical place ne, shima dai wajen ya burge Hajar sosai, da suka bar Bund suka je Museum da daddare, Shanghai Ocean Aquarium ne a ƙarshe a inda suka ziyarta a Shanghai city, kamar Hong Kong a nan din ma one weeks sukai, daga Shanghai next inda suka je shine Guilin, waoh nan din ya share komai da Hajar ta gani cause duk yafi birgeta, Guilin is so natural with breath taking scenery, hotel din da suka sauka ma a garin Guilin na traditional ne, seven places suka ziyarta a Guilin, reed flute cave, Elephant trunk hill, Lijiang, Fubo mountain, Yulong river, Chuanshan park and the last one Li river. Beijing suka koma suka fara shirin komawa Nigeria, ya rage saura kwana biyu su tafi ya kaita taga The great wall of china wnda yake nan garin Beijing, watansu ɗaya da sati biyu knn da baro Nigeria, ranar da zasu tafi Hajar ta shirya snn ta shirya ƴarta Nanerh wcca ta ƙara wayo don ynxu ta cike 3months old har da ɗoriya, Hajar na shiryata tana ɓangala mata dariya don ynxu yarinyar ta koma sarkin dariya, ƙarfe tara na dare suka isa Airport, bayan sun bi duk wata procedure suka shiga jirgi, kamar a zuwa wnn karon ma Hajar bacci tayi, da sassafe suka iso Nigeria Abuja, a take Nurain ya yankar musu flight ticket na zuwa kano, ai kam suka biyo jirgin da zai taho kano, bayan sun fito daga filin jirgi Nurain na riƙe da Nanerh wacca take ɓangalawa duk wnda ta gani dariya, ai kam mutane da yawa sai kaga suna murmushi wasu kam basa iya jurewa sai sun mata wasa. Tinda suka fito ta zuba musu na mujiya, lokaci guda ta miƙe daga kan kujerar da take jira bayan ta tabbatar da fuskar Nurain, har yaxo ya wuceta bai lura da ita ba, Hajar na gefensa sun jera suna tafiyar tare da farin ciki madawwami a fuskokinsu, Ruqayyah ta kasa jurewa ta juya tace "Dr..", at first Nurain bai tsaya ba saida ya sake jin an kira inkiyar tasa a karo na biyu snn ya juyo, Ruqayyah ta ƙaraso inda suke da murmushi kwance fuskarta tace "inata mgana baka ji ba Dr" ta faɗi hakan ne tana kallon Nanerh dake hannunsa wcca ta hau ɓangala mata dariya, Nurain yace "Ohh A Nurse", Hajar ta kalli Ruqayyah da wni irin expression, sosai Ruqayyah ta fahimci cewa wnn yarinyar ta hannun Nurain ƴarsa ce sbd kamarsu da ta ɓaci, Nurain yace "how are you doing A Nurse..?", Ruqayyah tace "great Alhmdllh... long time no see", Nurain ya kalli Hajar snn ya dubi Ruqayyah yace "Meet my beloved wife..", Ruqayyah tayi murmushi tana kallon Hajar tace "sannunki", Hajar da a lokaci guda taji bata son Ruqayyah tace "yawwa sannu", Ruqayyah ta amshi Nanerh tace "your daughter is so cute Dr", Nurain yace "thank you", Hajar ta juyar da kanta tana kallon wni position din, da gefen ido Nurain ya kalleta, Ruqayyah tace "naxo tarbar mai gidana ne", Nurain yace "ohh that's good" da haka ya amshi Nanerh yace "Toh na gaisheki A Nurse byee", da haka sukay sallama a mutunce, Ruqayyah ta koma ta zauna ta cigaba da jiran mai gidan nata Dr Sa'eed, bbu laifi sosai take jin daɗi zama da mijinta don kamar yacca na faɗa a baya ba shida matsala. Kwanan su Hajar 6 da dawowa aka shiga bidirin bikin Hafsah da Ahmad, Samm Nurain ya hana Hajar ta ringa kwana don shi lamarin biki ba burgesa yake ba, hka kurum wasu mazan su kalle masa mata, ai kam hka kullum Hajar take sintirin zuwa gidan biki saidai hakan bai dameta ba don da motarta take tafiya, though har ynxu hannunta bai faɗa ba amma kuma ta iya ba laifi, ansha biki iya biki don an zuba bajinta from both side, outside event biyu akay bayan na gida, ranar Juma'a akay ɗaurin aure, da yammacin ranar dangin ango suka xo tafiya da abarsu, har da Mami cikin wadanda suka zo ɗaukar Amarya don Maman ango close friend dinta ce, su Mami suka ɗauki Hafsah da aka shiryata cikin shigar amare na lafaya, Hajar tabi ƴan kai Amarya ta bar Nanerh a wajen Umma. Gidan Amarya Hafsah saidai muce masha Allah don kwa ya haɗu iya haɗuwa gashi danƙarere, Hajar ta shiga makeken bedroom din da aka ajiye Hafsah bayan rurumar ƴan kawo Amarya sun ragu, friends din Hafsah ne kawai a room din, Hajar ta durƙusa gaban Hafsah ta leƙa fuskarta dake a rufe, Hajar ta kyalkyale da dariya tace "Yau ga Hafsah a gidan Ahmad", Hafsah ta janyo Hajar ta rage murya tace "Na shiga uku na, wllh Allah ni tsoronsa nake ji..", Hajar ta waro ido tace "Mijin naki kike jin tsoro", Hafsah ta gyaɗa kai tace "wllh tsoro yake bani, ni dae gidanmu zan tafi", Hajar tayi dariya tace "A haba dai yarinya tin ynxu za wani kice kina jin tsoronsa, toh ki riƙe tsoronki zuwa nan gaba sai kiyi mai hujja..", Hafsah tayi ƙwal ƙwal da ido lokaci guda hawaye suka taru cikinsu tace "Na shiga uku", Hajar tace "wai ke meye haka", Hafsah ta yarfe hannu tace "ba zaki gane ba Allah kuwa..", Hajar tace "Ni kwa na gane tinda ni nan jiyau ce" ta ƙarashe tana dariya ƙasa ƙasa sai kuma ta zauna gefen gadon, hand bag dinta ta buɗe ta ciro wata leda ta amshi jakar hannun Hafsah ta saka ledar a ciki, Hafsah ta bita da kallo tace "meye wnn..?", Hajar tace "turaren sitz bath ne da musk soap", Hajar ba ta so kaiwa lokacin da Angwaye zasu zo ba amma Hafsah ta riƙeta, ai kam Angwayen na zuwa aka fita da Hafsah palour, sosai Hajar ta sha mamakin jin yadda hannun Hafsah dake cikin nata yana karkarwa, toh wai me yake damun Hafsah, ita bata ma kaita ba aka mata auren, Hajar na shirin zaunar da Hafsah kan kujera bayan sun iso palour Ahmad dake zaune palourn da friends dinsa su biyar ya taso, ba wani wala wala ko wata aba kunya ya taso ya rumgume Hafsah, wni irin zaro ido Hafsah tayi bayan ta shaƙi scent dinsa da ya tabbatar mata shine tinda fuskarta a rufe take, afujajan ta fara turasa, yayi murmushi mai sauti a saitin kunnenta yacca bbu wnda zai ji yace "Halal hug.. welcome home Baby", jikinta yayi lagwas ta dena tura san, Abokan ango suka hau ihu yayinda friends din Amarya suka hau shewa, Hajar kam kamar lips dinta zasu yage sbd murmushi, Finally dai ga Hafsah a gidan Ahmad as his lawful wedded wife. Washe gari da yamma Umma na zaune tare da Anty a palour, Anty ta ringa kallon Umma with a weird facial expression, Umma tayi kicin kicin da fuska tace "A gsky ni barin unguwar ma zanyi, tinda don masifa da bala'i da bita da ƙulli har inda nake ya nemo, wnn wni irin masifa ne da dogon wuya, maza yan bala'i ne ko uban wa yake tantance musu tsakanin mai aure da bazawara", Anty ta kwantar da murya tace "Toh ai mu hka muke so Addah, wnn ai rufin asiri ne babba, Kawu na Yola kawai zansa Iya ta yiwa mgana", Umma ta saki baki ta karkaɗa ƙafa tace "goɗai goɗai dani kike min mganar nan Jamilah, uhmm ai ni kam na gama aure har abada ma kuwa, nayi aure har na samu ribar cikinsa, Allah ya bani ƴaƴa har uku na gari wnda zasu kula dani, na rabu da mijina lfy snn na masa takaba cikin aminci, toh bayan wnn me nake nema a wni aure kuma, ai kawai a cigaba da gurgura rayuwa haka Allah ya bamu sa'a mu koma garesa da imaninmu", Anty ta buɗe baki da nufin convincing Umma, tini Umma ta shata mata layi tace bata son mgnar, hakan yasa Anty tayi gumm da bakinta ba ta sake cewa komai ba. Rayuwa ta cigaba da garawa Hajar cikin kwanciyar hankali da jin daɗi, daga kitchen Hajar ta fito da ƙaramin bowl mai ɗauke da plane Noodles with boiled egg, wajen Nanerh dake wasa cikin keken yaranta ta nufa, Nanerh na ganin Mamanta ta fara miƙa mata hannu tana so ta ɗauketa, Hajar ta ajiye bowl din noodles din kan hannun kujera snn ta durƙusa ta cicciɓo ƙatuwar ƴarta ta, ta zauna kan kujera ta ɗauki bowl din noodles ta fara bawa Nanerh, tini Nanerh ta hau zuƙulƙular noodles, 5months take da shi amma sosai ta kama abinci, bbu abinda bata ci bayan abincinta na gwangwani, daya daga cikin ma'aikatan gidan ce ta fito daga kitchen, ta zuba guiwoyinta gaban Hajar tace "Anty na gama aikin", Hajar tace "Ohk sannu, ina Binta..?", mai aikin tace "tana can ɗakinmu", Hajar tace "Ohk ayi noon duty", mai aikin tace "Toh" da haka ta tashi ta fita ta ƙofar kitchen zuwa backyard din gidan ta wuce boys quarters inda nan ne ɗakinsu, bbu jimawa mai aikin ta dawo tare da ƴar uwarta suka hau aikinsu, within few minutes suka gama gyara ko ina na downstairs din wnda daman a gyare yake, Hajar na zaune tana feeding Nanerh har suka gama, iya kacin aikinsu downstairs don ko hanyar upstairs bbu wnda ya taɓa bi, ita take gyara part dinta dana mijinta, Hajar na gama feeding Nanerh ta haura upstairs da ita, room dinta ta shiga da ita ta mata wanka ta sauya mata kaya, kafin ma ta gama shiryata har ta fara gyangyaɗi hakan yasa ta kwantar da ita ta cigaba da baccin, Hajar ta wuce part dinta tayi wankan itama, turare ta baza as usual ta saka wasu kaya na neman fitina, bom short ne wnda ko rabin cinya baixo ba ta haɗa crop wcca ta bayyana cibiyarta, As usual ta tarbi mijinta, tana riƙe da briefcase dinsa suka haura sama, yace "where is my Princess..?", tace "tayi bacci", saida ya shiga room din Nanerh ya dubata yayi pecking cheeks dinta snn ya wuce part dinsa, a kullum upgrading son da yake yima ƴarsa yake, after yayi refreshing kansa yayi wnka Hajar ta kawo masa abinci, ya zabga uban tagumi yana bin duk wasu moves dinsa, gaba ɗaya yaji ya tsani abincin kawai kallonta yake, walking like a cat ta iso inda yake ta zauna kan cinyarsa ta zagaye wuyansa tace "Cappuccino me zan zuba mka..?", ya haɗe thick eyebrows dinsa yace "No ni ba abinci nake so ba", ta waro ido tana wasa da sajensa tace "Toh me kake so...?", ya zagaye ƙugunta yayi kissing karan hancinta yace "i need you", ta noƙe fuskarta tana murmushi sai kuma ta maƙe shoulder, lokaci guda ta ɗagasa, wayarsa ce tayi ring, ya ɗauka ya kalli sceen din, tini yayi picking don Sakeena ce ke kiranta, ko 2 mins ba suyi suna wayar ba, ya ajiye wayar ya kalli Hajar yace "Noor ce ta haihu", Hajar tace "Masha Allah...", yace "bari naci abinci sai mu tafi ba", ta gyaɗa kai tace "Tom"…..……✍️
💛 HAJAR 💛

{96..}
Hajar na gama zuba masa abincin ta tafi room dinta, closet ta shiga ta sauya kaya, saida ta gama saka kayan snn ta sauka downstairs zuwa kitchen, catfish pepper soup din da tayi ɗaxu ta saka a microwave tayi warming dinsa, with few mins ta jera abincin da zasu kai asibiti a basket, sama ta haura ta shiga room din Nanerh, baccinta take lakadan cikin crib dinta, Baby Carrier Hajar ta ɗaura kafin ta ɗauki Nanerh ta haɗata da chest dinta snn ta ɗaure belts din, ɓangarensa suka wuce, already ma ya gama cin abincin ita yake jira don haka suka fito, bayan sun sauka downstairs Hajar tace "Moon zamu kai musu abinci yana kan Island", yace "Sure.." da haka ya shiga kitchen ya dauko basket din abincin, parking space Nurain ya wuce Hajar kuma ta zaga backyard zuwa boys quarters, masu aikinta su Binta ta gayawa cewa ta fita, Allah ya tsare sukay mata, tace Ameen da haka ta bar wajen, Other car din Nurain suka shiga ba wcca ya dawo da ita ba, ko nisa ba suyi ba suna tafiyar Nanerh ta tashi, ɗago kanta tayi tana kallon Hajar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login