Showing 246001 words to 249000 words out of 252835 words
dai garin kwaki ne suka jiƙa bbu sugar suka ci, su duka ukun rabin gwangwani suka sha sbd shi suka samu, Maimuna ce mai fita tayo bara saita samo musu na kaiwa baki, toh ynxu itama Maimunan idan ta fita ba samo abincin take ba, Sa'adatu kam hauka take tuburan lokaci zuwa lokaci, idan haukan bai motsa ba sai kaga ta zauna waje ɗaya tanata kuka, idan kuma ya motsa saita ringa doke doke, abin nata dai sai kace shafar aljanu, kuma idan ta tashi doke doke akan Maama take durango, tana dukanta tana kuka tana mata Allah ya isa da Allah wadai, Maimuna tace "kin bata ruwan tofin..?", Maama tace "shi naxo bata ta cafkeni ta lakaɗa min na jaki", Maimuna tayi zaman daɓaro a ƙasa ta rasa abinyi, rana zafi inuwa ƙuna, wnn wace irin rayuwa ce suke yi, tinda Allah ya yiwa Baba rasuwa duniya ta juya musu baya, ashe da cikin wadata suke da rufin asiri amma ruɗin zuciya ya hanasu gani, haƙiƙa mahaifiyarsu ta cucesu matuƙa, ta sabauta musu rayuwa, ta musu gurguwar tarbiyya ta hanasu bin ta mahaifinsu ta gsky, Maimuna ta miƙe ta nufi soro, Maama tace "ina zaki..?", Maimuna tace "zanje in nemo abinda zanci ne Maama, wllh yunwa nake ji kamar zan mutu, ƙirjina ma ciwo yake" tana gama fadin haka ta fita, bata bi ta hanyar shagon Iliya mai awo ba ta zaga ta baya, da ƙyar take jan ƙafarta bata ma san inda ta dosa ba, kawai ganin mutum tayi a gabanta, ya busa mata hanyaƙin wiwi da yake sha a fuskarta, Maimuna na ɗaga kai taga Bisi Ƙwale, ja da baya tayi ta zagaye zata wucesa, ya kashe wutar wiwin da yake sha a goshinta snn ya buɗa murya yace "kere na yawo zabo na yawo don haka dole su haɗu, yau bbu abinda zai hanani kakkafaki a nan wajen", Maimuna ta hau sosa goshinta da ya kwaile sbd wutar da Bisi Ƙwale ya manna mata, juyawa yayi ya leƙa kangon da suke zama ya kira Ƙwage, yana juyowa yaga bbu Maimuna a gabansa ta gudu, can ya hangota har ta masa nisa, ai kam tini ya saki iskar wandonsa yabi bayanta, Ƙwage ma da ya fito ya rufa masa, Allah ya taimaki Maimuna ta afka cikin gida, tana ƙoƙarin saka sakata Bisi Ƙwale ya banko ƙofar, ai kam gaba ɗaya ƙofa ta sauka daga jikin gini don ta gama ruɓewa, da gudu Maimuna ta shige cikin gida, Maama na tmbyarta lfy ina ba amsa, Bisi Ƙwale ya ɗauki wni icce da ya gani ya rufesu da duka, Ƙwage ya ɗauki wata murgujejiyar taɓarma, tashin farko ya saukewa Maama ita a cinya, Maama ta zube ƙasa cikin gunjin azaba, Maimuna ta rarrafa banɗaki Bisi Ƙwale ya bita yana sauke mata itace a gadon baya, ihu Maama da Maimuna suke suna neman agaji, Ƙwage yace "tsinanniyar yarinyar nan da tasa aka kaini gidan kaso..", Bisi Ƙwale yace "mu ƙaddamar musu kawai", Sa'adatu da ta ɗan dawo hankalinta ta leƙo ta window, ai kam Ƙwage ya hangota, ya saka taɓarya ya bige ɗan ƙaramin kwaɗon da aka rufe ɗakin ya shiga, saida ya shemar da Sa'adatu snn ya murguza mata tabaryar a baki gaba ɗaya haƙoranta na gaba guda shida suka sabauce, uku suka zube a take ragowar ukun kuma suka shige cikin dadashi, tini Sa'adatu ta sume don haka Ƙwage ya rabu da ita, Bisi Ƙwale ya fito daga banɗaki da ya tarfa Maimuna yana zazzare ido bayan yaga ta dena motsi, Ƙwage ya ɗaga tabarya ya ɓaurawa Maama a goshi, Bisi Ƙwale yace "Zo mu ware", da sauri suka fita daga gidan bayan sun wurgar da makaman da sukay aika aikar............✍️
💛 HAJAR 💛
{98..}
★Hajar ta fito balcony zata kira Sabrah da ta fito da Nanerh tana mata wasa, a tsakiyar compound ta hangosu suna kallon gate, daga ƙofar gate din kuma Binta ce mai aiki da Inuwa mai gadi, mai gadi yayi kane kane a bakin ƙofa alamar wni ya hana shigowa, Binta tace "ka ga Inuwa don Allah kaɗata wnn wace irin almajira ce mai nacin tsiya", daga waje Maimuna da hannunta ke nannaɗe da tsumma hawaye na bin kuncinta tace "dan girman Allah ku barni na shiga wajen ƴar uwata", Binta ta mata wni kallon tara saura kwata tace "wace ƴar uwar taki", Maimuna tace "wllh ni ƴar uwar matar gidan ce ubanmu ɗaya...", Binta tace "Chasss kuji mahaukaciya ke kin isa ki zama ƴar uwar matar gidan nan, ke asuwa..", Maimuna ta fashe da kuka tace "dan Allah ku bar ni na shiga..", Binta tace "kaga Inuwa bani hanya na koyawa jakar nan hankali", Inuwa yace "A'a bari ni na koya mata, wllh idan bata bar ƙofar gidan nan ynxu ba saina sumar da ita", Binta tace "barni da ita kawai, kar ka taɓata ace ka taɓa mai rai, wnn idan ka taɓata ai sai ka mata mummunar illa", Inuwa ya matsa daga jikin ƙofar, Binta ta maye position dinsa tana kallon Maimuna tace "baiwar Allah tin muna shaida juna ki tafi", Maimuna tace "ku dubi girman Allah...", ko jin sauran maganar Binta ba tayi ba ta zage ta hankaɗata tace "ke kin san girman Allahn da muka haɗaki dashi kika ƙi tafiya", Binta ta banke ƙofar gidan ta bar wajen, cikin gida ta dosa, Hajar dake tsaye balcony bayan ta saka Sabrah sun koma ciki da Nanerh tayi kiranta, da sauri Binta ta tafi wajen Hajar, tana isa gabanta tayi bowing tace "Anty gani..", Hajar tace "me ya faru a bakin gate na ganki a can kuna hayaniya...?", Binta tace "Wata mata ce wai saita shigo, irin Almajiran nan masu kama da tubabbu, wai cewa tayi ke ƴar uwarta ce shine ta bani haushi na kulle ƙofar", Hajar ta kalli gate din sai kuma tace "ta tafi ko tana nan...?", Binta tace "Wllh ba sani ba, amma da kyar idan ta tafi don irin wadan nan mutanen akwai baƙin naci", Hajar ta kunce mayafin doguwar rigarta da tayi ɗan kwali dashi ta yafa a wuyanta, walking a bit fast ta nufi gate, Binta tabi bayanta tace "Anty kar kije wajen wnn matar ba a rasa cuta a jikinta ba", Hajar bata tanka mata ba ta cigaba da tafiyarta har ta isa gate, tana zuwa gate din kam tasa Inuwa da ya koma kan kujera ya buɗe mata, ana buɗe ƙofar Maimuna dake maƙale da gate zaune rashadan a ƙasa ta ɗago kanta tana kallon Hajar, Hajar ma ta ringa kallonta tana ƙanƙance ido don bata ganeta ba, da rarrafen hannu ɗaya Maimuna ta rarrafa ta riƙe ƙafafuwan Hajar tace "ƙoƙon bara da maulata na kawo miki Hajara, dan girman Allah ki temaka min", Hajar ta ɗan ja da baya tana kallon Maimuna, Binta ta ɗauki farar kujerar da mai gadi yake zama ta tura Maimuna da ita tace "ke karki sake taɓata, muka san wace irin cutar ce a jikinki", Maimuna bata haƙura ba ta sake rarrafowa ta riƙe ƙafar Hajar tace "kar ki duba halina Hajara, kar ki duba halin mahaifiyata, kar ki duba halin ƴan uwana, ki duba girman Allah da Manzonsa, dan darajar Allah da ma'aiki ba dan ni ba ki taimaka mna Hajara, duniya ta mana ruku'un dila, masifa da bala'i ta ko ina Kunno mana kai suke, ƴan uwanmu duk sun gujemu, makwabta babu wnda yake jin kukanmu bare ya jiƙanmu, ke kaɗai ce wcca nake tunanin zaki taimaka mna...", Binta ta ɗaga kujera zata mangare Maimuna Hajar tace "rabu da ita Binta", Maimuna ta rushe da kuka tace "ki duba mahaifinmu Hajara", kukan ma da kyar Maimuna take yi sbd galabaita, ko mai cutar kwasheko ya fita kyan gani, Hajar taji wata ball ta tsaya mata a throat, Allah sarki Baba tabbas yaga jarabawa akan Maimuna da Sa'adatu da uwarsu Maama, ya haifi fanɗararrun ƴaƴa da suka zama annoba cikin al'umma, da ɗacin murya Hajar tace "idan tukunya tayi ɓori...", Maimuna tace "haƙiƙa kanta take ɓatawa", Hajar ta dubi Inuwa da Binta tace "ku fitar min da ita", wni azabar haushin Maimuna taji bayan ta tuna yacca suka gallazawa Baba, yadda Baba ya sha wahala akansu, ba ta jin zata iya taimakon su Maimuna bayan abinda suka yiwa Baba, habawa ai tuni Inuwa ya figi Maimuna ya jata ƙiyyy Binta na taimaka masa, Hajar ta juya da nufin komawa ciki amma saita kasa tafiya, tana jin Maimuna nata ihu, katamau Maimuna ta riƙe jikin gate su Binta na janta, Hajar tayi wni tunani saita juya tana kallon Maimuna, ai wni yana cin arzikin wani, Naseer da Huzaifa da Nabilah duk ƴan uwan Maimuna, tsakanin Naseer da Huzaifa bbu wnda ya taɓa mata wulaƙanci duk kallon ƙanwa kuma ƴar uwa suke mata, Nabilah ma a ynxu tana alfahari da ita kuma zata nunata a ko ina a matsayin ƴar uwarta, a da ne suka saɓa amma ynxu komai ya wuce, uwa uba kuma mahaifinsu ɗaya da Maimuna wnda ko taƙi kota so jini guda ne yake gudana a jijiyoyinsu, Hajar tayi ƙarfin halin yin magana ta dakatar dasu Binta, Maimuna ta sake rarrafowa har guiwarta ta dauje fatar wajen ta kwaile tace "ko kuɗin zuwa asibiti ne ki taimaka mna dashi, ga Maama can a gida ƙafarta zata ruɓe, ta karye a cinya har yau ba'a ɗorata ba, Sa'adatu kuma bakinta zai ruɓe haƙoranta duk sun shige dadashi". Can boys quarters Hajar ta kai Maimuna, ta saka Zaituna ɗayar mai aikinta ta kaiwa Maimuna ruwa da abinci, hannu baka hannu ƙwarya Maimuna ta rufa kan abinci, abincin da ta ci ko gardi albarka, Hajar ta ɗauko kaya cikin kayanta da ta fitar na bayarwa ta kaiwa Maimuna tace ta shiga toilet dake nan boys quarters din tayi wanka ta canza kayan jikinta, ko don ɗoyin da take bazata shiga da ita cikin gidanta ba, Maimuna ta shiga wanka Hajar ta fito daga boys quarters din ta shiga main building, a palournta na upstairs taga Sabrah tare da Nanerh da ta baza mata kayan wasanta, Hajar ta wuce bedroom dinta, wayarta ta ɗauka ta shiga kiran Umma, Umma na picking bayan sun gaisa Hajar ta wassafa mata me ya faru, Umma ta jinjina wnn mganar snn tace "ynxu haka ita Maimunan tana nan gidanki..?", Hajar tace "Eh, wai da zuwa anjima saina kaita gida...", Umma ta katseta da faɗin "ki kaita gida sbd ke kika kawota ko...?, karki kuskura ki fita daga gidanki akan wasu can mutanen da mutunci bai ishesu ba, kuma ynxu ba sai anjima ba ta bar miki gida", Hajar tace "Toh Umma, tace Maama da Sa'adatu na kwance ba lfy", Umma tace "Toh Allah ya basu lfy... ynxu ki tashi ki sallameta", Hajar tace "Tom" da haka ta kashe wayar, yadda Umma tace haka Hajar tayi, haka nan ta sallami Maimuna bayan ta bata kuɗi tace ta kai su Sa'adatu asibiti, Maimuna kamar zata haɗiye harshenta wajen yiwa Hajar godiya sai kace wacca ta bata arziƙin duniya. Umma suna gama waya da Hajar bata ajiye wayar ba ta kira Naseer, har ta gama ringing ta katse bai ɗaga ba, tana ƙoƙarin sake kira sai gashi ya kira, da ladabi Naseer ya gaida Umma, ta amsa masa kafin tace "Allah yasa dai baka koma Lagos din ba..?", yace "Ai kam dai ban koma ba gobe ne zan juya", Umma tace "Toh ina son ganinka yau din nan, idan ma zai yiwu ka taho ynxu", yace "Tom Umma". After like 40mins bayan nan Naseer ya iso gidan, da yaji Umma na nemansa urgent shine ya bar abinda yake ya taho, ita kanta Umma saida tayi mamakin yacca ya iso cikin ƙanƙanin lokaci, gaisuwa ya sake tisa mata duk da sun gaisa a waya, Umma tace "ban dai matsaka ba ko Naseer..?", yace "A'a ba damuwa Umma", Mu'azzam ne ya fito daga ɗakin Umma, Umma ta kallesa tace "ka ganshi..?", Mu'azzam yace "Eh" yana gyara agogon hannunsa, Naseer ya kalla yace "Yaya ina wuni", Naseer yace "lfy lou Mu'azzam... ya aiki..?", Mu'azzam yace "wllh Alhmdllh", Naseer yace "Toh yayi kyau Allah ya taimaka", Mu'azzam ya dubi Umma yace "Umma na fita", tace "Toh sai ka dawo Allah ya tsare hanya...", yace "Ameen" da haka ya fita, Umma ta ɗan sauke ajiyar zuciya tana kallon Naseer da kyau tace "ya wajen ƙannenka su Maimuna da Maama kuma..?", ya shafa kansa yace "suna nan lfy", Umma ta girgiza kai tace "A'a ba lfy ba Naseer, Anya kwa kana zuwa inda suke", ya saukar da kansa baice komai ba, Umma tace "baka zuwa knn..?", yayi ajiyar zuciya yace "Ina gudun fushin mahaifiyata ne, Maama ƙoƙarin yimin baki take akan abinda bai taka kara ya karye ba, ina yin iya ƙoƙarina na ganin na sauke haƙƙinsu a kaina amma Maama bata gani, indai naje gidan sai Maama ta faɗi mganar da zata min illa a rayuwa, ita da kanta tace idan na sake zuwa inda take saita tsine min, wnn dalilin ne yasa na jima banje gidan ba..", Umma ta girgiza kai tana auna gidahumanci da jakanci irin na Maama, Umma tace "Naseer ka daure kaje wajen mahaifiyarka, na tabbata ynxu bazata tsine maka ba, wncan karon ma faɗi kawai take amma baza tayi ba, bbu wata uwa da ta tsani ɗan ta har zata tsine masa bayan ya kasance mai mata biyayya", Sosai Umma ta gayawa Naseer mgana mai daɗi wcca tasa ya sauko daga dokin fushin da ya hau, har saida ya mata alƙawarin daga nan zai wuce wajen Maama. Ko da Naseer yaje gidansu wajen Maama kai tsaye taxi ya kirawo aka ɗura su Maama zuwa asibiti, ita kanta Maimuna data ɗan dawo hayyacinta bayan ta dawo daga gidan Hajar asibitin a kai da ita, shi dai Naseer kawai bin Maimuna yake da kallo ganin turtsetsen ciki a jikinta, ana kaisu asibiti aka shiga da Sa'adatu Theater aka ciro haƙoran da suke shige mata dadashi, Maama kam babban aiki aka shirya yi mata sbd karaya biyu ta samu a ƙashin cinya kuma ƙafa ɗaya, in banda kuka babu abinda Maama take tana cewa Naseer ka kiramin Nabilah da Huzaifa na gansu, zuwa washe gari akace za a yiwa Maama aiki a ƙashin cinya, likitoci sunce idan ya wuce gobe to saidai a datse ƙafar, Naseer ya kira Huzaifa yace ya kamo hanya, shi daman Huzaifa dan i don't care ne ga kuma zuciyar tsiya, tintini yayi watsin uwar watsi da lamarin su Sa'adatu da ita kanta Maaman, gashi Naseer ya gaya masa yacca sukay shiyasa ya sake fusata, a daren ranar kuwa Huzaifa ya iso Kano daga Dutse, saida ya fara duba Maama a ward din ƴan karaya snn ya wuce ward din da Sa'adatu take don itama tana jin jiki, Nurse ya tarar tana bata Yoghurt kasancewar bbu mai kula da ita mace, Huzaifa ya ringa kallon Sa'adatu kafin yace "wane ya fille mata kunne ɗaya..?", Nurse tace "A haka muka ganta dashi". Washe gari an shiga da Maama surgery knn saiga Nabilah, Umma ce ta kirata a waya ta sanar da ita abinda yake faruwa, itama Umman Naseer ne ya gaya mata yace duk an kwantar dasu a asibiti, Saida aka yagalgala tsokar Maama snn aka samu yi mata ɗorin ƙashi, wai nan ma don asibiti ne, baiwar Allah Nabilah ita ta ringa ɗawainiya da uwarta da Sa'adatu, Maimuna kuma Huzaifa ya kaɗata gida sbd tsohon cikin da take dashi, daga shi har Naseer sosai wnn cikin nata ya tsaya musu a rai, Maimuna da aka kaɗa gida ce take jagwalgwala abincin da ake kaiwa asibiti...........✍️
💛 HAJAR 💛
{99..}
Kwanansu Maama uku a asibiti aka canza Sa'adatu zuwa na mahaukata, lokaci guda ciwon nata ya tashi ta fara dukan Nurses, allurai aka ringa garƙama mata a asibitin mahaukatan, da aka mata gwajin kwakwalwa Sai aka ga kwakwalwar nata lfy lou bbu cuta, gida aka mayar da ita aka duƙufa neman mgani na Aljanu tinda ana tunanin su suka shafeta, Maama kam satinta biyu a asibiti tana jinya, ranar da ta cika sati biyu da kwana biyu aka sallameta, Naseer Huzaifa da Nabilah ne suke ta tiri tiri da ita. Washe gari Maama na zaune tsakar gida akan tabarma ta miƙe ƙafar data karye, Nabilah ta kawo mata abincin da ta dafa, Maama ta kalli Nabilah da idanunta da suka cika da ƙwalla tace "Allah ya miki albarka Nabilah", Nabilah tace "Ameen", Maama ta janyo ƙasan rigarta ta ringa goge hawayen da suka shiga sakko mata, da yammacin ranar Naseer ya shigo, tabarmar da Maama ke zaune tana jinyar ƙafa ya nufa, ya duƙa gabanta yana tambayarta ya jiki, kawai saita fashe da kuka wiwi, nadama da dana sani ne fal cike da zuciyarta, Naseer yace "Maama ki dena wnn kukan dan Allah..", Maama ta fyace majina tace "dole nayi kuka Nasiru, ban yiwa kaina adalci ba, ban yiwa mahaifinku adalci ba, ban yiwa ƴaƴan da na haifa adalci ba, haka zalika ban yiwa mutanen da na zauna dasu adalci ba, haƙƙin mutane ma kawai ya isheni, da baƙin cikina da na ƴaƴana da na yiwa gurguwar tarbiyya mahaifinku ya rasu, Nasiru dole nayi kuka idan na tuna haukan dana tafka...", dai dai nan Huzaifa ya shigo da ledar fruit da ya siyowa Maama, Huzaifa ya zauna kan dokin ƙofa yayi kiran Maimuna, daga ɗaki ta fito tana jan ƙafa, rama sosai ta ƙara gashi ta wani ɗashe kamar bbu jini a jikinta, ta samu guri ta zauna da kyar tace "Yaya gani", Huzaifa ya kalleta da ɗacin rai sai kuma ya dubi Naseer yace "Yaya ya za muyi da wnn...?", Naseer ya sauke ajiyar zuciya yace "Ai saita faɗi waye ya mata cikin", Huzaifa ya murtuke fuska yana kallon Maimuna yace "Ke..!!", Maimuna ta sunkuyar da kanta, Huzaifa ya daka mata tsawa yace "ba kiji mai akace ba", Maimuna tasa bayan hannu ta shaɓune hawayen dake sakko mata tace "wllh ban sani ba", Huzaifa yace "baki sani ba kamar ya, a ruwa ake sha..?", Maama tace "Maimuna kiyi mgana mna, nan ƴan uwanki da kika gani masu ƙwato miki haƙƙi ne", Maimuna tace "Billahillazi la'ilaha illa huwa ban sani ba, fyaɗe aka min" ta rushe da kuka. Tsakar dare naƙuda ta