HAJAR

Chapter 84 of 85

abincin da ake kaiwa asibiti...........✍️
💛 HAJAR 💛

{99..}
Kwanansu Maama uku a asibiti aka canza Sa'adatu zuwa na mahaukata, lokaci guda ciwon nata ya tashi ta fara dukan Nurses, allurai aka ringa garƙama mata a asibitin mahaukatan, da aka mata gwajin kwakwalwa Sai aka ga kwakwalwar nata lfy lou bbu cuta, gida aka mayar da ita aka duƙufa neman mgani na Aljanu tinda ana tunanin su suka shafeta, Maama kam satinta biyu a asibiti tana jinya, ranar da ta cika sati biyu da kwana biyu aka sallameta, Naseer Huzaifa da Nabilah ne suke ta tiri tiri da ita. Washe gari Maama na zaune tsakar gida akan tabarma ta miƙe ƙafar data karye, Nabilah ta kawo mata abincin da ta dafa, Maama ta kalli Nabilah da idanunta da suka cika da ƙwalla tace "Allah ya miki albarka Nabilah", Nabilah tace "Ameen", Maama ta janyo ƙasan rigarta ta ringa goge hawayen da suka shiga sakko mata, da yammacin ranar Naseer ya shigo, tabarmar da Maama ke zaune tana jinyar ƙafa ya nufa, ya duƙa gabanta yana tambayarta ya jiki, kawai saita fashe da kuka wiwi, nadama da dana sani ne fal cike da zuciyarta, Naseer yace "Maama ki dena wnn kukan dan Allah..", Maama ta fyace majina tace "dole nayi kuka Nasiru, ban yiwa kaina adalci ba, ban yiwa mahaifinku adalci ba, ban yiwa ƴaƴan da na haifa adalci ba, haka zalika ban yiwa mutanen da na zauna dasu adalci ba, haƙƙin mutane ma kawai ya isheni, da baƙin cikina da na ƴaƴana da na yiwa gurguwar tarbiyya mahaifinku ya rasu, Nasiru dole nayi kuka idan na tuna haukan dana tafka...", dai dai nan Huzaifa ya shigo da ledar fruit da ya siyowa Maama, Huzaifa ya zauna kan dokin ƙofa yayi kiran Maimuna, daga ɗaki ta fito tana jan ƙafa, rama sosai ta ƙara gashi ta wani ɗashe kamar bbu jini a jikinta, ta samu guri ta zauna da kyar tace "Yaya gani", Huzaifa ya kalleta da ɗacin rai sai kuma ya dubi Naseer yace "Yaya ya za muyi da wnn...?", Naseer ya sauke ajiyar zuciya yace "Ai saita faɗi waye ya mata cikin", Huzaifa ya murtuke fuska yana kallon Maimuna yace "Ke..!!", Maimuna ta sunkuyar da kanta, Huzaifa ya daka mata tsawa yace "ba kiji mai akace ba", Maimuna tasa bayan hannu ta shaɓune hawayen dake sakko mata tace "wllh ban sani ba", Huzaifa yace "baki sani ba kamar ya, a ruwa ake sha..?", Maama tace "Maimuna kiyi mgana mna, nan ƴan uwanki da kika gani masu ƙwato miki haƙƙi ne", Maimuna tace "Billahillazi la'ilaha illa huwa ban sani ba, fyaɗe aka min" ta rushe da kuka. Tsakar dare naƙuda ta kama Maimuna, tun tana jurewa ita kaɗai har ta ja jiki ta tashi Nabilah, Nabilah da taga bazata iya da Maimuna ba ta tashi Maama, ga Maama ba ƙafa saidai jan buttocks, Maama tasan naƙuda ce ta tahowa Maimuna, mgana ake ta tsakar dare bbu abin hawa ballantana a kaita asibiti, Naseer da Huzaifa ne suka tafi neman abin hawan, Maama ganin haihuwa ta taho don har Maimuna ta fara nishi kan ɗaya ya taho ta kalli Nabilah tace ta bata reza, Nabilah ta lalubo reza a jakarta wcca ta taɓa amfani da ita sau ɗaya, a duk wnn zazzafar wainar da ake toyawa Sa'adatu bata san anayi ba, kawai bacci take sai kace mushe, cikin azaba Maimuna ta haihu, ta haifi ƴa mace, saidai kuma tana haihuwar jini ya ɓalle kamar an yanka rago, wata mummunar tear ta samu tin daga sama har ƙasa ta yage, Nabilah ta naɗe jaririyar ta ajiyeta a ƙasa, gaba ɗaya sun gigice ganin yacca jini yake malala, cikin azaba da raɗaɗi Maimuna tace "wayyoh Allahna Maama, ƙirjina zai fashe", Nabilah ta rushe da kuka ta fita a guje ba tare da tasan ina ta nufa ba, lokaci guda Maimuna ta fara convulsion idanunta suka ƙaƙƙafe, hakan tasa Maama ta manta da karayar cinyarta ta miƙe a gigice ta nufi ƙofa, da ƙarfi ta taka ƙafar ai kam ɗorin ya goce, ƙashin ya huda tsokarta ya ɓillo waje, azaba tasa Maama ta tafi luuu ta faɗi a ƙasa bayan kanta ya daki dokin ƙofa. Nabilah kam ashe maƙota ta je ta ringa bubbuga ƙofa, cikin sa'a gidan Mukaila suka buɗe ta taho tare da matarsa, suna zuwa suka tarar da Maimuna Allah ya amshi abarsa, Maama kuma ta sume, kukan jaririyar Maimuna ne kawai yake amsa ƙuwwa a gidan.

★Wajen ƙarfe 10 na safe Hajar ta shiga part din Nurain, direct bedroom ta wuce, bata gansa a bedroom din ba don haka ta shiga closet, ta ɗan waro ido ganin kayan da yake sakawa tace "fita za kayi Husband..?", yace "Uhmm", tace "Ohk" sai kuma ta ƙarasa ciki ta tsaya daf dashi tace "fatan dai ba a min nawa aikin ba..?", yayi murmushi yace "yeah", ya miƙa mata links din da yake shirin sakawa, amsa tayi ta maƙala masa snn ta ɓalle masa buttons din riga, tace "Wai ina zaka yau fa Saturday..?", yace "you know Hammad..?", tace "Eh", yace "shine ya kirani ya bani location yace na samesa a wajen, sunxo kano ne sbd sunji labarin wani yaga ƙanwarsa Azeeza da ta ɓata anan garin", tace "Mother din wnn yaron da muka gani a gidansa..?", yace "Ashraaf... Eh Mamansa", tace "Allah ya bayyanata..", yace "Ameen", Hajar kawai Ashraaf take hangowa, har yau horse toy din da ya bawa Nanerh yana nan tana wasanta dashi, tace "breakfast is ready, sai kaci zaka fita ko..?", yace "Eh", tare suka fito, Hajar ta wuce ta sauka downstairs, shi kam room din Nanerh ya buɗe, kan floor mattress dinta mai faɗi ya ganta ga toys nan iri iri zagaye da ita, yayi murmushi yace "Princess", tini Nanerh ta jefar da toy din hannunta ta rarrafo da sauri inda yake tana ɓangala masa dariya, ya sunkuya ya ɗauketa ya ɗan cillata sama, nan ma ta kyalkyale da dariya, pecking cheeks dinta yayi, sai ƙamshin baby colories da perfume take, fess da ita kamar uwarta, an kama mata cikakkiyar sumarta da cotton band, Hajar na tsaye dining section tana serving abinci taji saukowarsu, ta ɗaga kanta ta kalli Nurain da Nanerh take wawurar hancinsa yana kaucar da fuska tace "Ehen ka ɗaukota ta hanamu cin abinci ko bayan ita ta cika stomach dinta", ya ƙarasa dining din ya zauna a kujerarsa sai kuma ya ɗora Nanerh kan table suka cigaba da wasansu, Hajar na gama zuba masu abinci ta shiga wani room dake downstairs, few secs ta fito da keken Nanerh, ta ajiye keken daga gefen kujerarta snn ta amshi Nanerh a hannunsa ta sakata cikin keken, ta ɗago kanta sukay ido huɗu dashi, ta ɗan turo baki tace "wnn uwar hidimar ce zata bar mu muci abinci lfy, ynxu zata baddala table din", da haka suka fara cin abincin, Hajar na bawa Nanerh wnda zata iya ci cikin abincin. Ƙarfe 11 da wni abun Hajar na closet dinta tana sake kimtsata duk da cewa a gyare take, tana aikin tana humming song, bayan ta gama aikin ta fito, wayarta da ta ajiye gefen gado kusa da Nanerh da take bacci ta ɗauka, 5 missed call from Umma, haka kurum taji gabanta ya faɗi, kiran Umma tayi, bayan sun gama wayar Hajar ta zauna gefen gado ta dafe kanta tace "innalillah wa'inna ilayhirraji'un". A ranar Hajar taje gidan rasuwar ta tarar da Umma acan, duk wnda yaji irin mutuwar da Maimuna tayi sai zuciyarsa ta karye, mutuwa ce ta shahada, ƴarta na nan goye a bayan Nabilah, wujijjigar da Maama tayi ba a cewa komai, bayan an kaita an gyara mata ɗorin da ya sake ɓarɓarcewa tace a dawo da ita gida bazata zauna a asibiti ba, sai ranar sadakar uku snn Hajar ta sake zuwa gidan rasuwar, abinci mai kyau ta kai wnda ta saka su Binta sukay, gidan rasuwar a ɗaɗe yake mutane ƙalilan ne suke zuwa, Hajar na zaune can gefe a tabarma ɗaya da Nabilah wacca take bawa ƴar Maimuna madarar da Huzaifa ya siyo mata, Ita Hajar jira take Umma tazo sai su tafi tare, ai kam bbu jimawa Umman tazo tare da Mu'azzam da Sabrah, Umma ta yiwa Maama ta'aziyya, Mu'azzam ma ya mata, Maama saidai ta gyaɗa kai don bata iya mgana tsabar yacca mutuwar ta daketa, Naseer ne ya shigo Umma ta masa ta'aziyya hakama Hajar, ya tashi zai fita Maama tace "Naseer karka fita, ka kirawo Huzaifa ma", Naseer yace "Toh", ya ciro waya ya kira Huzaifa wnda shima yana kusa, bbu jimawa kam ya shigo, Maama ta ɗan yunƙura tana kallon Mu'azzam tace "Mu'azzamu a bakacin Maimuna ni ina nema mata yafiyarka, dan Allah ka yafe mata abinda ta maka", Mu'azzam ya shafa kansa yace "Na yafe mata duniya da lahira", Maama ta kalli Umma tace "Faɗima dan girman ki yafemin abinda na miki, haƙiƙa na cutar dake ban barki kin zauna lfy a gidan mijinki ba, na cutar dake haka zalika na cutar da ƴaƴanki", Umma ta numfasa tace "na yafe miki, Allah ya yafe mana duka", Maama ta share hawayen da suke zubo mata tace "kowa da yake zaune nan nasan bbu wnda bashi da tabona, ku yafemin ba don halina ba", shiru tsakar gidan yayi bbu wnda yace komai, Sa'adatu ce ta fito tana cewa "Maama ni baki nemi gafarata ba bayan kece kika sabautamin rayuwa, duniya ta min ruku'un dila, duniya ta min gwatson kyanwa, duniya ta min juyin kwaɗo, duk kece sanadi Maama, Allah sarki Maimu Allah ya jiƙanta ya gafarta mata, ni bazan ce komai ba akan mummunar laifin dana tafkawa mahaliccina ba saidai zan dawwama yin istigfari har na koma garesa, ina masu hali irin nawa..?, ƴan mata, zawarawa, matan aure wnda suke aikata abinda yafi zina bala'i suke neman jinsinsu, ina kira da masu irin wnn hali nawa dasu tuba tin kafin lokaci ya ƙure musu, duniya ba wajen tabbata bace lokacinta ƙalilan ne, Zeenatu Mabaruka Teema da tsinanniyar shugabarmu mai ƙungiya naga darisa akansu da kuma kaina, bbu wnda acikinmu wnda bai amshi hukunci ba, nima na amshi nawa, ƴar uwa ki tina ba'a nan masifar take ba sai mutuwa ta riski bawa, rayuwar kabari har lokacin da zata tsaya gaban mahaliccinka domin amsar hukunci, Ni Sa'adatu nayi nadama kuma ina kira da masu irin halina su gyara tin kafin lokaci ya ƙure musu....", daidai nan ta zube ƙasa ta fara haukan nata tana kuka, Huzaifa ya jata ɗaki ya kulle tin kafin ta fara doke doke. Mijin Nabilah yayi kawaice sosai don baice ta dawo gida ba har Maama taji sauƙi, toh saidai ace sauƙi amma kuma ba sauƙi ba don ƙafar shanyewa tayi ta warke a haka, Maama bata iya tafiya saidai da sanda ko kuma ta hau keken guragu, ƴar Maimuna da aka mayar mata da sunan uwarta Nabilah ce ke kula da ita, Sa'adatu an ɗan samu waraka ta dalilin rubutun da ake bata. Da Nabilah tazo tafiya tace zata tafi da Maimuna ƙarama, Maama tace A'a ta bar mata ita wnn yarinya a jikinta take ganin kurwar Maimuna kuma gashi tana kama da uwarta, da kyar Maama ta shawo kan Nabilah akan yarinyar tace bata san ya dangin mijinta zasu amshi yarinyar ba snn kuma bata so wni abun ya haɗata da mijinta. Life continues... Naseer da Huzaifa suka haɗa hannu suka canzawa mahaifiyarsu gida ta bar unguwar dala, gwara ta bar unguwar ta koma inda ba a santa ba inda za a santa da sabon kyakkyawan halinta na yanxu, bil ƙalbi warruhi Maama take kula da Maimuna ƙarama da taimakon Sa'adatu wcca taji sauƙi sosai saida ta nakasta ainun don ba tada haƙoran gaba da kunne ɗaya, haka abun yake shegiya dai Maama ta ganta a kanta, yacca take kiran Hajar shegiya a da ynxu itace take rainon shegiya, shegiyar da take masifar mutuwar so. bayan watanni biyar akay auren Naseer inda ya auri ƙawar Hajar wacca sukay Islamiyya tare wato Zainab, idan kaga yacca Umma da Maama suke ynxu kai ka ɗauka basu taɓa zaman hatsaniya ba, sosai Umma ta shiga bikin Naseer akay da ita, Alhmdllh arziƙin Naseer ya ƙara burunƙasa don ynxu ba direba bane, acan dry port ta Lagos da Port Harcourt ya samu babban aiki, murna a wajen Hajar ba a cewa komai da Yayanta ya auri ƙawarta Zainab, Huzaifa ya baro Dutse ya dawo Kano da aikinsa, shima an kai kuɗinsa wajen budurwarsa dake dutse, Mu'azzam kam tukunna dai don tasa wife to be din Insha Allah bata isa aure ba, Anty tace ta basa Humairah, ita kuma Umma tace ta bawa Abdallah Sabrah, hakan zai sa zumunci ya ƙara ƙulluwa snn dangin ya ƙara girma......✍️
💛 HAJAR 💛

{100..}

Hajar ta shirya snn ta shirya Nanerh don yau juma'a ranar Umma zata tare a sabon gidan mijinta, bayan ansha gwagwarmaya Umma ta amince tayi aure, Kawunanta ne suka haska mata hanya yayinda Anty ma ta nusar da ita, tabbas aure shine rufin asirinta da na ƴaƴanta, ba a cewa uwarsu zaman kanta take ba ko kuma a kirasu da ƴaƴan mace, gashi kuma daman ba wni tsufa tayi ba don a shekara arba'in biyar kawai ta ɗora a kai, Babban mutum Umma ta aura wnda ya samu kyakkyawar shaida, danƙareren gida ya mallaka mata wnda anan ne zata zauna a gidan da yake matsayin nata, hakan tasa Umma ta tafi da yaranta biyu da suke gabanta, Mu'azzam da yake wni ɗan noƙewa wai shi babba tini ya saki jikinsa domin kwa a zahirin gsky mijin mahaifiyarsu mutumin kwarai ne kuma har ya fara musu riƙo irin na uba, tin safe sai yamma Hajar ta koma gida bakinta har kunne, ƴan uwanta sai samun cigaba suke a rayuwa, Ummanta ma has move on. Rayuwa mai mugun azabar daɗi da tsafta Hajar da Nurain suke shimfiɗawa, Happy family knn, shekarar Nanerh ɗaya Hajar ta yayeta daga mama, bbu wnda suka gayawa anyi yayen tsakanin Umma da Mami sbd kar wani yace a kaita wajensa, Nurain ne ya kissifa wnn shawarar don baya son a rabasa da Princess dinsa ko da kuwa na kwana ɗaya ne, Hajar ma tayi na'am da hakan don ita bata so a rabata da ƴarta, yarinyar akwai shiga rai da kyau kamar a sace, Hajar ba ta sha wni wahalar yaye Nanerh ba don already yarinyar ta kama abinci, tin kafin ma ta yayeta bata fiya shan mimin ba sai an bata, Nanerh na nan chubby da ita sai ma kyau da ta ƙara bbu wata rama na yaye. A kusan tare Hafsah da Khausar suka haihu, Khausar ce ta fara haihuwa ta haifi baby boy snn Hafsah da itama ta haifi baby boy, Nabilah kuma har yau Allah bai kawo haihuwar ba duk da cewa ta riga Khausar da Hafsah aure, komai iri ɗaya na kayan barka Hajar ta bawa Hafsah da Khausar, Hajar da taje barkar Hafsah sai taji dama ta kwana kawai sbd Nurain baya nan ya tafi Lagos wni workshop, amma dai bata kwanan ba tinda mijinta bai bata wnn damar da zai tafi ba, ranar da zai dawo tin asuba Hajar take shirin tarbonsa, kunshi da kitso daman tin jiya aka mata, favourite dinsa ta dafa iri iri, wajen sha ɗaya ya iso gidan, habawa kaga rige rigen zuwa tarosa tsakanin ƴa da uwa, Nanerh har dasu tuntuɓe, Hajar ta cake taƙi ƙarasawa ta tsaya kallon Nanerh, Nurain ya ɗauketa snn ya cillata sama, dariya kawai Nanerh ke ɓaɓɓaka masa, yayi pecking cheeks dinta yace "Princess", Hajar ta riƙe ƙugu kamar gske tace "wnn yarinyar..", Nurain ya ajiye Nanerh kan kujera ya wuce gurin Hajar ya rumgumeta, tace "Sannu da zuwa My Moon", yayi kissing lips dinta lightly yace "yawwa wifey". Bayan sallar la'asar Nurain yace Hajar ta shirya zata rakasa unguwa, veil da jaka kawai taje ta dauko tinda a shirye take, bata zama a hargitse a gidanta gsky, Nurain har ya ɗauki Nanerh sun fita compound, Hajar na fita compound ta nufi parking space ta buɗe front seat din motar da suka shiga, Hajar ta kalli Nanerh dake zaune a spot din da yake nata tana shan sweet, Hajar tace "ke Papa's bear or Princess kike that's my spot", Nurain ya ɗauke Nanerh daga kan kujerar, Hajar ta shiga ta gyara zamanta ta rufe ƙofa, sai a snn ya miƙa mata Nanerh, saida suka isa gidan Anty Zulaihah snn Hajar ta san nan din zasu ita tasha ma wni gurin ne daban, bayan sun gaisa da Anty Zulaihah wcca ta dauki Nanerh tana mata wasan kakanni Hajar ta tashi ta shiga ɗakin da Khausar take, tare ta ganta da Farooq wnda yake riƙe da babynsa, shima zuwansa knn, ai da tasan tare suke da Farooq da baza ta shigo ba amma kuma tayi knocking door Khausar tace ta shigo, Khausar tace "barka da zuwa Oum Nanerh", Hajar tayi murmushi tace "yawwa Maman boy", Hajar suka gaisa da Farooq ya tmbyi Nanerh, tace masa tana wajen Anty Zulaihah, Nurain ne ya shigo, firr Farooq yace Nurain bazai ɗauki baby ba ai ya makara, Nurain dai baice uffan ba don ya gane rama abinda ya masa yake, Hajar da ta gane itama ta ringa murmushi, basu wani jima ba suka tafi, gidansu Nurain suka wuce don daman yana son zuwa ya gaida parent dinsa tinda yau ne ya dawo daga Lagos, Hajar na zaune a main palour tare da Noor wcca ta kawo ɗanta Anaab wajen Mami yaye, Hajar tace "kai Noor yanxu yaushe Anaab din ya isa yaye, he is too young", Noor tace "na ji da wnda yake womb dina ma", Hajar ta riƙe haɓa sai kuma tayi dariya tace "har kin manta gidan glass din knn..?", Noor tace "ina fa na manta, da planning fa a jikina", Hajar tace "ikon Allah", Noor tace "Ai canza wani zanyi bayan na haihu", Hajar tace "Toh Allah ya raba lfy", Noor tace "Ameen... ya kamata a yiwa Nanerh ƙanwa gsky", Hajar tayi dariya tace "ba gashi nan zaki mata ba, ga Anaab ma already an mata, very soon Anty Sakeena ma zata mata wani", sai after isha'i su Hajar

Download complete TXT · Novel page