Showing 9001 words to 12000 words out of 162658 words
ya kai ni wajan Hadaan d'ina".
Gaba d'aya daga alhaji Sammani har wannan matar kallon Binty su ka yi ci ke da mamaki ta re da kuma waigawa don su ga dawa ta ke magana, amma wayam su ka ga ni sai mutanan da su ke wuce wa d'aya-d'aya su na shiga Saloon d'in.
"Binty dawa kike magana?" Alhaji Sammani ya fad'a ya na kallon ta at the same time kuma ya na kallon gefe da kuma bayan shi. Kasancewar gaba d'ayan su kallonta su ke yi.
"Kaka ma na, sai cewa ya ke yi wai ka da na bi ka, na bi wannan". Ta fad'i maganar ne ta na nu na wannan matar.
"Tun a in da ka d'auko ni ya ke ce wa wai ka da na bi ka. Yanzu kuma ya ce na bi wannan".
Zaro idanuwa Alhaji sammani ya yi jikinsa har ya soma b'ari.
"Ka da dai a ce aljana na 'dauko. Na shiga uku ni sammani". Ya fad'a cikin zuciyar sa. Can kuma wani zuciyar ta ce masa, kai Sammani kawai ka kai ta, idan ya so ko aljanar ce su su ka san yadda za su yi da ita. Kai dai ba ka kai ta ka fita ba.
"Ke Mss Raliya kwantar da hankalin ki, haka ta ke. Ta na da 'dan matsala a kwakwalwarta ne kad'an. Wani lokacin haka ta ke behaving". Fad'in Alhaji Sammani da turanci ta re da murmushi ya na shafa kan Binty.
Ajiyar zuciya Raliya ta saki ta re da fad'in,
"Allah sarki, I pity her. Allah ya ba ta lafiya. Muje ko beauty". Ta fad'i hakanne ta re da kama hannun Binty su kai gaba.
Ita kuwa Binty dad'i ne ya kashe ta kasancewar ta ji su na kiran ta da sunan da Hadaan ya ke kiran ta da shi.
Ciki su ka shiga, shi kuma Alhaji Sammani ya zauna a cikin mota ya na jiran su. Binty baki da hanci ta saki ta na kallon cikin katafaran Saloon d'in nan. Wani 'katon d'aki su ka shiga mai wahalar fasaltawa saboda tsaruwarsa.
"Zauna a nan ki jira ni". Raliya ta nuna mata wani kujera ta re da yin gaba ta shiga wani 'dan corridor da ke 'dauke da bathroom a ciki. Bayan minti biyar ta fito ta re da kiran Bintyn. Bintin ta tashi ta re da bin bayan ta. Cikin bathroom d'in su ka shiga. Raliya ta riga da ta had'a ruwan wanka da sai fitar da k'amshi ya ke. Ga sabon sponge nan da kuma toothpaste da brush a gefe. Cire mata kayan jikin ta ta yi tare da saka ta ta shiga cikin wani baf na wanka mai circle. Kai ta fara wanke mata wanda sai a wankewa na goma ya soma kumfa, don da sai wani irin coffee brown 'din datti ke fita da wani irin yauk'i yauk'i abun kyamma da k'azanta. A tak'aice dai sai da Raliya ta wanke kan nan sau goma sha bakwai ka na ya fita k'al k'al gashi bak'ik'k'irin da shi mai cika da tsayi har tsakiyar bayanta.
"Subhanallah! Masha Allah!". Raliya ta fad'i domin tun da ta ke aikin saloon ba ta tab'a ganin yarinyar k'arama mai irin wannan uban gashin ba. Wai a hakan ma don ba'a ja shi da hand drayer ba.
Wanka kuwa sai da farin sosan nan ya koma ruwan k'asa saboda dattin da ke fita daga jikin Binty. Sai da Raliya ta ga ta yi k'al jikin ta na sulb'i ka na ta na'dota cikin towel su ka dawo wani d'akin mai k'aton madubi gaba da baya. Ga kaya gyaran kai da su attachment nan kala-kala da su relaxer da sauran su a ciki. Wani man shafawa Raliya ta d'auko mai k'amshi ta shafe jikin Binty da shi ka na ta d'aurata akan wani dogon kujera. Wani irin juyowa Binty ta yi ta kalli Raliya ta re da fad'in,
"Ni ce wannan a cikin wannan abun? A she ina da kyau. Kalli gashi na ya canza kala. Mai ki ka min na koma haka?". Binty ta fad'a kasancewar ta na da shegen surutu. Kuma duk lokacin Allah ya sa ta ga fuskan ta cikin madubin mota ko kuma irin shagunan nan ma su slide, dak'an-dak'an ta ke ganin ta, kuma wancan lokacin gashin ya rine da kalar k'asa da kuma bola a jiki.
"Ke ce mana. Ai ke kyakkyawa ce. Ga ki da dimple da gashi mai kyau". Fad'in Raliya.
"Da ki ka min wanka sai naji jikina ya min iska da dad'i. Wai ke ya sunan ki". Binty ta fad'a ta na k'ara kallon kan ta cikin madubi.
"Sunana Raliya, amma ke ki kira ni da aunty Raliya kin ji?". Aunty Raliya ta fa'da ta na warware gashin kan Bintyn da ya zuba har bayan ta. Hand drayer ta kunna ta kai shi saitin kan Bintyn za ta fara busar mata da shi. Wani irin ihu Binty ta kwala ta re da wurgi da towel d'in jikin tai ta yi hanyar wa je da gudu. Da kyar Raliya ta ka mo ta. Amma fir tak'i tsayawa a busar da gashin nan, don bak'aramin tsoransa ta ke ji ba. Sai da Raliya ta ga dagaske fa Binty ba za ta tsaya ba sannan ta kashe hand drayan ta re da fita ta kirawo wasu mata guda uku su ka ri'ke mata Bintyn ta na ihu ka na aka jaa gashin nan da yai wani irn masifar tsawo da kyau sai kyalli ya ke yi.
*ASSALAMU ALAIKUM READERS, GA NI NA ZO MA KU DA SABON LITTAFI NA MAI SUNA A SAMA, WANDA YA ZO DA ZAFI-ZAFIN SA, KUMA NA TABBATA ZA KU JI DAD'IN SA. BA ZAN CI KA KU DA SURUTU BA, KAWAI KU BI NI A FREE PAGES, KU DA KAN KU ZA KU GA NE BOOK D'IN NA DABAN NE. KAWAI KU NU NA MIN ONE LOVE WAJAN SIYAN BOOK D'IN AKAN FARASHI AKAN FARASHI MAI RAHUSA KAMAR HAKA:*
*Normal group shine mutum zai bi ya 500 idan ka ti ne, idan kuma ta account ne 300.*
*VIP kuma 1000 ne idan kati ne. Idan kuma ta account ne 700.*
*MUTANAN NIGER KUMA ZA SU BI YA KAMAR HAKA*:
*Normal group shine mutum zai bi ya 500F idan ka ti ne, idan kuma ta account ne 300F.*
*VIP kuma 1000F ne idan kati ne. Idan kuma ta account ne 700F.*
*ʜᴀʙɪʙᴀᴛɪᴇꜱ ᴅᴀɴ ɢɪʀᴍᴀɴ ᴀʟʟᴀʜ ᴋᴜ ɴᴜ ɴᴀ ᴍɪɴ ʟᴏᴠᴇ ᴡᴀᴊᴀɴ ꜱʜᴀʀɪɴɢ*
🌼 🌹 🌹 🌼
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹 *BA NI DA GATA*🌹
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌼. 🌼
🌹
🌹 🌹
🌹 🌹
*ᴘᴀɪᴅ ʙᴏᴏᴋ*
*NARRATED & WRITTEN BY*
*ZULFA'U SA'EED IBRAHIM*
( *_MATAR SAYYADEE_*)
☀️ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION*☀️💪
( *Home of quality and trusted writer's of the nation*)💪🏻
*DEDICATED TO THE MOST BEAUTIFUL WOMAN IN THE WHOLE WORLD (MY MOTHER). ALLAH YA JIK'AN KI DA ℝ𝔸ℍ𝔸𝕄𝔸*
*__________________*
*FREE PAGE 9&10*
*__________________*
..............Bayan an gama busar da kan, aunty Raliya ta mai da ta kan kujeran ta re da k'ara gyara kan tai parking d'insa a tsakiya ta re da yi mata donut, sannan kuma ta saki jelar har tsakiyar bayan ta da shi ma ya sha stones ma su kyau, ta kuma sa ka mata wani kwalliya ma su kyalli da ya k'ara k'awata gashin na ta akan donut d'in. Wad'annan matan da su ka rik'e Binty a kai mata gyaran kai kuwa bakin su ya k'i rufuwa sai adoring gashin su ke yi.
Wata doguwar gown kalar pink Raliya ta fito da shi a cikin wani kwali da fad'ar tsaruwar shi b'ata ba ki ne. Pant ta fa ra saka mata fari k'al da shi ka na ta saka mata wannan had'ad'd'an gown d'in. Powder kawai ta shafa mata ta re da lipstick.
"Wow!". Fad'in Raliya sai k'ara kallon Bintyn ta ke yi kamar ta lashe ta. Domin fad'in irin kyawun da Binty ta yi b'ata baki ne. Za ka rantse y'ar shugaban k'asa ce ko kuma 'dan majalisa.
Hannunta Raliya ta ka ma su ka fito daga cikin wannan d'akin. Duk in da su ka wuce sai ido ya koma kan su ta re da gabon kyawun da Bintyn ta yi. Wasu ma har hoto su ke mata. Ita kan ta aunty Raliyar ta ma ta hoto ya kai kala ashirin. Akwai wanda su ka yi su biyu da kuma wanda ta yi ma ta ita kad'ai.
Ko da su ka zo wajan motar Alhaji Sammani, bai ga ne Binty ba, sai ce wa ya yi,
"Raliya kun dad'e fa, ina ita yarinyar ta ke?".
Nu na Binty ta yi ta na murmushi tare da fad'in,
"Alhaji ba ga tanan ba. Ka ga ta canza ko?".
Waro idanuwa Alhaji Sammani ya yi tare da fad'in,
"Haba dai? Wannan ita ce yarinyar da na zo da ita. Kai ina there must be mistake somewhere, wannan ba yarinyar da na kawo ba ce". Fad'in Alhaji Sammani ya na k'ara gwale idanuwa ya na kallon Bintyn da ke ta zuba masa murmushi kumatukanta na lob'awa.
"Wallahi sir itace, ita ce, ni kai na da na gyara ta ba k'aramin mamaki na ke da kyawun da Allah ya ni'imtata da shi. Don Allah Alhaji kar ka ce na cika tambaya, ya ka ke da ita?".
Shan mur Alhaji Sammani ya yi ta re da fad'in,
"Wannan ba matsalar ki ba ce, forward your account details in tura ma ki kud'in ki tun da kin ga ma aikin ki".
Tsuke baki Raliya ta yi ta re da daddanna wayarta. Cikin abunda bai fi minti biyu ba, har Alhaji Sammani ya turawa Raliya dubu d'ari biyu.
"Thank you Sir". Raliya ta fad'a ta re da shafa kan Binty ta ce,
"To Beauty sai mun sa ke had'uwa. Ki kula da kan ki kin ji?".
"To" shi ne kawai abunda Binty ta fad'a. Shi kuwa Alhaji Sammani ce wa ya yi cikin zuciyar sa,
"Shegiya sai dai a lahira, don wallahi na tabbata yau na kai wannan kyakkyawar yarinya k'ungiya, sai an ba ni muk'ami na musamman". Ya na gama fad'in hakan ya ka ma Binty ya d'aga ta ta re da sa ka ta gaban mota, ka na ya zagaya ya shiga mazaunin driver ya yi wa motar key ta re da reverse ya bar Saloon d'in ya nu fi wa ni eatery da ita domin ta ci abincin, don har an yi kiran sallar magriba. Waitress ce ta zo ta ka wo ma sa menu ya zab'i abunda za'a kawo ma su. Shi bai yi ordering ko mai ba, Binty ka wai ya sa a ka kawo wa pounded yam da miyan egusi da yaji stockfish da ganda a ciki. Ko da Binty ta ga abincin sai ta dinga bin abincin da idanuwa domin bata tab'a ganin irin wannan abincin ba a rayuwar ta.
"Ci mana Binty, ki yi sauri mu ta fi dare na yi". Fad'in Alhaji Sammani.
"Ni ban san abincin ba, ya ake yin sa? Ban tab'a ganin sa ba". Binty ta fad'a.
"Zan ci uwar yarinyar nan wallahi". Alhaji Sammani ya fad'a cikin zuciyar sa. Amma a zahiri sai ce wa ya yi,
"Ki gutsiri wannan, sai ki sa ka a cikin miyar ki sa ka a bakin ki, akwai dad'i". Ya fad'i hakane ya na mata demonstrating.
Kamar yadda ya gwada ma ta haka ta yi, aikuwa ta wa ni lumshe ido tare da fad'in,
"Kaiiiii wallahi akwai dad'iiiiiiii, kamar in ta ci kar ya k'are".
"Duk lokacin da ki ke so ki min magana zan kawo ki nan sai ki k'ara ci". Fad'in Alhaji Sammani ci ke da k'osawa.
Ba ta sa ke cewa ko mai ba, sai faman loma ta ke yi ta na jujjuya kai ta re da k'anana-k'ananan wak'a. Miyan kuma duk ya b'ata gaban pink 'din rigarta. Sai da ta ci sakwara biyar duk da cewar k'anana ne sai da Alhaji Sammani ya saki baki ya na kallon ta ci ke da mamaki cin abincin ta.
"Tun da kin gama tashi mu tafi kar mu yi dare".
Binty da ke lashe hannunta ta mik'e tare da share sauran miyan a jikin rigarta ka na ta d'au goran ruwan dake wajan ta yi gaba. Alhaji Sammani kuwa kiran waitress d'in ya yi ta re da bi yan kud'in ka na ya bi yo bayan Binty da ke tafiya ta na kwankwad'ar ruwan gora. Bu'de mota ya yi ta re da sa ka taa ciki shikuma ya juya ya koma mazaunin driver. Hotel d'in da ya sauka can ya nufa ta re da ruk'o hannun Bintyn ka har d'akin da ya ka ma. Makeken d'aki ne mai d'auke da royal bed da kuma wani rantsantsan Chinese carpet mai d'ankaran laushi. Ga kuma makeken gado samfarin italy.
Gaba d'aya Binty rud'ewa ta yi da ganin wannan d'akin, sai kalle-kalle ta ke yi ta re da k'if-k'if da idanuwa. K'afarta ta d'aga ta re da saukewa a kan wannan Chinese carpet d'in mai laushi. Wani ihu ta kwandara da ya firgita Alhaji Sammani, duk a tunanin sa ta hango abunda ke cikin jakar da ya shigo da ita ne. Domin ta kulle idanunta ne ta re da k'ank'ame jikinta.
"Ke lafiyan ki?" Alhaji Sammani ya fa'da ya na matsowa in da ta ke.
"Sansanin macijai na fad'a. Ka taimaka ka ciro min k'afata ka min na mutu. Na d'aura k'afata a kan maciji mai taushi".
Dariya ce ta sub'ucewa Alhaji Sammani, aiko ya kyakyata har da rik'e ciki ka na ya ce,
"Kwantar da hankalin ki Binty. Ba'a kan maciji ki ke ba, akan carpet ki ke mai laushi. Ba bu maciji a ciki n hotel d'in nan". Fad'in Alhaji Sammani ya na murmushi.
Sai a lokacin Binty ta soma bud'e idanunta kwara d'aya, ka na shi ma d'ayan ta bu'de sa. Doguwar ajiyar zuciya ta yi ta re da fad'in
"Kaiii amma Allah na gode ma ka. Na d'auka mutuwa zan yi ai. Yanzu wanna shi ne kapur? To menene kapur 'din? Me ya sa ake saka sa a nan d'in?". Binty ta fad'a ta re da duk'awa ta na shafa carpet d'in ta na dariya.
"Kapur d'in akwai d'an ban zan laushi. Hannuna lumewa ya ke yi a ciki. Kalla fa?". Binty ta sa ke fad'i ta na k'ara cusa hannunta a ciki n carpet d'in.
"Ammafin shi ke nan ai kwalliyar d'aki da shi". Fad'in Alhaji Sammani ta re da wucewa toilet ya bar ta a wajan sai zuba k'auyanci ta ke yi. Hatta bedside lamp sai da ta shafa ta na mamakin wannan miye.
Har Alhaji Sammani ya ga ma abunda zai yi ya fito daga toilet Binty na nan ta shafa wannan, ta shafa wancan.
"Ki kwanta a kan fado ki bacci, gobe da sassafe zan kai ki wajan Hadaan d'in ki, kin ji?".
Ci ke da farin ciki Binty ta kalli Alhaji Sammani ta re da fad'in,
"A wannan abun mai kyau zan kwanta? Kai amma na ji dad'i". Binty ta fad'a ta re da hawa kan gadon. Wani ihu ta sa ki ta re da mik'ewa ta zauna a tsakiyan gadon ta kuma gantsaro ba yan ta ta re da fad'in,
"Wayyoo Allah bola uwata ba ya na zai karye."
Alhaji Sammani tsaye ya yi ya na kallon ta, har ga Allah