Showing 3001 words to 6000 words out of 11107 words
kaita dan kawai yaji ƙarya,kai gaskiya inna bata masa adalci.
A nata ɓangaren inna borin kunya ta shiga yi tana faɗin"da basu dungure mata kan ba ay da bazatace su ɗin bane,"
Uwani dake gefe tana kallon ikon Allah ajiyar zuciya tayi tace "kowa ya biye zuciya zeyi dana sani,Allah ya kyauta"tana kaiwa nan ta miƙƙe ta shige ɗakinta.
Inna maimakon tayiwa Deeyanah faɗa,rungumota tayi jikinta,tana shafa kanta tace"barsu gudaliyata duk zasuyi su bari,ke ɗin dashen Allah ce"
********
A can Abuja ko IG daya koma ɗage zaman dayace zeyi yayi zuwa kwana uku masu zuwa,dan gaba ɗaya baya jin daɗin jikinshi.
Zaune yake a falon shi yana duba jaridun da aka kawo mishi kasancewar yau saturday yana gida.
Hajiya maryam ce ta shigo falon cikin wani leshi daya gaji da haɗuwa,tayi kwalliyarta data ƙara fito da kyanta.
Gefen mijin nata taje ta zauna ta langaɓar da kai gefe,dake nuna tana cikin damuwa.
Ɗago kai IG yayi ya dubeta,cike da kulawa ya ajiye jaridar hannunshi ya kamo hannunta dayasha jan lalle yace "ya akayi ne gimbiyata?,menene matsalarki?"
Kwantar da kai tayi kan kafaɗarshi tace cikin muryar shagwaɓa"Abban Deeyanah,yanzu fisabilillahi haka zaka zuba ido kabar Deeyanah a hannun Inna ba makaranta,ba ilimin addini bare na zamani,sede tallah da yawon banza tana ɗauko magana tarbiyarta na daɗa lalacewa?"
Runtse ido IG yayi dan matar tashi ta soso inda ke masa ƙaiƙayi,kullum da wannan baƙin cikin yake kwana yake tashi,cikin damuwa yace.
"a har kullum maryamu ban taɓa danasanin zama dake ba,kina sona kina son duk wani abu nawa,sede mahaifiyata ita bata sonki da duk wani abu daya shafeki,tunda Aisha ta mutu gun haihuwa,inna ta alaƙanta hakan dake,ko kaɗan bata ƙaunar ta bamu Deeyanah,na rasa yazanyi in amshi yarinyar nan in inganta rayuwarta,gaba ɗaya yarinyar yanzu in kika ganta wlh irin yaran nan ne marasa kunya ga ƙarya da haɗa sharri,kuma ita inna bata ganin hakan a matsayin laifi,ita har kullum son Deeyanar ne baa yi shiyasa ake mata hakan".
"Duk wannan Alhaji ni be dameniba,kawai tsorona ranar lahira Allah ze tuhumeka kan tarbiyar Deeyanah,yakamata de kayi wani abu akai"
Shuru ce ta biyo baya,kowa na saƙa da warwara azuciyarshi domin neman mafita.
Yinin Ranar IG yayi shi gun tunanin yadda zebi inna ta bashi ƴarshi cikin ruwan sanyi batare da sun samu matsala ba.
Bayan kwana biyu ya yanke shawarar zuwa kaita ya tuntuɓi inna akan maganar.
Da azahar ya isa garin,cikin rakiyar jami'an tsaro ko ina ya kaure da jiniya.
Yau ta gama suyar wainar rogonta kenan ya shigo gidan,dan haka arziƙin gurin zama ma be samuba se uwani ce ta shimfiɗa masa tabarma ya zauna.
"Deeyanah kiyi sauri kizo ki wuce rana tayi,kisamu ki shishshigar da ita kamin la'asar"cewar inna tana naɗa mata gammo.
Da saurinta ta fito,taci adonta tana gyara mayafinta,tace "inna yau in na siyar zan siyo rinbom acikin kuɗin"cewar Deeyanah wacce ko kallo mahaifin nata be isheta ba,sabida inna tace mata shi da matarshi ne suka kashe mata mahaifiyarta,Allah ne ma ya tsare da har da ita zasu haɗa.
Ɗora mata wainar tayi,tabita har soro tana mata fatan samun kasuwa,sannan ta dawo cikin gidan tayi kamar batasan dashi a gurin ba.
Wasu hawayene masu zafi suka gangaro daga idon IG ganin shi da yaba Milliyan dubu baya,gashi ƴarshi ta ɗauki tallan dabe wuce na dubu ɗaya ba zataje tayi gogayya da maza.share hawayen yayi sannan ya ƙarasa kusa da innar.
Tsugunawa yayi yace "inna barka da rana mun sameku lafiya?"
Seda tagama shan ƙamshi sannan tace"lafiya"
Shuru yayi na ɗan lokaci sannan yace"inna dama nazo ne neman alfarma agunki,kiban Deeyanah mutafi Abuja asata a makaranta,zamanta a haka beda amfani in kikayi laakari da cewa...."tass inna ta ɗaukeshi da mari,wanda yasashi yin shuru badan ya shirya yin hakan ba,lalle inna kin kai ƙwaruwa the whole IG guda.
Rintse idonshi yayi,ya dafe gurin,cikin tsantsan mamakin mahaifiyar tashi,da ta maida marin fuskarshi kamar abun wasa.
"a sata a makaranta ko kuma ku ida nufinku akanta nason ganin bayanta,to bazan baka ba,kai daga yau kakuma zuwamin da magana makamanciyar wannan wallahi seka gane kuranka,ɓacemin da gani,sullutu bawan mace".cewar inna bakinta har kumfa yakeyi.
Bece komai ba ya miƙe ya fice dag Gidan jamian tsaronshi dake waje suna jiransa suka mara masa baya.
Suna cikin tafiya,ya hangi Deeyanar gurin wasu leburori ta ajiye tallan tana ta rawa atsakiyarsu suna mata tafi,wani har jan hijab ɗinta yake.
Runtse ido IG yayi yana karanto duk adduar data zo bakinshi, umarni yabada a ɗauko masa ita.
Ba musu jami'i ɗaya ya fice a motar ya isa inda take bece komai ba ya sunkutota,tana ihu yasa ta a motar kusa da mahaifinta,direba yaja suka bar garin da hanzari.
Muje zuwa
Surbajo for life
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*SHIMFIƊAR AURENA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*na kuɗine 500 kacal,ki biya ayi tafiyar dake,akwai tarin ilimi acikinsa,da nishaɗantarwa uwa uba soyayya me tsayawa a zuciyar me karatu,ki turo naki mu jera dake😄*
*Zahra muhammed Nasir 2084024749 UBA*
*07044600044 Aturo shaidar biyan tanan,whatsapp*
*ta acct kawai ake biyan kuɗin littafin,in baki da acct akwai pos so in son siya kike se ki turo ta pos ɗin,nagode*
*6*
Tunda ta waigo taganta zaune kusa da mahaifin nata setaja bakinta ta tsuke,ta dena kukan dan tasan inde inna nada rai ba wanda ya isa yay mata tilas.
Koda suka isa katsina airport aka kaisu,lokacin da jirgin ze tashi ne Deeyanah ta fara ihu tana faɗin"wayyo Allah na innata zasu kaini saman jannati,wayyo kayan cikina duk sun kwashe su,wallahi amai zanyi ku saukeni"da ike a ɗaure take da seat bell ba wanda yabi takanta.
Suna isa Abuja kai tsaye gidanshi aka kaishi shi da Deeyanah.
Hajiya Maryam na zaune a falo taga mijin nata yashigo ya taso ƙeyar Deeyanar agaba tana turo baki gaba.
Cike da farin ciki hajiya ta miƙe ta kamo Deeyanar tana faɗin "Alhmdllh,ƴata ta dawo gareni,Allah na gode maka"
Da sauri Deeyanah ta kwace hannunta ta matsa gefe tace cike da tsiwa da rashin kunya "ƴarki ko de ƴar kishiyarki da kika kashe,ay wallahi nima nice ajalinki"ta faɗi ba tare da tsoron kowa ba.
A fusace IG ya ɗauketa da wani gigitaccen mari,wanda nan take ta saki futsari ta fashe da kuka.
Da sauri hajiya ta shiga tsakaninsu tace"haba alhaji taya zaka daka ta tata,ay yarinyace abi komai a sannu,in kace da zafi zaka bi komai baze haifar da ɗa me ido ba"ta ƙarasa maganar cikin sigar rarrashi.
Guri IG ya nema ya zauna,yana huci dan gaba ɗaya haushin Deeyanar yake ji kamar yay ta dukanta se ta dena motsi.
Jan hannunta hajiya tayi,da bazata bita ba amma tuno zafin hannun IG bata san lokacin data bi tan ba tana kuka.
Sashin yaran gidan takaita,dawowarsu daga makaranta kenan,suna ganin hajiyar kowa ya duƙa yana gaisheta,amsawa tayi cikin walwala,tacewa ƴar babbar wacce zasuyi saanni da Deeyanah "Munauwara ga sister ku nan ta gurin innarku ta kaita,maza ki sa tayi wanka ta kimtsa,taci abinci kamin in dawo".
Bata jira amsar su ba ta saki hannunta ta koma gun mijinta dan ta kwantar mai da hankali,dan ta fahimci acikin zafin rai yake.
Ruwa ta ɗebo masa me sanyi ta bashi yasha sannan tajashi zuwa ɗakinsa,ta taimaka masa ya rage kayan jikinsa,sannan taje toilet ta haɗa masa ruwan wanka ya shiga.
Kamin ya fito ta fito masa da kayan dazesa marasa nauyi,sannan ta kwaso abincinsa ta kawo ɗakin,yana fitowa taimaka masa tayi ya kimtsa,sannan ta zuba masa abincin yaci yasha ruwa ta kwashe kayan,sannan ta dawo.
Jikinshi taje ta kwanta,tace cikin taushin murya"Abban Deeyanah ina fatan de da yarda da amincewar inna kuka taho,dan naga tafiyar kamar ba shiri kuka yo ta?"ta ƙarasa maganar tana wasa da hannunsa.
Murmushin takaici yayi,sannan yace"maryamu bada izinin inna na taho da deeyana ba,"daga haka ya kwashe duk abinda ya wakana ya shaida mata.
Sosai tausayin mijin nata ya kamata wasu siraran hawaye suka shiga zubo mata cikin kuka tace "shekara da shekaru Abban deeyanah rashin jituwa kaida mahaifiyarka duk dan saboda ni,"da sauri ya rungumota jikinshi ya fara rarrashinta da kalamai masu daɗi.
Dena kukan tayi sannan tace"ayi gaggawar saka deeyanah makaranta,dan akwai duhu na jahilci a tattare da ita,sabida a samu ta natsu,duk wani sakarci dena shi zatayi in Allah ya yarda,"
"hajiya kiyi haƙuri da halayenta,ko kaɗan deeyanah bata da kunya,don Allah ki zama me juriya watarana ze zama labari"IG ya faɗi cikin sigar rarrashi.
Murmushi tayi sannan tace "uwace fa ni Alhaji,kadama wannan ya dameka insha Allahu zan jure har zuwa lokacin da zata fahimci gaskiya"cewar hajiya tana murmushi.
A can kaita kuwa,da Inna taga har laasar bata ga Deeyanah ba mayafinta ta ɗauka ta tafi neman ta hankali a tashe.
.Muje zuwa
Surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*SHIMFIƊAR AURENA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*free pages sun kusa ƙarewa,hanzarta ki mallaki naki 500 ne kacal ba tsada,domin ki shigo cikin tafiyar ayi dake,shimfiɗar aurena yasha bam bam da saura,shi ɗin na musamman ne*
*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*
*A turo shaidar biyan tanan 07044600044 ta acct kawai banda recharge card*
*9*
A zabure dukansu suka miƙe suna kallonta,dan sosai suka tsorata da ganin nata.
Baki na rawa hajiya maryam tace"sannu da zuwa inna"
Ay kamar jira inna take ta fara da cewa"munafuka baƙar daga me fasa taro,tauraruwa me wutsiya ganin ki ba alkhairi ba,kin tarwatsamin farincikina dana ahalina,"
IG ne ya matso kusa da Hajiya maryam yace mata cikin sigar rarrashi "go inside,please kiyi haƙuri"hawaye ke bin idonta amma seda tayi masa murmushin ƙarfafa guiwa sannan ta juya ta bar gurin.
"bariki alalen gero,wato habubakar ni ka maida ƴar iska sabida matarka,to wallahi ku da kwanciyar hankali se kun miƙomin jikata gareni,baku isa ba wallahi kunyi tsararo"
Tsugunawa yayi gabanta cikin damuwa da tsantsar takaici yace"inna kullum burinki shine kiga ina miki biyayya,sabida haihuwata da kikayi,amma ni fafur ƴata kin hana taga mutuncina ma bare har ayi tunanin zata soni wata rana,kinsa ta tsaneni bata ganin girmana,inna me nai miki ne da zafi har haka dayasa bakyason kwanciyar hankalina,nine fa Abubakar ɗinki ɗanki ɗaya tak a duniya,ba ƙya gudun ciwon damuwa ya kamani nima ki rasa ni shikenan kin huta"yayi maganar hawaye na biyo idonsa.
Sosai jikin Inna yayi matuƙar yin sanyi,jin kalamin na IG tabbas in ya mutu ko ta shiga uku,dan bata da sauran ɗan da zata nuna a mazaunin nata baya ga shi ɗin.
Hannunta IG ya kama ganin ta ɗanyi sanyin ya kaita kan kujera ta zauna batare da musun komai ba,ruwa ya kawo mata me sanyi,sannan ya je dinning ya haɗo mata abinci da zafinsa yasha kayan lambu da naman kaza yazo ya durƙusa agabanta,yasa cokalin ya ɗebo abincin ya nufi bakinta dashi,seda ta doka masa harara sannan ta amshi abincin,to dama in banda fitinar Inna ta ɗebo yunwa,dan haka sosai taci abincin da IG ya zubo matan,ruwa tasha tayi hamdala sannan tace "ina gudaliyata?"tayi tambayar kadaran kada han.
"inna deeyanah na lagos can na kaita karatu,kuma insha Allahu sun kusa samun hutu,da zaran ta dawo zaa kawo miki ita tai miki hutun acan"cewar IG cikin dabur dabur.
"lagos fa kace habubakar?kai ko wacce irin tsana ce kaiwa yarinyar nan daze sa ka kaita lagos makaranta?"inna ta faɗi cikin faɗa.
"kiyi haƙuri inna,ilimin can yafi nanan shiyasa na kaita ba ƙiyayya tsakani na da deeyanah har abada sabida ƴata ce kuma ina sonta,bazan taɓa yin abinda ze cutar da ita ba"cewar IG cikin biyayya.
"habubakar nifa ba kai ne bana so ba,matarka ce bana so ƙiriƙiri ta kashe Aisha amma ido da addini ka kasa miƙata ga mahukunta su kasheta itama, taya kake tunanin zan iya ganin farinta har in yarda jikata ta zauna agunta,to wallahi da sake"cewar inna cikin ɓacin rai.
"inna kinfi kowa sanin maryam ba ta kashe Aisha ba,hasalima taimakonta taje yi,tsautsayi da ƙarar kwana yasa Aisha ta rasu,to akan wanne dalili kikeso ki manna alhakin mutuwar Aisha akan maryam,inna kifa tuna zamu mutu muje ga Allah duk abinda muka tabbatar da bamu da yaƙini akansa abu mafi sauƙi mu watsar dashi dan wucewa lami lafiya"
Be ida me yakeson faɗiba yaji ta rushe masa da kuka,tana faɗin"habubakar nice nakewa matarka ƙarya da sharri ko,ni kasa agaba kana wulaƙantawa har haka,ba komai Habubakar na barwa maryam ɗin kai duniya da lahira tunda ta fini agurinka"
Cikin tsananin tashin hankali,ya zube a gabanta yana magiya kan ta janye furucinta na cewa ta barwa maryam shi,da ƙyar yashawo kanta ta haƙura ta janye.
Ɗakin saukar baƙi ya kaita da kanshi ya gyara mata gado da duk abinda zata buƙata sannan ya fito yajawo mata ƙofar.
Gaba ɗaya ya rasa meke masa daɗi,komai ya kulle masa yarasa ta ina ze fara. wannan wacce irin rayuwace.
*********;
Wata guda inna ta kwashe a Abuja zaman jiran dawowar deeyanah,ba irin wulaƙanci,ƙasƙanci da cin mutuncin dasu IG basu gani ba agun inna azaman nata a gidansu.
Ta hanasu saƙat acikin gida sede ko yaushe suna ɗaki,in ba gurin aykiba.dan motsin kirki sukayi agabanta se tace zaginta sukeyi,ko tace munafuncinta sukeyi.
Ana wannan bidirin ne Deeyanah ta iso daga lagos sakamakon hutun da aka musu.cike da mummunar manufa ta iso gidan na mahaifinta.
Ga mamakin inna rawar ƙafar da take tunanin deeyanah zatayi in ta ganta setaga batayiba,dan har wani shan ƙamshi takewa innar.
Hmmmm
Muje de zuwa
Surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*SHIMFIƊAR AURENA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*To jiya na kammala littafin TAYI MIN ƘANƘANTA,yanzu ga SHIMFIƊAR AURENA na kuɗine daban yake da sauran,kibiya 500 kisamu damar karantashi har ƙarshe,karki fara baki samu ƙarashen ba ki soni kiso littafina ki siya ki biya shine soyayya😄*
*Zahra muhammed Nasir 2084024749 UBA*
*07044600044 a turo shaidar biyan ta nan,ta acct kawai banda kati*
*7*
Inna yawo take lungu da saƙo na garin neman Deeyanah tun tana sa ran ganinta har ta soma fidda rai,zuwa yanzu kuka take wiwi,
Ta shawo kwanar lungun gidansu ta haɗu da Audu ɗaya daga cikin leburorin da aka ɗauki deeyanah agun su.ganin tana kuka ne yasa yace"Innar Deeyanah lafiya kike kuwa?"
Cikin kuka tace"Deeyanah ce tunda ta fita da tallah banganta ba,na nemeta har na gaji"ta ƙarasa maganar cikin matsanancin kuka.
"Deeyanah ay tun ɗazu wasu ƴansanda suka ɗauketa takai tallah gurinmu,sun tafi da ita a motocinsu masu jiniya"cewar Audu cikin yanayi na tausayawa.
Ay Inna bata jira yagama bayaninba ta juya da gudu ta nufi gun isa me waya tana faɗin"Shikenan gudaliyata Habubakar yakai min ke inda zaa kasheki kamar yadda aka kashe mahaifiyarki,wayyo ni fatima ina zansa rayuwata ba marainiyar Allah"a haka ta ƙaraso gun isan,jamaa se kallonta akeyi.
Isa na ganinta ya taso da saurinsa,yana faɗin "inna lafiya kuwa?"bata bashi amsa ba se cewa da tayi"ka kiramin yaron nan mara mutunci,nace ka kiramin habubakar yanzun nan"tace cikin ƙaraji.
Jikin Isa har rawa yake ya danna lambar baban Deeyanah.
IG na zaune a falo yaji ƙarar wayar daya ware domin inna,dama yasan zaayi hakan,dan haka cikin dauriya ya ɗaga wayar.
Isa na jin an ɗaga ya miƙa mata,ay yana bata ta fara da cewa.
"yau na tabbatar da cewa habubakar kai ba jini na bane,wato na hanaka tafiya da deeyanah shine kasaceta ka kaimin ita inda zaa kashe to wlh cikin daren nan ka kawomin ƴata"
"Inna kiyi haƙuri amma batu na gaskiya Deeyanah bazata dawo gunki ba sabida tsarin da kika ɗorata akai,in muka koma ga Allah ni zaa tuhuma game da amanarta da Allah ya bani,inna ina miki biyayya sede wannan karon Deeyanah ta dawo kenan kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki"yana kaiwa nan ya kashe wayar gaba ɗaya ya kwantar da kanshi jikin kujera yana tunanin mafita game da matsalar inna.
Inna ko jin ya kashe ne yasa ta shiga surfa masa zagi tana birgima agurin ita ala lalle dole se isa ya kaita Abuja.
da ƙyar isa ya rarrasheta yakaita gida,ranar kwana tayi tana kuka,inna uwani tayi rarrashin har ta gaji.
IG na kashe wayar miƙewa yayi ya nufi ɓangaren yaranshi,ayko suna ganinshi kowa ya taso yazo ya rungumeshi suna masa sannu da zuwa banda Deeyanah wacce tunda ya shigo take doka masa harara,gami da taɓe bakinta.
Zama yayi cikinsu yana sauraron kowa da damuwarsa,Abulkhairi ne yace "daddy waccan auntyn bata da kirki tun ɗazu take ta dukanmu"ya faɗi yana nuna deeyanah.
Ɗago ido IG yayi ya dubi Deeyanar data cika tana jiran ko ta kwana,murmushi yayi sannan yace "laifi kukai mata,shiyasa ta dokekun"
Taɓe baki tayi ta kauda kanta gefe.
Kallonta kawai IG yake,cikin nuna kulawa yace mata "mamanah ya baƙunci?"ya faɗi lokacin daya kamo hannunta.
Ƙoƙarin kwace hannun takeyi amma ta kasa,dan haka shuru tayi tana kallonshi,batare data amsa masa ba.
murmushi yayi yace"cikin satin nan zaki makaranta,ki samu ilimi dan ki koma gun innarki ki kula da ita"se alokacin tayi magana jin ya ambaci inna,"ni amaidani gunta banason makarantar,ay sabida rashin makarantar ne yasa ka tsani mamana har kuka kasheta dan ita bata da ilimin boko,to nima bana son makarantar"
Sosai batun ya taɓa zuciyarshi amma yasan deeyanah bata da laifi me laifin inna ce dan duk itace ta cusa mata ƙiyayyarshi a zuciyarta.
Be ce komai ba ya saki hannunta yabaro ɗakin yana saƙe saƙe a zuciyarshi.
Muje zuwa
************* Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.aihausanovels.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.
Email > aihausabooks@gmail.com
******* FOLLOW US ******
Facebook: Ai Hausa Novels
Twitter: Ai Hausa Novels
Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************
Surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*SHIMFIƊAR AURENA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*na kuɗine ki biya kan ki karanta,dan samun damar karance shi gaba ɗaya 500 ne kacal*
*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*
*A turo shaidar biyan tanan 07044600044*
*10*
Deeyanah wanka tayi taci abinci sannan ta dawo falo ta zauna tana girgiza ƙafa,tana cika da batsewa.
Inna ce ta shigo jikinta har ɓari yake taje kusa da ita ta zauna fuskarta ɗauke da murmushi,ta kamo hannun deeyanah tace"gudaliya ta kinga yadda kika ƙara yin kyau kuwa?"
Yatsina fuska deeyanah tayi sannan tace"ko?"
"Kwarai gudaliya shiyasa nakeso gobe muyi asubancin tafiya kaita,sabida nasan muna zuwa samari se sunyi kamar su cinyeki"inna ta faɗi tana washe baki.
"ku tafi ina,?ke da wa kuma?"deeyanah tayi tambayar tana ware ido.
"mu tafi kaita mana,ni da ke"inna ta faɗi tana dariya.
Wata shewa deeyanah tayi sannan ta miƙe ta fara juyawa agaban inna tana faɗin"haba inna yanzu ke ko dole aka miki kan ki tafi dani kaita kya fara,?kuma samari ay nafi ƙarfin na can sede na nan"ta faɗi tana wani kakkarya jiki.
Baki inna ta saki tana kallonta,da ƙyar ta iya cewa"nufinki ke bazaki koma can ba?"
"yauwa tunda kin fahimta,eh ni nazo kenan bazan koma ba,"deeyanah ta faɗi batare da damuwar komai ba.
Hawayene ke biyo idon inna,cikin kuka tace"yanzu ni zaki watsawa ƙasa a ido,deeyana,bafa