[12/5, 4:11 PM] Mom Islam: 💋💋💋
*SHA'AWA DA JARABA*
(Love and Romantic story)
💋💋💋
Mom Islam
Page 1-2
Gidane babba ƙerarre wanda ya kasance irin family house ɗinnan, kasancewar Akwai part part a cikin gidan,
Amma Babban parlor guda ɗaya ne, wanda yake part ɗin Alhaji Basheer, duka ragowar part ɗin sunada parlon sai dai madaidaita ne basu da girman na, Alhaji Basheer shine babba, Alhaji Mustapha kuma ya kasance ƙani gareshi, ubansu ɗaya sun taso cikin so da ƙaunar junansu, kasancewar su biyu Allah ya bawa iyayayensu, bayan rasuwar mahaifiyar Alhaji Mustapha, Alhaji Mustapha ya dawo gurin mahaifiyar Alhaji Basheer, kwatsam Allah ya yiwa mahaifinsu rasuwa, sakamakon haɗarin mota, dukkansu biyun sun koka sosai da rashin gatansu wato mahaifinsu, daga nan ragamar kula dasu ta koma gurin mahaifiyar Alhaji Basheer, Hajiya Sa'adatu ta kasance mace mai adalci da sanin ya kamata, hakan yasa bata banban tasu, batayiwa wannan abu bata yiwa wancan ba, sun samu kulawa da kuma tsaftatacciyar tarbiyya gami da sana'a mai inganci, dukkansu sana'arsu iri ɗaya ce, wato sunada gidajen bredi, irin na zamani wanda ake sarrafa breadi da na'ura.
Alhaji Basheer yanada mata ɗaya, Hajiya Zulaiha, shima Alhji Mustapha matarsa ɗaya Hajiya Mariya, dukkansu sunje ƙasa mai Tsarki bayan aurensu, kasancewar a rana ɗaya aka ɗaura musu aure.
Zaune suke a babban parlon dake part ɗin Alhaji Basheer, parlon ya kasance haɗaɗe mai ɗauke da mayan manyan Sofa farare masu taushi, acan gefe kuwa Dinning area ne wanda aka yane shi da labule mai shara-shara irin na zamani,