Showing 57001 words to 60000 words out of 120027 words

Chapter 20 - Halysaah Book 3 By Khaleesat Haydar

ko wani abu ne ya faru don nasan ki da banzan tunani, to babu abinda ya faru wallahi, kuma babu abinda zai taɓa faruwa cause we are not meant for each other, in ma zaki dena tunanin dake ranki ki dena, banda ma karen yasa na yar da makullin apartment dina a parlorn gidan kin zata zaki gan ni gidan nan ne, ba sai ma ya sake ganina a gidan zai yi attempting komai ba...." Safiyyah dai kawai tayi murmushi don tasan duk wannan nonsense din nata ya kusa zuwa karshe yau ko gobe, Ita dariya ma take bata, wai ba er cin amana bace ita, to amanar wa za a ci? Da ba don tasan Khaleesat na da ilimin addininta dai dai gwargwado ba da babu abinda zai sa bata yi tunanin ko dai islamiyya ne bata taɓa zuwa ba duk tsawon rayuwarta, wani lokacin in Khaleesat ta yi wata maganar sai tayi ta mamaki kamar warce ake controlling da battery don ko nazarin abinda zata furta bata yi, kanta tsaye take fadin duk abinda ya zo bakinta, wai ita ba er cin amana bace, Safiyyah ta taɓe baki tace "Samu kika yi, me yasa bakin ki wasn't this sharp for Abdul?? I wish zaki san value din da mijinki yake da shi wajen yan mata da yanda suke rubibinsa da burin mallakansa a matsayin miji da baki dinga shirmen nan ba, all because of Jawwad that is there enjoying his marriage...." Mikewa Khaleesat tayi ta shige bandaki ba tare da ta tsaya ta ci gaba da sauraronta ba. Har bayan la'asar Khaleesat na kwance dakin Safiyyah gaba daya mood dinta a dagule throughout, sai juye juye take yin kan gado, gashi har sannan her body was still weak from what happened in the morning, duk yanda ta so distracting brain dinta daga incident din hakan ya ci tura, don duk bayan mintuna kadan abinda ya faru sai ya fado mata a rai taji kamar it's happening at the moment, she still feels his hand gently moving round her chest, she still feels his rapid breathing on her chest, wani lokaci kuma taji kamar bakinsa na wuyanta don har sai ta kai hannu ta shafa wuyar jifa jifa, Safiyyah ta idar da sallah ta juya tana kallonta tace "Lokacin sallah fa ya wuce Madam" Khaleesat dai tayi shiru don ko magana taki yi da Safiyyah all through, a hankali ta sauka daga saman gadon ta nufi bandaki zata yi alwala Safiyyah ta bi ta da kallo, ta girgiza kai tana ɗan murmushi, dai dai nan wayarta ya fara ring, ta dau wayar ganin Ajay ne ta mike ta fita daga dakin, a parlor tayi picking call din nasa, maganar few seconds suka yi sannan ta fita can waje, gaban apartment dinsu ta gansa yayi parking yana jiranta, ta karasa har kusa da motar ya mika mata makullin hannunsa ta amsa sannan ya ja motarsa ya wuce. Sosai Khaleesat ta ji dadi bayan da Safiyyah ke sanar mata ai kamar akwai spare key din apartment dinta da Housemate ya taɓa bata da dadewa ta ajiye, Khaleesat tace "Don Allah kawo in ga ko shi ne, ko dai key din old apartment din mu ne" Safiyyah ta mike ta bude wani jakanta ta ciro makullin da Ajay ya kawo ta nuna ma Khaleesat tace "Duba ki ga, ban san ko na tsohon apartment din bane" Khaleesat ta wara ido ta amshi makullin tace "Ai kuwa na new apartment din ne wallahi, amma naji dadi sosai, let me just be going to my apartment dama na gaji" Safiyyah tace "To wayarki da kika baro can gidan fa?" Khaleesat ta hade rai tace "I don't want to talk about that" Safiyyah tace "To amma ki jira mu ci abinci don nasan ko kin koma ba abincin zaki ci ba" Daga haka Safiyyah ta fita daga dakin, ba a dau lokaci ba sai ga ta ta dawo da plate din shinkafa sai robobin drinks biyu, na zobo da wani me kamar kunun Aya, Safiyyah tace "Zan sha Zobon ke ki sha wannan" Khaleesat bata ce mata komai ba ta fara cin abincin a hankali duk da bata da appetite kwata kwata, kadan ta ci ta ajiye cokalin, zata dau ruwa ta sha Safiyyah tayi saurin cewa "To baki sha drink din ba ai" Khaleesat ta kalli robon drink din tace "Maman Aslam ce tayi?" Safiyyah tace "Eh mana, kin san lokacin tana Nigeria shi take siyarwa online, manyan mutane ke siyan natural drinks dinta, a nan ma ana saka order" Khaleesat ta bude ta sha kadan to feel the taste, can ta kalli Safiyyah tace "Kamar ba kunun Aya ba ai" Safiyyah tace "Mix nutritious kunun Aya ake ce masa, sai kin ci gaba da sha zaki ga ya ma fi kunun Aya dadi da gardi, shegen tsada fa garesa shi yasa na dauko daya kawai kar gobe ta kulle fridge dinta" Khaleesat ta ci gaba da sha don yana da zaƙi sosai, bayan ta sha ya wuce rabi ta ajiye sauran Safiyyah ta hade rai tace "To waye zai shanye wannan din da kika rage, salon ta kullaceni in taga na dau mata abu kuma bamu shanye ba" Khaleesat ta dau sauran ta shanye don bata son jaraban Sophie, bayan ta ajiye empty goran ta mike ta fara shirin tafiya Apartment dinta.... Tun da Khaleesat ta isa gida take kwance kan 3 seater a parlor tana jin jikinta duk a mace, weakness din da take ji har yafi wanda ta yini take ji yau, ta ma rasa gane yanayin da take ji a jikinta, kan kace me ta dawo kamar mara lafiya, wajen karfe bakwai da rabi ta mike zaune da kyar a ranta tana addu'an Allah ya sa akwai pad a gidan cause she is expecting her period is here, tashi tayi tana tafiya a hankali ta wuce sama zuwa dakinta, ta ciro pack din pad a cikin kayanta ta dau daya ta shiga bandaki, after taking her bath ta dauro alwala ta fito ta saka doguwar riga ta dau Hijab dinta a cikin press sannan ta shimfida darduma ta tada sallah, tana idarwa ta kwanta kan darduman ta lumshe ido. Washegari haka Khaleesat ta yini a sama tana bacci don daren jiya bata wani yi bacci isasshe ba, da yamma bayan tayi wanka tayi sallan La'asar tana kitchen tana dafa tea taji kamar an bude kofar apartment dinta, sosai gabanta ya fadi ta juya da sauri tana kallon kofar kitchen din duk da ba ganin wanda ya shigo parlon zata yi ba, a hankali ta kashe gas ta koma gefe ta tsaya taki fita daga kitchen din duk da hijab din da tayi sallah ne jikinta har sannan, tana ta tsaye har na minti goma daga karshe ta dake ta leka parlon, yana zaune kan kujera ya saka face cap idonsa sanye da Black glasses yayi keeping serious face, sosai taji gabanta ya fadi ta koma kitchen din da sauri ta jingina da cabinet kamar zata yi kuka, har cikin ranta taji tana tsoronsa kuma yanxu, ta kara tsayuwan wani minti biyar a kitchen din kafin tayi karfin halin fitowa ko ta kan shayinta bata bi ba don har taji shayin ya fita ranta, ko da wasa bata yarda ta kalli inda yake zaune ba kanta a kasa ta nufi stairs tana tafiya a hankali zuciyarta na bugawa, ya bi ta da kallon gefen ido ta cikin Glasses dinsa ba tare da ya juya kansa ba, sai da yaga zata haura stairs yace "Kee" Cak ta tsaya jin serious tone din da yayi using, sai kuma ta juya kamar munafuka ta ɗan kallesa, lokaci daya tayi saurin sunkuyar da kanta tana wasa da hijab din jikinta, duk da ba ganin idonsa take ba amma wani irin kunya taji take ji, after some seconds ya mike ya nuna mata kofar fita apartment din calmly yace "Mu je" Bata san sanda ta sake kallonsa da sauri ba gabanta na faduwa, sai kuma ta marairaice kamar zata yi kuka tace "Ni dai wallahi nafi son apartment din nan don Allah kayi hakuri ka bar ni pls, we are starting exams upper week ina son in dinga karatuna quietly a nan, nafi gane karatun a gidan nan" Ya hade rai yace "Fita mu je na ce" Hawayen dake makale idonta suka zubo, cikin rawan murya tace "Don Allah kayi hakuri ka bar ni...." Tsorata tayi saboda tsawan da ya daka mata ya nuna mata kofar fita daga apartment din, bata sake masa musu ba tana goge hawayen idonta jikinta na rawa ta nufi kofar fita daga apartment din ya bi bayanta, har suka koma can gidan hawaye take, sosai hankalinta ke a tashe and she felt just like she is with a total stranger, a hankali take haurawa sama tana goge hawayen da yaki tsaya mata bayan sun shiga gidan, tana jin yana biye da ita a baya amma taki yarda ta juya saboda tsoro, zata shiga dakin da take zama taji muryarsa yace "Walk straight" Sai a sannan ta juya ta kallesa, har lokacin yaki cire glasses din idonsa da face cap kuma kallonta yake directly in the eyes baya ko kiftawa, kamar ta sani ta sunkuyar da kanta, Calmly yace "Ba ki jin turanci ne?" Juyawa tayi ta ci gaba da tafiya a hankali walking down the corridor kamar yanda yace, kawai taga ya wuce ta, sannan yayi knocking kofar wani daki yayi sallama, after few seconds ya cire face cap dinsa da glasses din idonsa ba tare da ya bari su hada ido da Khaleesat ba ya bude kofar ya shiga ciki leaving the door open, Khaleesat: da gabanta ke ta faduwa wondering who was inside the room ta ɗan leka cikin dakin before going in, wani ƙara tayi tana zaro ido with surprise ganin Aunty Farida zaune cikin dakin, bata san sanda ta nufeta da gudu ba ta tafi ta fada kanta ta kankameta.
********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

WhatsApp Number: 09017242889


Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************
HALYSAAH PAGE 127

Tsabar farin ciki Khaleesat kawai fashewa tayi da kuka don bata taɓa zaton ganin Aunty Farida a Maryland ba, she thought she was dreaming, ta kara rungumeta muryarta na rawa tace "Wayyo Aunty baki gaya min zaki zo ba ai" Aunty Farida ta ɗan yi murmushi tace "Ai na zata Junaid ya gaya maki" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba tana hawayen farin cikin ganin kanwar Ummanta, tuni Ajay ya fita ya bar dakin, Aunty Farida na kallonta tace "Ya karatun?" A hankali Khaleesat tace "Alhamdulillah, za mu fara jarabawa sati na sama in sha Allah Aunty" Aunty Farida tace "Maa sha Allah, Allah Ubangiji ya baku nasara" Cike da shagwaba Khaleesat tace "Aunty ina Ummata da Baba har da Nenne?" Aunty Farida tace "Duk suna gaishe ki" Khaleesat ta gyara zama tace "Amma yaushe kika zo? Yau ko jiya? Kuma naga you look dull, ko dai gajiyan hanya ne?" Aunty Farida tace "Daxu da rana ya dauko ni Airport, dama dolw akwai gajiya mana...." Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya a hankali tace "Aunty naji dadin ganin ki sosai" Aunty Farida na kallonta tace "Bakya cin abinci ne kika rame" Khaleesat ta marairaice tace "Karatun final exams fa muke yi" Aunty Farida tace "Haka ne, Allah ya baku Sa'a" Sosai taga Khaleesat ta kara kyau, fatar ta sai wani sheki yake amma kuma ta rame, abincin da Ajay ya siyo ma Aunty Farida ta dau daya a ciki ta fara ci, don abinci kala hudu yayi ordering mata daban daban, Aunty Farida dai sai bin ta da kallo take, har aka yi magrib Khaleesat taki barin dakin sai labari take yi ma Aunty Farida, she look so excited don ma dai taga Aunty Farida kamar bata son magana don sama sama take amsa ta, kawai tayi tunanin saboda gajiyan hanya ne, dakinta ta tafi zata dauko extra darduma ta kai dakin da Aunty Farida ta sauka, tana shiga dakin taga wayarta saman gado a ajiye, daukar wayar tayi tana turo baki ta duba ko ya fashe taga ba abinda yayi, number Safiyyah tayi dialing babu bata lokaci ta ɗaga, cike da murna Khaleesat ke sanar mata da zuwan Aunty Farida, duk da Safiyyah ta san Aunty Farida na hanya dama amma tayi pretending tace "Ke haba dai? Da gaske Aunty Farida ta zo??" cike da murna Khaleesat tace "Wallahi in gaya maki" Safiyyah tace "Ai ko gobe da safe ina nan zuwa gidan, Aunty Farida a Maryland?? Lallai mun yi babban bakuwa, zan mata girki kuwa in taho mata da shi gobe" Khaleesat na murmushi tace "To sai kin zo goben, ki zo da wuri plss" Safiyyah tace "In sha Allahu kuwa" A haka Khaleesat ta katse wayar ta fita daga dakin tana rike da darduma, ido hudu suka yi da Ajay ya taho daga part dinsa, ta hade rai ta wani cinno baki kamar ba ita ke murmushi ba ta juya tayi tafiyarta dakin da Aunty Farida take, ya bi ta da kallo. Karfe tara da rabi na dare Aunty Farida ta kalli Khaleesat dake zaune kusa da ita tana danna wayarta tace "Ki tashi ki tafi sai da safe, ni kwanciya zan yi" Khaleesat ta ajiye wayar hannunta tana kallonta da mamaki tace "Aunty in tafi kuma, nan zan kwana ai muyi hira" Aunty Farida ta hade rai tace "Hiran uban me za ki min?" Ganin babu wasa tattare da ita yasa Khaleesat ta mike a sanyaye tayi mata sai da safe tana tafiya a hankali ta nufi kofa ta fita daga dakin, hawaye taji ya cika idonta, tun zuwan Aunty Farida taga ta ki sake mata fuska har tana tunanin ko duk gajiyar hanya ce, magana ma sama sama kawai take yi mata, haka nan Khaleesat ta koma dakinta cikin sanyin jiki ta kwanta tayi lamo kan pillow. Washegari da asuba Khaleesat ta shiga gaida Aunty Farida, Aunty Farida ta amsa gaisuwarta, Khaleesat na wasa da hijab din jikinta tace "Ya gajiyan hanya Aunty?" Aunty Farida tace "Lafiya lau" Kwanciya Aunty Farida tayi don dama zaune take saman darduma tana azkar, after some minutes Khaleesat ta mike a hankali ta fita daga dakin ta koma dakinta, zaunawa tayi gefen gado ta fara tunanin to ko dai Ajay yace mata tayi masa wani abu ne bayan babu abinda ta taɓa masa tunda take, hawaye ya cika idonta ta kwanta gefen gado tana goge hawayen, bata koma bacci ba har karfe takwas sannan ta shiga bandaki tayi wanka ta fito ta shirya ta dau hularta ta saka sannan ta sauka downstairs zata shiga kitchen ta dora breakfast, zaune ta tarar da Ajay da Aunty Farida a parlor suna hira, tana hada ido da shi ta wani hararesa fuska daure ta wuce kitchen, shi dai ya ci gaba da maganar da yake yi da Aunty Farida, har aka yi azahar Aunty Farida bata yi wani hira da Khaleesat ba sai ma voice note da take tayi da Umma suna hira, duk jikin Khaleesat yayi sanyi don har ta gama concluding akwai abinda Ajay ya gaya mata, wani azababben haushinsa ta dinga ji a ranta, tana kitchen tana duba abincin da ta dora wajen karfe biyu Safiyyah ta shigo kitchen din da warmers din abinci a hannunta tana washe baki tace "Su Khaleesat yau a kitchen ga kamshi duk ya cika gidan nan, sai fa Aunty Farida tayi zaton cikin lumana ku ke zaune gidan nan ke da Ajay, sai kace girki kika saba yi a gidan" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba ta amshi warmer din hannunta daya ta ajiye, Safiyyah na kallonta ganin mood dinta tace "Lafiya? Ya na gan ki haka? Me ya faru" Cikin rawan murya Khaleesat tace "Wallahi ban taɓa ganin devil kamar mutumin nan ba Sophie, gashi nan ban san me da me yaje ya gaya ma Aunty Farida ba don tun da ta zo taki sake min fuska alhalin shi tana ta hira da shi, ni kuwa da kyar take amsa min magana idan nayi mata, shi bayan iskanci har da gulma dama ya iya ban sani ba" Safiyyah ta bude baki tace "Kai haba? To ke baki tambayeta me yasa take amsa ki haka ba?" Khaleesat ta fashe da kuka tace "Wallahi taki kula ni mu yi hira tun jiya, alhalin shi sosai take magana da shi har da dariya, wallahi nasan sharri kawai ya laka min a wajenta, dama manipulator ne shi ban sani ba ashe" Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace "Amma anya kuwa Ajay na da wannan lokacin Khaleesat, yaushe zai je yace masu ai kin hanasa hakkinsa?" Khaleesat ta mata wani kallo ta tsuke fuska, Safiyyah ta rufe bakinta da hannunta da sauri tace "Au, to... cewa zan yi yaushe zai ce masu baku zaune lafiya bayan magana ma sai ya ga dama yake ma mutum, kema kin san ba shi da wannan lokacin sai dai ki masa sharri, mutumin da ko magana ma sai ya so yake yi, ni dai bari in je in sameta, Allah ya sa kar laifin ki ya shafeni, bari in tafi mata da shinkafar sai ki taho da miyan" Daga haka Safiyyah ta fita daga kitchen din sai kuma ta dawo da sauri tace "Dakin ki ta sauka?" Khaleesat ta goge hawayen dake makale idonta ta girgiza mata kai sannan ta mata describing dakin da Aunty Farida ta sauka, Safiyyah ta fita daga kitchen din ta wuce sama, a stairs suka hadu da Ajay ta gaishesa ya amsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login