Showing 12001 words to 15000 words out of 22155 words
Chapter 5 - Mata Maza Book 1 Complete Hausa Novel Document
kan wani vidéo da baka ganin komai sai duhu tsaki yayi ya kashe wayar ya kwanta agurin Yana tunani, sai Kuma yace" kardai wannan video din shine ,mutumin da be yadda asan sunansa bama shi zai yarda aga fuskarsa"? Tabbas ko shine ,Mike wa zaune yayi har gumi yake faman hadawa wajan kunna data hannunsa kuwa harrawa yake wajen danna video, kunnawa yayi yaji anfara magana Amma Bata ganin komai sai duhu " ASSALAMUALAIKUM" INAYIWA YAN,UWANA MAZA DA MATA BARKANKU DA ZUWA WANNAN TARO ME ALBARKA ,WADA ADUK SHEKARA NASABA HALARTARSA AKASA ME TSARKI WATO SAUDIYA, TO DA FARKO DAI SUNANA *AREEYAAN NOOR MUTALLAF* WANDA AKAFI SANI DA BOSS MAN WASU KUMA DAYAWA SUNA KIRANA DA LION KO AY.... Ay tun da AREEF yaji wannan sunan nasa na asali ya tabbatar da shine wan da yake nema yasa ya katse video din tare da ajiye wayar a gefe ya durkusa yayi sujjada Yana Mai yiwa Allah godiya da ya nunamasa wannan Rana. Mikewa yayi ya dauki number da hajiya Fateema ta turamasa yashiga rubuta message kamar Haka.
"ASSALAMUALAIKUM" inamaka barka da wannan lokacin sannan Ina maka fatan alkairi,nine dai AREEF Wanda akullum yake cikin nemanka Kuma bana gajiya da nemanka harsai ka fuskanceni ,doctor AREEYAAN wow suna me dadi inafatan kamar yadda kake da wannan sunan yasa ganinkama yaxamemin me kyau , ok nafatan kataimakeni kataimaki kanwata domin kayi mata ayki nagode ".
Daga Haka AREEF ya tura message din.
Cikin minti 2 yaji Kira ya shigo wayarsa ,Yana dubawa wazai gani doctor...... Bakinsa da jikinsa har rawa suke wajan daukar wayar yace "alhamdulillah Allah nagode maka Ashe dama' zanga wanan ranar "hello doctor AREEYAAN!!!!.
_______ "hello doctor AREEYAAN ,kana jina?" Daga can bangaren wani saurayine kekkewa dauke da tell phone a hannunsa ,ka dakaga wanna saurayin kaga asalin cikkakken balaraben usul ,bakinsa ya fara motawa Yana cewa " ba Yaya AREEYAAN bane AYAAN ne "
"To kenan Ina doctor din?" Yanzu Ina kokarin hadaka dashine abin da yasa nakiraka banason kace an wulakanta ka ko mu barka da jira shiyasa nakiraka don n'a fadamaka yayana Yana amsa wayane ta umarceni da nafada maka kabashi nan da minti 5 zai kiraka da asalin number sa" murmushi AREEF yayi yace" oky Tom Babu damuwa Bari zanjira shi" okay AYAAN ya kashe wayar kitt.
"Nafara yadda da abinda hajiya Fateema ta fadamin akan doctor ,yanzu shi Dan zaiyi wani uzurin sai yasa ankirani an bani hakuri Sabi da Kar ya batamin lokaci " ikon Allah ya saka hannunsa a kumatun da Yana zabga murmushi shikadai, jiyayi kamar muryar AFNAN tana cewa" Yaya murmushi me kake"? Dagowa yayi da sauri Dan ya tabbatar itace tayi maganar ,ayko ita dince Dan Haka ya karasa kusa da ita yace "AFNAN kin tashi ?" Sannu ko yajikin naki meyake damunki, ko kina bukatar wani abune?" Lokaci daya ya gigice Yana jefo Maya tambayoyi, wash Yaya dagani inason na maka magana " tom shikkenan kanwaty" ya karasa maganar tare da dagota zuwa jikinsa, "inajinki AFNAN" aziyar zuciya ta sauke tare da saka idanuwanta anashi Tace" Yaya AREEF kayafemin Dan Allah" nayafe Miki Kuna mekikai min!!? "Yaya nakasa jurewa ne shiyasa har takaini da saka hannu a gabana Dan Allah kada kace zakayi fishi Dani" uhm kanwata kenan ayni bana fishi dake Koda nayi ma bazan iya jurewa ba Dole sai na sakko, yanxu dai ba wanan ba albishirinka"? Goro!! Fari ko jaa?" Fari fat Yaya" to nasamu nasarar samun doctor a waya Kuma ma yamin alkawarin Nan da minti biyar zai kirani" hmm. Yaya Allah natsani doctor dinan "? Meyasa AFNAN shine fa Wanda zai taimakeki kisamu lafiya" Yaya Sabi da Yana wahalar min dakai natsani mutum irinsa Allah Yaya natsanesa" Kuma ay Naga lafiya ubangiji ne ke bayarwa ba shiba allah da ta halicceni da wanan abin shiyasan meyake nufi dani kuma shiyake son ganina a Haka, dan Haka koda ace zai min aykinann Banaso nafison nayi zamana a Haka narayu tare dakai cikin farinciki iya soyayyar dakake nunamin ta isheni yayaemin damuwa ta " ta karasa maganar hawaye na bin kuncinta" a,a AFNAN kada kiyanke hukunci cikin fishi Kuma ba acewa antsani mutum sai dai kice kin tsani halinsa, Kuma mu basanin asalin halinsa mukaiba balls har mumasa kallon mutum me wulakanta Dan Adam, AFNAN indai har kina Sona Kuma kin yarda Ni AREEF na Isa dake ki Bari ayi Miki aykinnan" runtse ido tayi ta bude Sana Tace" Yaya duk abin da kakeso Nima inaso Babu damuwa indai kanaso na amince ayimin aykin indai haka shine yafi alkairi arayuwar mu Baki daya"wow kanwata Daman Haka kika iya magana me dadi " Masha Allah Allah yayi Miki albarka"ameen Yaya na "ta Kara rungumesa tsam a jikinta.
*LONDON*
Babban gidan da yakasance daya daga cikin gidajen doctor na kasashe dadama tsayawa tsara kyau da ado da daula irin nagidan Bata bakine, Kai tsaye wannan saurayin Naga ya nufi wata kofa wadda take daga hannun dama' afalon wadda takasance itace kofa ta goma Sha biyu a gurin, shiga yayi dauke da sallama abakinsa ,saikuma yayi shiru can najiyo wata tausasassiyar murya daga ciki ance" yes" cikin nutsuwa ya tura kofar yashiga ciki, Baki nabude tare da sakin yawu kukukut tsabar haduwar dakin da tsaruwar sa dafarko idan kashiga dakin zaka tarasa yar madaidaiciyar loka a gefe wadda Tasha ado da kayan alatu na duniya, sai Gaba Kuma akwai gado Dan karami Wanda befi kwanciyar mutum daya ba ,Amma saidai kana hawansa saikasan ka hau gado ba muna gadoba ,wannan katifar ta kan gadon Kana hawa zakaji kamar a kan audiga kake tsabar laushi ,gefe guda Kuma covar ce itama karama me dauke da murfi biyu ,gaba kidaya jikinta kelkeline n'a gwaldin color, can gefe Kuma kujerace itace wadda na hango mutumin a zaune akai nai daga bayan sa yadda nagansa Zan iya fasal tamuku yanayinsa ,dogone sosai a Haka sai dai Yana da kauri ta sama ma,ana kirjinsa Yana da Fadi,duk da gashin kansa da na ga ya lullube Gaba daya kafadarsa da fuskarsa bana iya tantance wane irin mutum ne, karasawa AYAAN yayi yace" barka da safiya yaya" Kai kawai ta daga masa batare da ta juyo KO yayi magana ba , magana AYAAN yasake yi yace" yaya Yashirya fa ,yakamata ka taimakesa gaba kidaya angama tantancesa yacancanci a karbi aykinsa" kada kamanta Yana jiran kiranka ayanzu" Kai yakara dagamasa ta cigaba da abin da yake still dai be juyo ba ,Juyawa kaninnasa yayi ya fita tare da danna wani abu sai kofar dakin ta rufe.
Lokacin da yafito falon Ajiyar zuciya yayi yace" hooo yayana kenan "wanan mutumin saï a hankali narasa irinsa" daga Haka ya fice daga falon yashiga daya daga cikin kofofin dake falon.
Kilillllll wayar AREEF tashiga ruri, AFNAN ya rungume a jikinsa ya dakko wayar ya ga bakuwar number ,cikin sauri ya daga tare da karawa a kunnensa yace" assalamualaikum" daga can bangaren naji ance" Amin wa, alaikumussalam warahamatullahi"!! Zumbur AREEF ya Mike daga Dan kishin gidar dayayi atsorace harsai da ya tsorata AFNAN besan dan da bakinsa ta kubuce yace "wowwww wanna murya Haka macece ko namiji"? Yaya lafiya ban fahimce kaba me ya tsorata ka Haka" shiru yayi mata tare da saurin katse wayar yace " AFNAN wata daddadar murya naji wadda Tun da nake ko a mace banta ba jin irinta ba" Allah na tsorata"? Kay Yaya tsoro Kuma kirawo muji" kafin takarasa rufe Baki aka sake Kiran sa, hannunsa Har rawa yake wajen cewa hell.... Katseshi yayi dacewa" kana magana da doctor AREEYAAN" zaro Ido AREEF yayi yace" nashiga uku AFNAN kinajin abin da nakeji kuwa"? Yaya inaji Wallahi muryarsa dadadi Anya kuwa mutumne wanan kodan yaga munneman doctor ne yasa mukayi gamo da aljani" Tsaki AREEYAAN yayi ya katse wayar " tare da kirawo AYAAN, duk da bansan abin da yace masaba Amma Naga dai ya bashi waya ya Yi Kira , dagawa AREEF yayi yace Hello doctor?" AYAAN ne yace" bawan Allah kudaina zuzuta ko da daya daga halittar yayana, bayaso "to yanzu kunji muryarsa ma kun gigice ballantana ma kugansa?" Sorry walalhi mun tsoratane" okay to yanzu zai Kara Kira idan yakirawo kuyi Masa bayani kawai ,kada Wanda ya Kara santin muryarsa" daga Haka AYAAN yakatse wayar.
* Tun da AREEF yafita ya bar asbitin AFNAN kefaman kuka har tagaji, jitayi kanta yana juyawa kamar zai cire Dan Haka ta samu ta kawanta takalli sama tana tunanin AREEF ko zai dawo ko bazai dawoba.
_____kamal dake gefan wata mota Yana kallon yadda AREEF da iyayensa suka shiga motar har su ka bar asbiti, tsaki yayi yace "metseeeeew oh my God bansoba" daya daga cikin yaransane ya kallesa yace "oga ban gane bakaso ba?" Hmm bazaku gane ba naso ace iya AREEF ne kawai yake cikin motar banso iayayen da suka Shiga ba ,naso ace sai da tafara jin zafin mutuwar AREEF kamafi taji ta iyayenta Sabi da abubuwan zasu mata yawa karamar yarinyace kanta bazai dauki wannan abin ba" "Kash Wai dama' oga Sabi da wanan abin kake tsakai tab mu ay gwara duk su mutudin Dan wallahi har nagama lissafin abin da zanyi da dukiyar yarinyar Nan ,"mahaukaci kawai bazaka gane ba to yanzu da suka Shiga motar idan suka mutu Gaba daya uban sa Zai bani auren AFNAN kasan dai Dole sai ta amince Zan aureta Kuma kaga idan ban aureta ba bamu da yadda zamuyi mu samu dukiyar AREEF da iayyaenta da ita kanta AFNAN d'in" nasan idan da suna rayé zasu iya bani aurenta ko tanaso ko bataso Sabi da atunanin su Zan iya maye mata gurbin AREEF Tun da Ni abokinsane na kut da kut" "Dan Allah oga kabasar kawai indai sananne ko makota ay zasu iya daurawa kaidai kawai ka kwantar da hankalinka Tun da aykin Gama yaruga da yagama" " walalhi danasani nake nabi San zuciyata na kashe babban abokina Wanda ya nunamin kaunar da Babu wan da yata ba nunamin ita " mtseeeew mekake nufi ?"mukenan bama sonka kome?" "Hmm AREEF na da bannne idan da za a Tara mutane da yawa aduniyarnan be zama lallai asamu kwarra guda biyu masu kyewawan halaye kamar na AREEF ba" tom shikkenan kazauna jimamai har azo a kamamu Dan wallahi Ni tafiya zanyi ato" a,a kada katafi kabari idan mukaji sakon mutuwarsu sai mutafi ko "okay suka samu guri suka zauna suna jiran tsammani.
*LONDON*
AREEYAAN dake kwance acikin bargonsa me laushi ga tausi da tsada sai faman zuba kamshi yake a kance a kan lallausan bed dinsa, bazaki taba cewa da mutum acikiba Sabi da yadda gadon ya lotsa tsabar laushi gashi bargon da ya lulluba dashi hatta fuskarsa sai da ya rufe Baki iya ganin ko da hannunsa, daga cikin bargon ya furta " yasalam " ya runtse idanuwansa tare dacewa" so beautiful girl" murmushin gefan fuska kawai yayi ya dauki wayarsa tare da futa daga what's app din yashiga Kiran number AREEF.
AREEF Yana zaune acikin motar cikin tunani da fargaba yake tukin ,jiyayi wayarsa tana Kara Nan take ya fara kokari tsayawa domin ya daga Amma Ina motar taki ta tsaya neman kwacewa ma sitiyarin motar yake daga hannunsa, Babu yadda ya iya Dan Haka ta rike sitiyarin motar da hannu daya daya hannun Kuma ya zaro wayarsa ,number doctor AREEYAAN ce,dan murmushi yayi ya daga tare da mikawa Sadiq yace" saddiqu maza karamin wayarnan a kunnena" karba yayi ya karamasa ita ,sallama AREEF yayi yace " Assalamualaikum" wa, alaikumussalam warahamatullahi"barka da wanna lokacin doctor Ina fatan kaga sakona ko" eh nagani insha Allah Nan da jibi Zan sauka a *KOGI LAKWAJA* domin mutaho tare da ku sai ayi aykin" okay to doctor nawaye kudin kenan"?uhm karka damu abokina duk Wanda yakasance Yana da irinwanan halittar kyauta nake Masa ayki domin shi kansa abin tausayine ita KANTA yarinyar yadda na fahimta akwai matsalar Sha,awa guda biyu data Hadar mata, ga ta pussy ga ta dick" eh doctor Haka..... Ay Bay karasa fadar abin da zaice ba sai jiyayi an daki gefan motar sa, cikin hanzari ya saki wayar Sadiq yace" Yaya kakula babbar motace fa mutsaya Yaya tana Dada tun karomufa"innalillahi wa'inna ilaihirraju un" momy motar da Taki tsayawa wallahi anyanke Birkin motar munshiga uku" innalillahi wa'inna ilaihirraju un momy ta furta tare da cewa" shikkenan motamu takare innalillahi AFNAN yanzu yazamuyi da ita kenan mukadai gareta dan Allah kowaye me babbar motanan ta dakata mana" kokari. Tsaida motar AREEF yake Amma BABBAR motar Kara tun karosu take har tazo daf da su, sai jikukai gorafffffffff mutar ta tashi sama ta fado tawani irin juyawa ta hantsulo kasa tayi ragaraga, innalillahi wa'inna ilaihirraju un AREEF ya furta tare da cewa" lailaha,illah Muhammadur rasulillah daganan besake ko Ina daga hannunsa ba sukuwa su Abba da momy ko motsi basayi ,zaitun kuwa wanan glass din motar ne ta caketa,SADIQ da UMAR kuwa sun Dade da cikawa tun juyawar da motar tayi na farko, wayar da take hannunsu kuwa tsalle tayi tafada kasa can gefe, haryanzu kiranda AREEYAAN yayi bai katse ba ,domin dukkan abin da yafaru acikin kunnensa ta faru.
Zumbur yayi ya Mike daga kan bed din yawani baza gashinsa zuwa baya ,ware blue eyes din sa yayi gaba daya fararen idanuwansa masu kama da me bacci suka kada sukayi jajur ,kananun labbanta dasuke ja kamar yasaka jambaki ya taune yace " innalillahi wa'inna ilaihirraju un" innalillahi wa'inna ilaihirraju un" AYAAN ?" Dasauri ya durgo daga kangado bakinsa harrrawa yake hakama jikinsa tsuma yeke daga shi sai gajeran wando Wanda ya bayyana murdadden jikinsa, cover dinsa ya bude ya dauki jallabiyar sa baka yasaka .ya futa falo aguje, AYAAN" AYAAN" AYAAN?"dasauri AYAAN dake kwance adaki ya fito yace" Yaya lafiya?" "Inafa lafiya AYAAN ayanzunan ashiryamin jirgi tafiya zanyi" zaro Ido AYAAN yayi yace" jirgifa Yaya inazaka"? yamma tayifa.
"Akwai matsala AYAAN bansan dogon bayani kakiramin *SAJEN AMEER* banason kakara cewa komai Akan Haka kayi abun da nace" to Amma Yaya jallabiya cefa ajikinka" katsaya abi abin a nurse" short up"ya dakamasa tsawa tare da zazzare Masa Ido yayi Masa wani kallo wan da sai da cikin AYAAN ya kada, sumsum AYAAN ya fuce zuwa harabar gidan , wani part din ya nufa Kar tsaye cikin wani daki yashiga da sallama dauke abakinsa yace" assalamualaikum" daga canciki aka amsa Masa tare da basa izinin shigowa, Shiga yayi tare da kallon mutumin dake zaune Yana rubutu a takarda, karasawa yayi inda yake yace" barka da yamma AMEER" barka dai AYAAN lafiya kuwa da yamma nan?" Lafiya ba lafiya ba yau dai Naga abin da ya tsoratani" meyake faruwa" Yaya be yace ashirya masa jirgi yan zunan "jirgi Kuma Ina zaije" hmm ay Ni abin yafi karfina fadan da yafi karfinka ay sai kamai dashi Wasa Danni banta banin Yaya a furgice irin yauba"tom shikkenan AYAAN jeka ganinan zuwa. Yakarasa maganar Yana juya yafita
*KOGI LAKWAJA*
Tun da motar tasu takifa ,mutanen dake kusa da gurin suka karaso domin kawo musu dauki, Nan danan gurin yacika fal da mutane ,Abu kamar Wasa "yan jarida da "yansanda sun iso Nan take akashiga zarosu daya bayan daya dai dai lokacin da motar asbiti ta karaso, cikin sauri likitocin suka shiga dubasu Amma Ina kowanne daga cikinsu Babu Rai, Kamal kuwa dashi da sauran abokanan da tuni sun hallara agurin ,run the Ido Kamal yayi ya hankade kowa tare da tsugunawa a gaban gawar AREEF Yana kuka Yana cewa "innalillahi wa'inna ilaihirraju un yanzu wane' Mara imanine ya aykata muku Haka" wane laifi kukai musu, wayyo Allah na munshiga uku yanzu kenan AFNAN ce kadai tarage kuka yake har da majinar munafurci Yana jijigashi, hakuri Aka Shiga bashi ana ta tausar zuciyarsa ,masu hotuna da vidéo kuwa saï faman yi ake ana ta dorawa a Jafar sada zumunta ,wasu kuma gidan redio wasu t.v nan take mutuwar italan alhaji ABDULLAHI da dan sa millions A.R ta zagaya ko Ina.
Doctor na zaune a office dinsa Yana kallon wata Tasha yaga an dauke an Nuno accident din da su AREEF sukayi, Abu kamar bazata mikewa yayi cikin hanzari ya zame glass din sake idonsa ya kurawa gawawwakin Ido tabbas Babu makawa sune ,to Amma Ina AFNAN?" Zaro Ido yayi yace" kardai ace t.v dake dakinta a kunne take an shiga uku"ya kwasa a guje zuwa dakin datake kwance ,dadai lokacin da ta Kai kansa zai Shiga lokacin AFNAN takawo Kai zata fito tana faman rusa ihu, kanta ko dankwali Babu ruwan ma fincikewa tayi ta fito, daga ita sai jallabiyar AREEF dake jikinta ,rukota likitan yayi Yana cewa"lafiya kitsaya AFNAN kada ki fita ,yanzu bakya cikin hayyacikin" kacikani doctor kabarni ,yazakacemin na dakata bayan ga ahalinacan akwance Ina gani, wallahi koka cikani ko ayanzu namaka ihun kwarto" eh naji koma mezakice Amma ki dakata mutafi tare" "Baki tabude zatayi magana numfashin ta yashiga yin sama sama daker ta iya cewa" likita canciiiiiiii".... Dakata AFNAN yayi saurin sakinta ta watsa a guje, duk inda ta huce a asbitin kallonta ake wasu kuma su gudu sun zata mahaukaciya ce, gudu take zubawa akan titi duk motar da tataho sai dai ta kwauce mata badai ita tamatsa ba Dan Takoma bataji Bata gani da alamun tafara zarewa, inda taga mutane jingim da yansanda Nan gurin ta karasa aguje, tana zuwa ta hankade kowa ta huce, an zagaye gurin yadda Babu Wanda zaije Amma ita tusa Kai kawai take, dasauri dansan Dan ya rikota Yana cewa" yarinya lafiya kuwa"? Banza tamasa itadai Babu abin da take cewa sai" nashiga uku na lalace shikkenan narasa duk wani gata ,yau Babu momy Babu Yaya AREEF me kula dani innalillahi wa'inna ilaihirraju un" hannunta ta fincike ta fada kan gawawwakin tana kuka abin tausayi ,daga taje ta jijjiga wannan sai ta jijjiga wancan" AREEF ta kalla tana kuka tana ganin yadda yake kwance kamar me bacci sai dai baya numfashi, kuka take tana cewa" Dan Allah Yaya katashi kada kacemin bazaka tashiba* Dan Allah kace mafarki nake Yaya,Yaya AREEF kada kacemin tafiya Kai kabarni, Dan Allah Yaya katashi Dan Allah katashi sai da nace kada kafito Amma kaki" yanzu shikkenan narasaka wayyo Allah Ni AFNAN Naga rayuwa, nashiga uku Yaya katashi Dan Allah,