Showing 6001 words to 9000 words out of 27968 words

Chapter 3 - Tayi Min Kankanta By Zahra Surbajo

01 Dec 2025

16824

hankali tace"na barshi a matsayin sirrina,don Allah karka kuma tambayata"ta faɗi cikin kuka.

Taɓe baki yayi sannan yace"bazan kuma ba,amma kisani in ni baki faɗa min ba dole zaki faɗawa mijinki ay"yana kaiwa nan ya fice daga ɗakin.

Hankalin zahra yayi ƙololuwar tashi jin furucin muhammad,tabbas dole zata sanar da mijinta wannan mugun labarin,duƙar da kanta tayi ƙasa tana kuka me tsuma zuciya.

A haka mummy ta shigo tasameta,sosai hankalin mummy yatashi janyota tayi jikinta tashiga tambayarta abinda yafaru,cikin kuka zahra tace"mummy yanzu rayuwata a haka zata ƙare kenan,bazan taɓa aureba,in ko zanyi auren dole sena cewa mijina anmin fyaɗe? inde hakane nida aure har abada"ta ƙarasa maganar cikin kuka.

Tausayintane ya kama mummy ta shiga rarrashinta da duk wata kalma me daɗi,da ƙyar tayi shuru.

Mummy ɗakin daddy taje tasameshi yana shirin fita,ganinta cikin yanayin damuwa ne yasa ya nemi guri ya zauna yace"hajiya lafiya kuwa?"

Cikin damuwa tace"Alhaji yarinyar nan na cikin damuwa gameda fyaɗen da aka mata, baka ganin akwai buƙatar a binciko ko waye a hukuntashi sannan asa shi dole ya aureta?"

Shuru Alhaji yayi na ɗan lokaci sannan yace"nemo ko waye beda wani amfani,fyaɗe de anriga an mata,ba abinda ze sauya hakan,kuma ni modibbo inde na isa da Muhammad to tabbas shine ze auri Zahra,dan shi kaɗai ze rufa asirinmu"

Mummy itama ta gamsu da bayanin na alhaji,dan haka kwarin guiwa ta ƙara bashi kan ƙudirin nasa,sabida Allah yasani tana tausayin zahra matuƙa.

Alhaji be samu zama da Muhammad ba seda dare bayan ya dawo daga gun ayki.
Lokacin daya sanar dashi hukuncin daya yanke akanshi da zahra muhammad kaɗanne beyi fitsari a wando ba sabida firgici,bakinsa har rawa yake yace"daddy don Allah kayi haƙuri kabar maganarnan,nifa bana sonta,gaba ɗaya zahra nawa take da har zaay batun aurenta,ni tayi min ƙanƙanta daddy pls"
Yafaɗi kamar zeyi kuka.

"muhammad ba shawara fa nake nema ba,hukuncin dana yanke nake faɗa maka,wannan duk raayinka ne,ba nawa ba,nan da wanne lokacine zahra zata iya warkewa gaba ɗaya" daddy ya buƙata cikin haɗe rai.

Jikin Muhammad a sanyaye yace "wata guda"

"nasa lokacin auranku nan da watanni biyu masu zuwa,na ɗauke maka komai,kaje ka fara shiri"daddy ya faɗi sannan ya miƙe yabar gurin.


Muhammad na zaune kamar wanda aka dasa,yama rasa me zeyi yaji sanyi aransa,da ace ze iya kuka to ba shakka kukan ze ta rusawa.

A Hankali ya miƙe ya nufi ɗakinshi jiki a sanyaye ya faɗa gado yana nazari,shide gaskiya tayi mishi ƙanƙanta a aure to in ya aureta yace ya auri wa?shi fyaɗen da aka mata ba damuwarshi bane kawai de shi yafi son mace ƙatuwa ne.


Muje zuwa


Surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TAYI MIN ƘANƘANTA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*


*11*


Muhammad tsawon sati guda ya kwashe ba inda yake zuwa sabida firgicin da yake ciki,sosai zancan auransa yasakashi,a damuwa,

Zahra sanda mummy ta sanar mata auranta da muhammad sosai taji daɗi,sabida taga ɗan uwanta ne,ze rufa mata asiri,dan haka bata da damuwar komai aranta.burinta Allah ya nuna mata lokacin.dan ita tun haɗa idonta dashi na farko taji ya kwanta aranta.

Sosai walwalarta da jin daɗinta ya ƙaru agidan ba mummy ba har daddy ya fahimci hakan,wani sanyi yakeji aransa sabida ya mata abinda takeso.

Mummy gyara zahra take da duk wani abu data san baze cutar da lafiyarta ba,,cikin ƙanƙanin lokaci zahra tayi wani kyau na musamman fatarta ta murje tayi fari har wani sheƙi take,gashi yanzu ba wata rama ajikinta,sema wata ƙiba data mulka,zahran inna kenan matashiya ƴar kimanin shekaru goma sha shida.kyakkyawa ajin farko,


Saura kwana biyu ɗaurin aure,muhammad na zaune a lambun gidansu zahra ta ƙaraso gurin,yana ganinta ya ɗauke kai kamar be ganta ba,murmushi tayi dan tasan baya sonta,ita ko sonshi take dan haka zatai haƙuri da duk wani halinsa har shima ya sota,gefenshi taje ta zauna,kamshin da take ne yasashi ɗago kai ya dubeta,sannan ya maida kansa gefe.

"yaya dama inaso in baka haƙuri ne akan auran dolen da zaay maka"
Ɗagowa yayi ya dubeta rai aɓace yace"au auran dolen ni kaɗai zaayiwa kenan ke banda ke?"

Murmushi tayi kumatunta suka lotsa tace"banda ni gaskiya,kai de za'a yiwa,ni auran nagani inaso za'a min,"ta faɗi a kunyace.

Tsayawa yayi,yana ƙare mata kallo,tattaro hankalinshi yayi gaba ɗaya kanta,hannunta ya kamo ya dibeta a tsanake yace"zahra ni kikeso?"yayi tambayar a tsanake.
Murmushinta me sanyi tayi sannan tace "Tunda naganka,naga kuma irin taimakon daka ba rayuwata da lafiyata,yaya muhammad naji ina sonka,wallahi da gaske nake har raina"ta ƙarasa maganar kamar zatai kuka.

Yatsun hannunta yake kallo,sannan ya ɗago ya dubeta yace"zahra to ya zakiyi in kika fahimci ba matsuguninki a zuciyata?"

"addua zanyi,wataran zaka soni"ta bashi amsa batare da damuwar komai ba.

Murmushin takaici yayi sannan yace"to in kuma ba kya cikin kalar matan da nake so fa?"

"Zanyi ƙoƙarin maida kaina kalarsu insha Allahu"tabashi amsa.

"to ay ni zahra gaba ɗaya kin min ƙanƙanta a aure,taya zan iya zaman aure dake?"

"wataran zan girma yaya,in zama babba,sede ko kace sauran wanine baka so,inaga shine kawai dalilin daze hanaka aurena"ta ƙarasa maganar tana kuka,

Runtse ido yayi maganar na masa ciwo a zuciyarsa,a hankali ya dubeta yace"to naji zahra tashi kije kar mummy ta nemeki,"

Miƙewa tayi a hankali,tabar gurin tana waigenshi.

Shima miƙewa yayi yaja motarsa zuwa Hammad hospital dan ya sanar da amininsa halin da yake ciki,dan barin kashi a ciki baya maganin yunwa.


Muje zuwa


Surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TAYI MIN ƘANƘANTA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*


*12*



A harabar asibitin yayi parking,sannan ya fito ya taka zuwa office ɗin aminin nasa.

Da sallamarsa ya shiga office ɗin cike da fara'a ya taso suka rungume juna,suna ɗan dukan juna a baya,sannan suka koma kan doguwar kujera suka zauna.

Muhammad ne ya fara magana cikin yanayin damuwa"Abokina ina cikin damuwa fa,?"

"wacce irin damuwace wannan,?"abokin nasa ya buƙata cike da kulawa.

"jibi daddy ze ɗauramin aure da wata ƴar ƙanwarsa,na rasa inda zan tsoma raina".

A razane ya miƙe tsaye yana ja da baya,take duk wani annurin fuskarsa ya kauce kamar wanda yacewa gobe ze mutu.

Cikin kakkausar murya yace"HAMMAD kana nufin alƙawarin auren ƴarfillo daka lalatawa rayuwa yatashi a banza kenan?"

Miƙewa muhamnad yayi ya ƙaraso kusa da abokin nasa ya dafa kafaɗarsa yace"JAMEEL kafi kowa sanin irin son da nakewa ƴarfillo,wallahi babu macen dana keso a zuciyata sama da ita,kullum jameel bana iya bacci sabida ita,wallahi akan ƴarfillo zan iya ɓata ran kowa,sede itama wannan dazan auran akwai abun tausayi game da itan,kwatankwacin kaddarar data faɗawa ƴarfillo itama hakanne,wallahi zan auri yarinyar ne,kodan jihadin da zanyi na auranta Allah ya kawomin ƴarfillo na cikin sauƙi,pls jameel in baka fahimceni ba bame fahimtata"muhammad yayi maganar kamar zeyi kuka.

Waigowa jameel yayi,ya dubi hammad yace "b haka bane hammad ay kai mijin mace huɗune,bana de so ne sanadin auran da zakayi ka mance da ƴarfillo shine yasa"

"har abada bazan mance da ita ba jameel,kuma zanci gaba da nemanta har se inda ƙarfina ya ƙare"Muhammad yafaɗi cike da tabbatarwa.

Jameel kwantar masa da hankali yaci gaba dayi akan auransa da zahra,inda yace ya daure yayiwa daddy biyayya hakanne zesa in ya kawo ƴarfillo ya amince ya aureta.

Sosai Muhammad ya gamsu da shawarar aminin nasa,duka yakaiwa jameel yace yana dariya"wato jameel,da ace yadda kanka ke kawo wuta haka zuciyar ka take da nigeria batayi asarar soja ba,amma wai daga harbi ɗaya a baya,sega resigning letter wallahi ka bada maza,ay gashi nan ka ƙare a kallewa mata al'aura,da wuri zaka makance"ya ƙarasa maganar yana dariya.

Duka jameel yakai masa yace"ay duk namijin da baya gudu baya tsawon rai,da asara gara gidadanci,taya na hango lahirar nasha da ƙyar zan bari a ƙarasa ni,kaima kaga zaka iya ne shiyasa baka fita ba"

"bazan taɓa barin aykin soja ba Jameel sede in ze shiga tsakanina da ƴarfillo to tabbas zan fita".

Haka de sukai tayiwa juna barkwanci,basu rabu ba se dare,agajiye muhamnad ya dawo gida,zuciyarshi fal farinciki kamar yaga ƴarfillonsa.

To bari mu waiwaya baya😄

Kowa ta turo data se in ci gaba😎


Surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*AURE DA HAIHUWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*



*Page 13*



Mikewa tayi ta koma dakin ta, kudi ta dauko tasa hijabi,ta nufi gun megadi,yana hango ta nufo shi yataso da sauri yadan risina yace "barka da safiya hajiya,me kike da bukata?"amsawa tayi cikin sakin fuska tace"baba don Allah cefane nakeso kayomin,a wuse market,"

"To badamuwa ranki ya Dade kawo aje ayo miki"

Lissafa masa komai tayi sannan ta bashi kudin kimanin dubu tamanin,yatafi .

Kulle gidan tayi ta ciki sannan ta koma cikin gida,wanka ta shiga sannan ta shirya ta dawo falo zaman jiran akawo mata cefanen.

Baa jima sosai ba megadi yashigo mata da sakonta bayan ta bude masa gidan,sosai tai masa godiya sannan ta kwashe komai takai dakinta.

Dan karamin gas din datasa ya siyo mata ta kunna ta daurayo tukunyar daya siyo mata tazo ta hada komai ta Dora indomie acikin dakin Nata.
Dan duk abinda zata bukata seda tasa ya siyo mata.

Haka taci gaba da gudanar da rayuwarta a kulle acikin daki,koda wasa batason ganin Rayhan, shiyasa ta kulle kanta aciki,sabida akwai toilet acikin dakin Nata,

A nashi bangaren Rayhan ko tunda ya fice yabar gidan,kotu yaje ya shigar da karar doctor Amina sakamakon abinda sukawa matarsa,inda alkali yabada sati biyu su hallara agabansa.

Lokacin da sakon ya riski doctor Amina,tashin hankalin data shiga,bashida adadi.Neman Farhan take a waya tun lokacin data ga su Rayhan din amma bata shiga,wannan shine yakara daga hankalinta.

Ranar shiga kotun da safe Rayhan yaje kofar dakin na safna yace cikin dakewar murya.
"Ki bude kofa ki fito mu tafi kotu Dan yau alkali yabada mu hallara agabanshi ina jiranki a mota"yana kaiwa nan yayi fucewarsa abunsa

Safna jin maganar tayi kamar saukar Aradu,yau itace Rayhan yakai kara kotu?wannan wacce irin masiface.
Tunda ya fada tasan dagaske yakeyi,Dan karya bata daya daga cikin halayensa.

Jiki asanyaye ta janyo hijab tasaka,ta zura takalmi ta fito.bayan ta kulle dakinta.

A motar ta sameshi yana cika yana batsewa,ba me cewa shine Rayhan din ta me yawan murmushi.

A harabar kotun suka samu doctor Amina ma ta iso ita da maaikatan da suka gudanar da aykin.

Karasawa gunta Safna tayi suka gaisa,inda doctor Amina tace"Safna kinga kaddara ko?"
Hawaye ne suka gangaro daga idon Safna masu zafi sannan tace"doctor ina cikin tashin hankali"

Karasowar Rayhan gurin ne ya katse musu hirar,inda ya dakawa Safna tsawa da cewa "wuce mutafi".ba musu tabishi abaya suka shiga cikin kotun.

Bayan kowa ya hallara ne me gabatar da kara yatashi ya gabatar da karar da Rayhan Hashim ya shigar agabanta,yana me kalubalantar doctor Amina,da sauya kwayoyin halittarsa Dana wani ta sawa matarsa,Wanda hakan ya janyo matarsa ta dauki ciki,yana me rokon kotu datasa matarsa ta zubar da cikin,kuma yanaso kotu me adalci da ta bi masa hakkinsa.

Bayan an gabatar da kara ne alkali ya bukaci ganin doctor Amina,jiki asanyaye ta karasa inda aka tanada domun tsayuwar Wanda ake tuhuma taje ta tsaya.

"Munaso ki gabatar mana da kanki"cewar alkali,

"Sunana Amina Galadima,likita,kuma mamallakiyar Asibitin Galadima special hospital"

"Kinji korafin da aka shigar akanki shin haka akayi koko kina da ja game da hakan?"alkali yasake jefo mata tambayar.

"Duk abinda aka fadi ranka ya Dade haka ne,sede ba nice da kaina na gudanar da aykinba, kuma kuskuren suna aka samu ta hanyar kamanceceniyar suna,ina me rokon kotu datai mana sassauci".ta kwashe komai ta sanar da kotu gamida mika takaddu na bincike da kuma duk wani Abu daya shafi dashen tun kan ayi har zuwa bayan anyi,

Alkali ya bukaci maaikatan da suka gudanar da aykin dasu gabato gabansa,suma suka amsa sune suka yi,

Bayan dogon rubutu alkali yafara magana,"Bayan nazari da bincike,wainda ake tuhuma basu wahalar da sharia ba kotu ta gamsu da duk bayanan kowanne bangare,kuskurene babba suka aykata,Wanda dole ay musu hukunci,Na farko,kotu ta yankewa doctor Amina hukuncin biyan Tara ta dubu Dari,bisa laifin daukar maaikatan da suke sakaci da aykinsu,su kuma wainda suka aykata laifin,kotu na umartar da akaisu gidan gyaran hali na tsawon wata guda,ko zabin Tara,ta dubu goma goma"kotunce ta hargitse da surutu,kamin alkali ya tsawatar akai shuru, sannan yaci gaba

"Kotu na kira ga Rayhan da yayi hakuri bisa faruwar wannan Lamari,sabida kotu bazata sa Safna ta zubar da cikiba, Wanda aykata hakan zunubine,kuma shi wannan Abu daya faru,shima kuskuren ne babba, duba da tabbaci da aka samu daga bakunan maaikatan na cewa cikin an sameshi bada kwayoyin halittarka ba,kuma kamin ayi an tabbatar da bata da ciki,bayan anyi kuma baka kusanceta ba seda aka tabbatar da ta samu cikin,hakan ya tabbatar da cewa cikin jikinta ba naka bane,Dan haka kotu ta sallami wannan karar"

Gaba daya kotun ta kaure da hayaniya,Safna kuka take kamar ranta ze fita, wannan kaddara dame tai kama.

Haka ta mike tabi bayan Rayhan din daya fita afusace,

Sede kamin ta karaso tuni yaja motar sa yabar harabar gurin,Dan shi Sam ba haka yaso ba,so yayi asa safna ta zubar da cikin, sannan adaure doctor Amina, amma gaba daya ba hakan akayiba,

Hakanne yasa shi tunanin anya ma kuwa alkalin yasan aykinshi?


Muje zuwa


Surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*AURE DA HAIHUWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀



*Zahra Surbajo*



*Inna Ibrahim kime alkhairin Allah yakai miki, ina alfahari da haduwa dake arayuwata.*

*14*


Doctor Amina ce ta karaso inda take ta dafata, da sauri ta waiga taga waye,
Ganinta ne yasa ta rushe da kuka ta fada jikinta tana fadin,"doctor ki taimakeni banason rasa aurena,Ina son mijina sosai"tayi shuru sakamakon kukan dayaci karfinta.

Jan ta zuwa mota doctor tayi sabida jamaa sun fara taruwa akansu,da gudu ta fice daga harabar kotun.

Safna ko se aykin kuka take,har suka iso kofar gidan Rayhan din,bude mata kofa tayi ta fito,sannan tace"gobe zan dawo in mijinki ya fita Dan musan yadda zaa bullowa da abun ki kwantar da hankalin ki"

Jiki ba kwari ta tura kofar get din tashiga ita kuma doctor taja motarta ta bar gurin.

A harabar gidan tasameshi tsaye yana huci,kamar wani maciji,bata bi takanshi ba tayi hanyar shiga ciki,wata tsawa ya daka mata sai da cikinta yayi juyi ta waigo a firgice,.

Tsayawa tayi cak a inda take,har ya karaso,cikin fushi yake magana "Safna koda wasa ban dauka zaki ketare maganata ba,nadauka son da kikemin na gaskene,shiyasa na baki umarnin zubar da ciki amma kika ki,to ni bazan iya zama dake ina kwasar bakin ciki ba,Dan haka zan baki zabi wallahi sede ki zaba ni ko cikin jikin ki?"ya wurga mata tambayar batare da shayin komai ba,

Cikin kuka Safna ta tsuguna agabanshi tafara bashi hakuri"don Allah Rayhan kayi hakuri, kasan ina sonka, wlh nafi sonka akan cikin jikina,fushin Allah ne kawai banason na fada,sakamakon zubar da cikin,don Allah ka fahimceni"ta karasa maganar cikin kuka.

"Zabi na baki malama ni ko cikin jikin ki?"yafadi batare daya tausaya mata ba.

Rokonshi take da duk iyawarta kan yayi hakuri amma fafur ya kafe,ganin bata da mafitane yasa ta mike tsaye ta share hawayen ta tace asanyaye "na zabi cikin jikina Rayhan"

Kallon mamaki yay mata sannan yace "to kije na sauwake miki aurena dake kanki,na sakeki saki daya"ya yi saurin barin gurin sakamakon kukan dakeson kubce masa,yana son matarsa,yayi iya yinsa Dan yaso abinda ke cikinta amma yakasa,shiyasa ya sake ta gudun kar zuciya takai shi halaka.

Safna ji tayi duniyar tai mata nauyi,rasa abun yi tayi kawai seta kife agurin tana kuka,ta jima tana kukan kamin ta rarrashi kanta ta mike,ta shiga cikin gidan,dakinta ta shiga,ta hada kayanta na sawa se Jakarta ta hannu,

Ta janyo akwatin ta fice,daga falon tana kuka.

Shima dake tsaye ta window yana kallonta kukan yake kamar yabita,sede hakan da yayi shine masalaha agareshi.

Tana fita, taxi ta dauka drop zuwa jabi park, tana isa motar Daura ta hau,fasinga daya dama suke jira Dan haka direba yaja motar suka nausa kan titi.


Muje zuwa


Surbajo for life
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TAYI MIN ƘANƘANTA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*


*Marasa lafiyanmu Allah kabasu lafiya,masu ciki Allah ka saukesu lafiya,Allah kazaunar da kowa agidan auranta lafiya,Ameen*

*15*


Da asuba,da kanshi ya tasheta yabata jallabiyarsa tasa tayi rolling da rawaninsa tayi sallah,sannan ta koma bacci bayan ta cire masa rigar tasa,

Bata farka ba se tara na safe,tuni hammad yayi wankansa ya kimtsa,jin motsin da yayine yasa yazo ya sameta a zaune ta farka,rigarta take ƙoƙarin sawa amma zafin da gun ƴunar jiya ke mata yasa ta kasa sawa sabida rigar bata kai jallabiyar daya bata faɗi ba.

Da sauri ya ƙaraso gurinta,ɗago ido tayi ta kalleshi sannan ta sunkuyar da kai,

Zama yayi kusa da ita har jikinsu na gogar juna,waigowa tayi asanyaye ta kalleshi shima ita yake kallo,hannu yasa ya zagayota dashi ya kamo rigar yasa mata,sunkuyar da kai tayi ta runtse ido sabida zafin da taji,a hankali yace"sorry,"gyaɗa kai tayi sannan ta miƙe,ta fice daga ɗakin,yabi bayanta da kallo,yana haɗiye wani miyau.

Se da ta fice ne kuma kunyar ta faɗo mata,to tacewa mummy agurin wa ta kwana,kasa ƙarasawa cikin falon tayi ta tsaya tana wasi-wasi.

Hammad ne ya fito zashi gaida iyayen nasa,anan yaci karo da ita tsaye tana tunani,ƙarasowa yayi inda take,yace"ke lafiyarki ƙalau kuwa,tsayuwar me kikeyi anan?"
A raunane ta ɗago idonta ta dibeshi tana hawaye tace"kunya nakeji suji na kwana agurinka"

Murmushi yayi sannan yace "sabida kin kwana da kwarto ko?"

Da sauri ta girgiza kanta tana faɗin "Allah ya tsaremin miji da zama kwarto,ni mijina ba kwarto bane,aniyarka ta bika"sam ita ta mance ma matsayinsa agunta take wannan batun.

Be kulata ba hannu yasa yaja hannunta suka nufi falon,itako tirjewa take tana kuka tana "wallahi bazaa ganmu atare ba,nide kasakeni ka tafi kai kaɗai"a haka suka shigo falon,inda mutanen gidan ke zaune a dinning suna karyawa,ɓurarin da zahra kewa Hammad ɗinne ya dawo da hankalinsu kansu,
Shiko Hammad be saketa ba seda suka shigo falon,ay tana ganinta gaban su mummy,da sauri ta ɓoye abayanshi,duk yadda Hammad ya kauce itama da gudu zata koma gurin,sosai abun yaba su daddy dariya,a hankali daddy yace "rakata ɗaki mana muhammad,ka tsaida ita anan"

Murmushi yayi sannan yaja hannunta zuwa ɗakin nasu se ɓoyewa take agefensa.

Seda ya kaita sannan ya dawo gun mahaifan nasa,tsugunawa yayi ya gaishesu sannan yaja kujera ya zauna,

"Angama shirya komai na gidan da zaku zauna,anjima mummynka zasu kaita gidan,ka kwantar da hankalinka"daddy ya faɗi yana murmushi.

Sosai kunya ta kama Hammad,ya sosa ƙeya yana murmushi yace"daddy ay ko anan ɗinma zamu iya zama"

"kuci gaba da mana rashin kunya a cikin gida ko?"daddy ya buƙata.

Shuru Muhammad yayi dan se yanzu yagano ma manufar daddyn.

Haka yayi break fast duk a tsarge,yana gamawa ya miƙe ya bar falon.

Shiryawa yayi ya fice zuwa gun amininsa Jameel,kasancewar yana hutu be koma bakin aykiba.

Surayya ce tasamu zahra a ɗaki tayi wanka ta kimtsa cikin wata atamfa ja da milk me golden tayi kyau matuƙa.
Tana shiga ta fara mata tsiya,"kaga amaryar yaya,me bin angonta ɗaki"duka zahra takai mata tana faɗin"zanko haɗaki dashi,bari muhaɗu"

"ayya yarinya kwantar da hankalinki yau zaa kaiki gidanshi seku dena satar hanya"ta ƙarasa maganar tana tuntsira dariya,

Zahra de ba baka se kunne,seda su mummy sika bar falon sannan taje tayi breakfast

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login