Showing 69001 words to 72000 words out of 221033 words

Chapter 24 - UWA KO UKUBA COMPLT

24 Feb 2025

41711

friends, I will shower you with my love and affection sannan zan baki miji na gari kaman nasu Yayyinki Aya or standup and follow them kuje Kano but listen to this” Mom tadan gyara glass din idanunta tana kallon kwayar idanun Asmeey da kirjinta dake dukan uku uku tace “idan kinbi mutanen nan nayafeki as y’ata sannan Allah ya wulakantaki Asma’u!” Wani girrrrrrr kan Asmeey yayi kaman an kunna inji, Mom tace “idan kika bisu na daura bakina akanki Ya Allah yahanaki kwanciyan hankali!” Girrrrrrr haka kanta yakara kara this time around kaman ana zuge zip din riga, Mom tace “idan kika bari mahaukacin chan ya kwanta dake Allah ya hanaki farin ciki bazaki taba ganin daidai arayuwanki ba!”Saikuma Mom tadan sassauta murya tace “I hate mutanen nan sosai
Na musu tsana da bantabama wani ba, I hate Hamad, na tsani yaron nan sabida yataba Fawaz dan haka kikai zaman aure dashi ni uwarki kuma mahaifiyarki nace Allah ya tsine miki albarka!” Rawa kafafun Asmeey yafara hakan yasa Gwaggo da take tafarfasa ta taho wajen tasa hannu takama hannun Asmeey tace “sallaman ya isa haka wuce muje kafin afara cin zali” Mom tama Asmeey da Gwaggo keja wani kallo tace “you have two options trade carefully” Gwaggo tawani jaa Asmeey ta sauka daga jikin Mom tace “dalla muje” Gwaggo tashiga janta Asmeey na bin Gwaggo but kallon Mom take dataki kallonta saima wayanta taciro tana daddannawa wani karfi ne yazoma Asmeey sai kawai ta turje Gwaggo ta tsaya chak tareda juyowa ta kalleta tace “ke Asama” dukawa Asmeey tayi tasa guiwowinta akasa, Abba, Gwaggo, Kawu, Mama, Baba da su Ya Mustapa da matayensu dake cikin mota duk kallonta ake banda Hamad dake gaban motan Abba kansa akasa, Munir yataho kanta azuciye kafinma tayi magana yace “Asmeey don’t even say abinda kike shirin fadi, wai are you mad? Mom will kill you kika cigaba da zama anan?Sabida she hugged you just now is that it? Kin dauka u will keep getting daily doze of hugs ne? Ya Asmeey”?Fashewa da kuka sosai Asmeey tayi cus nobody will understand wat she is going through da tsinuwa da bakin da Mom tamata, kawai sai tayi kneeling tama kasa magana kuka take Ya Allah she is in pain, curses daban daban Mom ta daura akanta idan tabisu bakin uwa na kama yara, kowa kallonta yake, Anty Asiya Matar Ya Mustapa tace “Baban Areef maman yaran nan is a witch wlh, she will kill yarinyar nan eventually, I’m just feeling bad for Hamad and the poor girl as well” tayi tsaki ta dauke kanta cus kallon Asmeey nasa idanunta na ciko da hawaye, Baba strictly yace “Asma’u tashi muje” ahankali tana kuka tace “Baba kayakuri, dan Allah kayakuri bazanje ba” wani murmushi Mom tayi ta karkada kafa tace “Ya isa, tashi kizo muje ciki” babu musu kaman wata robot Asmeey tashiga kokarin tashi har Gwaggo saita bude baki hangame tana kallon ikon Allah, mikewa tayi daidai zata juya sai kawai suka hada ido da Hamad dake gaban motan Abba yana sanye da milk yadi dayamai shegen kyau yazuba mata idanu bazakace ga takamaimen menene kan idanunsa ba, sai kawai takasa daga kafafunta, takasa motsi, takasa daina kallonsa, sai kawai takara fashewa da kuka shikuma yana zaune yana kallonta kur, tasowa Mom tayi tazo wajen tasa hannu takama hannunta tace “dalla wuce muje me kike kallo awanchan mai tabin hankalin”? Tajuya tajata Asmeey na binta but kallon Ya Hamad take dake kallonta tana kuka kowa na kallonsu, chak Mom taji an rike Asmeey cus takasa janta dasauri Mom tajuyo dantaga waye aka dauke Mom da mari da saida taga duhu dayake is unexpected mari jikake taaassssss!!! Asmeey tayi ihu tace “Mommyyy!” Ganin an mari Mom dinta…….


TOM JAMA’A ANAN NAKAWO KARSHEN FREE PAGES 🤗

THANK YOU FOR READING MY STORY!

SHIN WAKUKE GANI YA MARI THE ALMIGHTY BOSSY MOM??

ANYA TAFIYAN ASMEEY KANO ZAI YUWU??

YAZATAYI DA TSINUWAN MAHAIFIYANTA??

AGANINKU TSAKANIN MOM DA BABA WA ASMEEY TAFISO???

KUNA GANIN ASMEEY NA SON HAMAD???

ZATA IYA TAKE TSINUWAN MOM TAYI XAMAN AURE DA HAMAD??

KUNA GANIN MOM ZATABAR SU SUYI ZAMAN AURE??

SO MOM TA IYA LALLABA YARA HAKA HARDA KIRAN ASMEEY AUTAR MATA NA! MY BABY! MY PRINCESS 👸

GROUP DAZAKI IYA SHIGA

EXCLUSIVE 5K (Email update)
VIP 2k (Telegram group)
GGM 1K (Telegram group)
GM 500 (Telegram group)

KINDLY PAY INTO
6353995766 M SHAKUR WORLD MONIEPOINT
OR
7032934950 AISHAT MUHAMMAD OPAY
OR
3107021073 AISHA MUHAMMAD FIRST BANK
CHAT ME UP DA EVIDENCE OF PAYMENY
wa.me/+2347012181461
PLEASE SUPPORT ME BY SUBSCRIBING ❤️❤️❤️

POSTING CONTINUES ON SATURDAY ❤️❤️
*UWA KO UKUBA*


2️⃣5️⃣


EPISODE



YA ALLAH NA KAGA ZUCIYANA GA HAKKINA NAN DUK WACCE TAKARANTA MINI BATARE DATA BIYABA BAN YAFE MATA BA!

JOIN OUR PAID GROUP AKWAI NA 500, 1k, 2k, 5k OR AREWABOOKS @mshakur

SUPPORT ME PLEASE 🙏
THANK YOU
PAY HERE AND WATSAPP ME
PAY INTO
6353995766 M SHAKUR WORLD MONIEPOINT
OR
7032934950 AISHAT MUHAMMAD OPAY
OR
0895672695 AISHAT MUHAMMAD GT BANK
wa.me/+2347012181461

Asmeey felt every pain na slap din Mom a fuskanta har wani runtse idanunta tayi cus gani tayi looking at mahaifiyanta da Baba ya mara agabanta is taboo tayi wani ihu kaman mara lafiya zatabi mahaifiyarta kasa ahaka Baba yafizgota, Asmeey takara juyawa tabude idanunta tana wani irin kuka tamikama Mom hannu tace “Mommmmy” Baba yajuyo da ita dan ya bala’in zuciya yadaga hannu zai kaimata mari Asmeey ta kankare a bala’in tsorace dan Baba baitaba dukanta ba hannun Baba daya daha sama looks like kaman wani big rock is about to fall akanta yanda ta sankare in fear sai kawai Baba ya dakata he can’t hurt yaransa especially yaro mai tsoro haka irin Asmeey, ya daka mata mummunan tsawa yace “is something wrong with you Asma’u?” Girgizama Baba kai tayi tama daburce duka, Baba kaman zai rufeta da duka, Baba yace “kin dauka yanzu wannan matan nada authority akanki ne? I do not have any authority on you nor your mother this is addininmu, are you a small girl? Tun kina karaman ko kinje islamiyya har gida ana koyarda ku, bakisan menene aure ba? You are Hussain responsibility and right! Karkashin mijinki Hussain kike! Aljannarki na karkashin kafansa! Idan kikamin wani hauka anan zan saba miki ainun!” Ashe iyayen da basa masifa basa dukan yaro ashe idan sukayi abin baya kyau, Asmeey har wani fitsari fitsari taji tanaji, tunda ta taso bata taba ganin Baba this angry ba, bata taba ganin Baba shouted at any one of them like this ba, sai yau, bata taba ganin Baba yay zuciya hakaba sai yau, tsakar gidan tsit hatta ita Mom kanta takasa motsi daga kasan kafafu sun rike, Baba yakalli Mom dake kallonsa yace “who do you think you are Salima? Wacece ke? Sabida I respected you nabaki freedom, na daura miki ragaman handling makarantan yarana doesn’t mean ke ce ke iko dani, yarnan!” Yanuna Asmeey dake kuka tana shaking yace “y’ata ce! Nina haifeta! Hakki ne akaina na aurar da ita ga miji na gari, idan kin isa naga kin hana yarinyar nan bin mijinta zuwa gidansu yau saina gwadamiki ke ba kowan kowa bace face turbaya!” Baba ya yajuya azuciye yace “Hamad! Hussain come here!” Bude kofar mota Hamadi yayi yafito kansa akasa, Mom na kasa dafe da kuncinta tana kallon ikon Allah dan Baba yagama disgata yau yacimata mutunci na bugawa a jarida gashi takasa tashi cus kafafun sun rike kam tazubama Hamad ido tanaji kaman ta tashi ta chakamai wuka, zuwa wajen Hamad yayi, Baba kawai yasa hannu yakama hannunsa yasa na Asmeey aciki, cikin kakkausan murya yace “ga Matar ka ku barmin gidana immediately!” Yanuna musu mota da hannu, yakalli Asmeey dake kuka yace “idan you try any nonsense bayan kinje Kano you will see abinda zan miki” kankame hannun Ya Hamad Asmeey tayi tana kuka sabida yanda ta tsorata da Baba, Baba yace “nace kuwuce ku barmin gidana!” Kan Hamad akasa yajuya rike da hannun Asmeey yafara tafiya Asmeey na binsa tana kuka sosai but still holding him tana kallon Mom dake binta da ido tana mamakin Asmeey dataga tafijin tsoron ubanta akanta, she thought babu wanda Asmeey ke tsoro aduniya sama da ita? How can this girl be afraid of Babanta sama da ita how? She thought after fadan Baba still bazata tafi ba especially with all abubuwan data gayamata but yarinyar nan ta bi yaron.
Suna kaiwa wajen Abba da kansa yabude musu bayan motan tasa yace “ku shiga nan” Asmeey yadan kalla ganin Mamanta take still shaking dakuma Baba bamatasan ina sukeba sai kawai yadaure da kyar yariketa zai sata a motan tasake fashewa da kuka tana kallon Mom, Baba yataho azuciye yace “Au bazaki shiga ba” da gudu ta shiga tawani kama Ya Hamad tace “Ya Hamad! Ya Hammad! Baba wayyoooo Allah na!” Dasauri Abba yatare Baba yace “Muhammadu Sani calm down” rai abace Baba yace “Yaya this girl tasaba da duka that’s the only language take fahimta nakega kabanni na cimata” shiga motan Hamadi yayi dawani irin sauri ta shige jikansa ta kwakumeshi tana kuka sosai! Abba yace “Faisal zoka jasu” ba musu Faisal yafito yashiga mazaunin driver, sai Abba yabudema Mamie gaba yace “zauna” zama Mamie tayi Abba yarufe motan Faisal ya kunna yaja yabar gidan, Munir yawani sauke ijiyan zuciya, Abba yace “suntafi toh wuce kaje dakinka calm down please Kawu go with him” Kawu yazo yawuce da Baba, Gwaggo tace “an dauka shiru shiru haukane makira kawai” Abba yabude mata mota yace “shiga” shiga tayi sannan yawuce yashiga mota shima duk suka fice su Kawu suka wuce flat dinsu da Baba, yaran kowa ya koma ciki har Munir ko ajikinsa Mom na kasa, Mama tazo wajen Mom takamata ta daga Mom tamike da kyar, Mom tace “ni Baban su Aya zai mara ni? Ni Salima”? Mama tace “kiyakuri Maman Aya muje” fizge hannunta Mom tayi tawuce flat nasu zuwa dakinta tana tafiya da kyar, rabon dataji bakin ciki irin kalan na yau ta manta arayuwanta yau Baba ya guma mata, ya chusa mata sosai.


Dakinta Mom tawuce tazauna kaman zata kama da wuta rabon dataji kalan bacin rai haka in her life wallahi ta manta, ita Baban su Aya zai mara agaban kowa? Ita? Ita da in the next at most ake shirin amaidata Chef of justice na Bauchi state gabaki daya ita zai mara? Ita Baban su Aya zai dauki yarta ya aurar batare daya shawarce ta ba? Bamata sani ba, did Baban Aya have any idea who she is kuwa? Barrister Salima AKA Mrs Saraki! Ita zai mara! This is an insult to her profession! Her dignity! Her worth! Shaking tafara tadaga waya, Yayanta ta shiga kira kusan 3miss calls ta mishi ana hudu ya dauka cikin kumfan zuciya tace “Yaya kaga abinda Baban su Aya yamini ya aurar mini da yarinya batare dana sani ba”? “Hakan shine daidai, niko ya kirani cikin mutunci da girmamawa kuma nazo har gidan nan har masallaci na shaida daurin auren Asmeey kuma nasa albarka, remember rannan danazo miki fada kin tuna amsoshin da kika bani? Salima kin dauka duk zafinki da fadin ranki da girman kai da sauransu kinfi karfin Allah ne? Kin dauka u own ur kids? Forget mu uba bamu cika zama da yaranmu ba sabida zuwa kasuwa da fita aiki but we own our children, mahaifi ba abin wasa bane, but ke gani kike kaman kece mai yaranki ke kadai, just take this as Allah ne ke sakama yarinyarki, zaluntarta dakike yayi yawa Allah ya dauketa yacireta daga hannunki”muryan Mom nawani irin shaking ganin ita kawai Baban su Aya ya maida mara daraja, kaskantacciya, sannan yaranta da yan uwanta duka sun munafunceta tace “Yaya so yanzu kasani, ka yarda that jobless boy mara abinyi ya auri y’ata? Ka bari mahaifinta ya aura mata shi?” Alhaji Mahmood yace “sanda kika auri naki mijin he was jobless too da yar secondary school dinsa but mun hanaki? Mun kirasa jobless? Look at him today he’s among the few best businessmen we have here a Bauchi, that Hamad is better than mijinki asanda kikai aure, shi at least yanada kwali har masters garesa, kuma yana aiki so many abubuwa na online, gashi hafizin Al Qur’ani, ga ilimi ga natsuwa, so don’t be suprise idan yara kalansu becomes president tommorow Salima! Dan hakin daka raina shiyafi tsole idanu” muryan Mom na shaking but ta hana kanta kuka cus she’s a strong woman, and Baba is too small to hurt her saidai ita tai hurting wannan mara ilimin tace “Yaya hardakai aka yaudareni yanzu? This is unbelievable” cikin zafi Alhaji Mahmood yace “kika yaudari kanki dai and lemme tell you this as a brother tun wuri ki maidama mutanen nan gidansu, zunubanki da hakkin kanki are way too much that you’ve already started paying for them ina gujemiki ki kara dana gado, dan haka return that gidan gado to them” yadanyi shiru saikuma yace “Salimah” dadan takaici yakira sunanta saikuma ahankali yace “Salima wat is wrong with you? Open your eyes mana and look at mutumin dakikema all this rashin mutunci? Muhammadu Sani ne fa? Mutumin nan supported you all through career naki, he sponsored your education, wace kasa ne bawan Allah nan bai kaikiba? He loved you regardless of yanda bakison yan uwansa da basu miki komiba, saisa ya karo miki aure, I don’t want to see you kin rasa komi, ni kadai kikeda shi we are orphans bamuda Mama ba Baba kar zuciyan nan naki da girman kai yakaiki kirasa komi miji da yaranki please Salima kinji, me kikeso ne haka? Shaidan sai kada miki ganga yake yana taka rawa, Salimah” Alhaji Mahmood yayi maganan cikeda lallashi yace “Salimeme” yakirata da sunan tsokana, ijiyan zuciya Mom ta sauke tace “all this things dakake gayamin daga baya kenan, tunda har za’a kiraka a sanar dakai batun aure u will not call me and tell me ina sister ka and katako kazo gidan nan ayi komi agabanka you didn’t give me hint yanzu kazo kanamin Salameme kaman kana sona, Yaya do you know how painful it is a aurar da yarka kana mahaifiyanta baka sani ba? I’m highly disappointed in you Yaya ka nunamin waye naka, I am not your sister kaje ka nemi wata” zata zare wayan daga kunnenta Alhaji Mahmood yace “Salima wai kin dauka tsoronki koko shakkan ki akeji?” Dakatawa Mom tayi bata katse wayan ba Alhaji Mahmood yace “sabida kowa na miki shiru shiru ana kyaleki kina yanda kikaga
dama baya nufin ana tsoronki and lemme tell you this, yes ban fadamiki ba sabida ni kaina I was happy inaso Asmeey tafita daga hannunki, tayaya zaki hada yarinya da wannan yaron Fawaz waye baisansa anan Bauchi ba? Wlh wlh da ko Babansu ya yarda ya aurama Fawaz ita ni saina hanasa wat nonsense is something wrong with you sabida kinga ina lallabaki? Me Asma’u tamiki dazaki iya hadata da kasurgumin dan iska suje wani wuri? Salima yarda kika haifa fa da cikinki kin tsana konine saina aurar da diyar for peace kuma kice ba’a İsa a gwada miki kinyi ba daidaiba, this is the problem of girman kai yafara shiga brain dinka, you feel kinfi karfin amiki fada, yaron nan saida ya karya Asma’u he almost raped her Allah ya takaita but still he traumatized that poor girl akan me mahaifinta bazai aurar da itaba? Gwara daya hadata da cousin dinta so just shut up ki dauki takardun gidansu ki kaimusu inba hakaba nan gaba idan karma ya cimmiki don’t come running to me for help you are 47 not 27, ke ba yarinya bace go and ask mijinki for forgiveness ki basa gidansa ku shirya, he still loves you tunda saki daya yamiki da nine da uku zan danna miki” Alhaji Mhamood yakatse wayan Mom takara kamawa da wuta wani zuciya na ingizata taje tama Baba rashin mutunci tama koresa ya tattara matarsa da yaransa subar gidan but kuma she feels bazata iya zaman gidan just she kaman mayya ba kuma tasan tana koransa abin zaimai ciwo dan gidan nan means alot to Baba but kuna yanada wasu gidan da zai maidasu abinda taketa contemplating kenan.
Ta zauna tai shiru tana saka da warwara sai kawai ta daga waya number Asmeey tai dialing amman baya shiga ta ijiye wayan tanajin wani takunkumin bakın ciki awuyanta data rasa yanda zatai dashi tana kara cewa “ni Babansu Aya zai aurar da Asmeey batare daya sanar dani ba”.

WAYYOOO MOM BABA YA KYAUTA DA MARIN NAN?
💫UWA KO UKUBA?💫



✍🏻M SHAKUR



EPISODE 2️⃣6️⃣

Tundaga gidan nan kuka Asmeey take akirjin Hamad har suka shiga hanya kuka take, she's crying about many things tsinuwowin da Mom tamata, sakin Mom dataji Baba yayi, marin Mom dataga Baba yayi, she's blaming kanta for everything cus tasan sabida itane komi yafaru, her biggest fear shine Mamanta da Babanta basa tare, she wants both her parents together, Babanta slapped her Mom all because of her, fitowa tayi daga jikinshi takoma gefe daya tanaji kaman an ijiye mata dutse a kirji, hatta Mamie bata mata magana ba cus kowa yasan she needed to cry this cry sabida taji dadi, aiko tayi harta gaji chan ta dago kanta tana share fuskanta tana kallon hanya tai lamo a kujera ijiyan zuciya kawai take saukewa, ko 3min batayi ba wani wahalallen bacci yayi awon gaba da ita, Mamie tadan leko daga gaba jintai shiru tace
"Alhamdulillah tasami bacci" takalli Hamad da kansa ke kasa baka gane wani state yake ciki sai batace komiba tamaida kanta gaba, Faisal bini bini yana kallosu ta mirror, cikin bacci Asmeey tawani kwanto tashi daya kanta yayi resting akan shoulder sa dasauri yajuyo yadan kalleta sai yadauke kai da sauri kunya tawani irin kamashi sabida Mamie da Ya Faisal dake gaban motan, dan satan kallon Asmeey yayi she's deeply asleep hawaye duk sun bushe a fuskanta, sai ijiyan zuciya take saukewa na kuka, lips dinta sunyi so pinkish tana kamshi that's simple mai dadi tana sauke ijiyan zuciya na wayanda sukai kuka sosai, taba Mamie Ya Faisal yayi asace irin ta kalli baya tagani, Mamie ta kallesa da baki yamata alamu ta kallesu ganin bata gane meyake cewa ba, dakuwa Mamie tamai da hannu alamun kaci mai garinku, turo baki Ya Faisal yayi ganin Mamie batada wassup da Hameed ne da yanzu sun sami chapter, Mamie tabude littafin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login