Showing 30001 words to 33000 words out of 56573 words

Chapter 11 - Bamagujiya By Oum Hairan

15 Dec 2025

6926

tumurmusa ya ɗauki waya ya kira wayar Sarkin gda yabashi umarnin turo masa Jakadiya yanzun nan.
Bata ɓata lkc ba kuwa ta iso ta kalleshi ta kalli Beebah ta sunkuyar dakai ita fah wannan abun ya fara buga mata kwanya musamman lkcn daya miƙa mata zanin gadon yace “ki haɗa da wancan kiyi musu ajiya me kyau zamu bukacesu idan lkcn hakan yayi"



_Idan kika karanta min littafi baki biyani ba ban yafe Miki ba, idan ka/ki karantamin littafi a YouTube batare da izinina ba Allah ya fitarmin da haƙƙina a kanki/kanka da gaggawa_
[5/2, 7:34 PM] AM OUM HAIRAN: BMGJY 25-26



Taƙabbalallahu Minna Wa Minkum.....May Allah subhanahu wata'ala Allah accept all our Ibadah forgive our sins and purify our souls...Ameen Eid Mubarak...

*FOR SALLAH PROMO*


Don ci gaba da karanta wannan littafin ki biya ta 3184512451 Fauziyya Tasiu First bank, ko hoton kati MTN ta WhatsApp number 09013718241 idan a Niger kike zaki tura katin Airtel na 400CF ta wannan number +227 95 04 58 22 sai kiyi screenshot ki turomin nasaki a group.


★★★~~~★★★~~~★★★


Miƙewa Jakadiya jayi ɗuwawu a salike ta fice ta nufi sashinsu a hanya suka haɗu da Larai ta jata suka nufi can bayan gidan Jakadiya tace “Larai bakina da salama nifa kaina ya kulle da wani abu dake faruwa a gdannan" zama Larai tayi tace “Akan Yarima Habeeb kikeson mgn ko? Jakadiya ina tsoronki uhm barima naja bakina na samasa saƙata bazakiji a bakina ba...."
Riƙota Jakadiya tayi tace “Zo fa muje ki gani" dakin Jakadiya suka shiga ta dauko zanin gadon ta ware mata ta rintse idonta da sauri Jakadiya tace “Ni kaina ya kulle yau da safe ya kirani yace na bata kulawa sannan na ajiye wannan za'a nemeshi yanzu kuma ya kuma kirana ya bani wannan to me hakan yake nufi? kodai fyaɗe yayiwa ƴar mutane?....." Rufe mata baki Larai tayi tace “bazai kasance haka ba kinsan akwai jumurɗarsu da mai martaba akan auren wata bamagujiya da yazo yace yanaso Mai martaba ya kori ƙudurin harma yaci alwashin indai yana raye ya haramta masa ita har abada ko?"
Jinjina kai Jakadiya tayi Larai ta kara yin ƙasa da murya tace “Banfa tabbatar ba amma raina yana faɗamin itace wannan yarinyar to amma kuma ai Kilishi tace ƴar' ƙanwarta ce to in hakane kenan ta bakin naki fyaɗe yayi mata?"




Yarfa hannu Jakadiya tayi tace “To biri yayi kama da mutum to amma kuma idan farko fyaɗe ne yanzu kuma da naje na tarar dasu a wani yanayi menene?" Hannu Larai tasa ta rufe bakinta tace “Uhm! Larai jikar me koko samawa kanki salama kar naje nayi ta albashi na" Jakadiya ce tace “Abin fah da daure kai ta bakin naki anya yarinyar nan babu wata ƙullalliya a ƙasa don alamu sun nuna Kilishi tasan komai"
Hanya Larai taci tana cewa “nikam abin faɗa na ya ƙare keda kike da abin taunawa saiki zauna kita tunanin rashin tabbas" harararta tayi tabita da masifa tace “Kedai kika sani tsohuwar kawai"


*******


Tunda ya fita ya barta kalamansa sukeyi mata yawo a kwanyarta zuciyarta tayi duhu suma a yau zasu tashi zuwa Umrah da dare lumshe idanunta tayi tace “lkc baija ba amma na fara gajiyawa da wannan ƙuntacciyar rayuwar yaushe ne zan bayyana matsayin mata kamar kowacce mata?"
Kawar da tunanin tayi ta hanyar ɗaga wayarta da take ring ta kara a kunnenta tace “Rasheedah!" Ajiyar zuciya Rasheedah Turaki tayi tace “Tun jiya da dare nake kiranki bana samunki yanzun kuma muryarki ta bayyana min kinada damuwa Habeebah Ni marainiya ce banida uwar da zan tattauna damuwata da ita da Allah ya haɗani dake sai naji na samu sauƙin wannan ciwon saboda kina bani shawara ta hankali ina kawo Miki matsalata kiyimin maganinta HH meye matsalarki don Allah?"
Lumshe idanunta tayi tasa yatsanta ta ɗauke hawayen fuskarta tare da ƙoƙarin kumbura zuciyarta da juriya tace “Kar...karki damu Rasheedah wannan damuwar lkc ne kawai zaiyimin maganinta ke meye taki damuwar don nasan kawai bazatasa ki rinƙa kirana a lkcn da nake cikin ƙila wa ƙalan rayuwa ba"




Jan zuciya tayi tace “Prince Habeeb Khalil..." Wata muguwar faɗuwa gaban Beebah yayi ta miƙe zaune tace “Ya haka? Meye yayi Miki..." Murmushi Rasheedah tayi tace “A zahiri baiyimin komai ba baɗini ne da matsala bansan komai game da soyayya ba tun ranar da muka zo da Captain gurinki idanuna yayi tozali dashi nakejin rayuwata tana cikin wani yanayi na neman tallafinsa wlh zuciyata ta kamu da muguwar ƙaunarsa ta yanda bantaɓajin zan iya hƙr dashi daidai da rana ɗaya ba....."
Slow numfashi Beebah ya rinƙayi tana ƙoƙarin daidaita shi yana ƙara ƙwacewa kanta na wata irin sarawa tashin hankali na ratsa duk wata kofar jini ta jikinta cikin mutuwar jiki da rawar murya Tace.
“Hab... Habeeb Rasheedah!?" Cikin karayar zuciya Rasheedah tace “Yeah it's true Habeebah inason cousins ɗinki Habeeb....."




Rintse idanunta tayi tanajin kalmar inason cousins ɗinkin kamar watsuwar ruwan zafi a jikinta ta ajiye wayar kawai batare data iya sanya hannu ta kashe ba ta koma ta kwanta duk ilahirin jikinta ciwo yakeyi da haka Kilishi ta shigo ta sameta ta ɗago idanunta da suka kaɗa sukayi jawur ta saukesu akan Kilishi dasu Hudah Hudah ta matsa tace.
“Sannu Sis ɗazun nazo naji ƙofar a rufe halan kina bacci ne?" Iska ta furzar ta kawar dakai tare da sanya hannu ta share hawayenta wayarta nata ring ta kasa ɗagawa sai Khalisee ce ta ɗauka tace “Yane Rash?" Kallon Beebah tayi ta miƙa mata wayar ta karɓa ta kashe hakan ya tashi hankalin Rash wannan shine karon farko da Beebah ta kashe mata waya hakan ya hanata nutsuwa ta ɗauko mota ta fito batare da kowa ya sani ba ta nufo gidan sarautar.
A dakin Kilishi kuwa babu hankalin wanda bai tashi ba yanda duk dauriya da basarwa na Beebah ta kasa jurewa ciwon da kecin Zuciyarta ta kifa kanta saman katifa take wani kuka me cin rai, rarrashin duniya taƙi yin shiru ganin abin nata bana nutsuwa bane yasa Kilishi ɗaukar waya ta kira Habeeb yana gaban Mai martaba lkcn ganin me kiran yasashi miƙewa yana cewa “Shikenan Allah ya taimake ka amma fah bazan fasa jaddada maka ba banason wannan haɗin ku barshi zaifi alkhairi idan kuma kun dage kuyi abinda zai faru gaba kuma nima bansanshi ba saboda raita Habeebah kawai takeso....."




Binsa Mai martaba yayi da kallo tare da ayyana abubuwa da yawa a ransa yaja ƙwafa yace “Bantaɓa hukunci Anja ba sai a kanka kasani Habeeb bazaka taɓa samun wannan bamagujiyar ba zansa a ɓatar da ita a duniya tunda ta kasance silar saɓawa umarnina"
Habeeb part ɗin Kilishi ya nufa ya ishe su sun sata a gaba sai aikin rarrashinta sukeyi da tambayar abinda yasata kuka amma taƙi magantuwa ya taka ya tsaya akanta suka janye ya tsugunna gaban gadon ya dafa kanta yace “Habeebatullah" janyewa tayi ya fincikota da karfi ta wuntsilo jikinsa ya ɗago kanta ya sanya Harshensa ya lashe hawayen tare da jorner bakinsa cikin nata ta saki ajiyar zuciya me ƙarfi tasa hannunta tana tureshi.
Kallon kallo aka shigayi tsakanin Hudah Khalisa da Rasheedah Da ƙirjinta yake bugawa da ƙarfi wani abu yana tasowa daga ƙasan Zuciyarta ta kafesu da idanunta cikin tsoro tace “Ya hayyu ya ƙayyumu...." Janye bakinsa yayi daga nata yana shafa sumarta yayi musu wani irin mugun kallo da basu Hudah ba hatta Rash Saida ƙirjinta ya buga sumsum suka fice daga ɗakin, yayi ƙasa da muryarsa yace “Meyene to ko tafiyar ce kikeso na fasa?" Ajiyar zuciya tayi ta girgiza masa kai yace “Uhm inajinki faɗi ayi Miki yanzu uwar ƴaƴana" sake lafewa tayi a jikinsa tace “Idan kace kanasonta mutuwa zanyi...." Da sauri ya dago a firgice yace “Wa?" Sharrrr hawaye ya sulalo mata ta janye a jikinsa tace “bansanta ba kawai inajin kamar wani abu na shirin faruwa dani da zai iya zama ƙarshen alaƙata dakai Hero idan na rasaka ina zan kama?"




Tausasan yatsunsa yasa ya rufe mata baki yace “don Allah ki bari banson wannan muguwar fatan naki Habeebah duk da cewa akwai ƙura a gabanmu amma bantaɓa jin akwai ranar rabuwa tsakaninmu ba wlh ko zan rasu akanki na shirya daga jiya zuwa yau na ƙara tabbatar da cikar darajarki wadda a duniya babu wata mace da zata zomin da kalarta inganta bare har na tantance, Wyf kin zama sirrina Nima na zama naki ke kaɗai wlhl Azeem matsayinki bazai taɓa daidaituwa da wata ɗiya mace a duniyar nan a zuciyata ba ki riƙe wannan a ranki duk inda Hero ɗinki yake yana tare dake a zuciyarsa....."
Hugging ɗinsa tayi tayi kissing lips ɗinsa tare da lumshe idonta tace “Same to you and double love you...." Sake haɗe bakinsu yayi ta janye tanajin wani mugun tsoro saboda yanda taji Sandarsa tana wani yunkurin miƙewa ta kuwa shammaceshi tayi fit ta fice, yayi murmushi ya miƙe yana saita kansa ya fito parlourn bai ganta anan ba hakan ya tabbatar masa ɗakinta ta gudu....




Rasheedah ce ta buɗe ƙofar ta shiga ta tsaya jikin ƙofar ta zubawa Big hips na Beebah idanu itanma kallonta takeyi ta cikin mudubi Rasheedah ta tako ta iso bayanta ta tsaya idanunta kafe akan Beebah ta zatayi mgn tayi saurin dakatar da ita da cewa.
“Zan iya sadaukar da kowanne farin ciki banda shaƙuwata kuwa rayuwata Rasheedah ke ƴar gata ce koda mahaifiyaarki ta mutu ta barku cikin gata gaban mahaifinku me sonku da baku kulawa nikuwa nawa iyayen suna a raye amma sun barratani da kansu saboda bambancin addini al'ada da kuma aƙida da kuma uwa uba rashin sanin haƙƙin zuciya,
Rasheedah na yarda shine ƙaddarata abinda yake faɗamin kullum Nima nice ƙaddararsa bansani ba ko gaske ne duk da inajin a raina Bazaimin ƙarya ba yanajin fiye da abinda nakejin akansa. Rasheedah Habeeb Shine Rayuwata shine ƙaddarata kuma shine duniyata ki sani duk wanda ya shiga tsakanina dashi zai zama silar yankewar numfashina....."
Zama Rasheedah tayi saman kujera saboda jirin da taji yana ɗaukar ta tace “Meye alaƙarki dashi?" Sunkuyar da kanta tayi tace “Mijina ne....." “Wht?" Ta faɗa tana miƙewa itama ta miƙe tace.




Na daɗe ina faɗa Miki Ni matar aure ce kina banzatar da furuci na Rasheedah auren Hero shine ya kawoni Masarautar Dutse a matsayin ƴar aiki ya kawoni Kilishi tace nafi nan ta bayyana Ni matsayin tsatso cikin tsatsonta sunana matar aure ba kamar kowacce mata ba domin kowacce mata dangin mijinta sun santa a matsayin mata, Ni kuwa kilishi ce kawai ta sanni matsayin suruka amma ko abokaina su Hudah basusan matsayina a wajen yayansu ba duk da cewa sun jima da ɗora ayar tambaya akansa game da lamari na, kiyi hƙr bansan cewa zakis....."
Rufe mata baki tayi tana murmushi tace “nice ya kamata na baki hƙr da nayi azarɓaɓin furta Miki kalamin daya tayar da hankalinki akan mijinki Wlh da wata ce ba ke ba da har gaban abada abotarmu ta watse kiyi hƙr Habeebah inda gaban abada na cire mijinki a raina zan tayaki addu'a ku rayu cikin aminci dashi....."



_Idan kika karanta min littafi baki biyani ba ban yafe Miki ba, idan ka/ki karantamin littafi a YouTube batare da izinina ba Allah ya fitarmin da haƙƙina a kanki/kanka da gaggawa_
[5/4, 8:11 PM] AM OUM HAIRAN: BMGJY 27-28
_Masu buƙatar a tallata musu hajojinsu ku yimin mgn cikin farashi me sauƙi👌🏼_

_Haramun ne a juyamin wannan labarin ta kowacce siga ko a karantamin shi a YouTube channel_


_Alhmdllh daga wannan Page ɗin na gama happy sallah duk me so saiya bi hanyoyin dake ƙasa ya biya ya karanta cikin aminci_




_Don ci gaba da karanta wannan littafin ki biya ta 3184512451 Fauziyya Tasiu First bank, ko hoton kati MTN ta WhatsApp number 09013718241 idan a Niger kike zaki tura katin Airtel na 400CF ta wannan number +227 95 04 58 22 sai kiyi screenshot ki turomin nasaki a group._


_Please don Allah kiyi hƙr idan baki shirya ba karki min min kiga kamar na wulaƙantaki wallahi ba wulaƙanci bane mutanen ne da yawa very important nake bawa attention in littafi kikeso 300 Spcl 700 evidence of payment kawai ya wadatar idan talla kikeso page 1k status 500 per day👌🏼_


★★★~~~★★★~~~★★★



Kama hannunta Rasheedah tayi ta zaunar da ita itama ta zauna tace “Amma meye yasa aurenku ya zama a haka meye alfanun ɓoyewar?" Kawar dakai tayi tace “Wani sirri ne daban idan lkcn sanin yayi zaki sani saidai Nima banason wannan yanayin kawai dai naji na karɓa nayi biyayya ne badon son raina ba sai dan hakan shine ya dace da nayi"
Daga haka ta miƙe ta nufi bathroom wannan ta tabbatar wa da Rasheedah Beebah bazata ƙara cewa komai ba, ruwa ta watsa ta fito lkcn bakwai na dare ta ishe ƴammatan sun shirya suna jiranta a ɗakin Khalisa tace “Haba kekuwa Beebah kinsan takwas da rabi zamu tashi amma kinyi bulunbuƙwi a ɗaki ko tunanin kada mu makara bakiyi" lumshe idanuwanta tayi ta ɗauki kayanta tasa ta tayar da sallah bayan ta idar ne ta dubesu tace “Afwan nafa ɗan shiga yanayi ne muje waye zai kaimu airport ɗin?" Haushi bai bar Khalisa ta bata amsa ba tayi ficewarta itama tabi bayanta Hudah na cewa.
“Waini gurɗewa kikayi a ƙafarki ne naga bata takuwa sosai?" Itadai bata bata amsa ba tayi ficewarta suka shiga Mota Kilishi nayi musu fatan alkhairi suka wucce airport Beebah Zuciyarta tab tunanin Hero ɗinta shima yanzu haka yana can yana keta gajimare.




Da wannan tunanin suka isa airport ɗin duk wani abu da akeyi akayi musu sukayi zaman jiran cikar lkc sannan jirginsu ya ɗaga zuwa birnin Jidda, tunda suka taho kanta ke juyawa har suka sauka Ita dai ƴar kallo ta zama har sukaje masauki ta rage kayanta ta kwanta gajiya ta rashin sabon doguwar tafiya na tambayar jikinta.
Sun kwanta sun huta gajiya sosai kafin Hudah ta fara tashinsu tana cewa “Ku tashi kuyi sahur kada ku makara" Khalisa ce ta fara tashi sannan Beebah suka ɗauro alwala sukayi sahur ɗin duk jin abin takeyi bawai, karonta na farko a rayuwarta da zatayi azumi, bayan sun nutsa ne sukayi raka'atainul fajri suka gabatar da asuba sannan suka sake kwanciya bacci me nauyi sukayi har wajen azahar sannan suka tashi sukayi wanka suka nutsa cikin garin Beebah ta zama ƴar kallo koda sukaje shop na abubuwan da zasu buƙata komai sune suka ɗaukar mata tana gefe manne da waya tana waya da Hero ɗinta tanata dariya sukan banda kallonta babu abinda sukeyi suna mamakin yanda yanayinta ke nuna nutsuwarta da wanda take wayar dashi.




Koda taga sun nufota saita kashe wayar babu wanda ya tambayeta domin sunsan ko sun tambayeta ba amsa zata basu ba saidai tayi murmushi ta basar dasu.
Cikin kwanakin ibadar da sukayi a ƙasar Saudiyya Hudah da Khalisa sunji daɗinsu Ita ko tunda sukayi sati biyu ta fara rasa walwalarta saboda wani irin yanayi da ya sarketa bacci da kasala su kansu abokan tafiyar tata Saida abin ya fara damunsu ganin ko masallaci sukaje wani lkcn saidai in sun gama abinda zasuyi su tasheta.
Satinsu uku a Saudiyya suka wucce Dubai tunda sukaje Dubai kullum yanayinta ƙara ta'azzara yakeyi ko abinci bata iya cin na kirki da suka gaji ne suka shirya domin zuwa suga likita batare da tunanin komai ba saboda ƙuruciya zuciyarta bata taɓa kawo mata komai ba ta.
Haka ta rinƙa bawa likitar amsa tana rubutawa gwaje-gwaje tayi mata masu yawa sannan ta biyosu reception inda suke zaune dake Khalisa ce jagorar zuwa asibitin ita likitan ta kira tayi mata bayani bayanin da ya nemi kai Khalisa ƙasa saboda kaɗuwa da tashin hankali ta dubi Beebah gabanta na tsananta faɗuwa tace .
“Ku tashi mu koma masauki" yanda tayi mgnr a hargitse yasa Hudah miƙewa itama Beebah ta mike suka nufi motar data kawosu suka shiga babu me cewa wani har suka ƙarasa masaukin.
Suna isa Beebah ta samu ƙasan tiles ta kwanta tana ajiye numfashi kasancewar ko yaya tayi wani motsi me wahala sai tayita haki ko kuma ta rinƙa jin kanta na juyawa.



Bata gama saituwa wa ba ta tsinkayo Muryar Khalisa na cewa “Tabbas mutum ba abin yarda bane mutum bashi da kyau ko kaɗan nikam bansan da wanne bakin zan fara furta wannan mugun labarin ba, waima dan Allah Habeebah meye ya jaki ga aikata wannan mummunan aikin har tabonsa yake neman tsira a jikinki?"
Tunda Khalisa ta fara mgnr Beebah ta kafeta da idanu batare data fahimci inda zancen Khaly ya dosa ba, batakai ga magana ba Hudah tace “Wai don Allah meye ne yake faruwa kike ta yi mana hanya-hanya Ni wallahi banason zanje da jan lafazi kawai ki faɗa musan abinyi tun muna mu uku kafin mu zama mu huɗu"
Da sanyi jiki Khalisa ta zauna ta dubi Hudah tace “Huddatu binciken ƙwararrun likitoci ne ya tabbatar da Habeebah tana da shigar juna biyu na kwanaki arba'in da biyu...." Basu aune ba sukaga Beebah a tsaye cikin tashin hankali tace “Innanillahi Khalisa dan Allah daina banson wannan wasan ciki kuma...?" Miƙewa Khalisa tayi tace “Hakane cikine dake Habeebah Ni dama tun farkon yanayin da lalurarki ta fara nunawa zuciyata ta karye amma sai na danneta saboda bakiyi kama da wacce zata aikata ba Habeebah waye kika yarda ya cutar da rayuwarki haka har ya ɗura Miki me zafin?"




Cikin kuka tace “Garin yaya meye yake shirin faruwa dani hakane ciki fah ni Habeeba...." Kukan da yaci ƙarfinta ne yasata katse maganar da take yi ta miƙe ta nufi ɗaki da gudu saboda aman da yake taso mata ta faɗa bathroom ta rinƙa shekashi kamar zata amayar da hanjinta.
Hudah itace taje ta taimaka mata ta gyara jikinta suka fito ta kwanta kan gado tana nishin wahala zuciyarta na zafi kanta na juyawa batajin haushin Habeeb akan komai ƙoƙarin ganin ya gujewa ɓacin ran mahaifinsa ne yasashi barinta a matsayin daya barta ita kuma gashi ta raba gari da Mahaifanta akansa.
Kuka takeyi sosai harda shassheƙa Khalisa ta shigo ta zauna a kusa da ita ta sanya hannu ta share mata hawayenta tace “Kinyi kuskure da kika amincewa yaudarar maza har kika sallama mawa wani fasiƙin kanki yayi Miki babbar illah yanzu ba lkcn kuka bane Habeebah lkcn neman mafita ne kafin lkc ya ƙure mana gsky akwai babban tashin hankali idan muka koma 9ja da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login