Showing 51001 words to 54000 words out of 56573 words

Chapter 18 - Bamagujiya By Oum Hairan

15 Dec 2025

6923

“Wai Beebah banan tazo ba Baba?" Duk da Baba Jimo yana cikin halin tsananin fushi Saida gabansa ya faɗi yace “batazo ba ina tayi cemaka tayi zatazo nan?"
Hannu Habeeb ya zuba a kansa yace “Na shiga uku Ni Habibu Habeebah ina kike....."




Cakumarsa Baba Jimo yayi yace “Na rantse da abar dogarona kamar yanda ka ɓatar min da Bibo kaima labarinka saiya shafe saina ɓatar dakai...." Shi baima damu da riƙon da yayi masa ba hawaye kawai yake shara yana cewa “Mai Martaba ka cuceni ka wargatsamin gda ka tafi da farin cikina, yanzu ina Beebah tashiga ita ba cikakkiyar lafiya ba?"
Fir Baba Jimo yaƙi sakin Habeeb kawai sai huci yakeyi yau ga ranar yayansa Uda gashi mutuwa tayi gaggawa, daƙyar mutane suka raba hannun Baba Jimo da kwalar rigar Habeeb rigima ta sarƙe shi Habeeb na roƙonsa ya bashi matarsa idan yasan tazo shi kuma yana rantsuwar saiya fito masa da yarsa rigima har gidan Dagaci koda Dagaci yaji abinda ke faruwa a bakin Habeeb hankalinsa yayi mugun tashi shima tabbas abin akwai tashin hankali gashi babbar damuwar baasan inda za'a nemi Beebah ba.
Duk yanda Dagaci yaso Baba Jimo yabar Habeeb ya tafi yaji da damuwarsa hanawa yayi Saida Dagacin yasa aka kira irin bokayensu na tsubbu suka tabbatarwa da Jimo Habeebah tananan cikin aminci kuma zata dawo saidai basusan inda take ba, to sannan ne fah hankalinsa ya kwanta yabar Habeeb ya tafi amma da sharaɗin duk inda Habeebah take ya nemo masa ita tunda ubansa bayason zamansa da ita to ta gama aurensa har abada.
Shidai bai bawa mgnrsu muhimmanci ba burinsa kawai sanin inda Beebah take, hakanan ya ɗauki hanyar Dutse ikon Allah ne kawai ya kaisa gida kai tsaye ɓangaren Khausar ya shiga ya tarar da ita taci wanka sai faman taunar cingam takeyi kamar karuwa.





Babu furuci ba komai ya ajiye mata takarda a cinyarta ya fice daga ɗakin da sauri ya nufi ɗakin Beebah ya faɗa gadonta yaja rigarta ya rungume a ƙirjinsa numfashinsa na ɗaukewa yana janyoshi da ƙyar yanda zuciyarsa ke masa zafi a yanzu
Haka baya buƙatar kowa a tare dashi ji yake yi ma kamar ya tashi yabar garin, zuciyace ta bashi shawarar dole ma ya bar garin da daren ya tattare komansa washegari daga masallaci ya ɗauki mota sai Abuja Saida ya shiga cikin garin Abuja ya kira babban amininsa da sukayi karatu dashi a Oxford cikin murna engineer Wali yazo ya taroshi daga yanayi ya fahimci Habeeb na cikin damuwa haka dai suka ƙarasa gdansa zama Habeeb yayi ya dafe kansa da yakeyi masa wani mugun ciwo, dafashi Wali yayi yace “Nayi mamakin ziyararka ta bazata haka duk da dai yanayinka ya nunamin baka cikin nutsuwa shin ko zan iya sanin meye ke faruwa?"
Iska ya furzar ya miƙe ya nufi wani ɗaki ya buɗe ya shiga bathroom ya watsa ruwa yana fitowa ya kwanta zazzaɓi na sauko masa me zafi.




Shigowar Wali ce ta sashi sake jan bargo Wali ya janye yace “wai meye yake faruwa ne Habeeb ina matanka ko wani abu ya faru ne?"
Numfashi ya sauke me huci yace “Ka kiramin likita" baiyi masa jayayya ba ya dauki wayarsa ya latsa wayar cousins dinsa Dr Al'Amin yayi masa bayani yace masa ok yanzun yanakan wata petiant ne amma yana gamawa zaizo. Haka sukayi sallama ya aje wayar sukaci gaba da zaman kurame Wali ya gaji yace “Don Allah ka faɗamin meke faruwa ina Hudais da mamansa?" Zubawa Wali ido yayi can yace “Bansan inda Habeebah take ba tafiyar da nace maka nayi zuwa Lagos wasu abubuwa suka faru har yasanya Mai Martaba yanke hukuncin sakarmin mata da bakinsa bada nawa ba kuma ya ƙwace mata ɗanta ɗaya data ɗauki so ƙauna da burin duniya ta ɗora masa ɗan da takejin zata iya rabuwa da komai dominsa Zubair Habeebah na sona amma na tabbatar da a yanda take da haƙuri da kawaici kuma a lkc guda idan hƙrnta ya kare take da kafiya Wallahi ba zata nemeni ba koda kuwa sona zai zama silar yankewar numfashinta, meye yasa Mai Martaba zai rabani da zuciyata Zubairu Habeebah rayuwata ce inajin yanda zuciyata take zafi da zugin ciwo tsaf zata iya daina aiki indai babu Wyf a kusa dani Wanne taimako zaka bani ta dawo gareni Zubair don Allah Please help me....."
[5/20, 9:07 PM] AM OUM HAIRAN: _*BMGJY Bonus 47-48*_


_Ku biya ta acct detail 3184512451 First bank ko kati MTN ta WhatsApp number 09013718241._
_Normal 300 PC 700_
_Ƴan Niger zaku biya 500f ta wannan number +227 95 04 58 22_


_Ban amince a juyamin littafi ta kowacce siga ba_



Jinjina kai da girman lamarin Engineer Wali yaci gaba da yi can Habeeb yace “kasa na faɗa maka damuwata kuma kayimin shiru Shikenan tunda bakada abin faɗa kaje kaima kubarni na mutun in hankalinku zai kwanta...." Katseshi Wali yayi yace “Not ka gane Friend ina tunanin rayuwa irin taku ta gidan sarauta meyesa bakuson bare a cikinku ne meye yasa kuke yanke hukunci da son rai Wallahi duk da cewa bantaɓa ganin Maman Hudais ba amma zuciyata bata amince zata aikata wannan abinda akace ta aikata ba haba shi Mai Martaba hankalinsa ne ya gushe ko kuwa rufa ido akayi masa yarinyar da batasan kowa ba sai kai da Ahlinka yarinyar da kai da kanka Saida kukasha ƙwarbai kafin ta amince dakai har ku fara gudanar da Sunnah da ita yarinyar da kowa ya sani ko ƙawa bata taɓayi ba sannan batada fitina kullum cikin nutsattsen yanayi take Habeeb wato kayi gaggawa daka datse igiyar aurenka dake kan ƙanwarka Khausar inada yaƙinin ita tasan komai kuma bazai wucce shiri da tuggunsu ba"





Numfashi ya sauke yaci gaba da cewa “Kai akaso a dasawa kokwanto tsana da ƙyamar Maman Hudais sai aka ga wannan bazai yiwu ba domin bakai ka dasawa kanka yarda da soyayyarta ba shine aka juya lamarin kan Mai Martaba ta yanda zaka tabbatar da abin shiri ne

Meye ya kawo Mai Martaba gidanka a wannan lokacin kuma meye yasa ba'a bari anji abinda ita Beeban zatace ba sannan meye yasa ba'a kiraka ba domin sanar dakai a daidai lokacin? To duk waɗannan abubuwan abin dubawa ne amma bamu da lokacin dubasu kawai ta ina kake tunanin zamu fara neman yarinyar nan?"
Taɓa ƙofar akayi hakan ya dakatar da hirar tasu Engineer Wali ya tashi ya buɗewa Dr Al'Amin ya shigo yana duban Habeeb sukayi musabaha ya dubi Wali yace “Bro wake ba lafiya?" Kallon Habeeb Wali yayi yace “Gashinan abokina ne da nake baka labari munyi karatu a Oxford dashi ya fara karantar harkarku mahaifinsa Sarkin Dutse yasa ya juya zuwa ɓangaren mu kaganshi nan ciwon soyayya ne ke wahalar dashi ko kunada maganin matsalar?"
Murmushi Dr Amin yayi yace.




“Turƙashi lamari ya ɓaci kenan ciwon so akwai wahala Nima gashi ina neman faɗawa a karo na biyu duk da dai inata kwaɓar zuciyata kada ta shigar dani inda bazan fito ba" yana maganar yana gwada BP ɗinsa ya dubeshi da sauri yace “Ya Salam Engineer ka rage wannan damuwar kaga yanda BP naka yayi sama kuwa?
Gaskiya ka rage damuwar komai zai wucce insha Allahu girgiza kai yayi ya sharce hawayen dake ƙoƙarin zubo masa yace “Kayi aikinka kawai babu wani abu da zai iya rabani da wannan damuwar sai dalilinta" daga haka bai kuma cewa komai ba Dr Amin ya gama rubuce rubucensa ya bawa Wali ya juya yana cewa “Ka kula da kanka Please akwai yanayin hauhawar jinin da ka iya haifar da komai Allah ya shiga lamarin" amsawa Wali yayi suka fita tare har asibitin suka sayi maganin sannan ya juyo yana mamakin yanda yayan nasa bashi labarin yanda akayi ya sami petiant ɗin tasa da ya dauki kulawar duniya ya ɗorawa.




Komawa yayi tare da yima Habeeb bayanin magungunan ya karɓa ya zubesu Saida ya takura masa sannan yasha maganin yaci gaba da jinyar jikinsa tare da baza cigiyarta jaridu talabijin da rediyo duk da kasancewar Amin ɗan nacin karanta jaridu kwana biyun yanayin jikin Beebah da kuma rashin lokaci yasa baisan wainar da ake yi toyawa ba.
A haka Beebah Saida ta shafe kwanaki arba'in a asibitin tana jinyar ƙafarta sannan taji sauƙi sosai lokacin kuma cikinta ya fara bayyana sosai abinka da itan ba doguwa bace sosai shi yasa cikinta baya ɓuya watanni biyar kowa na iya ganinsa, Dr Amin dakansa ya yankar mata katin files na awo a asibitin sai lokacin ne ya fara tunanin ta yanda zaijewa da Safeenah maganar, koda ya tunkareta tayi masifar bashi mamaki yanda ta nuna ai babu komi ya kawota su zauna har zuwa lokacin da zatayi bayanin daga inda take ita da kanta take cewa dashi yarinyar ta bata tausayi daga ganinta wartako akayi daga gidan mijinta kodai asiri ko kuma bakin ciki ya hanata faɗar daga nahiyar da take.




Yaji daɗi sosai a ranar kuwa Beebah ta dawo gidan da zama Safeenah nata bata kulawa musamman dataga cikinta ya fara tsufa haka tayita zolayarta hardai ta saki jiki sukaci gaba da rayuwarsu a gidan gwanin ban sha'awa babu hantara bare kyara duk da cewa zuciyar Beebah na gurin ɗanta da mijinta amma haka take daurewa saidai idan kewarsu ta dameta ta shige ɗaki tayi kukanta ta ƙoshi idan Safeenah ta ganta ta rinƙa bata hƙr daƙyar Safeenah ta samu Beebah ta bata labarin abinda ya fito da ita daga gidan mijinta sosai Safeenah ta kaɗu da jin wannan mugun makirci ta tausaya mata taso ta faɗawa Dr Amin amma fir Beebah taƙi barinta ta rinƙa roƙonta tabarshi batason komawa gidan Habeeb akanta abubuwa da dama sun faru dashi gashi har mahaifinsa yanajin ta cancanci ya ari bakinsa ya saketa.
Ajiyar zuciya Safeenah tayi tace “Shirme ne kawai da ɓacin rai ai Shari'a ce kawai take da ikon sakarwa mutum mata shima kuma sai idan ya amincewa hakan, Beebah har yanzu kinanan matsayin matar mijinki kawai dai basu iskar yanada amfani amma dai don Allah karki azabtar da bawan Allah ki daina cewa bazaki komawa aurensa ba yayi don ke basani kema kinyi dominsa kiyi hƙr ki bayyana masa inda kike ko ya samu sauƙin damuwa kada kiyi kisan rai"



Batajin wannan magiyar abubuwa da yawa suke sata ƙin saurarar Safeenah idan ta tuna ta rabu da komai saboda Habeeb ta rasa komai sabodashi ta zaɓeshi fiye da iyayen da suka kawota duniya tabarsu tabisa amma ta kasa samun mafaka a gurinsa ɗan da takejin shine raba gardamarta shima sun karɓe sun barta batada tsuntsu bare tarko.
Takanyi kukan nadama da tunanin ta yanda zata tunkari iyayenta.
Kwanaki sukayita tafiya cikinta na tsufa har ta shiga kwanakin haihuwarta kullum sai sun fita motsa jiki Allah kuwa ya kawo mata haihuwar da sauƙi a gida ta haifi yarinyarta mace cikin dare ita kaɗai a ɗaki.




Sai bayan haihuwar ta kira Safeenah ta sauko tazo taga abin mamaki ta koma da gudu ta taso Dr Amin dakansa ya gyara yarinyar suka gyara maijego Safeenah ƙin komawa saman tayi ta zauna a gurinsu.
Karon farko taji tanason sanar dashi abinda ya shafeshi wayarta ta dauka ta latso number sa ta rubuta masa gajeren saƙo kamar haka.
_“Inayiwa Mijina fatan alkhairi da nasara akan duk abinda yakeyi yanzu, ina mai farin cikin sanar dakai yau ajiyar ka ta fito mun samu ƙaruwar ƴa mace....."_
[5/24, 8:42 PM] AM OUM HAIRAN: _*BMGJY Bonus 49-50*_


_Ku biya ta acct detail 3184512451 First bank ko kati MTN ta WhatsApp number 09013718241._
_Normal 300 PC 700_
_Ƴan Niger zaku biya 500f ta wannan number +227 95 04 58 22_


_Ban amince a juyamin littafi ta kowacce siga ba._



Tana gama rubutawa ta karanta tare da tura masa sannan tayi maza ta kashe layin.
Habeeb dake kwance saman kujera three sistar yaji shigowar saƙo kamar bazai buɗe ba ya gyara kwanciya, zuciyarsa taƙi nutsuwa ya ɗauki wayar ya buɗe saƙon baisan sanda ya tashi tsaye ba yana duba saƙon number babu suna ya sake duba saƙon yace “Habeebatullah kenan? Kece kika turomin saƙo?"
Da sauri ya fara kiran layin abin takaicin ta riga ta kasheshi wannan tasa shi zama daɓar tare da dafe kansa yana furta Innanillahi wa inna ilaihirraji'un sake gwada wayar yayi har zuwa lokacin a kashe ransa ne ya fara faɗa masa to ko ta koma Tsaunin gawo ne?
Da wannan tunanin ya tashi ya zari key na mota ya fice daga dakin komawa yayi ya zauna tare da duba agogo 3:20am yasani koda yake motar kansa ce ba ƙaramin ƙalubale zai fuskanta a garin Abuja kafin yace zaije Kano daga Kano ya ɗauke hanyar Tsaunin gawo kwanan zaune yayi asubar fari zakara ya bashi saa ya ɗauki hanya wajen goma ya isa Kano ya ɗauki hanyar Tsaunin gawo lokacin daya isa duk maza suna gona.




Jumme ya tarar tana shanyar ganyen albasa ya tsaida motarsa ya fito tana ganinsa ta nufi gida da sauri ya bita tare da cewa “Barka da safiya Mama!" Tsayawa tayi ya rusuna ya gaisheta, cike da kunya irin tasu ta mutanen karkara ta amsa ya sosa kansa yace “dama Habeebah nakeson gani...." Da sauri ta juyo tace “Tana ina ɗannan Nima ita nakeson gani"
Wani abu yaji me nauyi ya saukowa ƙirjinsa daƙyar ya miƙe tsaye ya koma cikin motarsa ya kira wani yaro ya zaro kuɗi da baisan adadin su ba ya bashi yace yakaiwa Jumme ya tada motar yabar ƙofar gidan baiyi nisa ba ya tsaya ya ɗora kansa bisa sitiyarin motarsa ya lumshe idonsa hawaye suka fara sintiri Mai Martaba ya cutar dashi duk shine yaja masa amma yanzun wai dashi yake fushi saboda ya sakar masa zaɓin nasa.
Ajiyar zuciya yayi tare da tada motar ya koma cikin garin Kano anan ya samu wani hotel ya sauka ya huta yana kwance wayar Wali ya shigo yana gani amma ya kasa ɗagawa saboda ransa a cushe yake kalma ko ɗaya bayajin zai iya furtawa me amfani.




Kira na biyu ne ya sashi ɗagawa Wali yace “nazo gdanka bakanan ina kaje?" Buɗe idanunsa yayi cikin gajiya yace “ina Kano" amsawa Wali yayi yace “Ok dama inason ka rakani gidan Al'Amin ne" a yatsine yace “
Ko kwanaki kace nazo muje nace maka banida interest akan hakan so waima meye Ni sai ka rinƙa jana gidan matan aure?" Murmushi Wali yayi ya riga yasan halin izza da son isa irin ta Habeeb shiyasa yace “Allah ya huci zuciya dama Ahmad abokinka ne ya dameni tun jiya nazo naga bbynsu ƙanwar Mamansu ce dake zaune a gidan ta haihu shine dake naji kace kanason zuwa ka gaisa da Ahmad na sanar dakai"
Numfashi ya aje yace “ok kaje inna dawo ka rakani tunda Ni yanzun saina shiga Dutse zan wutto nan" sallamewa sukayi ya tashi ya fara shirinsa ya ɗauki mota sai dutse koda yaje bai saurari mai martaba ba sashin Kilishi ya shiga suka gaisa cikin watanni biyar ɗin duk ya rame ya susuce sai ido da hanci kawai taja fasali tace “Meye yasa bazaka fawwalawa Allah komai ba Habeebullah ubangiji ba da kansa yake cewa (ashe haka zan barku kara zube? Shin bazan jarabceku ba?) Habeeb Allah nason bayinsa masu haƙuri da fawwala masa komai daya shafesu" hawaye ya share ya miƙe zai bar wajen ta riko hannunsa tace “meye ne?" Ƙasa yayi da kansa




Yace “Ta haihu Kilishi yanzu Shikenan yarinyata bazata Sanni matsayin ubanta ba?" Da sauri Kilishi tace “Habeeban? Yaushe ta haihu ina kaji kai ya akayi ka sani???" Ta jero masa tambayoyin cike da ruɗewa ya kawar da kansa yace “yau da asuba naga saƙonta kuma tun lokacin nake kiran wayar taƙi shiga" jinjina kai tayi tace “To a bibiyi number mana ai za'a gano daga inda ta rubuto saƙon" sosai yaji daɗin shawarar Kilishi domin da gaske ya manta da ana wani bibiyar number waya don gano daga inda ake amfani da ita.
Fasa shiga ɗakin nasa yayi ya fito ya kira Najeeb tare suka yini a campanyn layin wayar ba ƙaramin al'ajabu Habeeb ya shiga ba da akace masa Beebah tana garin Abuja inda tayo test ɗin ne suka kasa ganowa saboda layin ba akan waya yake ba.
Jikinsa har ɓari yakeyi da aka sanar dashi inda take ashe zuciyarsa ce a gurin shiyasa ya kasa barin Abuja ko zaman London ya kasa ko yaje baya jimawa yakejin hankalinsa ya dawo Abuja.




A ranar bai kwana a Dutse ba ya wucce Abuja ya nemi Wali yayi masa bayanin komai shima ya cika da mamaki nan suka kuma ɗimawa suka fice domin Habeeb ya hanashi kwanciyar hankali gani yakeyi suna fita zasu ganota.
Haka suka shafe kwanaki suna jigilar nema abu kamar wasa sai gashi sun ɗauki kusan sati.
Ranar wata asabar tun safe suke zaga gari yamma suna zaune cikin wani garden Habeeb ya kifa kansa saman tables ɗin abin duniya yabi yayi masa zafi, wayar Engineer Wali tayi ring ya zarota a aljihunsa tare da manna ta a kunnensa suka gaisa yace “kace zakazo taron raɗin suna kuma banganka ba" numfashi ya sauke yace “kayi afuwa abune yayi yawa Wlh amma bari yanzu mu taho dama muna ta arear taku" kallonsa Habeeb yayi kamar yace bazashi ba Wali yace “karkace komi don Allah inci wannan arzikin Dr Amin yafi ƙarfin haka a gurina"




Tashi yayi suka nufi mota daga inda suke zuwa gidan Dr Amin babu nisa suna isa suka ishe Dr Amin ya fito raka baƙi suka gaisa yayi musu jagora zuwa parlourn baƙin aka cika musu gabansu da abinci Habeeb dai tsakurar abincin kawai yakeyi Dr Amin ya kira wayar Safeenah yace “A kawo ma su Engineer Wali Ummusalma su sanya mata albarka" Habeeba dake zaune saman gado Safeenah ta duba tace.
“Kanin Dr ne yazo ki kai musu Bbyn su ganta" itadai Beebah hakanan taji gabanta na faɗuwa, ta jima bata tashi ba Saida Safeenah ta matsa sannan Beebah ta tashi ta fito daga dakin ta ɗauki kwalliya ta ban mamaki sai sheƙi takeyi.
Nufar ɗakin bakin tayi idanunta na kan Ummusalma.




Ta shiga dakin tare da sallama yana ganinta ya miƙe da mugun sauri ya fara nunata da yatsa itama ɗagowar da zatayi tayi tozali dashi ta sake ware injin idanunta akansa tace “Hab... Habeebullah....." Saurin juyawa tayi da mugun gudu zata fice a dakin yayi wani kukan kura ya cafkota cikin tsananin farin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login