Showing 183001 words to 186000 words out of 417803 words
acikin nasa kana yace.
“Ina da kadaran da zan iya sayarwa amma ta yaya awani lokaci zan samu ace ansiya se anbani kuɗina sannan na wane”.
Kasa ƙara sa maganar yayi kawai saiya janye hannunsa dake cikin na Moddibo ya rufe fuskarsa yana mai furta.
_“Allahumma Ajirni fii musibati wa'ahlifli khairan minha Hasbunallahu wani'imal wakin La'ilaha Illah anta subhanaka Inni kuntu Minal zhalimin”_.
Hajiya Karima dake dafe da kuncinta ta ɗago kai tare da kallon Abba kana tace.
“Alhj ai dole dama za ayi ciniki dasu idan yaso sai anemi ragi”.
Moddibo kuwa kai ya girgiza tare da kallon ta kana yace.
“Idan da ace sunzo mana da sauƙi da kuma Imani acikin zancen zamu iya hakan amma fa kiga yanda idan sunyi magana sai su yanke mana kiran baza su tsaya suji ta bakin muba sai sun kwana ɗaya ko biyu kafin su sake kiran mu”.
Da ƙarfi ya runtse Idanunsa tare da cije labɓansa na ƙasa kana ya cigaba da cewa.
“Basa tunanin shin wani irin yanayi ko hali zamu kasance aciki ba yaya zamuyi, da wannan kuɗin da suka kira”.
Ya ida maganar cikin raunin murya.
Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe kana yace.
“Nima abinda nake tunani kenan idan nace musu babu zasu iya yiwa Jameel Illah”.
Girgiza kai Moddibo yayi tare da cewa.
“Abba kar ma kace musu babu sai muyi ƙoƙari duk yanda zamuyi mu haɗa kuɗin nan muyi ƙoƙari mu basu”.
Ahankali Abba ya furta.
“Ya Salam”.
Hajiya Turai kuwa cikin matsanancin kuka ta kalli Moddibo kana ta maida kallonta kan Abba tare da cewa.
“Ai abayar ɗin yafi Alhj duk wani abinda kake dashi ka sashi akasuwa kawai asamu asayar akarɓo Jameel meye fi maka Jameel aduniyar nan Alhj, kawai asayar da komai akai musu kuɗin akarɓo shi”.
Cikin sauri Hajiya Karima ta kalli Hajiya Turai kana tace.
“Kamar ya asaida komai Hajiya Turai kifayi tunani akan abinda kike faɗa idan aka sayar da komai muku mu murayu aya kenan?”.
Sai kuma ta maida kallonta kan Abba kana ta cigaba da cewa.
“Alhj ya za ayi ɗauki irin wannan maƙudan kuɗin amulmula abasu kaga idan wa'annan ƴan Kidnapping din da suka kinnafe Jameelu sunji dadi an basu abinda suke so to wasu kuma ai sauran ƴaƴan zasu zo su kwashe”.
Ta ida mgnar tare da sauke numfashi kana ta cigaba da cewa.
“Suma sauran ƴaƴan sai aje a kinnafesu su kuma idan kuɗin da za'a fanshe su bai rage ba ya za ayi kenan.
A gaskiya wannan ba shawara bace ace za aɗauki wannan maƙudan kuɗin abasu sai kace ba asha wahala wajen ne mansu ba”.
Ahankali Moddibo ya ɗago kumburarrun Idanun sa ya kalli Hajiya Turai dake dafe da ƙafaɗan Abba tana sharɓan kuka kana ya maida kallonsa kan Hajiya Karima data zabga tagumi.
Girgiza kansa yayi.
Sosai hankalin Abba yayi masifar tashi yama rasa wani irin tunani zaiyi Aransa ya gaza tantance abin cewa.
Sannu a hankali idanunsa suka fara lumshewa jikinsa ya saki baya yaja tare da gyara kwanciyarsa akan 3sitter tare da lumshe idanunsa Atake Bacci ya ɗauke sa sabida magungunansa da Hajia Turai ta bashi yasha sun jiƙa sunbi jininsa.
Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe tare da miƙewa kana yai musu sai da safe tare da ficewa yashiga motarsa kai tsaye gidan Ummi ya nufa.
Awaje yayi Parking motarsa kana ya fita iska na kaɗa ko wani sashe na jikinsa ahankali ya murɗa handle din ƙofar ya tura bakinsa ɗauke da sallama ya shiga.
Idanunsa suka sauƙa akan Ummi dake zaune kan Sallaya hannunta riƙe da Carbi yayin da Malam Ahmad ke zaune gefenta yana rarrashin ta.
Ganinsa yasa Ummi ta ajiye carbin dake hannunta kana ta maida hankalinta kansa,Anutse Moddibo ya ƙara sa tare da miƙawa malam Ahmad hannu sukayi musabaha kana ya koma ya zana agaban Ummi.
Jin Sallamar sa yasa Asma'u da Bashir suka fito daga Bedroom tare da zama gefe da gefen Ummi ya zamana sun sashi a tsakiya kana cikin raunin murya suka gaishesa atare zuwa lokacin shima Bashir kuka yake sosai duk yayi zuru-zuru.
Ahankali Ummi ta zubawa Moddibo Idanu kana cikin sanyin murya tace.
“Babana ya akayi sun sake kira?”.
Kai ya gyaɗa tare da sun kuyar da kansa ƙasa kana yace.
“Eh”.
Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da cewa.
“Me suke buƙata?”.
Still Kansa na ƙasa yace.
“Ummi kuɗi suke so”.
Numfashi ta fesar kana tace.
“Kuɗi suke so?”.
Kai ya gyaɗa amma bai ce komai ba.
Cikin tsira masa ido tace.
“Kuɗi kamar nawa suke so?”.
Cikin rauni ya kalleta kana ya kalli malam Ahmad, Asma'u da Bashir ya fesar da numfashi tare da cewa.
“Ummi kuɗin suna da yawa kuɗin da suke buƙata sun wuce zatonmu”.
Gyara zama tayi kana tace.
“Toh Meye amfanin kuɗin mahaifinsa?, Meye amfanin kuɗin Babansa?,Menene amfanin duk tattalin da yake yi!?”.
Girgiza kai Moddibo yayi kana yace.
“Ummi kuɗin sun wuce tunanin mai tunani!?”.
Ɗa gowa Ummi tayi tare da tsira masa ido kana tace.
“Kamar nawa suke buƙata Babana?”.
Cikin raunin murya da alamar sarewa Moddibo yace.
“Ummi har Million ɗari biyu suke buƙata”.
Cikin wani irin yanayi mai cike da rauni, tsoro, mmki Ummi taja ajiyar zuciya kana ta maida kanta ta jingina da jikin kujeran da Malam Ahmad ke zaune tare da lumshe Idanunta kana Muryanta na rawa tace.
“Ƙarya sukeyi ba kuɗin suke so ba so suke su kashe min Jameelu lallai Mahaifinsa mai arziƙi ne amma be kai matakin da za'a matsesa lokaci ɗaya ace ya fito da Million ɗari biyuba, kawai dai yaudarace suke mana anya ma Jameelu yana raye kuwa?”.
Cikin sauri Moddibo ya girgiza mata kai kana yace.
“Yana raye Ummi ina ji ajikina J yana raye kuma na faɗa miki munyi magana dashi”.
Girgiza kai tayi tare da cewa.
“Yau da suka kira kunyi magana dashi?”.
Shiru yayi yana kallonta amma baice komai ba.
Kallonsa Ummi tayi cikin muryan kuka tace.
“Babana ka faɗa min gaskiya tsakanin ka da Allah yau kunyi magana dashi?”.
Girgiza mata kai Moddibo yayi tare da faɗin.
“Ummi ba muyi magana dashi ba, amma naji muryan J ƙasa-ƙasa yana cewa Abba abasu duk abinda suke so”.
Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare da rintse idanunsa kana tace.
“Babana ka tabbatar gaskiya kake faɗa min?”
Jinjina kai Moddibo yayi kana cikin sanyin murya yace.
“Wallahi Wa rabbul Khaba Ummi naji muryan J ƙasa. yana magana bawai sun bashi bane amma naji yana magana”.
Kuka Asma'u da Bashir suka fashe da shi atare kana lokaci ɗaya suka haɗa baki wajen cewa.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n ya Allah ka kuɓutar da Yah Jameel Ubangiji kada ka basu ikon cutar dashi ya Allah kaine gatanmu Yah Jameel shine ka wakilta da isar mana gatanmu ya Allah ka karesa da karewaka”.
Numfashi Malam Ahmad ya fesar kana cike da tausayawa yace.
“Asma'u ba kuka ya kamata kuyi ba addu'ar mu Jameelu ke buƙata idan kuna kuka ya kuke so Ummin ku tayi?”.
Cikin sheshsheƙan Kuka Asma'u tace.
“Abba Yah Jameel fa Yah Jameel yana cikin mawuyacin hali Abba kaji fa maƙudan kuɗin da suke buƙata Abba ya za'ayi mu samu irin wannan kuɗin mu karɓo Yah Jameel Abba Ina tsoron kada su cutar mana dashi”.
Girgiza kai Malam Ahmad yayi cikin sanyin murya yace.
“Insha Allah da izinin Ubangiji babu abinda zai samu Jameelu, ko wani bawa da kalar tashi ƙaddaran tun kafin a haifi Jameelu Ubangiji ya zana masa ƙaddaransa muyi masa addu'ar Allah ya sauƙaƙa mana zafin ƙaddararsa”.
Jinjina kai Moddibo yayi yana jin wani irin azabebben zafi aƙirjinsa.
Kallon Moddibo Malam Ahmad yayi kana yace.
“Moddibo mai Yakamata ayi acikin wannan al'amarin!?”.
Moddibo da kansa ke ƙasa ya ɗago ya kallon Malam Ahmad a hankali yace.
“Malam abinda yakamata kawai afara cuku-cukun neman kuɗin nan sai muga abinda zai kasance”.
Girgiza kai Ummi tayi still tana jingine da jikin kujera tace.
“Babana ina zamu samu kuɗin nan Million ɗari biyu fa da ace Million biyu suka ce koni kaina ma zan bada su”.
Ta faɗa tare da ɗaukar wayarta tayi checking balance kana tace.
“Gashi yanzu anan ina da Million ɗaya da dubu ɗari huɗu da hamsin da ɗaya sannan kuma ba matsala gobe in Allah ya kaimu zan tafi cikin.
Taraba zan kai gwala-gwalaina”.
Sai kuma ta ɗan tsaya, jin numfashin ta na yankewa, da ƙarfi ta fizgo numfashin tare da cije labɓanta na ƙasa hawaye cike da Idanunta murya na cike da rauni ta cigaba da cewa.
“Zan saida su inga nawa zan samu ajikinsu zan haɗa harda na Asma'u sannan, motata itama zan saidawa muga nawa zan samu awurina”.
Jingina kai Malam Ahmad yayi kana cikin sanyin Murya yace.
“Har gidan nan ma asashi a. Kasuwa asayar dashi”.
Kallonsa Moddibo yayi tare da girgiza kai kana yace.
“A Malam ayi haka”.
Kai Malam Ahmad ya gyaɗa kana yace.
“Asiyar Moddibo menene Jameelu baiyi mana ba aduniyar na, kasancewar sa atare damu shiyafi mana komai”.
Ahankali Ummi ta ɗago kanta tare da tsira masa ido hawaye na bin kuncinta ta sani fili dai filinsa ne halalinsa mallakinsa, amma baki ɗaya ginin dake ciki Jameel ne ya musu bayan yasa an buge tsohon ginin taɓon.
Girgiza kai tayi cikin rauni tace.
“A'a ba sai anyi haka ba bari muga abinda Mahaifinsa zai samu”.
Girgiza kai Malam Ahmad yayi tare da kallon Asma'u da Bashir da har zuwa lokacin suke kuka a hankali ya fesar da numfashi tare da cewa.
“Ni dai na sadaukar da wannan gida ga.
Jameelu wallahi na yafe masa shi duniya da lahira na amince asa shi akasuwa muddin za a samu masu siya, to asa shi akasuwa mu samu muga aƙalla dai awajen mu ace an samu Million goma kuɗin zaifi gwaɓi”.
Sun kuyar da kai ƙasa Ummi tayi hawaye masu masifar zafi suka zubo mata.
Hannunta Moddibo ya riƙe cikin sanyin murya yace.
“Ummi dan Allah ki daina wannan kukan idan kina kuka muku ma ya zamuyi Ummi babu abinda J ke buƙata awajen mu face addu'a ganin ki awannan yanayin naya sake raunatamana zuciya”.
Kai Malam Ahmad ya gyaɗa kana yace.
“Sosai ma wannan kukan da kike Fatima saidai ya haddasa miki wani ciwon amma babu amfanin da zaiyi dan Allah ki daina ki cigaba da yi masa addu'a. shi kansa ba zaiso ace kina masa kuka ba”.
Kai ta gyaɗa tare da share hawayen ta kamar yarinya kana tace.
“Na daina Insha Allah zan cigaba da yimasa addu'a Ako da yaushe”.
Saida Moddibo ya tabbata ta daina kukan kafin ya mata sallama ya fice cike da tausayinsu Driving yake ahankali har ya isa gida yayi Parking kana ya fito ya rufe gate din tare da wucewa sashen Innayi bakinsa ɗauke da sallama.
Kwance ya samu Innayi cikin Yanayin damuwa gefenta da Radio tana sauraro wanda ɓatan M Jameel ake sanarwa.
Miƙewa tayi ta zauna tare da amsa Sallamar sa kana tace.
“Moddibo ya labarin Jameelu?”.
Cikin sanyin murya yace.
“Innayi sun sake kira ɗazu”.
Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da cewa.
“Toh kunyi magana dashi yana cikin ƙoshin lafiya?”.
Girgiza mata kai yayi kana yace.
“A'a Innayi bamuyi waya dashi ba amma bisa duk kan Alamu J baya jin daɗin zaman wajen can”.
Ahankali Innayi ta jingina bayanta da jikin bango kana ta matsar da Radio gefe tare da cewa.
“Dama Moddibo ya za ayi yaji daɗin zaman wannan wajen. kasan yanayin da yake ciki ai dole bazai ji daɗin zaman wannan wajen ba amma me suke buƙata?”.
“Innayi kuɗi suka nema”.
“Kuɗi suka nema to aisai abasu aje a karɓe shi”.
“Innayi kuɗin da suka nema na fitar hayyacine!”.
“Kuɗi har nawa suka nema? Da zai zama na fitar hankali”.
Dafe goshinsa yayi kana yace.
“Innayi Million ɗari biyu suka nema kuma cikin ƙanƙanin lokacin fa”.
Ita kam Innayi baki ɗaya lissafin ta sincewa yayi jin maƙudan kuɗin tama rasa nawane, kallon Moddibo tayi tare da cewa.
“Dubu ɗari biyu?”.
Kai Moddibo ya Girgiza tare da cewa.
“A'a ba dubu ɗari biyu bafa Million fa Million ɗari biyu”.
Daga kanta sama tayi alamar tunani sai kuma ta kallesa tare da cewa.
“Million biyu?”.
Still girgiza mata kai Moddibo yayi kana yace.
“A'a Million ɗin goma, ashirin, hamsin, ɗari, ɗari da hamshin har ɗari biyu”.
Dafe kirji tayi kana tace.
“Million ɗari biyu?”.
Jinjina mata kai Moddibo yayi.
Girgiza kai tayi tare da cewa.
“Ban gane lissafin ba Aliyu”.
Lips ɗinsa duka biyu ya cije a lokaci guda kana yace.
“Ba zaki gane lissafin ba Innayi kuɗi ne masu tarin yawa suke nema”.
Cikin sanyin murya Innayi ta jujjuya kanta kana tace.
_“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Hasbunallahu wani'imal wakin Layukalliful nafsi illa wusɗaha_
Toh yanzu mai Baban nasa yace?”.
“Innayi Abbansa bashi da wannan kuɗin a ƙasa kwanan nan dama ya gama yi mana ƙorafi bashi da kuɗi”.
Lumshe idanu Innayi tayi kana tace.
“Ya Salam ya Ubangiji Allah ka dube mu da idon rahama, ya Allah ka yayemana ya Allah ka sauƙaƙa mana ya Allah ka tsare Jameel ka kare mana shi, Allah ka tseratar da wannan bawan naka”.
Cikin sanyin murya Moddibo yace.
“Ameen”.
Kallon second biyar zuwa bakwai Innayi ta yiwa Moddibo kana tace.
“To amma kai Moddibo mai kake ganin zakayi akai?”.
Still hannunsa na dafe akansa yace.
“Innayi akwai kuɗi awajena zan tattara su in haɗa su muga nawa za'a samu awajena”.
Kai ta gyaɗa kana tace.
“Yafi kam”.
Bayan sun sake tattauna ne Moddibo ya miƙe tare da yi mata Sallama kana ya nufi Sashen sa ahankali ya tura Murfin Kofar shiga tare da mayarwa ya rufe.
Kana ya jingina bayansa da jikin da kofar tare da rintse idanunsa sautin murya M Jameel ya farayi masa kai-komo AJ bansan idan nakeba,
Lumshe danunsa yayu zuciyarsa na bugawa da masifar ƙarfi yana bada sautin dif-dif-dif cikin sauri ya buɗe Idanunsa jin muryan M Jameel na yawo a kansa yana cewa A.J A.J Kallon kan 3sitrer kurui ji yake kamar zaiga J dinsa a wurin, cikin raunin murya yace.
“J Why are you?, Zuciyata zata fashe ya Allah kaji ƙaina ya rabbil Izzati ka dawo da J garemu cikin aminci da salama ya Allah kada ka bawa waɗɗanan azzaluman daman cutar dashi”.
Ya kai 15 minutes yana mai jero Addu'o'in cike da rauni, kafin ya miƙe kamar wanda aka mitsina ya nufi Bedroom ɗin sa kai tsaye toilet ya shiga ya watsa ruwa kana ya ɗaura alwala ya fito ya kwanta bisa gadonsa yayi rigingine duk da yasan cewa da wuya bacci ya ɗauke sa amman ya lumshe idonsa domin yau kwana uku rabon da ya samu wani wadataccen bacci sai wani irin azabebben ciwon kai da yakeji tamkar kansa zai rabe da ga wani irin sarawa da yakeyi yana bada wani irin sauti mara daɗi gau-gau-gau!.
A hankali ya bude idon sai kuma yayi saurin
Lumshe Idanun sabida sarawa da kan yayi masa.
Cikin zazzaƙan muryansa mai cike da rauni ya fara raira ƙira'ar Suratul Yusuf hawaye masu ɗumi suka riƙa fita daga idanunsa suna shiga kunnensa cikin wannan yanayin da cikar Sa'adatu da karatun Alqur'ani mai girma ya samar masa, wani irin kiɗimemmen baccin da bai shirya masa ba ya sace sa.
Acan cikin baccin sa kuwa zaune ya hangosa akan wata.
Tattausan shimfiɗa cikin wani masha'hurin falo mai masifar kyau da ƙawa.
Sai dai kima yana ta dariya hartada karketawa, yayinda idanunsa kuma sunyi jawur jikinsa na rawa jin.
A hankali ya fara jujjuya kansa yana mai ci gaba da dariyar ya juyo kansa gabansa, jin alamar tafiya tare da wani ƙamshi daya ratsa hancinsa yasa ya ɗaga manyan idanunsa da sukayi luhu-luhu ya sauƙe ganinsa akan Khausar dake zuwa garesa cikin wata iriyar ƙasaitacciyar shiga, ido ya zira mata ko ƙebtawa bayayi har ta isa garesa, a hankali ta zauna gefensa.
Tare da tsira masa manyan Idanunta masu haske wanda ke ciki da ruwan hawaye kana ta miƙa masa wani hankief fari ƙall mai masifar ƙamshin turare.
Ƙin karba yayi saima lumshe idanunsa da yayi wanda sai lokacin ya samu wasu irin tafasassun hawaye suka samu damar kwaranyowa, hakan yasake kawar da kansa gefe tare da sakin sheshsheƙa.
Ahankali Khausar ta matsa gabansa har suna shaƙan nunfashin juna kana ta sanya hankief ɗin ta shiga share masa hawayen cikin wata Sanyayyar murya mai cike da nutsuwa da kuma rauni tace.
“Yah Jameel Addu'ar mu yake buƙata ba kuka ba idan kai kana kuka.
Toh Ni kuma ya zanyi addu'a za muyi masa kaji ko Abu J”.
Ta ida mgnar da kiransa da sunan da ta raɗa masa, tare da faɗawa jikinsa ta fashe da sassayan kuka dai-dai lokacin kuma ya farka.
Kansa ya dafe tare da miƙewa ya shiga toilet ya ɗaura al,wala kana ya dawo ya shimfiɗa Sallaya ya fara nafillah yana cigaba da yiwa M Jameel addu'a.
Ba tare da yabi ta kan mafarkinba, domin yanzu kam idan da sabo ai yaci ace ya saba da yawan ziyarar kutse da nacin da Khaisar keyi masa cikin rayuwar baccinsa.
Washe gari Ummi ta tattara baki ɗaya Sarkoƙi, ta da ɗan kunnen zobe da awarwon Gwal nata dana Asma'u ta shirya ta tafi Tarata.
Tana isa kai tsaye babbar kasuwar su ta wuce kana tashiga shagon saida gwala-gwalai ta bayar aka gwada cikin sa'a ta samu sunyi farashi sosai kasancewar Manyan Sarƙoƙine nata dana Asma'u wasu nata tun tana gidan Abban Jameel ne, suka haɗa mata kuɗin ta Naira Million biyu da dubu ɗari huɗu da hamsin sukayi mata transfer dinsu.
Daga nan gidan kai tsaye gidan Ƙawarta Hajiya Salma Wanda mijinta ke saida Motoci yawanci awajensa M Jameel ke siyan mota ko kuma can zawa.
Mai A dai-dai-tan na sauƙeta ta miƙa masa kudinsa kana ta shiga cikin tangamenen coumpund ɗin daya tsaru kai tsaye ciki ta nufa tare da Knowking ɗin ƙofar kana ta murɗa handle ɗin tashiga bakinta ɗauke da sallama.
Hajiya Salma dake zaune akan kujera ta miƙe cikin sauri kana tace.
“Hajiya Fatima sannu da zuwa ga wajen zama”.
Kai Mommy ta gyaɗa tare da cewa.
“Yawwa Nagode”.
Sannan ta zauna tare da sakin Ajiyar zuciya.
Bayan sun gaisane.
Cikin sanyin murya Hajiya Salma tace.
“Ayyah Hajiya ashe ga abinda ya faru da ɗana Jameel kuwa?”.
Cikin yanayin sanyin ɗaya zamewa Ummu jiki, ta gyaɗa mata kai tare da cewa.
“Ummm bari ke dai Hajia Salma duniya tayi min zafi”.
Cikin tausayawa Hajia Salma tace.
“Ba komai in sha Allah, kada ki damu Hajia Fatima.
Ubangiji Allah ya bayyanar da Jameel aduk inda yake Ubangiji ya karesa daga sharrin mai sharri”.
Cikin sanyin Murya Ummi tace.
“Ameen ya Allah ameen ya hayyu ya ƙayyum”.
Cike da tausayawa Hajiya Salma tace.
“Wallahi Koda wasa banji ba sai ɗazu da safe Alhj na duba jarida ya gani shine yake sanar min”.
Kai Ummi ta gyaɗa kana tace.
“Allah sarki ai yanzu anshiga kwana na huɗu kenan.
Uhmmm dama nazo kiyiwa Alhj Abdallah magana ne akan ya duba motata ya siya”.
Ajiyar zuciya Hajiya Salma ta sauƙe kana tace.
“Ubangiji Allah ya tsare Malam Jameel aduk inda yake”.
ta faɗa tare da shigewa ciki tsaye ta samu mijin nata yana ƙoƙarin fita Kallonsa tayi kana tace.
“Alhj Hajiya Fatima ce ta zo mahaifiyar Malam Jameel”.
Kai ya gyaɗa tare da cewa.
“Ikon Allah muna shirin zuwa kuma sai gata”.
Ya faɗa tare