Showing 201001 words to 204000 words out of 417803 words

Chapter 68 - Sakayya By Aisha Aliyu Garkuwa

murya yace.
“Amma meyafaru meka gani bawan Allah!”.
Girgiza kai Buba yayi da faɗin.
“Abinfa ba daɗin gani, domin ya wuce tunanin mutum”.
Ajiyar zuciya Malam Arɗo ya sauƙe tare da faɗin.
“Toh Allah ya rufa mana asiri amma baki ɗaya zamani ya zama abin tsoro, to amma Ori mai kagani acikin dajin da har ya gigita ka haka, bayan ku Fulani daji kun saba ganin abubuwa!”.
Cikin sauri Ori ya girgiza kai da faɗin.
“Kai gane ganen da muka saba ba irin wannan bane! Duk abinda muke gani na yau da kullum lamuran iska ko halittun dajine”.
Alhj Musa dake fuskantarsane yace.
“To amma meka gani haka?
Ya kamata idan kunga abu irin wannan na tsoro Ku riƙa faɗa acikin gari wurin jami'an tsaro”.

Girgiza kai Ori yayi cikin sanyin murya yace.
“Uhm muna tsoro ai”.
Lamiɗo ne ya sauƙe Ajiyar zuciya da faɗin.
“To amma meka gani?”.
Gyara zama yayi tare da sauƙe ajiyar zuciya kana yace.
“Abinda nagani abin tsoro ne, to amma dai banga amfanin ɓoye muku ba, yau tsawon kwana bakwai kenan ina kiwon shanu na akan Dutsen Membilla”.
Duk ido suka zuba masa tare da maida nutsuwarsu kansa suna saurarensa.
Gyara zama Ori yayi kana ya cigaba da cewa.
“Ina nufar kan dutsen sabida ɗebo kanya, naji wani irin wari mai gigitarwa da fitar da hayyacin ɗan Adam Atake tsoro ya kamani na rasa wani irin wari ne wanan.
Saboda ban taɓa jin wari makamancin wannan ba!”.
Cikin sauri Lamiɗo ya kallesa da faɗin.
“To wannan wani irin wari ne!?”.
Ajiyar zuciya ya sauke da faɗin.
“Hmmm Lamiɗo nima kaina na gigice.
Saboda ban taɓa jin makamancin wari irin wannan ba a duniya!”.
Alhj Ibrahim ya fesar da numfashi kana yace.
“To amma me kagani awajen haka?”.
Girgiza kai yayi da alamun damuwa atare dashi yace.
“Ban taɓa ganin abinda ya tayar min da hankali ya kiɗimani ba irin wannan domin ina jin warin na haura na nufi wajen agindin wata Bishiyar kanya”.
Cikin zaƙuwa da gajiyawa za tsinkewar zuciya Modibbo yace.
“Uhmmm!!”.
Shi kuwa Ori runtse Idanunsa cike da damuwa ya cigaba da cewa.
“Ina haurawa kan dutsen. Naga gawa ɗaure a jikin bishiyar, da igiyoyi tako ina.
Wanda da alamu abin ya kwana biyu domin tuni mutumin ya rasu gawace aɗaure, bisa ga duk kan alamu tunda ransa aka dauresa har ya rasu domin har ya kumbura yayi dam sai wani irin sheƙi fuskarsa duk sauran jinka keyi, fuskara ɗauke da murmushi duk da ya rasu, sai kuma alamun kwaranyar hawaye a kan kumatunsa gemunsa da sajensa sai sheƙi sukeyi tamkar wanda kullum ana shafa masa maine kai in ka ganshi kace balarabene wannan warin ne kaɗai ke nuni da gawane, domin a lokacin bai fasheba jikinsa fes”.
Cikin sauri da wani irin azabebben tsinkewar zuciya Moddibo ya runtse Idanunsa tare da taune lips ɗinsa na ƙasa kana yace.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Hasbunallahu wani'imal wakil”.
Malam Arɗo kuwa cike da tsoro ya kalli Ori kana yace.
“To amma kai Meyesa baka zo ka faɗa acikin gari ba!?”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe kana yace.
“Tsoro nakeji domin Atake awajen na fara sheƙa amai da gudawa saboda warin dana shaka karshe ma agigice na koma gida, domin bana cikin nutsuwa ta kuma tunda na koma saida nayi kwana uku bani da lafiya ko kiwo sai ƙanina ne ya karba, kuma dole muka canza wajen kiwo saboda warin da wannan yankin keyi”.

Cikin sauri da ɓacin rai Lamiɗo yace.
“Haba Ori ya za ayi kuyi haka kuda kuke tare dani ai idan kunga makamancin abu irin wannan, sai ku kirani ku faɗa min idan yaso in tura ƴan sanda su duba ko menene ya za ayi kuyi shiru!?”.

Cikin tsoro da cikekken gaskiya Ori ya sauƙe ajiyan zuciya tare da Girgiza kai kana yace.
“Hmmm ire-iren waɗannan abubuwan gaba ɗaya mu Fulani ma zauna daji ake ɗaurawa alhakin sa, wanda bamusan komai ba banda Bautar Allah da kiwon dabbobin mu, amma baki ɗaya an ɗauki baƙin jini da tsana an ɗaura mana”.
Kallonsa kawai suke zuciyarsu na tsinkewa.
Shi kuwa a hankali ya cigaba da cewa.
“Mutanen gari na cewa Fulani sune ƴan Kidnapping, to idan mun faɗi ire-iren waɗannan abubuwan sai azo ace mu muka aikata ayi ta kamamu, shiyasa mukeyin shiru, kuma nima Aruɗe na koma gida baki ɗaya bana cikin nutsuwa ta shiyasa”.
Cike da damuwa Malam Arɗo yace.
“Allah mai iko kai wannan zamani Allah ya rufa mana asiri”.
Kallonsa ya mayar kan Moddibo da har zuwa lokacin jikinsa ke tsuma kana tun lokacin daya runtse Idanunsa har yanzu bai buɗe ba cikin sanyin murya Malam Arɗo yace.
“Amma Moddibo ka shirya muje wajen mu duba gawan waye!”.
Cikin sauri Moddibo ya buɗe Idanunsa dake rintse ya kallesa kana yace.
“Nikam bazan jeba Malam Arɗo me kake nufi kana nufin J ɗina ne?”.
Girgiza kai Malam Arɗo yayi tare da cewa.
“Ba haka nake nufi ba bakaji bahaushe yace idan raƙumin ka ya ɓataba ko cikin ramin allura ka duba ba to muje mu duba mana”.
Jinjina kai Lamiɗo yayi da faɗin.
“Tabbas kam ya kamata aje aduba yanzu kuje ku faɗawa Mahaifinsa Ni kuma zan kira hukumar ƴan sanda sai muje dasu”.

Girgiza kai Moddibo yayi tare da fesar da numfashi mai zafi kana cikin rawan murya yace.
“Nifa bazan jeba dan nasan in Sha Allah ba J ɗina bane, bakuji yace muku gawa bane kuma tuntuni ya mutu har ya kumbura ni kuma J ɗina bai mutuba inaji Ajikina in Sha Allah yana raye”.

Dafa kafaɗar sa Malam Arɗo yayi tare da cewa.
“Moddibo kada kiɗima yasa ka furta kalmar alamar sanin gaibu”.
Cikin sauri Moddibo ya Girgiza kai kana muryarsa na rawa yace.
“Astagafirullah³ amma dai inaji Ajikina kamar J ɗina yana raye”.
Cikin sanyin murya Malam Arɗo yace.
“Eh duk da haka dai muje”.
Girgiza kai yayi tare da cewa.
“Nifa bazan jeba”.
Cikin lallashi Lamiɗo yace.
“A'a Moddibo ka daure dai kuje Allah yasa ba shiɗin bane amma dai aje aduba ɗin”.
Kai Buba ya gyaɗa kana yace.
“Eh suje su duba kuma alokacin ma na samu an ajiye wayoyi agabansa da kuma goran ruwa fuskarsa ma bata wani kumbura ba dan kyanshi bai ɓaceba”.
Atsorace Moddibo ya kallesa zuciyarsa na bugawa da masifar ƙarfi yace.
“Harda waya kuma shikenan bari Muje mu gani ɗin?”.
Ya faɗa tare da miƙewa suka fita kai tsaye gidan Abba suka nufa kana malam Arɗo ya masa bayani.
Kallon Abba Moddibo yayi cikin raunin murya yace.
“Abba ni dai inaji Ajikina in Sha Allah ba J ɗinmu bane, amma dai tunda sunce muje to muje ɗin”.
Cikin rarrashi Malam Arɗo yace.
“Alhj kayi haƙuri muje mu gani”.
Cikin sanyi da rauni kana da tsinkewar zuciya Abba ya gyaɗa kai dai-dai lokacin da folisawan suka iso tare da Lamiɗo.

Fita sukayi cikin shirin tafiya Abba, Lamiɗo malam Arɗo da Moddibo suka shiga mota ɗaya Ori kuma ya shiga motar Ƴan sanda suka tafi.

Suna isa dajin bayan sunyi Parking din Motar daga can nesa, suka fara haurawa saman dutsen.
Da sauri suka fara kallon juna sabida jin wani irin ni'imtaccen ƙamshi mai sanyin shaƙa, babu wari kamar yanda ya faɗa musu yasa Moddibo juyawa ya kalli Ori kana cikin sanyi yace.
“Ya gaba ɗaya babu warin da kace sai ma wani irin amintaccen ƙamshi”.
Kallonsa Ori yayi da faɗin.
“Toh yaufa kusan kwana takwas kenan da labarin dana baku ai dole wari ya baje dan zuwa yanzu Nasan gawar ya fashe bare kuma ruwan sama da ake ai dole zai za gonye sai dai kuma nima nayi mamakin wannan ƙamshi!”.
Cikin sanyi Malam Arɗo yace.
“Allah mai iko wannan wani irin ni'imtaccen ƙamshi ne a tsakiyar daji”.
Abba kuwa kasa furta komai yayi sai zuciyarsa dake bugawa da masifar ƙarfi yana jin wani irin masifaffen tsinkewar zuciya haka zalika Moddibo suna masu shaƙar ƙamshi.
Lamiɗo da polices din kuma sai lumshe idanu suke sabida daɗin ƙamshin da Ubangijin talikai ya wadata wurin dashi.
Yayinda suna kara haurawa suna ƙara jin ƙamshin.
Cikin tsanananin fargaba da tsinkewar zuciya suka cigaba da haurawa wajen suna gama haurawa Ori yayi saurin cewa.
“Yawwa ga can bishiyar”.
Da sauri Moddibo ya ɗaga Idanunsa tare da kallon jikin Bishiyar ganin gawa ɗaure ajikin Bishiya yayi har ya zagwanye idanunsa sun rarake sai ramuka kaɗai sai kuma maiƙo dake zube aƙasa da wani irin sassayan ƙamshin dake tashi a wurin.
Cikin tsanananin tsinkewar zuciya ya sauƙe idanunsa akasa dai-dai kan ƙafar gawar dake maƙale da takalmin cikin sauri ya runtse Idanunsa tare da dafe ƙahon zuciyarsa dake bugawa da masifar ƙarfi.
Abba kuwa da sauri ya ƙarasa jikin Bishiyar dai-dai Inda goran faron ke ajiye Idanunsa suka sauƙa akan wayoyin dake wajen hannunsa na rawa ya ɗago wayar tare da jujjuyawa.
Cikin tsanananin tashin hankali da ruɗu yace.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n!”.
Juyawa yayi tare da kallon Moddibo cikin raunin murya yace.
“Aliyu wayoyin Jameelu na neeeee”.
Cikin sauri Moddibo ya juya tare da dafe saitin ƙohon zuciyarsa cikin raunin murya mai cike da tsantsar tashin hankali yace.
“Abba wayar J kuma”.
Kai Abba ya gyaɗa yayin da wasu irin hawaye masu masifar zafi ke koro juna subabin kuncinsa murya na rawa yace.
“Eh”, Ahankali Moddibo ya juya ta gefen da gawar ke daure tare da tsaida idanunsa akan hannun gawar na dama da har ya bushe idanunsa ya zubawa zoben dake hannu gawar.
Cikin tsanananin kaɗuwa da wani masifaffen tsinkewar zuciya mai cike da ɗimuwa da tashin hankali Moddibo yace.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Abba kalli zobunnan hannunsa zobunnan hannun J ɗina ne da agogon”.
Ya ida maganar tare da yanke jiki ya faɗi babu numfashi atare dashi....!


Wannan littafin dai na kuɗi ne.





By
*GARKUWAR MARUBUTA*SAKAYAH

32

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


Spndeɗɗ. Baya Moddibo ya koma. Suuuuuu ya faɗi a sume, cikin sauri Lamiɗo ya tarosa, ya faɗa jikinsa cike da tashin hankali Lamiɗo yace.
“Innalillahi ya suma fa Subhanallah!”.
Cikin sauri Malam Arɗo ya ƙara sa kusa da Lamiɗo idanunsa akan Moddibo ya shiga kiran sunan sa yana faɗin.
“Moddibo!, Moddibo!!, Moddibo!!!”.
Ina tuni Moddibo ya sume babu alamar numfashi atare dashi.
Abba kuwa kansa ya ɗaga tare da kallon fuskar skeleton M Jameel kana ya maida Idanunsa ƙasa kan takalmin dake sanye aƙafarsa ahankali ya leƙa bayan idanunsa suka sauƙa akan guntun rigarsa da bai gama sauƙa daga jikin skeleton ba jinjina kansa yayi cikin wata dakakkiyar murya ya juya ya kalli Moddibo dake sume kai ya girgiza tare da sakin murmushin da yafi kuka ciwo murmushi da yafi ihu zafi, murmushin da yafi ciwo, Ciwo murmushin da yafi raɗaɗi zafi, ya saki kana ya juya ya kalli sauran mutanen dake tsaye sai ya kuma kalli fuskar skeleton tare da maida kallonsa kan yatsun hannunsa.
Cikin wata dakakkiyar murya me ɗauke da tarin raɗaɗi da ƙuna yace.
“Uhmmm Jameelu na ne”.
Kallonsa ya mayar kan Moddibo da har zuwa lokacin yake. Rungume a jikin Lamiɗo taune lips ɗinsa yayi tare da cewa.
“Kai kam Aliyu kahuta, inama ace nima zan sume ko kuma in mace ma gaba ɗaya da hakan yafi min sauƙi”.
Cikin sauri ɗaya police ɗin ya juya tare da isa gefen Abba ya riƙe sa cike da alhini da tarin tausayawa yace.
“Alhj Bashir kayi addu'a kaji”.
Kai Abba ya gyaɗa cikin wata dakakkiyar murya yace.
_“Innalillahi wa'inna Ilahi rajiu'n lahaula wala ƙuwwata Illah billahil aliyul Azhim Hasbunallahu wani'imal wakil Allahumma Ajirni fii musibati wa'ahlifli khairan minha La'ilaha Illah anta subhanaka Inni kuntu Minal Zhalimin”_ sune Adduo'in da yake iya maimaitawa afili da kuma ransa.

Ori dake tsaye ciki ruɗu da tausayawa yayi saurin ƙarasawa gaban skeleton gawar M Jameel ya ɗauko goran ruwan kana ya dawo tare da miƙawa Lamiɗo yana mai cewa.
“Lamiɗo gashi ayayyafa masa”.
Karɓa Lamiɗo yayi kana ya buɗe tare da yayyafawa Moddibo dake kwance jikinsa amma ko kaɗan Moddibo bai motsa ba.
Kallon Buba Lamiɗo yayi kana yace.
“Ori taimaka min mu saka shi cikin Mota”.
Kai Buba ya gyaɗa.
Ɗaya daga cikin Folisawan ne yace.
“Ranka shi daɗe bari mu saka shi”.
Ya faɗa tare da kallon ɗan gidansa da Ido ya masa alamar yazo su kama Moddibo ƙarasawa yayi sannan suka ɗauki Moddibo suka sauƙa kasan dutsen, tare da sanya shi abayan Motar Malam Arɗo.

Folisawan kuwa ƙara sawa sukayi suka shiga ɗaukar hoton gawar skeleton M Jameel.
Bayan sun gama ɗauka tare yan dube-dubensu, da Babbansu da sauran suka saka handglove suka ƙarasa gaban gawar da niyyar sunjanye gawar Babbansun najan Igiyar da aka ɗauɗaureshi ƙasusuwan suka kakkarye tare da zubewa a ƙasa babu ta yanda zasu iya daukarsa Babban su ya umarci Coustable yaje ya ɗauko musu kwali abayan mota kana suka tattara gawar suka zuba acikin kwalin kana suka kwashe takalmansa da wayoyinsa suka saka awata leda.
Abba kuwa cikin wani irin yanayi ya nufi cikin jejin yana tafiya ba tare da shi kansa yasan inda ya nufaba.
Cikin sauri Lamiɗo ya nufesa tare da riƙe hannunsa cike da tausayawa yace.
“Alhj banan zamu bi ba can baya ne, hanyar kazo innu na maka hanyar da zamu bi”.
Kai Abba ya gyaɗa tare da bin bayan Lamiɗo baki ɗaya baya cikin nutsuwarsa ya kasa gane shin mafarki yake ko kuma azahirance komai ke faruwa.
Bayan sun isa Lamiɗo da kansa ya buɗe masa mota yashiga sannan shima yashiga.
Folisawan kuwa kwalin da gawar M Jameel ke ciki suka ɗauka tare da sawa abayan motarsu suka tafi gida.
Abba kuwa kallon hanya kawai yake baki ɗaya baya cikin hayyacinsa ganin yanayin da yake ciki ne yasa Malam Arɗo ya fara yi masa Adduo'i yana tofa masa kana yana faɗa afili.
Ahankali Abba ya fara sakin Ajiyar zuciya kana yashiga maimaita Adduo'in sannu Ahankali ya fara jin hankalinsa ya fara dawowa jikinsa.
Motar da Moddibo ke ciki Ori da police ɗaya ne aciki direct Asibiti suka nufa dashi.

Yayin da Motar dasu Abba da kuma gawar M Jameel ke ciki kai tsaye gida suka wuce, suna isa kai tsaye falonsa suka wuce police ɗin ne ya ɗauko kwalin Gawar M Jameel ya shigo dashi kana ya ajiye agabansu.
Hajiya Turai dake sashenta tana jin tsayuwar motoci ta fito zuwa falon Abba.
Ganin Abba zaune tare dasu Lamiɗo yasa ta nufi gefen Abba cikin yanayin damuwa tace.
“Alhj lafiya ya ake ciki Gawar waye kuka samu?”.
Ahankali ya ɗago Idanunsa da suka kaɗa sukayi jawur ya kalleta kana yayi ƙasa da kansa cikin raunin murya yace.
“Gawar Jameelu na ne!”.
Arazane Hajiya Turai ta kallesa zuciyarta na bugawa da masifar ƙarfi Idanunta akansa tace.
“Gawar Jameelu kuma!?”.
Kai ya gyaɗa mata Cikin tsananin tashin hankali da ruɗu ta fashe da kuka me tsuma zuciya tana furta.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n ina gawar yake?”.
Da hannu ya nuna mata kwalin dake gabansa.
Da kallo tabi kwalin cikin sauri ta sake Kallonsa Idanunta cike da ruwan hawaye tace.
“Gawar Jameelu ne acikin kwali haka?”.
Kai ya gyaɗa batare daya ɗago kaiba yace.
“Shine”.
Wani sabon kuka ta fashe dashi tana Girgiza kai Kukanta ne ya fito da Hajiya Karima itama ganin abinda ke faruwa yasa ta fashe da kuka.

Acan Asibiti kuwa ana kai Moddibo likitoci suka shiga bashi temakon Gaggawa saidai koda wasa bai farfaɗo ba ganin haka yasa suka dauƙo wani na'ura mai kama da Iron akafara danna masa aƙirji.
Amman ina babu alamun zai motsa, sosai likitocin suka dugufa wurin ganin sun cetoshi, a karo na biyu suka kuma danna mishi a ƙirjunshi, amman ina, Dr Lukman ne ya karɓi aikin tare da goggoga jikin na'urar ya manna masa a kirjinsa da ƙarfi.
Cikin ikon Allah yaja wani dogon numfashin sake dannawa yayi da karfi wani irin maraitaccen numfashi ya sake ja amma still bai farfaɗo ba sake dannawa sukayi akaro na biyar ne yaja wani dogon numfashi tare da buɗe idanunsa kana yace.
“Jyyyyyyy”.
Malam Arɗo da bai daɗe da dawowa daga gidan Abba bane, yayi saurin riƙe hannunsa tare da cewa.
“Moddibo kayi addu'a”.
Duk da cewa baya Cikin nutsuwarsa hakan bai hanashi maimaita duk wata addu'a da tazo bakinsa ba ahankali ya ɗago kansa tare da kallon Malam Arɗo yace.
“Malam J ɗina nefa!”.
Jinjina kai Malam Arɗo yayi cike da tausayawa yace.
“Eh shine Moddibo Allah ya karɓi Jameelu muyi masa addu'a Allah ya karɓi shahadarsa”.
Girgiza kai Moddibo yayi tare da cije lips ɗin sa duka biyu, kana ya runtse Idanunsa cikin wani irin yanayi mai wuya yace.
“Malam Arɗo mutuwar azaba suka masafa, ɗaure sa sukayi suka ajiye masa goran ruwan agabansa ta yanda yana ji yana gani bashi da damar sha sun barshi da azabar ƙishi”.
Kallonsa Malam Arɗo keyi cike da tausayawa yana ganin yanda zuciyarsa ke bugawa da ƙarfi.
Cikin wata raunan'niyar murya Moddibo ya cigaba da cewa.
“Malam ɗaure sa sukayi suka ajiye masa wayoyinsa agabansa ta yanda yana kallon muna kiransa bashi da damar ɗauka bare yace mukawo masa ɗauki”.
Sai kuma ya rintse idanunsa da masifan ƙarfi zuciyarsa na cigaba da buguwa da masifaffen ƙarfi kana yace.
“Ɗaure sa sukayi ta yanda yana ganin ga hanyar tsira sai dai bashi da damar kiran wani ya kawo masa ɗauki ɗaure sa fa sukayi ta yanda yana ganin kiran mu amma bashi da damar ɗauka”.
Jujjuya kansa ya farayi kamar zautacce hawaye na bin gefe da gefen idanunsa har suna shiga kunnensa cikin Muryan kuka yace.
“Ɗauresa fa sukayi ta yanda yana ganin kiran Abbansa bashi da damar ɗauka,Mutuwar azaba da raɗaɗi suka masa da ƙishi fa suka kasheshi”.
Kasa ƙarasa maganar yayi kawai ya fashe da matsanancin kuka mai tafiya da numfashi Atake numfashinsa ya ɗauke ya sake sumewa!.

Cikin sauri Malam Arɗo ya miƙe tare da kiran likitoci kana ya sanar dasu ya sake suma taruwa likitocin sukayi akansa kana suka shiga bashi temakon Gaggawa da kyar da temakon Allah suka samu ya farfaɗo ganin ya farfaɗo yasa Dr ya masa Alluran bacci Atake baccin wahala ya ɗauke sa.
Ajiyar zuciya Malam Arɗo ya sauƙe tare da miƙewa ya fita kana yayi dearling number Lamiɗo yana ɗauka yace.
“Ranka shi daɗe yaron nan fa gashi agigice yake baki ɗaya da zaran ya farfaɗo sunan Marigayi Jameelu yake kira, yana kiran sunan kuma zai sake suma!”.

Acan gidan Abba kuwa zaune yake afalonsa hannunsa riƙe da waya tunda suka dawo yake zaune awajen ya kasa koda motsawa se kwalin Gawar Jameelu daya zubawa Ido yana jujjuya wayar hannunsa ajiyar zuciya ya sauƙe tare da kiran number Ummi Yana Jin tayi picking ya fesar da numfashi kana yace.
“Fatima”.
Cike da mamaki Ummi tace.
“Abban Jameel”. Jin muryansa.
Cikin raunin murya ya sake cewa.
“Fatima”.
Anutse Ummi ta amsa da.
“Na'am”.
Runtse Idanunsa yayi kana yasake cewa.
“Fatima”.
Cikin dakiya Ummi da taji zuciyarta ya tsinke da Masifar ƙarfi tace.
“Na'am Abban Jameel ka faɗa min me yasamu Jameelu na sun kira ne ko kuma yaya!?”.
Cikin rauni yace.
“Hmmm”.
ya faɗa tare da katse kiran kana ya fito da Number Malam Ahmad.

Malam Ahmad na

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login