Showing 90001 words to 93000 words out of 417803 words

Chapter 31 - Sakayya By Aisha Aliyu Garkuwa

ya koma Adamawa dashi da Abba suka tafi.

A ɓangaren Khausar kuwa tunda daga ranan da Hajja Nana tayi mata maganar aure ta watsar da maganar kasancewar Momynta bata sake yi mata maganar ba ita ma bata sake tada maganar ba hakan yasa bata ɗauki maganar da muhimmanci ba ita kuwa Mommy tasa aranta tun daga Ramadan ya kawo kai ta samu dama ta yanda zata roƙowa ƴar ta al'khairi idan har Aliyu al'khairi ne agareta Allah ya tabbatar mata da al'khairi idan kuma ba al'khairi bane Allah ya zaɓa mata mafi al'khairi shima kuma Allah ya musanya masa da mafi al'khairi.

Yau ya rage azumi saura kwana biyu da hantsi Mommy na zaune afalo taji Sallamar sabon mai gadinsu da aka kawo kallon Khausar dake riƙe da hisnul Muslim tana Azkhar tayi sai kuma ta maida kallonta ga Haiydar dake danna wayarta ta gyara zamanta tare da cewa.
“Haidar jeka duba lafiya Namadi ke Sallama”.
Kai Haiydar ya gyaɗa kana yace.
“Toh Mommy”.
Sannan ya miƙe ya fita.
Kallon Namadi dake tsaye yayi kana yace.
“Lafiya kuwa”.
Kai Namadi ya gyaɗa tare da faɗin.
“Kayane Alhaji ya aiko dasu Azo ashiga dashi ciki”.
“Ok kashigo dasu”. Ya faɗa tare da juyawa ya koma ciki.

Kallon Mommy Haiydar yayi kana yace.
“Kayan azumine Abbah ya aiko dasu shine Namadi zai shigo dasu”.
Jinjina kai Mommy tayi tare da cewa.
“Ok”.
Da Sallama Namadi yashigo kansa ɗauke da buhun shin kafa ya ajiye a store kana ya koma ya ɗauko na ɗanyen shinka yakai, sannan ya kuma kimawa ya rinƙa shigo da catton ɗin indomie, Catoon ɗin Spaghetti, Cotton ɗin Macoroni, Couscous, Buhun fulawa, Buhun niƙeƙƙen garin gero na kunu, buhun wake, buhun sugar Corn Flakes, Madara, Patoto, Doya Crate din ƙwoyi Jarkan mai Jarkan man ja haka ya riƙa shigowa da tarkacen kayan buƙata na Ramadan.

Kamar yanda ya kawo sashen su Khausar haka ya kai sashen Hajiya Bunayya.

Yayinda hakan take a kowani gida haka magidanta suka riƙa shiga da kayan azumi domin shiryawa wannan wata mai falala.

Acan ɓangaren gidansu Moddibo kuwa shida M Jameel amota Moddibo ke driving yayin da M Jameel ke gefen mai zaman banza sai kuma wani yaro daga baya mai suna Iro wanda ke musu aika hong sukayi aƙofar gidansu Moddibo kana suka shiga cikin gidan bayan Iro ya fita ya buɗe musu.
Innayi na zaune atsakar gida akan kujera ƴar tsugunno taji ƙaran mota na shiga cikin harabar gidan aranta tace yau lafiya Moddibo ke shigowa da mota har cikin gidan.
Moddibo kuwa kusa da Innayi yayi Parking motar tare da buɗe Murfin motar ya zira ƙafarsa ɗaya awaje ɗaya kuma na ciki M Jameel da Sadik kuma suka fita kusa da Innayi M Jameel ya zauna shi kuwa Sadik Boot ɗin motar ya buɗe tare da fito da buhun far n gero, Buhun wake, Buhun shinkafa ɗanye da gumi, Catoon ɗin indomie, Catoon, Spaghetti, Bushesh-shen kifi crate ɗin ƙwoyi, Gongwanaye mayen madara da Vournvita buhun, Sugar kwalin Lipton sai kuma naman rago da aka gyara gaba ɗaya ga kuma na shanu ga kifaye duk Sadik yasa su a fridge

Kallon Moddibo Innayi tayi sai kuma ta maida kallonta kan M Jameel dake kusa da ita tayi tare da cewa.
“Lalle kayan Azumi sun saƙƙo ga Azumi sai ƙaratowa yake yau saura kwana biyu ko uku”.
Kai M Jameel ya gyaɗa kana yace.
“Ai dai kam Innayi azumi yazo”.
Ya ida maganar tare dasa hannu acikin aljihunsa ya ciro Bandir ɗin kuɗi kimanin dubu ɗari ya miƙawa Innayi tare da faɗin.
“Innayi gashi babu yanda banyi da Moddibo ba yabarni in saya miki kayan Azumi amma dake ɗan baƙin haline baya so in samu lada yaƙi furrr yace komai shi zai siya gashi wannan ki riƙe kiyi yadda kika ga dama dasu”.

Kallon kuɗin Innayi tare da Girgiza kai kana tace.
“Ayyah Jameel am bana son wannan shungullan yanzu ni kuma me zanyi da wannan kuɗin kabar su Jameel am ni ba ɓuƙatar su nake ba”.

M Jameel kuwa zama ya gyara tare da fuskantar Innayi da kyau kana cikin wata raunan'niyar Murya ya lumshe idanunsa tare da cewa.
“Tunda muke tare daku tsawon shekaru Innayi daga ke har Moddibo ban taɓa ɗaukar abu in baku ku karɓa ba, duk abinda na baku sai kun mayar min dashi baya, ban sani ba wataƙil shi Moddibo yana ɗaukar Maganar Aunty Karima keyi amatsayin matakin ƙin karɓan abu awajena”.
Lumshe idanu Moddibo yayi tare da jingina kansa da Murfin motar yana sauraron abinda aminsa ke faɗa.
Ita kuwa Innayi idanu ta zuba masa tana nazarin kalamansa.

M Jameel ya cigaba da cewa.
“Abinda Moddibo bai saniba koya karɓi abu awajena ko karya karɓa ita gani take komai na rayuwarsa Ni nake masa dan haka gwara ma ya karɓa idan yaso ta tuhumesa da tushe”.
Ya furzar da iska mai zafi kana ya cigaba da cewa.
“Kema kuma Innayi ina ganin maganar mutane kike ɗauka da suke cewa Babana ke daukar ɗawainiyar ku amma ni nasan ba haka bane. Allah ne kaɗai ya barwa kansa sanin yanda kuke rayuwarku duk da aminantakar dake tsakani na da Moddibo har yau ɗin nan bansan taya kuke mu'amala da rayuwarku ba bansan ta yanda kuke samun abinda kuke biyan buƙatar rayuwarku ba kama daga karatun Moddibo kab babu aƙaramar makaranta zuwa hidimar fitanmu Makarantar waje ina sane ina kuma tunawa Naira biyar kun ƙi karɓan tallafi awajen Babana ku keyin komai abinda yasa mutanen gari suke ɗaukar haka suna lura da Moddibo ba wani sana'a yake ba sannan ana mamakin irin buƙatun da kuke yafi ƙarfin samun ku ko kuma tattalin ku Innayi!”.

Dariya mara sauti Innayi tayi tare da jinjina kai kana ta tsaida idanunta akan Moddibo daya dafe kansa sai kuma ta kalli M Jameel daya dafe kansa tayi murmushi tare da cewa.
“Abun aduhu ne Jamilu barshi kawai babu ɓuƙatar sai ansani, shi kansa Moddibo bai san komai akan al'amuran rayuwar nan ba bare ya gaya maka”.
Moddibo kuwa Sanyayyar Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da kallon M Jameel ya buɗe masa hannunsa alamar kaji dai nima bansan komai ba a cikin abubuwan da kake son sani.
Sai kuma Moddibo ya numfasa tare da lumshe Idanunsa kana cikin sanyin murya mai cike da rauni ya kalli Innayi tare da cewa.
“Kagani ni kaina ban san komai ba kama daga lokacin dana ke karatu.
Ni dai nasan tana min komai idan nayi magana sai tace gadon Iyayena da suka bar min ne, bansan inda ta ɓoye kuɗin ba na girma ma yanzu ta bani gadona ahannuna taƙi ko gani take har yanzu ban kai ba oho.
Kai kuma kana tuhumata kamar acikin aminantakar mu akwai abinda nake ɓoye maka, bayan kuma J ka sani babu wani shamaƙi tsakaninmu”.
Ya ƙarisa mgnar tare da
runtse idanunsa a take kuma ya buɗe su akan M Jameel da shima shi yake kallo, a hankali ya furzar da iska mai sanyi tare da cewa.
“J ba'ayi wani abu na duniya da ni Aliyu zan iya ɓoye maka ba, aminantakar mu ta wuce babin in ɓoye maka wani abu”.
Jinjina kai M Jameel yayi yana kallon amininsa cike da tausayawa.

Innayi kuwa murmushi tayi tare da jinjina kai amma ba tace komaiba ba.
Moddibo kuwa kallon Innayi yayi kana yace.
“Yanzu kuma hidimar da nake kai kan ka kasan inda nake samu tunda muna aiki kuma ana biyan mu sannan kuma. Ni kaina wataran saidai inga tayi min abu misali yanzu mota dai ni bansa araina ba kafin in ankara har ta saya anyi komai kafin ma mu dawo”.
Numfashi ya sauke kana ya cigaba da cewa.
“Babu yanda banyi da ita ta faɗa min ba idan ma a kuɗin gado nane tunda na girma ta bani abuna zan iya sarrafawa”.
Hararansa Innayi tayi kana tace.
“Anƙi abaka”.
Shiru M Jameel da Moddibo kai ya jinjina ba tare da tace komai ba sai tsirawa Innayi ido da sukayi.
Miƙewa M Jameel yayi yace.
“Bari mu tafi Innayi”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Allah ya tsare”
Suka amsa da.
Amin
Shi kuwa Moddibo Kallon Innayi yayi kana yace.
“Innayi har yanzu yarinyar nan bata zoba?"
Jinjina kai Innayi tayi tare da cewa.
“Dama wannan shekarar Ummin Asma'u tace in bari zata turo min Asma'u dan ƴaƴan ƙabilun in sun zo gaba ɗaya lalata sukeyi sannan basajin magana to Asma'u zata zo ta tayani”.
Cikin kula ya kalli Innayi kana yace.
“Innayi anya Asma'u zata iya ayyukan da suna da yawa fa kinga akwai abincin da za'a dinga fitarwa na masallaci”.
Jinjina kai Innayi tayi kana tace.
“Zamu iya ai naga Asma'u tana da kuzari kuma nima da kuzarina da kuma lafiyata zan iya”.
Kai ya gyaɗa kana yace.
“Toh Allah ya temaka”.
Ta amsa da.
“Ameen”,Kana tace.
“Ai girkin ma na iya tsawon kwana goma sha biyar ne zamuyi”.
Kai M Jameel ya Jinjina kana yace.
”Eh haka ne Innayi”.
Sallama suka mata sannan M Jameel ya Miƙe.
Dama already Moddibo na cikin motar yaja suka tafi.

Kai tsaye kasuwa Moddibo ya sake nufa Kallonsa M Jameel yayi kana yace.
“Mai zamu kuma yi a kasuwa?".
Ba tare da Moddibo ya juya ya kallesa ba ya lumshe idanunsa kana yace.
“Idan muka je za kaga ni”.
Shiru M Jameel yayi har suka isa kasuwar kamar yanda Moddibo yayiwa Innayi siyayya haka ya sake sayan wasu Kallonsa M Jameel yayi tare da cewa.
“Wannan kayan na waye haka?”.
Anutse Moddibo yace.
“Ina ruwanka”.
Daga haka yaja motar suka fita kai tsaye hanyar gidan Ummi ya nufa.
Da sauri M Jameel ya juya ya kallesa kana yace.
“Ai baka isa ba Ummi ba zata karba ba ai kai ma idan zan kaiwa Innayi abu hana wa kakeyi”.
Moddibo kuwa baki ya taɓe kana yace.
“Ai ba Umminka kai ka ɗai bane harda ni dan haka kabarni in samu lada”.
Murmushi M Jameel yayi Amma baice komaiba.


Koda suka isa aka shigar da kaya, M Jameel yayi wa Ummu bayanin yadda sukayi.
Ita kam Ummi sai ta riƙa sakin murmushi bayan ta gama jin jawabin M Jameel sai kuma ta kalli uban kayan da aka shigo dasu ta juya ta kalli Moddibo daya tanƙwashe ƙafafunsa tare da sunkuyar da kansa ƙasa tayi murmushi fuskarta ɗauke da murmushi cike da ƙaunarsu ta saki ajiyar zuciya kana tace.
“Ubangiji Allah ya Albarkanci rayuwar ku Ubangiji Allah ya baku ƴaƴan da zasuyi muku biyayya fiye da yanda kuke mana”.
Atare suka amsa da.
“Ameen”, Bayan sun sake taɓa hira suka miƙe tare da yimata sallama suka tafi...!







By
*GARKUWAR MARUBUTA*
[7/17, 5:24 AM] AMINA KABIR CAPS: 📝✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇

*SAKAYYAH*
_Pape 14_

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*Free page ne ƴar uwa saura uku kacal mu gama free page, har yanzu baki makaraba ki biya*

*Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa ki biya ki karanta cikin Aminci da salama babu haƙƙin wani kanki. SAKAYYAH 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. Kana sai in saki a Group, ɗin da zan rinƙa posting.*


*WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*

_Ina kuke Ma'aurata masu sha'awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau'ikan sirrin sahihan magungunan ma'aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki...Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba'a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al'khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace, ka masin Daɗi har Maɗigan Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni'ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni'imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan, da dai sauransu...Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu'umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba...._ _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu'uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_
_Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)...Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu'uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa 'yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma'aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba'a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma'aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 09097853276 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah 'yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci...._



🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,


Washe garin washe gari.
Da daddare watan Ramadan ya bayyana.

Haka yasa dukkan ɗauka cin Musliman duniya suka cika da farin ciki tare da yin niyan ɗaukar azumin watan Ramadan ɗin, kana kowa yana shirya bukatunsa dan miƙa su ga Ubangiji Mabuwayi gagara Misali.

Washe gari Ranar Litinin gaba ɗaya al'ummar Musulman duniya sun tashi da azumin watan Ramadan abakinsu gaba ɗaya ɗaukan farko ɗauka ɗaya akayi duk duniya abinda aka daɗe ba'a yiba tsawon lokaci mai yawa wannan shekarar ansamu kowa na cike da farin cikin wannan al'amari azuciyar musulmai.

Da daddare Misalin ƙarfe 9:00 pm Babban masallacin juma'a dake ƙofar gidan Sarki cike yake da.
Al'ummar Musulmi maza da mata wanda duk shekara idan aka shigo Ramadan bayan an idar da sallar isha'i M Jameel da Moddibo ke gabatar da Tafseer Alkur'ani mai girma duk shekara Moddibo ke jan baƙi yayin da M Jameel keyin Tafseer yana fassarawa.

Masha Allah kamar yanda suka gabatar ashekarar Bara ayau ma hakane Cikin Masallacin Maƙil yake da dubban jama'a yayin da Moddibo ke zaune akan wani ƙayatenccen kujera gabansu babban table ne dake ɗauke da system jikinsa sanye da Jallabiya Armygreen mai yauƙi da sansti kana gaba ɗaya ilahirin jikinsa na fitar da sanyayyan ƙamshi tularensa, idanunsa alumshe yana motsa laɓɓansa alamar tasbihi yake.
Yayin da M Jameel ke zaune gefensa cikin shiga na alfarma Bugaggiyar shadda ce fara sol anyi masa ɗin kin ƴar ciki da gariya sai hula baƙa sosai yayi kyau gaban jikin rigarsa maƙale da microphone.

Cikin tsantsar nutsuwa da kamala M Jameel ya hura microphone ɗin tare da gyara zamansa kana yace.
_“A'uzubillahi Minal Shaiɗanir rajeem Bismillahir Rahmanir Rahim. Innal hamdillah Nahmud wanastainuhu wanastaghfiru, wa'nazubillahi min shuriri anfusna, wamin sayyi ati a'amalina, manyah dillahu fala mudillah waman yudil fala hadiyala, Wa'ash hadu Allah ilahalillahu wahdahu lasharika lahu Wa'ash hadu Anna Muhammad Abduhu warasuluhu._
Ya ɗan sauƙe numfashi tare da sauƙe numfashi kana ya sakin ajiyar zuciya sannan ya cigaba da cewa.
_“Ya ayyuhallazina amanut taƙullaha haƙƙu tuƙatihi wala ta mutunna illah wa'antum Muslimun ya ayyuhan nabiyu taƙu rabbakummalazi wahida wakalaƙa minha zaujuha wabassa min huma rijalan kasiran wani sa'a wattaƙullahal lazi tasa aluna bihi wal arhama innalaha bikum kana alaikum raƙibaaa_

Baki ɗaya ciki da wajen masallacin ya kacame da sowa da sassarfan waɗanda ke harabar masallacin da suke shigowa da sassarfa.

M Jameel kuwa idanu ya lumshe tare da buɗesu kana yace.
“Amma ba'ad faya Ikhwatul musulmi Assalamu alaikum Warahmatullah Wabarkatuhu”.

Gaba ɗaya cikin masallacin da harabarsa suka amsa da faɗin. “Wa'alaikum Salam Warahmatullah wabarkatuhu”.
Gyara zama M Jameel ya yi tare da kallon ɗumbin jama'ar dake masallacin kana a hankali ya numfasa sannan yace.
“Insha Allahu zamu cigaba da Tafsirin Alkur'ani mai girma kamar yadda muka saba, zamu kuma ɗaura daga inda muka tsaya bara. A cikin suratul Nisi'i awancan shekarar mun tsaya akan aya na ɗaya wanda ya zamana shi muka karanta Ramadan ya ƙare cikin ikon Allah gashi ya sake sada mu acikin watan wanda da yawa wasu daga cikin wanda mukayi tafsiri dasu wancan shekarar yanzu basa nan kana da yawa wanda muka fara ayau da ƙyar zamu ga ƙarshen amma muna roƙon Allah daya nuna mana ƙarshen wannan wata mai falala da kuma al'barka lfy”.

Baki ɗaya wajen suka amsa da faɗin.
“Ameen”.
Domin wasu daga cikin masu sauraron karatun suna zuwa ne saboda yanda M Jameel ya ƙware awajen Tafseer gashi kuma yana da zafi nama da kwarjinin tafsir.
Juyawa M Jameel yayi tare da kallon Moddibo da kansa ke ƙasa ya tsirawa System ɗin sa idanu ya gyara zamansa tare da cewa.
“Bismillaha Alaramma jeka cikin Suratul Nisa'i ka karanto mana muji abinda Allah ma ɗauka kin sarki yake faɗa”.

Jinjina kai Moddibo yayi tare da gyara zamansa kana ya jingina bayansa da jikin kujera sannan ya lumshe idanunsa cike da nutsuwa ya motsa laɓɓansa kana yayi gyaran Murya cikin Sanyayyar muryarsa mai daɗin saura da sanya nutsuwa da ratsa zuciyar bani adam ya fara kamar haka;
“Bismillahir Rahmanir.

Gaba ɗaya illahirin yaƙin da sautin muryarsa ya ratsa kunnuwansa, sit sukayi babu abinda wani sauti ko hayaniya, wurin yayi sit kai kace babu mai rai a wurin bare numfashi, gaba ɗaya an nitsu, wanda hakan kuma a jinin Modibbo yake, duk hayaniyar wuri muddin yayi basmalla a take kab za'a nutsu.

Idanunsa ya ɗan lumshe kana ya buɗe su a hankali yana kallon taron al'ummar Annabi dake tare maƙil, cike da nitsuwa ya fara karatu cikin zaƙin murya ya kawo aya ta biyu cikin suratul

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login