Showing 279001 words to 282000 words out of 417803 words

Chapter 94 - Sakayya By Aisha Aliyu Garkuwa

samu abin kushewa ba.

Na forkon ta buɗe wanda tun a gida Asma'u ta haɗa dukkan abin buƙata da kuma kayan da Khausar ɗin zata saka har gama bikin.
Wata Dubai Abaya Ummi ta zaro mata, Black color sai kuma zare golding color da aka yiwa rigar aiki zuɓi na musamman mai masifar kyau da ratsin fari kaɗan rigar irin mai ɗan faɗin nanne musamman daga sama. sai kuma ta zaro mata wani tattausan mondo Wanda bazai wuce iya guiwarta ba, sai bra su duka fararare, turare ta zaro kusan kala uku ta feshesu dashi. Kana ta ɗauko Kulaccar sirri wacce ta saya wurin AYSHA ALIYU GARKUWA, miƙa mata tayi tare da cewa.
Gashi ki shafa wannan.
Amsa Khausar ɗin tayi tare da cewa.
“Ayyah Ummi a tubke min gashin nan”.
To Ummin tace tare da fara tubke mata shin.
Tana gama ta nufi falo tare da cewa.
In kin gama kizo, kai kawai Khausar ɗin ta gyaɗa mata.

A can Falo kuwa Hajia Bunayyah ce ta miƙe jiki a salube ta shige ɗakin da nanne masauƙinsa inta da Aunty Hajara da kuma Aunty Ruƙayya.
Da sauri ta maida ƙofar ɗakin ta rufe tare da dannawa Hajia Lami kira a wayarta.
Bugu ɗaya ana biyu Hajia Lami ta ɗauka tare da cewa.
“Mutanen Marocco yaya akayi?”.
Cikin fesar da numfashi mai zafi Hajia Bunayyah tayi kwafa tare da cewa.
“Wllhi Allah Hajia Lami munyi babbar asara daba Samira wannan yaron ya auraba. Na rantse miki da Allah munyi asarar samun daular duniya.
Wannan shegiyar yarinya mai idanu kamar na mujiya ko yaushe suna lunshe kamar mai jin bacci anya ma kuwa ba idanun dunane da ita ba.
Kinga tayi nisa ta barmu da Naseer ɗin da ubansa ko Sarkin tasha bai taɓa samuba, ke kuwa ta bar miki ƴa da wari da yoyon ƙazanta”.
Nannauyan numfashi Hajia Lami ta fesar tare da cewa.
“Toh yanzu me abinyi?".
Cikin tsananin hasada Hajia Bunayyah ta buga hannunta da jikin gini tare da cewa.
“Wallahi Allah ni dai na rantse da Allah, sai na kashe auren nan, koda zan tafi tsirarane sai na watsa aurenan, muddin ina raye wlh Khausar bazata ji daɗin rayuwarta a gidan nan ba, idan zaki zo mu haɗa hannun da ƙarfe mu tumɓuke auren nan, mu shiga da Samira gidan to ki fara shiri, domin ina dawowa zamu bazama".
Cikin ƙeƙashewae zuciya Hajia Lami tace.
“Ai ke dai Allah ya dawo dake lafiya, Ƙawata na sama mana labarin wani ƙasurgumin boka a ƙasar Niger cikin dajin Damagaran ance min aikinshi kamar yankan wuƙane, babu haufi shi bazama ka biyaba sai buƙatar ka ta biya”.
Cikin yaƙini tace.
“Ke dai ki shirya ina dawowa zamu tafi”.
Daga nan suka katse kiran kana ta fito.

A falon kuwa da sauri su Ummi suka ƙali ƙofar falon jin sallamar Jakadiya da kuma su Lalla Khadijah da Hafsat.
Cikin sakin fuska Ummi da Innayi suka amsa tare da nuna musu wurin zama.
Zama sukayi cikin sakin fuska da cikekken fulatancinsu da suka iya ta sanadin Didi suka kalli su gaisa cikin mutumtaka.
Jakadiyace ta kalli Lalla Hafsat tare da juyowa ta kalli innayi kana tace.
“Dama yayun Aliyu ne suka zo ganin ƙanwar tasu tare da marabtanta.
Cikin jin dadi Ummi tace.
“Ayyah to babu laifi barin in kirawota”.
Sai kuma ta mike ta nufi dakin da Khausar take.
“Masha Allah diyata kinga yadda kikayi kyau kuwa". Murmushi tayi tare da rufe fuskarta da tafukan hannunta.
Ita kuwa Ummi kamo hannunta tayi ta ajiyeta tare da cewa.
Zo mu je ki gaisa da yayun Modibbo.
Da sauri ta sunkuyar da kai ganin yadda Ummi ke gyara mata tarhan da tayi da gyalen abayar sosai tayi masifar kyau ta fito cas da ita a matashiyar budurwar yar kimanin shekaru 19 zuwa 20. Duk da rigar nada faɗi bai hana kyan surar jikinta bayyana ba.

A hankali suka fito falon.
Khausar kam kanta a ƙasa take wani irin amintaccen taku mai cike da nitsuwa.

Da sauri Lalla Khadijah ta miƙe tsaye lokacin da suka iso tsakiyar falon.
Hannunta ta buɗewa Khausar tare da faɗin.
“Wow Masha Allah, Didi dai ta samu ƙarin diya wannan ai in an ganta da Rahama kai kace tagwayene". Murmushi mai yelwa Lalla Hafsat ma tayi tare da miƙawa Khausar hannun a hankali Khausar ta ɗan janye jikinta dan jikin Lalla Khadijah ta ɗan saketa.

Ruggumeta Hafsat tayi tare da cewa.
“Masha Allah, Khausar muna farin ciki da shigarki Mouley family. Allah ya baki hikima da basirar zama tsakiyar wannan Fada”.
Kusan a tare suka amsa da Amin ita kuwa Khausar yatsun hannunta take ɗan murza tare da ɗan rusunawa kana ta gaidasu.
Amsawa sukayi suna mai ƙare mata kallo. Cikin ɗan sakin fuska Hafsat tace.
“Ai wannan komai nata kamar na Rahama zaiyi mata dai-dai”.
Cikin girmamawa Jakadiyarsu tace.
“Sosai ma kuwa”. Ita kuwa Hafsat hannun Khausar ta kamo tare da cewa.
“Takalmi sise nawa kike sawa”.
Cikin sanyin murya tace.
“37”. Da sauri Khadijah tace.
“uhm jinjina sise ɗin Rahama kenan”.
Sai kuma ita Khadijah ta kamo hannun Khausar tare da ajiyeta gefen Innayi kana tace.
“Zauna abinki. Didi da Niyna sunyi miki Barka da zuwa, masarautar Mouley. Yanzu mu zamu fita ne.”
A hankali tace.
“Allah ya kiyaye hanya."
Amin sukace a tare sai kuma suka ɗan kalli Asma'u tare dayi mata murmushi suke.
“Ke me sunanki?”.
“Asma'u”.
Murmushi Khadijah tayi kana tace.
“Yauwa toh in ba matsala innayi zamu tafi da ita, ai kin san sise ɗin Khausar da kalanta ko?”.
Cikin fara'a Asma'u tace.
“Sosai ma kuwa, Nama fita sanin abinda yake mata kyau”.
Dariya sukayi ganin hararar da Khausar ta cilla mata..
Ummi kuwa murmushi kawai tayi.

Daga nan suka fita da Asma'u.

Sune basu dawoba sai gab da Maggarib.

Acan Side din da Modibbo yake kuwa.
Zaune yake shi da Ibrahim da Dr Jameel.
Cikin tsuke fuska ya kalli Dr Jameel dake zoro wayarsa daga aljihu.
“Baby”. Ya faɗa a saman lips enshi.
Sai kuma ya tsaida idonsa kan Modibbo da ya wani irin tsaresa da idanu.
A hankali yace.
“Yah dai Malam kallon nan fa?”.
Fuska Modibbo ya kuma tsukewa tare da cewa.
“Kaji tsoron Allah, Dr J kasani. Abinda kakeyi kana tafiya cikin fushin Ubangiji ne, kuma masifar zunubinka zaiyi ta bibiyarka tun anan gidan duniya, kasan cewa abinda kayiwa ƴaƴan wasu za'ayiwa ƴaƴan ka, shin me ribarka a cikin in har ka jazawa ahlinka. Ka tuna shifa zina tsananin muninsa yasa Allah baice kada kuyi zinaba, cewa yayi kadama ku kusaceshi fa. Shifa mazinaci baya zina har sai an zare mishi imaninshi. Kasan kuwa abinda Allah ya tanadarwa mazinata abinsha a cikin jahannama?”.
Cikin tsananin sanyin jiki Dr Jameel ya rumtse idanunsu tare da cewa.
“Nifa shiyasa badon Abualeey da kansa yace min dole in kasance kusa da kaina wlh bazanzoba sabida na lura kai mutumne mai tsaraɓe-tsaraɓen halal da haram”.
Cikin takaici Modibbo yace.
“Koda baka zo inda nakeba kasa a ranka in dai ina cikin ƙasarnan, sai na kasance tare da kai, na kuma yi al’ƙawari zan ƴaƙi shsiɗanin dake tare da kai, in Sha Allah sai ka dawo managarci tamkar J na”.
Murmushi Dr Jameel yayi tare da kallon hadimai guda huku da suka shigo da manyan jakukkuna guda biyar masu ɗauke da tambarin Anfaplace mall Marocco.
Da sauri Ibraahim ya miƙe tare da cewa.
“Ku shigo dasu cikin bedroom kada ku barsu a nan”.
Jin hakane yasa suka bishi a baya.
Kusan a tare suka shirya kayan cikin wodurob.

Daga bisani suka fito falon, a tsaye ya samu Dr Jameel.
“Mujeko Ibraahim”. Cewar Dr Jameel.
Kai Ibraahim ya gyaɗa tare da bin bayanshi sai kuma ya juyo ya kalli.
Moddibo dake cewa.
“Wai dan Allah Ibraahim sai yaushe za'a buɗeni in samu zuwa jam'in salla, wlh abinfa yana damuna.
Sassan numfashi Ibraahim ya fesar kana a hankali ya juyo ya dawo gaban Modibbo tare da cewa.
“Kayi haƙuri Yah Aleey in Sha Allah gobe dai a jam'i zakayi sallan magarib. Akwai babban dalilin ne da yasa ba'a barka ka fitoba.
Ƙwaffa Modibbo yayi tare da lumshe idonsa Allah ya sani suna ƙona mishi rai da batun hanashi jam'i da wotoyinsa.

Shi kuwa Ibraahim juyawa yayi yabi bayan Dr Jameel suka tafi.

Washe gari tun safe Dr Jameel da Jabeer bin Jabeer da kuma Ibrahim suka shigo wurin Modibbo.
Tare da wani Kekkyawan matashi wanda bazai wuce sa'an Modibbo ba.
Cikin sakin fuska matashin ya bawa Modibbo hannu tare da cewa.
“Sunana Zakariyya Khallin”.
Cikin ɗan sakin fuska Modibbo yace.
“Masha Allah”.
Ibrahim ne ya amshi mgnr da cewa.
“Yah Aleey Wannan ɗan Goggo Salma ne ƙanwar Abualeey. Shi a India yake shima likitane, taron gabatar da kaine ya kawoshi.”
Murmushi Modibbo yayi tare sake bashi hannun, shi kuwa Zakariyya ruggume Modibbo yayi tare da faɗin.
“Duk da zumuɗin Mami na rigata ganin ɗan yayanta”.
Shi kuwa Modibbo Ibraahim ya kalla jin yana cewa.
“Dr Jameel ma ɗan Goggonmu ne Aunty Sahrah itake bin Goggo Salam, kuma babanshi Aminin Abualeey ne ɗan ƙasar Turkey, duk dangin babanshi suna can”.
Dr Jameel kuwa numfashi ya ɗan fesar kana yace.
“Ni ya labarin Yusuf ne, kwana biyu bamuci wayaba”.
Da sauri Zakariyya yace.
“Ya tafi Mexico kasanshi ya nacewa Zeeyada yar Lalla Hafsat”.
Sai kuma ya kalli Modibbo tare da cewa.
“Yusuf ɗan Unclee Haroon Mouley ne, ƙanin Unlee Youseep Mouleey”.
Cikin fahimta Modibbo yace.
“Na fahimta, toh amman kuma tunda nazo banga Unclee Haroon ɗinba”.
Cikin sanyi Dr Jameel yace.
“Dashi da Mamina, da Abbana duk rana daya sukayi haɗari, su sun rasu shi kuwa har yau baida lfy tsawon shekaru ashirin da biyar kenan”.
Cikin sanyin jiki da tsananin tausayi Modibbo yace.
“Allah sarki Jameel Allah ya jiƙansu da rahama yasa sun huta shi kuma Unclee Haroon Allah ya ya bashi lfy”.
Da Amin suka amsa baki ɗayan su.
Shi kuwa Modibbo cikin sanyi ya kalli Dr Jameel tare da cewa.
“Dan J kabar abinda kakeyi ka zamewa Aunty Sahra da Abba al'waladussaliha ko dan basa raya ka zame musu sanadin samun lada”.
Cikin sanyi jiki Dr Jameel yayi ƙasa da kansa yana mai taunan lips inshi na ƙasa.
Shi kuwa Modibbo a raunace yace.
“Mu kuwa zamuci gaba dayi maka Addu'o'i Allah ya shiryeka”.
Amin suka amsa a tare.
Sai kuma Ibrahim yace.
“Yauwa mu shiga daga ciki masu gyara zasu shigo gyara nan ɗin".
Toh sukace kana suka shiga Corridor nan tare suka shiga ƙofar nan ta dama inda Modibbo yake, a falon suka zauna.
Zamansu ba jimawa Rahman ta shigo da hadimai da sunka kawo musu breakfast.

Acan Side ɗin dasu Khausar suke kuwa, suma tuni an kawo musu breakfast, dama dukkan abin buƙata.

A nan wannan falon kuwa, zuwa bayan an isar da sallam la'asar duk an gama ƙawatashi da shiryashi irin shirin nan na al'farmar da kamala.
Kujerun gaba ɗaya an mannasu da ginin duk da girman falon wai dan a samu ya ƙara girma.
Wata kujera mai zaman mutum biyu aka ajiye daka san tsakiyar falon. Sai kuma wasu datsa-datsan Turkiy Carpet masu masifar kyau da taushi. Da aka shimfiɗa a gaban kujerar, wacce duk ta inda ka shigo zaka kalli waɗanda ke ka kujerar. Sai kuma wasu tukwanen kasa masu zanen ɗawisu da aka jere gefe da gefen kujerar yayinda daga sama tukwanen kuwa, gashin gezan ɗawisunne a cikin mai cikekken launi daban-daban, sai kuma wani tim-tim da aka ajiye a guda biyu a gaban kujerar wanda da bisa alamun anan waɗanda zasu zauna kan kujerar zasu daura sawunsu.
Sai kuma hadimai guda uku ɗaya na bayan kujerar ɗaya na gefen dama ɗaya na gefen hagu.
Kana duk inda ka wulga idanunka a falan kaskon turaren wutane mai fasar da sassayan kanshi.
Sai kuma sanyin ac dake ratsa ko ina, an sassake labulayen, tare da kuna wutan falon baki ɗaya a ƙalla falon zai iya ɗaukan mutun settun zuwa tamanin.

A nan sashin dasu Khausar suke kuwa.
Wasu matane guda biyu, aka kawo dan shirya kausar, Kasancewarsu ƙwararrun masu shirya amare, wanda suke zaune acikin masarautar musamman domin gyara da kuma ƙyale amare.
Wata Haɗaddiyar rigar Caftan and Takchitas suka sanyawa Khausar din, wacce ta kasance farace ƙal, mai ɗauke da ratsin adon gold da kuma sky blue wato kalan sararin samaniya.
Rigace me tsananin kyau da takasance traditional wedding dress wanda ƴan masarautar Mouley morocco ke sawa lokacin biki, sosai rigar ta zauna ajikin kausar, tayi mata ɗas tare da k’ara bayyana tsantsar kyaunta, musamman da suka ɗaura mata tsadadden sarƙan gold da kuma ƴan kunne haɗi da awarwaro da kuma zobunan gold, wanda suka ƙara cika adon nata, babban mayafin daya kasance fari ƙal, wanda aka kewaye bakinsa da tsararren ado me kalan sky blue, suka sanya mata akanta, wanda ya sauko har yakai ga ya rufe kyakkyawar fuskarta.
Masha Allah da wannan tsananin kyaun da kausar tayi, wanda kallo ɗaya zakayi mata kasan ta cika mace har mace, saboda tsananin kyaun da traditional wedding dress din yayi mata, a kyawawan ƙafafunta kuwa wani haɗadɗen takalmi irin nasu na sarauta me kalan sararin samaniya suka sanya mata, daya sake k’awata shigan nata. Duk da kafafun nata ba lalle dan innayi ta hana a saka mata.

Su kansu sun yaba da kyaun yarinyar domin tunda suke shirya amare basu taɓa shirya amaryar da tayi kyau sosai kamar wannan ba, kai kace asalinta balarabiyar Morocco’n ce, musamman yanda jikinta ke fitar da sihirtaccen k’amshi kulaccar sirri da me matuk’ar ratsa zuciya haɗi da daɗin shaƙa.

“Masha Allah, tsarki ya tabbata ga Ubangiji me tsara kyawawan halittun da yayi wannan halittar da ta kasance tamkar farin fure acikin tarin jajayen furanni, Allahumma Barik.”

Cewar Lalla Khadija da shigowarta kenan, cikin shigar ƙasaita.

“Masha Allah.”
Ta kuma faɗa tana me miƙawa su Asma’u, Dija da kuma Asiya kayan dake hannunta, wanda suna ɗaya daga cikin kayan da aka kawowa kausar jiya, dogayen riguna ne guda uku masu matukar kyau.
“Ga wannan kuma ku sanya, domin naga kaman kune ƙawayen amarya.”
Amsa sukayi suna godiya..


*Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa ki biya ki karanta abinki cikin Salamah 1k nefa kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP NUMBER'N 09097853276, in tura miki littafin ki karanta abinki cikin salama kana in saki a Group ɗin*



By
*GARKUWAR MARUBUTA*SAKAYAH

45

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇



Assalamu alaikum mutanan arziki masoya kamshi ma abota kamshi Amaren kamshi masu jargon kamshi Yammata wadanda sukasan darajar kamshi ni Aysha Aliyu Garkuwa na kawo muku tallan wasu Amintattun turarukana masu matukar kamshi da Kama jiki
Masu saukin farashi sannan ga biyan bukata
Yarhjya_incense_and_more
Ta shirya tsaf domin ta gwangwajeku da Turaruka na alfarma
Farar khumrah
Bakar khumrah
Turaren Wanka
Oil 6ml 1
Oil 12ml 1
Turaren fesawa 24 hours guda 1
Duka Akan 10k kacal
Sannan kayanta suna tafiyane da guarantee duk wacce tasiya taji babu kamshin nan na alfarma ko kuma basuda lasting to tayi alkawarin mayar muku da kudinku
Wannan garabasar zata kare on 5th September insha Allah
Ku hanzarta ku mallaki naku domin kayan yarhjya babu Danasani a cikinsa saidai kuyi alfahri da siyan kayanta
Account number 1419787445 Amina Umar usman access bank
Kitura evidence of payment to
08092664954
Kuyi saving number TA domin ci gaba da ganin Turaruka Kala Kala


Yayin da gaba dakin sune bin Khausar kallon, sabida yadda annurinta ya cika fuskarta, tare da haska ɗakin, lokaci daya ta zama tamkar tauraruwar da tafi ko wacce haske acikin duniya.

Acan cikin sauran ɗakunan kuwa, tuni su Ummi da kuma su Aunty Hajara, Aunty rukayya, Hajiya Bunayya, sun sha kwalliya cikin shigar Alfarma, had’i da kece raini, sun kuwa yi matukar kyau, domin hatta su Innayi da Hajja Nana ba abarsu a baya ba, musamman Hajja Nana duk tsufanta, bai hanata yin kyau cikin doguwar rigar data sanya ba kasancewarta ƴar duma-duman tsohuwa kai hakama bata shekarun da take da suba, dukansu sunyi kyau sai ɗaukar idanu suke, kowanne daga cikinsu kuwa kaga ni kasan yana cikin farin ciki, musamman Innayi da ayau farincikin dake kan fuskarta ya kasa ɓuya.

Hakama ɓanƙaren su Abban Jameel da Lamiɗo da Malam Arɗo Bappa Jimeta da Haiydar harma da Dr Jameel sosai sukayi shiga ta al'farmar.
Su tuni sun iso wurin taron bisa jagorancin Sheykh Jabeer.

Hakama su Innayi suma tuni sun sauƙo bisa jagorancin innayi, sun zauna a gefen inda su Abban Jameel suke, don dama an ware musu wurin zamansu na musamman.

Aɓangaren Moddibo kuwa tsaye yake acikin cikin ɗakin da ya lura nanne ɗakin Ibraahim, yayinda yake cikin wata irin Amintacceyar shiga ta al'farmar da kamala.
Dandatstsiyar jalabiya ace a jikinshi Sky blue mai masifar kyau da shaƙi sai ɗauke ido take tamkar madubi, sai kuma wata tattausar Al'kebba fara ƙal mai ratsin Sky blue da golding kala na zaren da aka yayyarfawa alkebbar wani irin Mashahurin aiki mai cike da tambarin masarautar Mouley ɗin. Sai kuma farin hirami mai gidan dara-dara Sky Blue, wow Masha Allah. Wani irin sheƙi da ƙyalli yakeyi kai kace taurarone sajenshi kuwa sai walwali yakeyi fuskarshi ta fito ras.
Cikin ɗan fesar da numfashi yace.
“Anya zan iya wannan tsaraɓe-tsaraɓen kuwa”.
Yayi mgnar cikin ƙosawa da yadda ake wani shiryashi kamar yaro.
Murmushi Ibraahim yayi, had’i da cewa.
“A’a zaka iya, mana, kayi haƙuri kasan al’adarmu ce anan, duk ranar da za’ayi wani abu na musamman, shirya mutum ake, musamman irinka masu girman daraja.”
Kai Modibbo ya girgiza cikin yanayin k’osawa yace
“Afwan ni a barni haka”.

“A’a Yah Aleey dan Allah, kasan nan masarauta ne, kuma kana da matsayi na musamman, kadai bari ashirya kan.”

Kokarin magana yake, sai kuma ya fasa saboda Sheykh Jabir daya shigo, cikin shiga ta alfarmar da takasance shigarsa akoda, wanda a wurinshi Modibbo ya gaji don irin wannan shigar, ganin Modibbo’n azaune yasa shi, bud’e baki da mamaki yace.

“Har yanzu Aleeyu basu gama shiryaka ba, lokaci yana k’urewa, tashi maza a ƙarisa shirya ka da hanzari.”

Ya k’are maganar yana me jawo hannunsa, suka nufi gaban dressing mirror wanda yake cike tab da ababen gyaran jiki, komai na wurin tsabtsab yake, komai neat da alama Ibraahim din gwanin tsabta ne.

Suna isa wurin ɗaya daga cikin hadiman ya ja mishi kujera, ya zauna, bisa umarnin Sheykh Jabeer way’annan hadiman suka ci gaba da shirya, shirin da ya bayyana cikakken kwarjininsa me burgewa.
“Masha Allah.”
Ibraahim ya fad’a lokacin da kwararrun hadiman nan suka nad’a masa kyakkyawan farin hirami me ratsin adon sky blue akansa, da yayi matuk’ar k’ara bayyana kwarjininsa, still suka gyara mushi zaman tattausan farar, alkyabbar da taji ado, me d’auke ido da jan hankali, wacce tana da faɗi kuma a buɗe take, tabbas zan iya cewa Modibbo bai tab’ayin kyau irin na yau ba, domin shi kansa ya shaida hakan, saboda tsananin kyaun da yayi, Sheykh Jabeer da Kuma Ibraahim murmushi kawai suke idan sun kalleshi.
Kyakkwawan takalmin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login