Showing 402001 words to 405000 words out of 417803 words

Chapter 135 - Sakayya By Aisha Aliyu Garkuwa

daga Adamawa wanda direct zai kaisu Taraba ƙarfe huɗu daidai suka nufi Taraba.

Karfe goma dai-dai suka isa Membila kai tsaye gidansu Lamiɗo suka nufa.
Wanda a dai-dai lokacin kuma tuni Momy ta gama shirya musu abinci da komai zasu buƙata duk ban ɗakin gidan ta saka musu ruwan zafi.
Ƙarfe 10 dai-dai Motocinsu suka shiga coumpund cike da matsanancin farin ciki Momy tace.
“Sannun ku da zuwa,Marabanku”.
Cikin farin ciki da gajiyar tafiya suke amsawa kana suka nufi Side ɗin Momy dukan su yayin da Hajiya Bunayya ta wuce Side ɗin ta cikin ƙunan zuciya da matsanancin hassada da ƙyashi.

Lamido kuwa da kansa ya kai su Abualeey da Galadima da Waziri da Baban Zakariyya masauƙi na musamman a cikin gidan nasa wanda tuni an gyara komai.

Aunty Ruƙayya,Ummi Hajja Nana,kao tsaye Momy tayi musu iso zuwa ɗakinta Yayin da Aunty Hajara, Asma'u, Asiya, Dija aɗakin Khausar suka nufa.
Cike da farin ciki Momy ta kallesu tare da cewa.
“Sannun ku kunsha hanya”.
Sai kuma ta fita ta kawo musu abin motsa baki kallon Hajja Nana tayi tare da cewa.
“Hajja Nana Bismillah ko zaku shiga kuyi wanka akwai ruwan zafi ku shish-shiga kuyi wanka kafin na ƙarasa kawo muku abinci kun dai yi sallah kam ko Ummin Jameel?”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Eh munyi sallah a hanya”.

Ummi kuwa bayan sunyi wanka Momy ta kawo wa Hajja Nana, Ummi,Aunty Ruƙayya, Hajja Umma bedroom ɗin ta.
A can ɗakin Khausar kuwa Aunty, Hajara, Asiya, Dija, Asma'u abinci kala-kala Momy takai musu tuwo miyan yakuwa da yaji tantaƙwshi, ga kunun nono daya damu ga kuma tea Mai zafi da yaji kayan ƙamshi sannan
Ga indomie da yaji gesha da soyayyen ƙwai a cewar ta tasan su Asma'u shi zasufi so, sai Jollof ɗin spaghetti Mai zafi wanda yaji busheshshen kifi da nama...


*Morocco*
Akuma dai-dai lokacin Khausar ce zaune afalon Didi, Didi na gefenta yayin da Moddibo ke zaune daga can gefe sai kuma Rahama data zo ta mikawa Khausar wani kula bisa ga duk kan alamu nama ne agashe sai kuma ta kalli Didi tare da cewa.
“Didi gashi na gama amma naji kamar ya ɗan yi yaji”.
Cikin sauri Didi ta kalleta tace.
“Yayi yaji kuma? bayan kinsan Yah Aleey ku baya son yaji kuma sai da na gargaɗeki Rahama”.
Cikin sanyi Rahama tace.
“Amma baiyi yaji sosai ba Didi nasa vegetables aciki ya kashe zafin yajin be fito sosai ba”
Kai ta gyaɗa cikin sauƙe numfashi tace.
“Toh da sauƙi”.
Khausar kam ahankali tace.
“Nikam ma na ƙoshi”.
Sai kuma ta ɗan gyara alamar zata kwanta awajen.

Kallonta Didi tayi tare da cewa.
“A'a Khausar dare nayi tashi kije kisa masa Abinci naga tunda kuka zo da yamma kuka ci abinci baku sake zuwa ba”.
Ɗan juyawa Khausar tayi ta kalli Moddibo
daya zuba mata ido kana tace.
“In sa maka ne?”.
Kai ya gyaɗa tare da faɗin.
“Muje kisa min”.
Baki ta tura kana cikin kasa da murya tace.
“Mu tafi kuma?,Ni anan zan kwana zan kwana tare da Rahama”.
Dai dai lokacin kuma Didi ta nufi bedroom ɗin ta jin alamun ana kiranta awaya kuma Yau itace da girki za tayi wanka ta tafi turakan mijinta takai masa abinci ganin Didi ta shiga ɗaki yasa ya jawo hannunta yace.
“Mu tafi”.
Cikin tura baki tace.
“Ni wallahi anan zan kwana da Rahama”.
Wani kallo ya mata sai kuma ya tsuke fuska yace.
“Ki kwana da Rahama kuma? Rahman ce mijinki?”.
Baki ta tura amma batace komai ba yatsunsa biyu yasa ya kama Lips ɗin ta tare da cewa.
“Mu tafi”.
Rahama kam cikin sauri ta maida idanunta kan waya.
Da hannun yayi mata alamun su tafi ganin yadda ya tsuke fuska yasa tayi gaba kana ya bita a baya.
Suna isa ta nufi falonta,
cikin sauri yabi bayanta cikin wata kasalalliyar murya yace.
“Yau anan kike son mu kwana kenan?”.
Fuska ta shagwaɓe tare da tura bakinta gaba tace.
“A'a ni ka tafi ɗakin ka Ni zan kwana anan”.
Yana ƙarasa shiga ciki yace.
“Shegen tsoro kamar farar kura dare-dare zaki tashi kina lalubemin jiki da Ihu kina sawa mutanen gida suyi tunanin kamar na miki wani abun ne”.
Cikin kasala tayi miƙa kana tace.
“To ai kana yi min wani abin ma”.
Matsawa daf da ita yayi yace.
“Toh yanzu dai kawo mu gani danni yunwa nakeji gaba ɗaya kin ƙwaƙule min ciki”.
Asangarce ta kallesa tace.
“Kamar ya na ƙwaƙule maka ciki?”.
Shafa cikinsa yayi yace.
“kin ƙwaƙule min ciki mana baki san cewa duk tattalin lafiya da kuzarin namiji na tsawo kwana uku a dare ɗaya mace ke kwaƙuleshi ba”.
Juyawa tayi ta nufi kichen taɓa tura baki, plate ta ɗauko kan ta dawo.
Gefen ta zauna tare da zuba gashesh-shen naman mai ɗan ruwa da romo-romo yaji albasa,da kayan haɗi.
Ganin ta ajiye masa agabansa yace.
“Kici mana”.
Kai ta girgiza tare da faɗin.
“Na ƙoshi bana jin yunwa”.
Cikin sauƙe numfashi yace.
“Na lura fa tun safe ba kici abincin kirki ba tun safe kuka kika tayi da rana ma babu abinda kika ci da yamma na da muka sauka ina kallo ba wani abin kirki da kika ci sannan yanzu ma Kice baza kici komai ba”.
Kusa da ita ya matsa ya ɗauki tsokan naman tare kai mata b....


*WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*

_Ina kuke Ma'aurata masu sha'awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau'ikan sirrin sahihan magungunan ma'aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki...Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba'a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al'khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace, ka masin Daɗi har Maɗigan Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni'ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni'imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan, da dai sauransu...Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu'umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba...._ _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu'uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_
_Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)...Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu'uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa 'yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma'aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba'a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma'aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 08069423567 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah 'yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci...._



🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,



By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYAH*

*70*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*Masu son Maganin infection da maganin mata, ku marmatso wannan account no in ne naku ta ciki zaku turo kuɗin ku 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA, Sai ki turo shaidar biyanki ta WHATSAPP NUMBER'N na 08069423567. akwai sabbin kaya masu zafi suna nan bisa hanya, ki turo kuɗinki a saki cikin lissafi. Kayanen mata masu zafi sadidan daga Chadi akwaisu Garukan daka, gumbunan, Tsumummuka, cida Ciccibi Abodi cida kaza ci da jan nama kwanon ƙasaitacciyar mace biyar sirri, furar mata, gumbar madara Gumbar kolli mai ƙyallin al'khairi gumbar uku al'khairi, gumbar da ba'a baiwa mai kishiya, gumbar riɗi, garin maɗi garin melɗamhi garin ilanwaddihi garin mallaka, tsumin riɗi tsumin tsirtai tsumin kinfi budurwa, tsumin riɗi, tsumin ta baje Sabaya, matsin maliƙi mai masifar matse mace matsin daɗi har maɗiga, mai ɗan kare kyau. Kullacar sirri al'ajabu shu'umar Humra, da duk sauran kan ƙamshi. Haɗin amarya budurwa ko bazawara haɗin mai jego ko uwar gida, akwaisu Available set ɗinmu hawa hawane akwai manya akwai ƙananan, ƙanan daga 40k ne 35k 30k 25k 20k 15k 10k shine ƙarami haɗina na karshe sai kuma haɗin kwanon ƙasaitacciyar mace shi 7k ne shine ƙarshen haɗina kenan... Manyan set ɗin kuma daga 50k 60k 70k 80k 90k 100k ke zaki faɗi haɗin nawa kikeso anyi miki kana kimin bayanin yadda kikeso da matsalarki ni kuwa nasan abinda zan haɗa miki, ina araha kam amman ina hana bashi*



Haka dai yinin ranan Didi suka yini da ita kana suka kwana Asma'u kuwa sai da Dr Jameel ya gama duty inda suka tafi tare da barin Dr Esha.

Washe gari da sassafe Asma'u ta zo hannunta riƙe da wani madaidaicin Basket Dake ɗauke da Warmer masu kyau bisa ga duk kan alama abinci ne tayi kana kafadarta maƙake da waya ta ƙara sa shiga ɗakin alamar waya take yi sai kuma tace.
“Eh Ummi gata nan ma yanzu na shigo”.
Ta ƙare maganar tare da miƙa wa Khausar wayar kana ta ajiye Basket ɗin hannunta tana mai gaida Moddibo dake magana da Dr Jameel.
Khausar kuwa cikin sanyi tace.
“Ummi”
Cike da kulawa Ummi tace.
“Khausar lafiya dai kike jin jikin ki ba abinda yake Miki ciwo?”.
Kai ta gyaɗa kamar tana gabanta tare da cewa.
“Ummi ba abinda. Yake min ciwo fa”.
Cikin jin sanyi da tausayinta Ummi tace.
“Toh Allah ya rabaku lafiya ”.
Tana ɗan lumshe Idanunta ta gyara zamanta tare da cewa.
“Ameen ya Allah Ummu kuyi min addu'a”.
“In sha Allahu muna miki kuma zamu ci gaba daya miki yanzu ma mukayi waya da Momynki tace min yanzun jirginsu zai tashi”.
Juyawa Khausar tayi ta kalli agogon wayanta tare da cewa.
“Yanzu ma ai sun tashi tun da gashi har tara da rabi kuma tara dai-dai ma jirginsu ya tashi”.
Cikin sauƙe numfashi Ummi tace.
“Toh Allah ya kawo su lafiya”.
Ameen ta amsa suna cikin waya da Ummi taga kiran Hajja Nana ya shigo ta wayarta cikin sauri ta miƙa wa Asma'u wayarta kana tayi picking nata takai kunnenta atake muryan Hajja Nana ya ratsa kunnenta tana cewa.
“Khausar”.
Ahankali Khausar tace.
“Na'am”.
Cike da so irin na Kaka da Jika Hajja Nana tace.
“Ya jikin naki?”.
Tana ɗan lumshe Idanunta ta gyara zamanta tare da cewa.
“Da sauƙi”.
Cikin sauke ajiyar zuciya Hajja Nana tace.
“Jiya mukayi waya da Momy take cewa baki jin daɗiba ma tana kan hanya zata zo”.
Kai ta gyaɗa tana kallon Asma'u dake cire warmers cikin Basket tace.
“Eh lafiya lau ba abinda ke damuna Hajja Nana amma wai ance Theater za'a min”.
Cikin son kwantar mata da hankali kana da son sama mata nutsuwa tace.
“A'a kada ki damu ki kwantar da hankalinki ai Theater ba abinda yake yi nima in Sha Allahu da izinin Ubangiji zanyi ƙoƙari in zo”.
Murmushin tayi cikin jin daɗi ta gyara zamanta tare da cewa.
“Allah ya kawo min ke lafiya Allah yasa ki same ni araye”.
Cikin rashin walwala Hajja Nana tace.
“Wani irin magana ne wannan in Sha Allahu ma araye zan sameki kar ki karya min zuciya”.
Murmushi tayi tare da faɗin.
“Toh Allah ya kawo ki lafiya”.
Ameen ya Allah ta amsa kana sukayi sallama.
Kallonta ta mayar kan Moddibo dake riƙe da hannunta cikin rauni yace.
“Kina so ki karya min zuciya ko Minha? wani irin kalma ne kike faɗa haka”.
Ɗaya hannunta ta ɗaura akan nasa tare da cewa.
“Bakomai Yah Mu'allim”.
Dr Jameel kuwa kallon Asma'u dake tsaye gefensa yayi wacce tunda ta cire Warmers cikin Basket bata zauna ba yace.
“Toh ki zauna mana”.
Ahankali tace .
“Toh bari in sa mata abinci”.
Idanunsa ya zare tare da cewa.
“Dear wa yace Miki idan za'a yiwa mutum Theater yana cin abinci ai baza taci abinci ba sai bayan an fito da ita”.
Kallonsa Khausar yau cikin langwaɓar da kai tace.
“Kuma wallahi yunwa nake ji Dr”.
Idanunsa akan Asma'u yace.
“Ki ƙara haƙuri in Sha Allahu ana fito dake ba daɗewa zaki samu ki ɗanci wani abu”.
Rau-rau tayi da Idanunta tare da faɗin.
“Toh shikenan”.
Bayan zuwan Asma'u ba daɗewa Niyna da Innayi suka iso wanda hakan yasa Didi ta samu ta koma gida tayi wanka ta sake shiryawa.

12:30pm dai-dai suka fito da niyyar komawa Asibitin wanda kuma yayi dai-dai da Jirginsu Ummu ya kusa sauƙa hakan yasa tace da Ibraahim dake driving ya wuce da ita Airport kana sai motar Hadimai dake biye dasu wanda sun kai huɗu motar Ajere-Ajere suke tafiya motar Hadimai ɗaya agaba saina su Didi sai kuma sauran ukun abaya ƙarfe 1:05pm dai-dai suka shiga cikin airport Akuma dai-dai lokacin jirginsu Momy yayi Landing.

Bayan Fasinjoji sun fiffito Momy ta fito hannunta riƙe da Raudhat yayinda wani yaro daga cikin ma'aikatan wurin ke gabanta da troling su.
A hankali take tafiya tana ɗan jujjuya ido alamar tana neman ta inda zataga fuskantar da ta sani, sai kuma tayi saurin juyawa jin Raudhat na cewa.
“Oyoyo Didi Yah Ibraahim Oyoyo”.
Murmushi Momy tayi kana tace.
“A'a gasu can ma”.
Ibraahim kuwa sunkuyawa yayi tare da buɗewa Raudhat hannu da gudu tajeta ta rungumesa tare da cewa.
“Ina Addah Khausy?”.
Yana ɗan Sharking ɗin hannunsa acikin nata yace.
“Addah Khausy na asibiti”.
Cike da zumuɗin son ganinta tace.
“Toh mu tafi inganta ina son ganinta ”.
Miƙewa yayi tana riƙe hannunta yace.
“Toh shikenan ”.
Cikin sassarfa Didi ta rungume Momy tare da cewa.
“Momyn Khausar Barka da zuwa”.
Fuska ɗauke da Murmushi Momy tace.
“Barka dai ya mai jikin?”.
Suna tafiya Didi tace.
“A'a Alhamdulillah mai jiki tana can anata hira da ita amma yanzu nan da minti arba'in za'a shiga da ita sai muyi ƙoƙari mu tafi asibiti kafin a shiga da ita”.
Momy ta gyaɗa kai tare da cewa.
“Toh shikenan”.
Daga nan suka shiga motoci Madadin su wuce gida kai tsaye asibiti aka wuce dasu.

Dai-dai lokacin kuma Lalla Khadijah da Rahma ne da Asma'u ke tare da Khausar, cikin kulawa Lalla Khadijah ke kallon Khausar ɗin jin yadda tayi mgnar a yunwace.
“Ayyah Rahma kije ki tambayi Dr Jameel, zan iya shan tea ne”.
Cikin kula Rahama tace.
“Ai ɗazuma naje Lalla Khausar cewa yayi ki ɗan ƙara haƙuri”.
Gyara zama Lalla Khadijah tayi tare da cewa.
“Kiyi haƙuri ko Khausar ba komai zuwa yamma dai zaki samu kici wani abu”.
Ɗan kwaɓe fuska tayi tare da kallon Asma'u dake cewa.
“Toh ni bari inje in kira Dr suzo su shiga suyi mata mana ta samu taci abinci”.
Ta ƙare maganar tana fita.

Su Momy kuwa da Didi tafe suke suna hirarsu, duk da dai duk karfin hali suke.
Raudat kuwa sai surutu take zubawa Ibraahim.

Acan asibitin kuwa lokacin da Asma'u take ta kira Dr zuwa lokacin 1:30pm yayi, haka yasa suka fara shirya komai, nan da nan suka gama shirya komai da komai na asibiti kasancewar ƙarfe 2:00 dai-dai za'a shiga da ita ahankali Dr Eshaa ta shiga ɗakin hannunta riƙe da wani riga da hula irin wanda ake sawa idan za'a shiga da mutum ɗakin C's miƙa mata rigar tayi tare da cewa.
“Gashi zakisa wannan ɗin”.
Kai Khausar ta gyaɗa tare da karɓa kana ta juya ta kalli Moddibo cike da tarin ƙaunarta da kuma tausayinta Moddibo yace.
“Insa Miki ne?”.
Langwaɓar da kanta tayi tana rau-rau da Idanunta tace.
“Nikam tsoro nake ji zuciyata bugawa take Yah Mu'allim”.
Kamota yayi kana ya ruggumota jikinsa cikin wata amintacciyar murya mai cike da jin ƙai da tausayi yace.
“Bakomai Minha, ba abinda zai sameki sai alkhairi kinji ko Minha”.
Ya ƙarashe Maganar cikin sanyi haka nan yake jin jikinsa ya mutu kana zuciyarsa na tsinkewa ya rasa mai yake masa daɗi a duniya.
Ganin haka yasa Dr Jameel da Dr Eshaa juyawa suka fita Ahankali Asma'u ta yunƙura da niyyar fita da sauri Khausar ta riƙo tsintsiyar hannunta tare da cewa.
“Asmeey ina zaki je?,Ki tsaya mana”.
Cikin rauni da karyewar zuciya Asma'u ta kalleta kana tace.
“Khausar abinda kike faɗa yana tayar min da hankali ance Miki bakomai a Theater Nan Amma sai wasu maganganu kike masu tarwatsa lissafi da hargitsa mana nitsuwa”.
Araunane ta sunkuyar da kanta tare da cewa.
“Toh ya za muyi da abinda Ubangiji ya tsara mana Asma'u”.
Cikin ƙarfafa mata gwiwa tace.
“In sha Allahu Alkhairi Ubangiji ya rubuta mana”.
Kallonsu tayi sai kuma tace.
“Hmmm Allah yasa”.
Asanyaye Asma'u tace.
“Ameen”.
Shiru ɗakin yayi na wasu mintuna katse shirun Khausar tayi ta hanyar cewa.
“Gashi kuma har yanzu Momyna bata zoba”.
Kallon time Asma'u tayi tare da faɗin.
“Ai zata zo kafin a shiga dake in Sha Allahu yanzu naji Didi na waya da Innayi tana cewa sun taho asibiti”.
Sake jingina bayanta da jikin Moddibo tayi kana tace.
“Allah ya kawo su lafiya ta ganni inganta koda ma na karshene waya sani!?”.
Cikin sauri Moddibo ya sake janyota jikinsa ya rungumeta haka nan yaji wani irin rauni tausayi jin ƙai baisan lokacin da shesh-sheƙan kuka ke taso masa daga ƙasa ba yace.
“Minha meyesa?”.
Kai ta girgiza tare da cewa.
“Bakomai fa Yah Mu'allim”.
Haka yaita rarrashinta tare da kwantar mata da hankali yace.
“Bakomai Minha babu abinda zai sameki sai alkhairi lafiya za'a shiga dake afito dake lafiya”.
Ɗan Murmushi tayi tare da cewa.
“Ameen Yah Mu'allim in Sha Allahu ya Mu'allim na daina damuwa amma ina neman yafiyarka iya tsawon rayuwar da mukayi tare tun daga makaranta har zuwa dana kasance ƙarƙashin Inuwar Aurenka idan akwai abinda nayi maka ka yafe min kayi min aikin gafara”.
Cikin sauri ya sake ƙanƙameta ajikinsa kana yace.
“Babu abinda kika yimin Minha.
Ni kuma me zakiyi kin aduniya Ni babu abinda kika yimin kuma koma akwai na yafe miki duniya da kiyama”.
Kanta ta sake mannawa da ƙirjinsa tare da cewa.
“Nagode Yah Mu'allim”.
Ahankali Dr Eshaa ta sake turo ƙofar ta shigo tare da kallon Moddibo tace.
“Asa mata rigar yanzu fa sauran minti goma a shiga da ita kunga har 1:50 yayi”.
Kai ya gyaɗa kana ya cire mata rigar jikinta ya zira mata na asibitin sai kuma ya tsugunna ya zare mata

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login