Showing 57001 words to 57985 words out of 57985 words
sune yakara jefa shi a rayuwar dayayi nadama ce sukayi Mara amfani domin mahuta tuni ya rigamu gidan gskia saidai muce Allah ya gafarta masa mukuma ya kyautata karshan mu👏🏻.
"Yammata ne guda biyu kyawawa babbar fara tas wacce bata Gaza shekara Goma ba Mai suna Husna, sai Mai bimata chocolate color hartafi Babban kyau, Mai suna Rahma suna cemata "Ummita" sai karamin namiji Wanda shine karamin su Wanda bazai Gaza shekara hudu ba inda sunan Alhaji Muktar yaci suke cemasa "Calipha" babu Abunda ya bari na ubansa kama yakeyi sak da Ak babu abunda ya bambanta su, Hajiya Aisha wacce tagama zama babbar mace ceta fito daki sanye da doguwar riga baka yayinda take turo Dan karamin bakinta hayaniyar yaran dukta isheta inda kai tsaye kitchen ta dosa a dalilin kaurin dataji, sanye yakeda Apron ya zake sai game yakeyi da yaran a wata katotuwar wayar shi yana biye musu sunata ihu duksun makalkale shi yayinda yake zaune a doguwar kujerar kitchen din basa kojin kaurin da dake tash kai tsaye ta kashe gas din Wanda tafashen nama ya Dora zai musu abincin dare kasancewar Aishar bata iyayin girki saboda uban laulayin daya tasata a gaba inda Ak keyi duk sanda yake gida kokuma ya dibesu suje restaurant kokuma gidan Mamie kona "second Grandma" wato Ramata kamar yanda yaran kece mata, kwata kwata bai yarda da abincin yan aiki ba dukda sunada su"Haba Haba 1st love duk kuncika gida da ihu bakwa kojin kaurin naman da yake konewa katasa yaranka kun hanani Bcci, Shiru sukayi mata kamar basusan da ita a wurin ba, " dear magana fa nakeyi ko baku ganni bane? "Sorry wife mun jiki muna zuwa please bari mudan gama wurin nan, " Husna, ta kira sunan babbar diyarta, "Yes mommy ta amsa batareda ta kalli mamar tata ba sai ihu sukeyi da daddyn su ganin basuda lokacin tane kamar yanda suka saba mata hakan yasa itama taimusu abunda tasaba, kwace wayar tayi dadan gudu gudu ta fita tsakar gida inda gaba daya suka biyota suna ihu harda Daddyn su, Please mommy please mommy ki bamu wyyooo mommy za'a cinyemu, Ak neya fadi cikin muryar magiya kamar yanda yaran keyi, Damkarta sukayi suna ihu A'daidai lokacinda Mai gadi ya wangale gate din gidan wata bakar hadaddiyar mota tashigo nan yaran suka fara tsallen murnar ganin motan kai tsaye suka rungume bilki wacce takeda yara biyu a lokacin duk maza Mai aikinta ce tafara fitoda manya mantan kulolin shake da abinci kala kala Wanda bilki ta tsara domin yin dinner a gidan yayyin nasu itada iyalan gidanta gaba daya dama sunayin haka jefi jefi saboda karuwar zumuncin nasu kai tsaye suka rankaya katafaran parlon dake gidan inda Ak ke tsokanar Eeashar sa, " Maman yan hudu taka a hankali, harara ta wurga masa, 'dayan ma yana kare? Gskia daga wannan zan huta....wlh baki isa ba, duk shekara saikin sullubo mun kyawawa masu kamada ke idan har Allah ya bamu saikin haifo mun yara Ashirin insha Allah, "Yeeeeaaaaahhh mommy zata Haifa yara ashirin inji Calipha Wanda keta faman tsallan murna A tunanin shi cikin jikin Mommyn nasa ne dauke da yara Ashirin, dariya akai tamasa inda " Aisha taketa faman hade rai sanin yanda Ak ke kaunar yara ita kuma tana bukatar hutu, 'Gskia ni wlh hutawa zanyi Yara ishirin inyi Yaya dasu? "Wlh koki haifo mun kokuma in nemo Mai haifo mun, yafadi cikeda zolaya " Aiko baka isa ba indai akan haihuwa zakai mun kishiya duk bayan wata Tara na yarda zan dinga sulluboma yara......."kai Mommy kowa ya fadi duka yaran dake wurin harda iyayan suka furta suna zare ido tareda rike habar su, "ku kyale mun Eeasha ta da gskiar ki dole kiyi kishin mijinki First love nayi miki Alkawari daga ke babu wata dake kadai zan rayu insha Allah, " Yeeeeeaaaah gskia mommy kin Iya zaben miji am so jealous, "Inji Husna tafadi tana cuno baki tareda Dora kafadarta akan na Ak wai tana kishin mamarta, "kanta Aisha ta ture inda ta Dora nata a kafadar Ak harda rikeshi da duka hannuwa biyu, " Ki kyale mun 1st love Dina kowa ya nemo nashi, Allah ya barmu tare mutu ka raba insha Allah. Dariya aka hauyi Ana tafi ganin yanda soyyar su kullin kekara zama sabuwa fil duk sanda zaka gansu tabbas zakaga soyyar na Kara haihuwa shiyasa gidan nasu yake cikeda farinciki da kwanciyar hankali.
*Alhamdulillah anan nakawo karshan littafi na 🧕🏼Ustaziya ko Yar'duniya🤷🏻♀ kuskuran danayi Allah ka yafemun👏🏻 Allah yasa mu Amfana da darasin dake ciki tareda watsar da abunda ke akasin hakan.👏🏻*
*Godiya ta musamman ga masoyan littafin nan ustaziya fans group 1 har zuwa group 8, tareda Anty Mamie's novel 1&2 da kuma Zama na amana Facebook,Kai da duk wani groups dinda nake ciki Wanda lissafo su zai Iya kararmin da Alkalamina dama wadanda bana ciki Ina mika tarin godiya Mai yawa Allah ya hada fuskokinmu da Alkairin sa.*
*Ina gaisheda kowace marubuciya bazan Iya kiran suna ba kowa tawace Wanda nasani dama Wanda bansani ba Ina yinku sosai Allah yakara mana hadin kai*.👏🏻
*Bazance ga Randa zaku kuma jina ba, zaku Iya jina a'koda yaushe zakuma ku Iya jina shiru ya danganta, Amma karku manta Ana tare🤝🏻totally😍*.
*Matar Saddiq ce.*
********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.aihausanovels.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.
Email > aihausabooks@gmail.com
******* FOLLOW US ******
Facebook: Ai Hausa Novels
Twitter: Ai Hausa Novels
Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels
WhatsApp Number: 09017242889
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************