Showing 6001 words to 9000 words out of 57985 words
ban Al'ajabi?* duk maiso ya daga hannuππ»ββ
*Mrs Sadik Rumahπ
π»*
π§πΌπ§πΌπ§πΌ
*Ustaziya ko Yar'duniya?π€·π»ββπ€·π»ββπ€·π»ββ*
*Written by Anty Mamie*
*Dedicated to sister Husnah*
7
Bakaramin San halima mahuta keyi ba inda ya kudira a Ranshi idan lokacin auren shi yayi zai iya Rayuwa da ita dukda yakai munzulin auren amma a cewarshi bayaso ya tsufa abunda ya lura Aure na saurin tsufar da mutum tun bare idan yafara Tara yara gara nanda kamar shekara 45 ya daure yayi, suko iyayan shi ko'a kwalar rigar su Dan suma American style sukeyi basa takura ma yaro a cewar su rayuwar shice yanada yancin yin komai, duk cikin bebs dinshi bai hada leemah da kowa ba a cewarshi saboda tana nishadantar dashi yanda ya kamata, kullum jinta yakeyi zamzam ko kadan bata sakaci da maganin mata hakan yasa yake mata duk abunda takeso gudun kada ta naima a waje abunda baisani ba Yammata irin halima basuda Alkawarin rike saurayi daya tunda zata iyama iyayanta basaja shi awa? yanda cikin takun ta take kula Gayu sosai tareda basu kanta jinta takeyi bazata taba Rayuwa da namiji guda daya a rayuwar taba saboda karfin Sha'awar da takeda shi hakan yasa kullum saita samu mai debe mata kewa inda take abunta cikin kwarewa tareda taimakon maganin Hana daukar ciki, tunda tataba yin ciki kusan sau biyu dakyar tasha inda a lokacin Mamarta keta zuzuta yanda tayi haske dakara cika aiko nan ta sanarda mahuta sukaje asibiti aka burge shi bakaramin wahala tasha ba hakan yasa aka daure mata bakin mahaifa, dayake Allah ba'a mai wayau saiga wani Alamar cikin a jikinta a lokacin su meenah ne suka farga cikeda tashin hankali suka koma Asibiti Ashe mahaifar budewa tayi ba karamin wahala tasha ba inda har jinya saida tayi a gida amma ankasa ganewa mama tadage da dafa mata huntu da ararrabi a cewarsu shawara ce taimata mugun kamu hakan yasa duk Wata saitaje an duba lafiyarta a Asibiti saboda ba kowani maganin planning ke amsarta ba shiyasa yakara cika ta dam dam harta fara losing shape ba tareda ta farga ba.
Halima tana cikin jerin mata masu matsaikacin tsawo itaba gajera ba bakuma doguwa ba, tanada haske farace amma ba Sol dinnan ba dirin jikinta ma babu laifi saidai batada cikar kirji sannan basuyi Kanana sosai ba, yar madaidaiciya yayinda hancin ta Dan daidai yadan bude kadan baiyi tsini sosai ba saidan karamin bakin ta tareda ido masu Dan girma, baza'a kirata mummuna ba tanada kyau mai sanyi, tareda zubin halitta mai kyau saidai kan nan nata ne toh masha Allah kamar kwallon goribaπa takaice dai irin gashin sister Husnah garetaπ€£π€ amma tareda taimakon karin gashi wanda dorawa kawai takeyi akai bata yarda aimata kitson shi saboda tsaro shima tana gama abunda zatayi take tunbuke shi saidai kan nata dukda bawani gashi a tsaftace yake zaka ganshi Ras da kitso maiban Sha'awa kwarjinin ta shike Sa manyan Gayu ke mutukar kaunarta duk kankantar ka indai zaka zube mata kudi toh babu abunda zai hanata budema kafa a takaice dai *The definition of halima is fake*
*Cigaban labari*
Shiryawa tayi cikin kayan makarantar nata doguwar Riga wacce tadan haura kugun ta da dogon wandon har kasa sky blue sai hijab dinta iya guiwa fari tas takalmin gida tasa flat a cewarta tunda karatun WAEC sukeyi ba'a takura musu daka ganta kaga student fuskarta babu kwalliya I'lla pawder da man baki Mara kala dukda haka tayi kyau ba laifi, wurin 7:30 tafito dauke da Karamar jaka Wanda katon littafi guda dayane a ciki shima dandai daukan nashi yazama dole ne, iyayan ta tasamu zaune a matsaikacin parlor dinsu Wanda babu komai a ciki sai ledar tsakar daki a gefe daya kuma katon dirowa ne shake da littattafai kala kala na Addini ko'ina tsaf gwanin ban Sha'awa suna zaune akan tabarma da Alama Karin safe sukeyi, dukawa tayi ta gaishe da iyayan nata cikin faraa suka Amsa mata, 'uwata ya karatu? Yakuma haddar taki? Duk inda kike da matsala wurin rashin fahimta ki gayamun sai inkara doraki akai, inji Malam liman, Toh Abba insha Allah bama Wata Matsala, "toh toh yayi haka akeso aita dagewa shi ilimi da kike gani kogi ne sai gaba zakiga amfanin shi maza zauna ki karya ki hanzarta kada ki makara ya fadi yayinda da kanshi ya tsiyaya mata koko cikin kofin dake hannun shi da Alama ko gama sha baiyi ba tura mata yayi gabanta harda ledan kosan daya siyo musu na Kari, mamanta ce ta turo mata wani kwanon Samira ta ajiye gabanta, dumamen tuwon dawa ne miyar kubewa danya sai tururi yakeyi, 'maza ki hada da wannan saboda kiji nauyi nauyi tunda keda dawowa sai shida na yamma, 'a'a mama kosan maya isheni tafadi tana shan koko cikin natsuwa, dari biyu babanta ya mika mata dari Na abun hawa dari kuma kozata siya wani Abu darana saboda yinwa gashi zata tsaya lesson din WAEC, 'baba kabarshi Wanda kabani jiya da daddare ma yananan tafadi , a'a uwata hada duka aikin chanchanci komai gurina babu abunda bazan iya miki ba dakyar ta Amsa Naira dari wacce tace kudin mota zatayi dashi, 'mikewa tayi cikin natsuwa tabar gidan a'daidaita ta nema drop ta dauka basu zame ko'ina ba sai gidansu na isa kaita Wanda yake a U/rimi GRA rabonta dawata shegiyar Boko harta manta a cewarta babu abunda kudi bazai siyan mata ba kuma tana dasu, hakan yasa harta biya ansamu Wanda zaimata komai da komai da sunanta batareda ciwon kai ba. tana isa mai'gadin su dayake zaune kofar gidan sanin cewa daidai lokacin take zuwa, gaishe ta yahau yi Kota kanshi batabi ba 'kada abar kowa ya shigo batareda ambaka izinin yin hakan Ba, tafadi yayinda tashiga cikin gidan, batajin zata iya tarban baki da safe saita huta domin bccine sosai a idon nata.
*Mrs Sadik Rumahπ
π»*
π§πΌπ§πΌπ§πΌ
*Ustaziya ko Yar'duniya?*
π€·π»ββπ€·π»ββπ€·π»ββ
*Written by Anty Mamie*
*Gskia sai jiya na tabbatar da masoyan littafin nan Nada yawa fiyeda tsammani na wayata har daukewa takeyi saboda ruwan comments da Addu'a a gareni nayi matukar farinciki tareda mamakin yanda kuka karbe shida hannu biyu biyu, bazan daina fadi ba comments dinku nasani matukar nishadi tareda karfin typing, Godiya mai tarin yawa Ga makarantaππ*
Sorry nayi mistake a last page inda zansa Sunan Aisha nasa Zainab, Afuwan typing error ne.
*Dedicated to sister Husnah*
9
*Shin wacece Aisha? Wanene kuma AK?*
Ya'u shine Mahaifin Aisha tareda mahaifiyarta Ramata Asalin yan cirani ne daga Damagaram dake jahar Nijar, inda suka shigo Nigeria lokacin da yaransu biyu, namiji da yar'karamar yarinya mace wacce mahaifiyarta Ramata ke rike da ita a hannu, a lokacin bazata wuce shekara biyu a duniya ba, namijin suna kiransa da garbati, yayinda macen suke cemata shatu, Sanye suke da bakaken kayan buzaye yayinda sukasha nadi a kansu daka gansu kaga bakin haure, daga Ya'u har Ramata irin dogayen buzayen nanne sosai wankan tarwada kyawawa Tubarkallah, yayinda cikin ikon Allah suka sauka garin Kaduna a unguwan shanu kai tsaye gidan mai unguwa sukayi inda suka gayamai kudirin suna San fara sana'a yanda zasu tallafa rayuwar su, cikin ikon Allah mai unguwn yabasu daki daya Wanda ke zauran cikin gidajan shina unguwan aiko ba karamin murna suka dinga yiba tareda godiya da Addu'a a gareshi, dakin karami ne baida girma sai window kwaya daya rak, inda Allah ya taimake su zauran nada dan fadi hakan yasa Ramata keyin sanwa a lungun zauran, yayinda suka hada bayi da mutanan dake cikin gidan dukda gidan bawani Babba bane dakuna Uku ne a cikin gidan sai bayi guda daya da kitchen dinda kowa ke Amfani dashi, batareda bata lokaci ba Ya'u ya kafa Karamar teburin shayi a gaba da gidan nasu nan danan yafara Tara customer's bakaramin ciniki yakeyi ba darana kuma saiya kasa rake duk anan wurin yayinda Garbati ke tayashi Zama a lokacin yanada shekara goma a duniya akwai tazarar shekara takwas tsakanin shida Aisha, Ramata kuwa baa barta a baya ba, wankau tafara a cikin gida, itama babu laifi tana samu hakan yasa tace barita gwada shiga cikin gidajan masu kudin unguwan kila zata Dace su dauketa wani aikin, cikin ikon Allah nan saman layin su sosai inda gidaje masu kyau suke nanta tunkara duk gidan data shiga bata dacewa harta fara gajiya ga zafin rana Ga Aisha dake bayanta sai kuka take tsalawa, ganin sauran wani gida daya Wanda yafi duk Wanda take zuwa tsaruwa tana shirin komawa gida hakanan tace bari ta gwada sa'ar ta, tun daga kofar gidan mai gadin gidan ya dakatar da ita, 'hajiya lafiya? Yana Kare mata kallo sama da kasa, kafun takaiga bashi Amsa sukaji karan horn din mota Alamar masu gidan ne suka dawo, matsawa tayi gefe tareda rusunawa, koda suka shigo hajiyar gidan ce dayara guda biyu tareda ita, babban shekaransa goma sha biyar mai suna Abdulkareem yayinda dayan bazai wuce sha'daya ba, shikuma Abdulhakeem kallo daya zakai musu kaga kallar kamarsu da mamar tasu wacce take fara kar, 'a'a lafiya? Wacece wanchan? Hajiyar ta tambaya tareda nuna Ramata daketa zuba zufa cikin tsakiyar rana, Kafun mai gadin yabata Amsa ta karaso tareda Kara dukawa gaban hajiyar tana gaishe ta, 'amsawa tayi cikin sakin fuska, 'hajiya Dan girman Allah ki taimakeni kibani aikin yi, ta furta cikin rawar murya, achan kasan layinku gidanmu yake Mijina ne mai saida shayi da rake a kasan layi, 'shigo mu shiga ciki hajiyar ta furta ganin yanda Aisha keta tsala kuka kamar zata suma, samarin kuwa tuni sukayi cikin gida hannun su rikeda Leda da Alamar siyya sukayi da mamar tasu.
A babban parlon dake kasan gidan sukai masauki kassncewar gidan gidan sama ne, parlon ya tsaru sosai, a gefen kujera Ramata ta zauna yayinda hajiyar tayi tayi ta zauna kan kujera taki, Wata dattijuwa ceta shigo parlon rikeda farantin ruwan sanyi da lemu tanama hajiya sannu da zuwa, amsawa tayi tareda mika ma Ramata ruwan aikuwa ta Amsa ta sha sosai tareda kwanto Aisha tabata tasha nan tayi shiru tana Ajiyar zuciya da Alama zafi neya dameta dama.
Basu bar gidan ba saida hajiya taimata Albishir din bata aikin wanke wanke da gyaran kitchen da tsakar gida, tunda sunada mai musu girki sannan ba abincin kowa suke ciba, cikin Ikon Allah tafara zuwa tareda samun Alheri mai tarin yawa inda kusan anan take saman musu abincin da sukeci a gida, kassncewar idan abinci ya kwana basa ci, nan hajiya taba Ramata izinin dauka tunda dama Almajirai ake dunduma ma, dukda ranar juma'a ana girki na musamman da yamma Almajirai na layi amsar sadakan abinci mai rai da lafiya, nanfa duniya tadawo masu ya'u da Ramata harma da yaransu sabuwa sunyi fes sunyi kyau sosai sun murmure Aisha kuwa sai wayo takeyi tayi bulbul da ita gwanin ban Sha'awa takawa takeyi ko'ina.
*Mr's Sadik Rumahπ
π»*
π§πΌπ§πΌπ§πΌ
*Ustaziya ko Yar'duniya?π€·π»ββπ€·π»ββπ€·π»ββ*
*Written by Anty Mamie*
*Dedicated to sister Husnah*
11
Tunda Aisha tazama cikakkiyar budurwa a lokacin tanada ilimin Addini Daidai gwargwado, Boko kuma tana SS1 Makarantar gwamnati, nanfa samari suka yo mata chara, yawancin marasa jin unguwan ne duk Wanda yasan unguwan shanu yasan ba laifi akwai marasa ji saidai Allah ya shirya kawai, hakan yasa bata kula kowa ganin duk babu na kwarai koma akwai babu hurumin shi a gefen zuciyarta, nanfa suka Kara samata ido wasu harda zagi idan tafito, tana diyar mai shayi da rake amma tana girman kai, wasu suce rufa mata Asiri zasuyi danta samu ana Santa diyar Dan kwaya, hakan yasa tasa katon audiga tareda toshe kunnan ta, Ramata kuwa Kullum cikin hannunka mai sanda take mata yayinda yayanta garbati abun yafi damun shi fiyeda kowa amma ya zaiyi? Wasu yan'iskan ma cewa sukeyi darajar shi takeci mai akai da diyar mashayi dan cha-cha?
Ya'u kuwa ko'a kwalar rigarsa hidimarsa yakeyi.
Cikin masu takura mata akwai wani Saurayin dake zaune a cikin gidan su Wanda yake dan'sara suka ne yayi suna a unguwar wurin rashin ji, duk inda ka ambaci *Virus* tohfa harta yaro yasan da zaman shi a unguwar, maguwar Sha'awar Aisha yakeyi tunda ya kyalla ido yaga surarta, hakan yasa yaita mata tayin soyyar Sa babu yanda baiyi ba ko darajar magana baya samu dukda yana aiko mata da kananan kyauta kozata kula shi saidai ta kori Dan sakon tareda sakon, Wata rana da yamma tadawo daga islamiyya Virus na zaune a kofar gida ganinta yasa yatare karamin kofar shiga cikin gidan, tsayawa tayi dataga bayida niyyar matsa mata kallan shi tayi, 'zan wuce, 'kallon ta yakeyi sama da kasa tareda lashe baki kamar tsohon maye, 'ki wuce mana, tareda Dan bude mata hanya kadan, rabawa tayi ta gefen shi cikin natsuwa ta manne da bango gudun kada jikinsu yataba juna Virus kuwa dayake bahaka yaso ba yaso yadan ji dumin ta koda Dan gogarshi ne tayi hakan yasa kafun takarasa wucewa taji PA's ya bugan mata gefen duwawu har yana Danna hannun shi, wooooooooo kafun yarufe baki aiko Yaji saukan Mari a gefen fuskarshi, karamai wani tayi tana huci Ranta yayi mugun baci ta kudiri aniyar duk abunda zai faru saidai yafaru tagaji da rainin wayaun su, hannun ta aka kama daga baya, 'zoki wuce, inji Ramata wacce tafito duba sanwar data Dora a zaure, babu musu tabi bayanta sukabar Virus na hucin ganin babu namijin daya isa yayi mishi haka amma yau saboda ya latsa duwawun mace yasamu mari biyu abun takaici kuma a gaban yaransa dake zaune a gefe, aikuwa masu dariya damai kirari nayi masu bashi hakuri nayi nan yakara kulewa tareda Alkawarin daukar fansa.
Kuka takeyi da takaicin rayuwar data tsinci kanta a ciki bakowa yakara jamusu abun gori ba I'lla baban su daya kasance mutumin kwarai babu Wanda zai watsa musu shara, nan tayi mai isarta yayinda Ramata batabi ta kanta ba itama dazata samu mai lallashin nata so takeyi, Aisha kukan fili takeyi itako tadade tanayin na zuci, batada yancin shiga cikin mata sa'an ninta iyaye koda kuwa sha'ani ne na cikin unguwan inko taje an dinga ya'da mata habaici kenan saikace itace keyin cha-cha ko shaye shayenπ€·π»ββ gidansu AK ne kawai basu chanza mata ba.
Bayan an kwana biyu, zaune suke a'dan tsukukun dakin su cikeda jimamin rashin dawowar ya'u gida kusan kwana biyu kenan babu shi babu labari, shiba wayaba bare a kira duk inda akesa ran ganinshi bayanan hakan yasa suka dangana tareda zubama sarautan Allah ido, garbati ne ke zaune gefen mamar tasu da Aisha yana cin tuwon masara miyar kuka Auta kuwa tana gefe daya tazuba uban tagumi sai tausar su yakeyi akan baban nasu zai bayyana gobe da sassafe zai Kara dubashi ko za'a Dace, dakyar ya lallaba sukaci tuwon suma tareda musu sallama zuwa makwancin shi a lokacin yabar dakin su ganin rashin dacewar hakan shiyasa yakoma dakin abokinshi dake unguwan yana kwana, sallama yayi musu yayinda yawuce a lokacin sunada matsalar wuta gashi lokacin zafi ne babu halin kulle kofa dukda sunsan akwai hatsari barin kofar a bude tohya zasuyi? Gashi kofar gidan nasu dan kwano ne akeja ake kullewa.
Wurin sha'dayan Dare dukansu sukayi bcci ga azabar sauro da zafi hakan yasa Ramata ke daure da zani a kirji Auta ma haka, Aisha kuwa vest ce sai underwear a cewarsu zafi bazai kashe suba.
Kafarta yake shafawa a hankali, nan yafara kokarin tube mata Riga,cikin bcci taji ana shirin cire mata kaya gashi ana shafa mata jikin ta, aikuwa kwanciya yayi sosai a jikinta jin nauyin shi yasata sakin ihun da Ramata ta farka, nanta dinga zuba ihu daduk karfin ta aikuwa kafun kace kwabo muryarta ta karade ko'ina, magana yafara cikin maye, meeeeyeee......ha.ka, Raaaa.. a'a
Mikewa tayi ganin ana shirin keta ma diyarta haddi akan idonta Kwanan samiran dake gefenta ta kwada masa akai, sannan ta tuna da tuchlight dinda ke gefen katifar su, ihu Ramata keyi akan akawo musu dauki kwarto ya shigo aikuwa tana kunna tuchlight din idonta ya sauka akan Ya'u dake shirin cirema Aisha underware harya fara yaga mata vest din jikinta, bin bango tayi tana salati tareda dafe kirji tuchlight din hannun ta yafadi kasa hakan yayi daidai da karasowar virus da ihunsu ya tashi kowa na gida, ihu yasaka jama'a uba kecin diyarsa shiyasa aka hanamu dandane ashe cikin zafin nama ta tattaro duka karfin jikin ta tahau buga mai duk wani Abu dake kusa da ita, virus kuwa ihu kawai yakeyi yana shela a unguwa ya gansu turmi da tabarya, diyata? Duk karuwan gari sai diyata? Wlh kashe ka zanyi Ya'u Allah ya la'ance ka Allah ya hanaka farinciki Aisha sumewa tayi ganin ubanta neya yaga mata suturar jikinta yayinda Auta bilki tayi mutuwar tsaye numfashi na sama da kasa.........
*Mrs Sadik Rumahπ
π»*
π§πΌπ§πΌπ§πΌ
*Ustaziya ko Yar'duniya?π€·π»ββπ€·π»ββπ€·π»ββ*
*Written by Anty Mamie*
*Dedicated to sister Husnah*
*Woooo page biyu harda Read more har biyuπ€©dukda haka some one must complainπ¨π°lemmi c*π
10
Alhaji muktar babban Dan kasuwa ne kuma ma'aikacin gwamnati inda yake aiki a NGO yayinda yake zaune a unguwan shanu, tareda matarsa hajiya Bilkisu wacce sukai Auran saurayi da budurwa cikeda soyya, Alhaji muktar Dan Asalin jahar katsina ne matar shi kuma yar Yola ce bafulatana kyakyawar mace sun hadu dalilin wani zuwa Yola dayayi cikin ikon Allah har sukai Auran soyya tareda Arzikin yara biyu duka maza, Abdulkareem shine Babba Wanda akafi Sani da AK, sai Abdulhakeem tun akansu haihuwa ta tsaya musu chak dukda a duniya babu abunda suke Sha'awa kamar Tara yara masu yawa Wanda burin hajiya Bilkisu wacce suke kira da Mamie bai wuce ta ganta da diya mace ba, hakan yasa kullum Addu'ar ta kenan samun mace,