Showing 42001 words to 45000 words out of 57985 words

Chapter 15 - Ustaziya Ko Yar Iska Complete Novel

18 Sep 2025

6724

inda leemah tayi shame shame a bakin kofa tuni ta Dade da sumewa sakamakon naushin daya dinga mata a ciki fuskar nan jini da majina dukta chabe ta bugu iya bugawa, shari'a nidake har a lahira sai an mana kwankwasa kofar dakin su akeyi Wanda kusan minti biyar da suka wuce ake buga kofar tasu bakowa bane sai Aisha kukan leemah da magiya ya hanata bcci daga farko tadauka sabon iskanci ne saidataji muryar AK da kukan leemah da kalaman da yakeyi ga karan duka Wanda yagama karade gidan da alamar karamin yaki akeyi a dakin, kuka yakeyi sosai mai fitarda sauti, yah Allah ban kasance mazinaci ba na kasance bawanka mai matukar kyamar zina yah rabbi Laifin mai naimaka daka hadani da mazinaciya? Wacce alamu ya nuna duk mazan gari sun gama saninta?
'Yaya AK Dan girman Allah kabude kofar, tafadi da muryar kuka bakaramin tausayi yabata ba, mikewa yayi tareda bude kofar batareda bata lokaci ba ya rungume ta tsam a kirjin shi har suna shirin faduwa kasa sakin mata nauyin shi yayi gaba daya jikinshi ya mutu, Aisha, ta cuceni Aisha ya zanyi na Auri mazinaciya 'Aisha nasan babu Wanda kika tsana sama dani a duniya, kiyimun Alfarma yau daya ki lallashe ni ki dauki hakan da zakiyi kamar taimakon Addini, Aisha zuciyata zata fashe Aisha kiji tausayina ki gayamun kalamai masu dadi na lallashi Aishaaaaa, rufemai baki tayi da hannunta inda suka zube kasa kanshi na kwance akan cinyar ta tana shafa gashin kanshi a hankali sai zufa yakeyi hawaye daya nabin daya, kyamar zinar danakeyi sai Allah ya hadani da kototuwar Yar'duniya a tunanina Ustaziya na Aura, kanshi takeso ta janye jikinta a hankali, riketa yakarayi dukya chukuikuye ta please dnt live me Eesha karki barni please Eesha am sorry My Eesha harda hakkin ki wlh zan rayu dake har karshan rayuwa ta gara ke nasan Ga yanda na Aureki ina tareda dake please eesha kaina zai fashe zafi kaina Aisha....Kara rungumar ta yakeyi 'yaya AK ruwan sanyi zan dibo maka......'nooo noooo karki tashi nafi bukatarki fiyeda ruwan sanyi, sun kwashi minti shabiyar a haka kafarta dukta sage kassncewar bata zauna da kyauba, leken fuskar shi tayi taga idonshi a lumshe kamar mai bcci har yanzu hawaye nabin idon nashi, ta tsani AK amma duk wani mai'imani idan ya ganshi a haka saiya tausaya masa, Kara tashi zatayi a karona biyu, ina zaki?
'Zan rufe mata jikinta ne naga barinta a haka bai Dace ba, mikewa yayi tunowa dayayi leemah na kwance yashe a kasa' kada ki kuskura kije kusa da ita jikinda iskar duniya tagama busarda shi wani sutura ya rage mata a gidannan? Bafa ta numfashi yaya AK kada wani Abu ya sameta....wlh zanso haka kinga na kashe banza, wayarsa ya dauko cikin daran ya kira doctor dinshi tareda shaida masa yanasan ganinsa da asuban fari Akwai Emergency a gidanshi yanaso idanda Hali yazo da masu tayashi aiki harma da kayan aikin Kwajin kanjamau yakeso Aimasa.


Kulle dakin nasa yayi bayaso yakara kallon leemah inda Aisha takama hannun shi tajashi har dakinta sai layi yakeyi dakyar tasamu yayi wankan tsarki inda ya zube a kasan dakin jikinshi na rawar sanyi zazzabi mai zafi ya rufe shi bargo ta jawo mishi kasa tareda rufeshi ruf, hannunta ya rike Alamar bayaso ta barshi sunanan a haka har akayi asuba inda sukai sallah a daddafe saida gari yafara washewa da dabara Aisha tabar dakin wurin leemah taje inda har yanzu take yashe numfashi sama sama dakyar take iya bude idonta daya kumbura Halittar jikinta dukya chanza saboda bugun datasha ba karamin tausaya mata tayi ba koba komai itama macece yar'uwarta suturta mata jikinta tayi cikin doguwar bakar Riga inda takejin ana kwankwasa musu kofar nasu ko bata duba ba tasan doctor ne.






*Mrs Saddiq RumahπŸ’…πŸ»*
πŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌ
*Ustaziya ko Yar'duniya?πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€*



*Ummu minal marubuciyar nafi karfin shi inamai baki shawarar toshe kunne ki maida komai ba komai ba tattarasu zakiyi gefe daya gaba daya kiyi musu sallar gawa ki share surutun banzan su ki cigaba da typing dama ai bawanine yasaki ba kuma ba Wanda akaima dole saiya karanta muna jiran next post dinki pleaseπŸ™πŸΌana tare.*🀝🏻



*Dedicated to sister Husnah*



33



Daki takoma tareda saka katon hijab tare suka fitoda AK kai tsaye kan kujera ya nufa inda Aisha tabude ma doctor kofa cikeda gaisuwa gaba daya suka karasa parlon yayinda suka zauna, 'doctor sonake ka diba jinina aje a auna sannan ka diba jinin Yar'iskan chan, yafadi tareda nuna dakin leemah shima a auna inasan inga results da gaggawa please, batareda bata lokaci ba likita yayi abunda aka umarceshi inda Aisha ta nuna mishi dakinda leemah ke ciki kememe taki yarda a diba jininta babu yanda doctor baiyi ba, cikeda takaici AK yashiga dakin nan yaita ball da ita kamar yasamu kwallo yanayi yana zaginta dakyar Doctor ya kwaci leemah a hannun Sa inda Aisha na gefe daya tareda kallon fadan dayafi karfin ta, daga ummm sai uhmuhm kawai take cewa hakura leemah tayi ganin AK zai halakata daga daran jiya zuwa yau tunda take a duniya bata taba ganin Wanda akaima dukan mutuwa irin wannan ba gashi yau anmata kuka takeyi tana jamasa Allah ya'isa kasa kasa inda sai ihu takeyi ya kala mata sharri ya cire mata budurci Ga azabar budurcin daya cire mata Ga zafin ciwo damai zataji ga bugu ya akai yasan ba budurwa bace indai shima ba danawa yakeyi ba, a fusace yakara dosar dakin inda Aisha ta tareshi Abun yafara bata dariya ma, 'Ubanwa ya cire miki budurcin? Lallai yarinyar nan ki kalla tsabar idona ki raina mun hankali zanyi maganinki karyar rashin mutuncin kikeyi, Jan kafarta takeyi tareda dauko hijab da sauri da sauri ta wuce ta gefen Aisha sotake tabar gidan tun kafun doctor yadawo ta tabbata kashe ta kawai zaiyi idan yasan tana dauke da ciki, AK na ankare da ita wani wawan Mari ya Kara zabga mata Wanda yayi sanadiyyar toshe kunnanta saida taga taurari na yawo a sama dif kakeji tayi shame shame a kasan parlon kukanma yaki fitowa sai nishi takeyi Tareda danasanin Kaddarar dataja mata Auran AK bata tabajin labarin mugu irinshi ba baida imani ko kadan, Zaune suke zuru zuru kamar masu zaman makoki leemah na yashe a kasa, kitchen Aisha ta nufa ganin Dramar da akeyi da matarso a gidan nasu bamai karewa bane Hadaddan shayi ta hada tareda katon burodi da soyyan kwai, parlon takoma harda kunna TV tana karyawa tana kallo dukda ana neman karfe bakwai na safe ne ko karabin takansu batayi ba indata hade Ranta sama da kasa AK kuwa sai Satan kallon ta yakeyi ganin yanda take saka lomar burodi batareda wani damuwa ba ko alamar tayi babu dukda Kota mishi baci zaiyi ba, zaune suke a wurin Doctor yadawo tareda mikama AK sakamakon gwajin, hannu ya mikama AK tareda fadin, *Congratulations sir your wife is Three month pregnant.*
'Kallan shi AK keyi yakasa fahimtar abunda yake nufi inda doctor ya maida hannunshi daya gajida mikawa, What? Yimun magana da Hausa yanda zan fahimce abunda kake cewa likita, 'yalla'bai ina nufin Matarka Nada shigan cikin Wata Uku a takaice, 'wyyooooo ni halima wlh fyade akaimun.......'wait wait wai ciki? Ai kowa Nada ciki AK ya furta yana zare ido cikin tashin hankali, "yes sir kowa Nada ciki but nata na mutum ne Mai rai, Bby na Rayuwa a ciki harna tsawon Wata uk...... Kam bala'e what a ina? A gidana? Matata? Amarya? Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, ya dinga maimaitawa babu Adadi Aisha kuwa kashe TV tayi tausayin shi dukya mamaye ta bakaramin firgita maganar taimata ba bata taba tunanin leemah zatayi haka ba, rarrafawa leemah tayi har wurin kafar AK dake zaune a kasa yayi zaman yan'bori rike kafarshi tayi da hannu biyu biyu, Kaimun Rai ka rufamin Asiri kamar yanda Allah ya rufama Wlh fyade akaimun mijina na tuba nabi Allah kuma nabika kallonta yakeyi cikeda kyama yama rasa mai zaiyi ya zaiyi? Taya zaifara? Dagayin First 9yt sai ace Amarya Nada cikin Wata Uku, tana nufin da cikin wani tazo gidanshi kenan kuma tasan da cikin ta Aureshi, hawaye daya nabin daya ya kalla doctor, 'yah kanjamau fa? Akwai ko babu? 'Alhmdlh babu wani ciwo tareda ku dukanku likita yafadi cikeda Al'ajabin abunda yake gani, shigowar mai'gadi neya katse musu shirun inda yake shaidawa wani yazo neman hajiya Amarya damai gidan a cewarsa yanada Ajiyar mutum sukutum a gidan, mahuta neya danno kanshi sanye da kananan kaya bakake wando da Riga fuskarshi daukeda murmushi inda yake shafa sajen dake fuskarshi, Halima gidan hutu dakin hutu diyar malamai mai tarin ilimin hutu a daki, ooops forgive my manners please, Assalamu Alaikum banyi sallama ba kasancewar ina cikeda murnar ganin unborn bby Dina dake kwance a dakin hutu, Mutuwar zaune limah tayi........mmmaaaa...huta tafadi cikin rawar murya, mai kakeyi a gidannan? Ya zakaimun haka? Waya kawoka waya nunama gidana? 'Sorry baby Sanin inda kike bamai wahala bane kawayanki suka kawoni yanzu haka nabarsu a mota Sunce ma in gaishe ki su meenah nake nufi, 'Malam uban waye kai? Maiya shigo dakai har cikin gidana wurin iyalina da izinin wa kato dakai? Calm down Yalla'bai Kwantar da hankalinka zanma bayanin kaina ai, sunana mahuta Saurayin halima uban babyn dake kwance cikin mahaifarta nazo ne inga lafiyar bby na jiya nakwana da zullumin cikina Allah yasa kuna ciyar dashi sosai,.......... karfin da baisan yanada shiba ya tattaro tareda kaima mahuta mugun naushi a baki nanda nan jini ya balle duka yake kai mishi tareda Alkawarin kashe shi da hannun shi, kwarto kwarto har gidana wlh dukanku mai rabani daku sai Allah babu yanda Mai'gadi da doctor basuyi ba ina sunkasa raba AK a jikin mahuta Wanda akaima jini da majina a fuska sai zare ido yakeyi dukya galabaita baitaba tunanin zai riske haka ba saida AK ya cire mishi hakori daya dakyar yasha inda yakwasa a 360 babu koh waige lallai AK baida hankali yayi dana'sanin zuwa gidannan Kan leemah ya dosa wacce tayi hanyar waje tana dingisa Kafa dakyar da sunan guduwa kiran mahuta takeyi ya taimaka ya rike mata hannu su gudu tare tabbas AK babu abunda zai Hana bai kashe su ba, ganin AK ya dosota kamar zaki tuni ta taka kafa tareda kwasa ana Kare har waje yabisu tuni mahuta yaja mota leemah kuwa ta kule tanata tikar gudu babu ko takalmi bare mayafi ko waige batayi, nishi yakeyi sama sama tareda kokawa da numfashin Sa kafun a Ankara tuni ya zube a kasa ihu Aisha tasaki hadeda kiran sunanshi tana kuka da taimakon likita suka sashi a motar likitan Aisha da Ak na baya kanshi akan cinyarta sai girgizashi takeyi, kada ka tafi idan katafi basuda asara ni sukaima asara ya zanyi Yaya AK kafi kowa sanin kaine farincikina Dan Allah ka kasance dani wlh bazan gujeka ba koda zaka dinga dukana kada ka mutu, kwantar da hankalinki madam bazai mutuba insha Allah inji Doctor daketa zuba gudu a titi, Kai tsaye dakin Emergency akayi dashi Dakyar aka Hana Aisha shiga wacce tagaji dacin kuka harta gaji.

"Baki na bude ni Mamie ganin yanda Aisha ta bankeni harsai Dana kai kasa a kokarina nabinsu Asibiti domin dauko muku rihoto inaji ina gani aka badeni da kura suka barni tsaye nida baba mai'gadi, kokarin shiga gidan nakeyi tsawa mai'gadi ya dakamun, 'toh uwar gulma masu gidan basanan mai zaki musu a gida kuma?Sakata yasa yabarni cikeda takaici na watsar da Alkalamina nayi cikin fushi 'muma mijinnan munada shi bare a karya mishi ni a banza😑da gudu nayi wurin My RumahπŸƒπŸ»β€β™€πŸƒπŸ»β€β™€naga kowa nashi yasani.




*Mrs Saddiq Rumah πŸ’…πŸ»*
πŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌπŸ§•πŸΌ
*Ustaziya ko Yar'duniya?πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€πŸ€·πŸ»β€β™€*



*Written by Anty Mamie*



*Dedicated to sister Husnah*



34




Bakaramin artabu akasha wurin daidaituwar numfashin nasa inda saida aka kwasa mintuna mai yawa sannan Aka samu nasarar numfashin Sa Kiran su Mamie Aisha tayi tana kuka ta shaida musu suna asibiti batareda bata lokaci ba Mamie da Daddy harda Abdulhakeem suka rankayo Auta bilki ma ba'a barta a baya ba Ramata kuwa cewa tayi zatazo da yamma duba jikin nashi, aikin lallashi bilki ta shigayi inda Aisha ke makale jikin Mamie yayinda take musu bayanin iya abunda tasani salati suka dauka gaba daya daddy na girgiza kanshi cikin takaici, maganin shi kenan ai duk Wanda baijin Maganar iyayanshi taya yake tunanin ganin mai kyau a rayuwar Sa yara ana nuna muku gabas kuna yamma tafi kyau Wanda baiyi sharar masallaci ba wlh harta tasha zaiyi ina amfanin irin wannan? "Haba Alhaji haba Alhaji kadaina yin furucin nan shin bawa na wuce kaddarar sane? Mudauki haka akan shine jarabawarsa Saimu rakashi da Addu'a tareda nasarar cinyewa, tausasa daddy Mamie keyi ganin yanda Abun yaimasa ciwo sosai ita kanta Mamie tausayin dan'nata neya gama rufeta doctor neya katse musu jimamin da sukeyi yana share zufa da farin hankacif cikeda gaisuwa yake sanarda daddy akan zaiyi mgn dashi a Office inda hali, binshi daddy yayi nan likita yafara bayani, " duk mai imani yakamata ya tausayama AK halinda yake ciki Wanda komai yafaru akan idona saidai muce Alhmdlh Allah ya takaita munyi iyakar kokarinmu wurin dawoda numfashinsa dake kokawa sanadiyyar bakin cikin dayake ciki Wanda zuciyarsa tafara kumbura da taimakon ubangiji tunda bayin mu bane Alhmdlh komai yana shirin dawowa daidai Dan Allah Alhaji arage bata masa rai kassncewar Sa mai zurfin cikin gaske shiyasa Ciwon yayi saurin tasiri a gareshi yanada damuwa tattare dashi ku taimaka mana dashi kanshi wurin kwantar masa da hankali tareda dauwamar da murmushi a gareshi, godiya daddy yayi cikeda tausayin AK.


Tunda mahuta ya figi mota bai zame ko'ina ba sai gidan iyayanshi inda tun'da mai'gadi ya bude mishi kofa ya watsama su meenah kallon banza wadanda suke cikeda gulmar sanjin abunda yafaru amma ganinshi a halin nan yasasu tsuke bakinsu dukda ba hakan sukaso ba amma ko banza sun huce haushi tunda sunsan bakaramin bomb Aka tadar a gidanba tabbas yakuma tashida dakin hutu.......uwar mai kukemun a mota kananan yan'iska ko bina gidan iyayena zakuyin? Jiki na rawa ganin yana shirin huce haushi akansu suka shafama kansu lfy inda Meenah ta leko da kanta ta windon motar, "dan Allah kabamu na mota wlh bamu fitoda jaka ba.......idan banci ubanda ya haifeku ba shege nake, kokarin bude motarshi yakeyi a kufule tuni suka kama gabansu ganin yana shirin musu tijara da sanyin safiya suna tafiya suna tikar dariyar murna harda hawayan farinciki inda basuda burin daya wuce na ganin leemah tareda sanin halinda take ciki.

Mahuta na layi kanshi kamar zai fashe mommy sane da daddy suna karyawa a dinning section ihu momnyn Sa tasaki ganin shalele na shirin faduwa fuska jini da majina da gudu suka tashi har'rige rigen rikeshi sukeyi itada daddyn Sa inda babanshi yaita kunduma manya manyan Ashar tareda rantsuwar daukan fansa akan duk Wanda keda hannu akan abunda akaima dan'sa likitoci yashiga kira saikace Wanda yarasa kafafu inda yakira commissioner of police tareda lauyoyi manya guda biyu a cewarsa suzo akwai katon tashin hankali a gidansa yanaso yayi shari'a dawasu daga yau har'igiya tayi rara, 'batareda wani kunya ba mahuta ya gayama iyayanshi duk abunda yafaru cikin sha'gwaba nan mommy takara kulewa, 'matsiyata suba abun farinciki bane ace Dan lele kamarka yama diyarsu ciki ita mijin nata ai abun yayi murna ne jininka na Rayuwa a gidanshi akan dan'karamin abunnan ne zasu nakasaka harda cire hakori saikace Wanda yaima Yammata dubu ciki muba matsiyata bane idan bamasan cikin sai a burge idan munaso kuma dandai rai daya jal sai'a dauko masu aiki suyita kulada babyn mukayima wasu banza bare namu tsiyar rashin wayewa kenan ina ranar dakikanci? wlh wlh bazan yarda ba harta iyayan yarinyar sai munyi sha'ria dasu akanka aka farama mata ciki? Koko dole kayi mata har'tayi cikin?......'Mamie mijinta fa Babba ne daga gani shima Dan babban gida ne ina ganin kawai abar case dinnan abari ta haifo mun bby na kawai dukda ban shirya Zama tsoho ba but zanyi hakan a matsayin daukar fansa inbata sunan iyayanta diyar manyan malamai cefa.....'kaci gidanku, daddy yaimasa dakuwa, kana nufin sun bugi banza kenan?

Leemah kuwa kamar mahaukaciya tadawo duk inda ta gilma sai kallonta akeyi wasu najin kyamar ta wasu na tausaya mata chan gabada unguwar sosai ta tsaya a cewarta kada AK ya biyota dakyar tasamu napep dinda ya dauketa yayinda ya kaita gidanta na Isa kaita, fitowa tayi tashiga buga gate din mai'gadin gidan ya bude saida tabashi tsoro..........haaaajjiiya.....kece kuwa? Kodai bake bace? Subhanallah hatsari kikayi abun babu kyan gani wlh, 'banasan surutu karamin munafuki sallami mai a'daidaita kakuma kulle mun gidana......'isowar su meenah neya katse mata maganar ta yayinda suka fito suna salatin ganin ta a haka cikin munafunci ransu yayi fari kar' kamar audiga, "ubanwa yayi miki haka kinga fuskarki kuwa saikace zombie, meenah tafadi tana shirin shafa fuskar leemah, kul kada ki kuskura munafukin hannunki ya sauka a jikina Algunguma butulu maciya Amana wadanda basusan mutunci da Arziki ba matsiyata....'haba dakin hutu mai yayi zafi haka yanzu dai dan Allah bani kudi mu sallami mai abun hawannan, kudinda ubanku yabani ajiya? Tafadi tareda bude idonta dayayi suntum dakyar take iya ganinsu, Kallan mai'gadin sukayi, sallame su Dan Allah sai binmu sukeyi da ido, yana shirin basu kudi leemah ta buga masa tsawa, su kakema aiki koni? Wlh muddin kabiya kudinnan kamar ka yanki takardar barin aikinka a gidannan ne, oooh hajiya kuyima Allah kuyi hakuri har mutane sunfara kallan ku, 'kuma kada kabar kowace yar'iska shigan mun gida tunda gidan bana uban mutum bane, zuciya taja meenah jin Abunda leemah kecewa, ke gidan na uban naki ne mai dattin hula?
'Dukda bana ubana bane amma da sunana aka siyeshi sannan nikeda mallakin shi Baku ba, dama ance tsintacciyar mage bata mage.....aiko
nan suka damko leemah suka hau jibgarta dama a kule suke da ita kafun kace kwabo jama'a ancika akansu layi ya kaure da tikar dambe dakyar aka kwaci leemah a hannun su wacce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login