Showing 30001 words to 33000 words out of 57985 words

Chapter 11 - Ustaziya Ko Yar Iska Complete Novel

18 Sep 2025

6723

danasani Wanda harka mutu bazaka Kara kamarsa ba, mtsewee tafadi tareda fita BAMMM ta banko kofar office din yayinda ta bangaje nurse dinda ke kusa da ita, Kamar Wanda aka dasa haka ya sankare saida doctor dinya girgiza shi kusan sau biyu sannan ya maida kallon shi wurin doctor din, mukullin motan shida ke kan table din yaja baibi takan kowa ba yafita kamar zai tashi sama.




*"Zaiyi wuya kujini gobe da jibi shiyasa nai muku mai yawa, but idan nasamu sarari zaku iya jina."*





********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

WhatsApp Number: 09017242889


Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************



*Mrs Saddiq Rumah💅🏻*
🧕🏼🧕🏼🧕🏼
*Ustaziya ko Yar'duniya🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀*


*Written by Anty Mamie*


*Godiya Mara iyaka Ga duk Wanda ya halarci bikin sister na dama Wanda bai samu halarta ba mun gode da Addu'ar ku tareda soyyar ku a garemu🙏🏼Allah ubangiji ya zaunar damu a gidajan mu lfy wadanda basu samu sun shiga ba Allah yaimusu zabin Alkairi.🙏🏼*


*Dedicated to sister Husnah*



25




Tafiya yakeyi sauri sauri sai faman waige waige yakeyi waiko zai ganta amma ina babu Aisha babu Alamar ta Ranshi ya baci sosai yanda ta yarfa shi lallai Ashe itama haka take Ashe? Fuska ne bata samu ba tabbas Aisha batada kunya nan gaba kadan ya rage sufara dambatawa ganin yanda ta naimi kaishi kasa dazu, tsaki yaja yana jijjiga hannun shida ke faman mai zugi tareda dosar motar shi yana jinjina lamarin kai tsaye gida ya wuce yasan zai taradda ita so yakeyi suyi wacce zasuyi a'yau toh karya yaimata? Shifa baiga abun fushi ba a maganar Sa tsakani da Allah yayi laifi daya kaita Asibiti domin Duba lafiyar ta? A'a ikon Allah shifa yanasan kanshi yasan maizai faru gaba yanda kullum take bankare bankare kila ta kawo mai hari shiyasa yaima kanshi gata tun yanzu kada ta shafa mai masifa, shi kadai yaita surutun shi harya isa gida baba mai gadi na bude masa gate ya sauke Window motarshi, Aisha ta dawo? 'Yalla'bai bata dawo ba tunda kuka fita tare, cikeda mamaki yakarasa parking din motarshi toh ina taje mishi da igiyar Auransa har guda Uku? Shifa bazai dauki iskanci ba da izinin ubanwa ta fita? Kasa sukuni yayi sai kaiwa da kawowa yakeyi, wayarsa ya dauka tareda shiga contact dinshi, 'mtsew Ashe ma banda number ta, oooh God tohko Mara kunyar kanwar ta zan kira inji ko tana gida? Yah rabbi banida number kowa nata why? Saboda irin haka yakamata insamu number wani nata, wayarsa ya dauka tareda kiran mamien Sa, suna gaisawa ta tambayi Aisha, Au Ashe bata karaso ba tun dazu tacemun zatazo muku wuni zata fara biyawa gidansu daganan zatazo nan wurinki, Au Allah sarki aiko bata karaso ba inajin saidan anjima zatazo, 'yauwa Mamie please a tura wani gidan nasu a gaya mata tagama duk abunda zatayi dawuri zanzo in dauketa karfe biyar na yamma insha Allah, 'a'a harsai an tura wani kabari idan tazo din basai a gaya mata ba, a'a Mamie adai tura, ikon Allah toh kai ka kirata a waya mana, 'nakira Mamie wayar bata shiga inaga matsalar network ne,
Toh ba matsala zan aika yanzu, idan kazo inaso muyi magana ka sosamun inda kemun kaikayi Allah yasa ba abunda nake zargi kukeyi ba haba shiru shiru muma munaso muga yan dagwas gwas a gaban mu kodai planning kukeyi? Hmmmm bari kawai Mamie idan nazo mayi maganan nima abun na damuna, toh Allah Shi kyauta saikazo, a'haka sukai sallama, kaji tsofaffin nan su Sam basuda damuwa sun hadani da bala'e suta jikoki sukeyi ma duk nasan abunda zan muku bazaku kashe niba, yace a fili yana tunanin hukuncin da zaima Aisha.

Kodata fito bata zame ko'ina ba inda kai tsaye bakin titi ta nufa cikin Sa'a tasamu keke napep empty Allah yasa tanada chanji a jikinta gidansu ta wuce kai tsaye inda tana shiga dakin nasu ta fashe da kuka nan hankalin Ramata da bilki yayi mugun tashi inda sukaita lallashin ta babu yanda basuyi akan ta gaya musu dalilin kukan nata Sam taki, nan Ramata a karona farko tace mata idan taga da cuta a zamanta da AK ta tattara ta dawo gida tabata goyan baya ganin Aishar bata taba yin hakan ba tunda tayi Aure kullum nuna musu take tanajin dadin zamada mijinta shiyasa ganinta yau ya tada hankalin Ramata bataso ta shiga hakkin yar'ta mai hakurin gske, cemusu tayi zata shiga makwabta nan Ramata ta fita tabarsu da bilki tayi hakan ne waiko kila zata gayama bilki matsalar ta tasan bilki zata bata shawara mai kyau tunda ita takasa gaya mata ba mamaki ta gayama yar'uwarta, aiko bilki tasata a gaba saida ta gaya mata wasu Abubuwa nan bilki taita masifa tana zagin AK, kuka take taya yar'uwarta sosai inda tabata shawara akan bata yarda ta rabuda AK ba harsai ta gasa masa aya a tafin hannun Sa a cewarta idan ta barshi yanzu yaci bulus duk wahalar daya gana mata yatafi a banza, haba Anty wlh kina bani haushi bubeki Dan Allah mace har mace ni kaina zubin halittar ki burge ni takeyi wlh kowace mace saita kyasa ki bare namij, haba inada irin surar nan taki Malam mai akai da maza? Nan bilki ta cire kunya taita kintsa ma Aisha hanyar daukan fansa wuni sukayi cur tana tsara mata yanda zatayi Aishar kuma ta dauki darasin sosai kuma taji dadin hakan a cewarta itama mutum ce kuma tanada zuciya ta kudiri sai AK yazo ya tsuguna ya bata hakuri sannan yabata takardar ta tagaji, ana haka ne mai aikin Mamie Wata yar'budurwa taxo tareda basu sakon AK tana fita Aisha ta kalli bilki, sis kinji koh? Wlh baisan nan zanzo ba kinga daya daga cikin sharrin nasa koh, dariya bilki tasaki tana salati harda tafa hannu, oooh Allah ni Bilkisu namiji da makirci Lallai mijin nan naki saike wlh wuri yasamu nuna mishi zakiyi kin fishi iyawa keda kike mace har za'a gayama makirci? Nan bilki takara zugata tareda Dora mata sababbin karatun da suka zauna sosai a kanta inda Aishar taita dariyar mugunta harta kosa ta koma gida tareda Alkawarin ta daina bari hannun shi yana sauka a jikinta ita ba jaka bace takuma daina aikin bauta.

Misalin karfe hudu bayan la'asar Bilki ta Rakata har gidan Mamie inda suka tadda ta a kitchen nan suka hau tayata aiki cikin sakewar fuska ta tarbe su harda rungumar Aisha sam Mamie ta watsar da komai inda ta rike Aisha da hannu biyu biyu ganin hidimar da Aisha take musu muddun zataso saita kawo musu girke girke masu mutukar dadi ta dauke su tamkar sune suka haife ta hakan yasa suke matukar kaunar ta, wurin shida saura suka gama taya Mamie aiki inda nan bilki taja Aisha bedroom din Mamie a cewarsu bayi zasu shiga, kwalliya taima Aishar mai kyau sai zuba kamshi takeyi nan suka fito bilki tanama Mamie dake zaune a parlor sallama ya shigo cikin shigar kananan kaya hannun shi rikeda katuwar Leda da Alama siyya yaima iyayan nashi, mintsinin Aisha bilki tayi tana mata nunu da ido Wanda Aishar ta fahimce abunda take nufi darasin da sukayi yau takeso yafara aiki tun yanzu, 'mai sona, Aisha ta furta hadeda kashe masa ido daya Wanda chak ya tsaya kamar Wanda akaima umarni kodai kunnan shi ke jiyo mishi gaibu? inda takarasa wurinshi cikin natsuwa tareda amsar ledar hannun shi, 'sannu da zuwa Ur Excellency, ta furta cikin yalwatatciyar murmushi harda dan riko hannun shi inda ya bita zagwai zagwai kamar rakumi tagama kashe shida mamaki, Anya Aisha Nada hankali kuwa? Meye haka kuma? Mamie kuwa sun gama burgeta kana ganinsu kaga masoyan da suka jike a soyya hakan yasa taita zuba murmushi tareda Kara godema Allah daya Kara hade kansu, oooh namiji munafuki ji yanda ya bita saikace bashi bane yayi gudun hijira ranar da aka daura musu Aure,oooh yaran yanzu saisu, Mamie take zancen zuci inda takosa daddy yadawo taimasa Albishir, Bilki kuwa Dan dukawa tayi ta gaishe da AK, ina wuni yaya, kallon ta yayi ganin ko kallon Arziki bata masa tun daga Randa ta same shi yana dukan Aisha ko sallama batayi idan tazo gidan, bata jira amsar shiba nanta waiga ta kalli Aisha, oooh sister saboda yaya AK yazo shiyasa aka Fasa rakani bakomai Mamie kinga tun yanzu anfara min hannunka mai sanda koh idan naji haushi nima inyi Aure, 'da gskiar su takwara ta kema kiyi Aure ki kyale mun yara na banasan Sa ido, yauwa Mamie gaya mata, inji Aisha tafadi tana tunkarar dinning dinda suka gama jera abinci akai, 'bari ma kigani mijina zan sama abinci nasan baici komai ba tunda yau ban wuni a gida ba shikuma ba abincin waje yake ciba, 'aiko dai ya gado daddyn kune daughter shima haka yakeyi baicin abincin kowa inba nawa ba, Wucewa bilki tayi renta yayi fari fes ganin tunda AK ya shigo da sallama yana zaune kamar Wanda aka dasa shiko gogan sai bin kowa dai'dai yakeyi da ido yana ganin Dan karamin dramar da ake tsarawa a parlon nasu, shirya abincin tayi a gabansa inda shima ya kalleta, wato dashi zata buga game kenan ohk let's c who will succeed, yafadi murmushi a fuskarsa, 'Amma kinsan bani kadai nake cin abinci bako? Mamie kinga saboda gulmar ganinki yau takicin abinci dani ya fadi da iyakar gaskiyar Sa yayinda ya Mike harda rikoma Aisha Hannu zaunarda ita yayi a kasan carpet din shima ya sauka, bari in dauko extra spoon tafadi tana shirin mikewa, 'nooo honey bunch ban yarda ba yanda mukeyi a gida zamuyi da spoon daya zamuci, yafadi yana mata kallon let's keep playing the game, 'ooooh ni Bilkisu naga abunda yafara fin karfina haka soyyar ta maidaku? Babu ko kunya AK kuyi abunku lokacin kune nima bari in lalubo tsohon mijina inji inda yake tafadi tareda dosar dakinta dauko waya ta kira daddy a cewarta itama tanada mijin kuma ta iya soyyar, tana wucewa ya dauko full spoon dinda ya cika tafda shinkafa da miya bakin Aisha ya dosa murmushin mugunta kwance a fuskarsa saida yazo saitin bakinta ya Saki spoon din nan abincin ya zube a jikinta harda chokalin, Oooops am sooo sorry darling wiffy yafadi yanasa hannu da niyyar kakkabe mata da gayyah yake dukanta inda cikin ikon Allah gaba daya ta naimi tsoran AK a Ranta ta rasa, Worry not hubby karka damu Anything for you my luv, tafadi tareda shafa gefen bakinsa, 'Anya Aisha ba gamo tayi ba😫wasa wasa fa yaga kamar ba Aishar saba har cikin idonshi take kallo yanzu batako kyaftawa a'a kodai a Asibiti tayi gamo da Aljanar rashin kunya ne? Idan zai tuna da safe har kuka saida taimasa tana durkushe a gabansa, Mamie ceta katse su inda take shaida musu daddy nakan hanya, 'yauwa dama magana nakeso inyi daxu dukanku, tattara kwanukan dake wurin Aisha tayi Wanda itace ta cinye kusan abincin dake ciki, saida ta gyara gun sannan tadawo ta zauna tareda fuskantar Mamie, banaso ku fassara maganata nasan komai nufi ne daga Allah babu mai badawa kuma mai hanawa sai shi, tafadi ko kadan Aisha banaso ki fassara magana ta dawata fuka sanin kanki ne bakida banbanci da diyarda na Haifa a cikina harga Allah ina jinki sosai a Raina, abun na damuna Aisha nakosa inga jikokina nida daddyn ku a karo da dama munso muyi muku Maganar amma bamusan ta inda zamu fara ba idan wani Abu ne na daban sai a nema taimako idan likita zaku gani gara asan abunyi amma Abu shekara Uku shiru kodai kun tsaya sisi ne? Tafadi tareda kafe Aishar da ido, yauwa Mamie AK ya furta Ranshi fal farincikin yanda zai gumama Aisha, Wlh Mamie maganarki haka take, ya furta tareda mikewa ya koma kujeran Mamie, kwalla ne suka fara ambaliya a fuskar Aisha dake Duke a kasa ganin yanda AK ya Mike tasan wani bomb din zai Dana mata, "have confidence wani sashi na zuciyarta kece mata, dnt let him see ur weaknesses again u r far more beyond that Aisha.
, subhanallah Daughter maiya faru kuka kuma? Idan maganata yamiki zafi kiyi hakuri daughter......ko kadan Mamie kin Sosa mun abunda ke damuna wlh babu yanda zanyi ne Allah ne shaida ta shike bani maganin Hana daukar ciki a cewarsa bayaso jikina ya baci ina haihuwa zan Zama mama kuma bai shirya Zama baba ba Wanda shine da naki amincewa munsamu sabani akan hakan yafita harkata haka nan na Amince amma wlh raina baiso ba amincewata shine sanadiyyan shiryawan da mukayi yanzu tareda Soyyah da farinciki a gidanmu.....Ashe kai mutumin banza ne Abdulkareem? Innalillahi mai nake shirin ji ni bilki? Whatttttttt sukaji an furta da karfi yayinda kallon su yakoma kan Daddy da shigowar shi yayi daidai da bayanin da Aishar keyi, mikewa AK yayi jikinshi na digarda zufa kallon Aishar yayi charaf suka hada ido nanta kashe mishi ido daya harda gwalo fuskarta taf da ruwan hawaye.








*Mrs Saddiq Rumah💅🏻*
🧕🏼🧕🏼🧕🏼
*Ustaziya ko Yar'duniya?🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀*


*Written by Anty Mamie*




*Dedicated to sister Husnah*



26





Daddy wlh ba haka bane, Daddy.....'Bani kaima ba Abdulkareem kanka ka cuta bakowa ba Kekuma Allah ya saka miki cutar dake dayake yi, wlh kaji na rantse nakusa sallama ka cikin yarana AK, daddy yafadi da iyakar gskiar Sa, akan yarinyar nan zan dauki mummunan hukunci fiyeda tunanin ka mutum banza kawai Wanda baisan ciwon kansa ba, wucewa dakinsa daddy yayi cikeda takaici, "Ai Alhaji kai naka kadan ne Abdulkareem muddin ka Kara musgunama yarinyar nan ban yafe maka ba, kekuma daga yau sai yau idan yakara baki magani kikasha kema ban yafe miki ba menene Amfanin iyaye? Kema Aisha Ashe wawiya ce ina miki kallon mai hankali maiyasa tuntuni baki sanar damu ba? Idan ya lalata miki mahaifa wa keda asara? Ke kikeda asara shi namiji ne zai iya nemo Wata ta Haifa masa kefa? Yagama da rayuwar ki idan maganin yakeso shi maiyasa bai Shaba? Yi shiru share hawayen ki kikuma kwantar da hankalinki insha Allah zan dinga zuwa gidan naku akai akai inga yanda zaman naku yake muddun naga sabani daga gareka zakasha mamaki na kuwa, 'rungume Aisha Mamie tayi tana Kara lallashin ta tareda goge mata hawaye, 'maza ku wuce kubar mana gida, Mamie tafadi tana banka mishi harara, diyata zamu karasa magana a waya saida safe, shigewa daki Mamie tayi bata Kara waiwayowa ba, hijab dinta ta dauko tareda sakawa inda yake binta dawani mugun kallo yama rasa mai zai Mata ko kadan taki bari su hada ido dukda tasan kallon ta yakeyi, saida ta shirya tsaf ta wuce ta gefen shi kamar batasan da mutum a gurin ba kai tsaye tabar gidan domin neman Abun hawa a cewarta tunda ba tare sukazo ba bataga dalilin da zaisa su koma tare ba ta tabbata bazai taba daukar ta a motarsa ba, tana tsaye baki titi tana neman Abun hawa ya wuce ta gabanta da gudu kamar zai tashi sama harda badeta da kura, nan jama'a akaita magana akan irinsu masu banke yaran mutane saikace sunfi kowa uziri, mtsew aikin banza koka tsaya ba shiga motarka zanyi ba, kodata koma gida kai tsaye dakinta ta shiga tareda yin sallar magrib bata nema komai ba kasancewar cikinta a cike yake hakan yasa ta dauki wanka tareda tsara kwalliya mai burgewa yar Karamar matsatsiyar rigarda bai gama rufe mata cinya tasaka maroon color mai santi yanada siririyar hannu Rabin kirjinta a waje ita kanta saida taji kunyar kanta amma tariga ta kudiri daga rana irinta yau zaman Yar'duniya zata dinga yi a cikin gidannan gara tazama yar'duniyar da yake mata fatan Zama kullum gashin kanta ta Kara gyarawa tareda tufke shida ribom din kayan tayi matukar kyau ita kanta tasan tayi kyau ba karya, turaruka masu sanyin kamshi ta fesa a kowace ga'ba na jikinta inda daga karshe ta shafe jikinta dawata fitinanniyar humran matan Aure Wanda wani zuwa datayi Mamie tabata harda mata bayanin amfanin shi wato ba'a sashi sai an shirya🤪🙊, parlor ta koma tana tafiya tana yauki kamar karkashi inda ta jona bornar na turaran wuta nan kamshi ya mamaye kowani lungu na gidan ta kunna TV tareda kure volum tashar waka ta kama bakinta na taunar cingum strawberry na Orbit ji kake karararassss rasss Ras cikin kwarewa kallo daya zakai mata kasan Aisha ta rikide tadawo Yar'duniya a hankali ta Mike tsaye tana taka rawa cikin kwarewa da nishadi bata damuda volum dinda ta kure ba dama haka takeso tanaso a yau basai gobe ba ta kararma farin mugu da ruwan kanshi itama ta cike katin zaman cikakkiyar bakar muguwa daga rana tayau, 'kwance yake rufda ciki abun duniya dukya dameshi akan Bakar yarinyar nan iyayan shi ke neman yimai baki, idan baiyi wasa fa tabbas Dan hakkin daya raina zai kwakule masa ido bawai tsolewa ba, sauti yafara ji sama sama tun yanaji kadan kadan harya fara jin abun yawuce hankali saikace club an kure volume ga tashin speaker's ta ko'ina tsaki yaja tabbatar da cewa a cikin gidan shi karan ke fitowa, belt din wandon shi ya zaro sanye da farar singlate da blue dogon wando a jikinsa, bude kofar dakin yayi mai zai gani? Wata ce sanye da Killer dressing kallo daya zakai mata kasan babbar mace ce babu Raini duk inda ake neman classy beb takai, baki bude yake gwale ido ganin yanda take rawar cikin kwarewa tana kasa da sama sai bankarewa takeyi kamar kifin tarwa'dah, tunda ya shigo Taga shigowar shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login