Showing 240001 words to 243000 words out of 431207 words

Chapter 81 - Mijin Buzuwa By Makawa

04 Dec 2025

18345

wullakan ta bamu ba don dai Ya AA zai iya rabuwa dake mukuma yana tare da mu har abada.
Nan suka fice suka barta tana jefan su da bakaken magana masu zafi suna fita faiza tace kunga abinda nake fadi tun a gida akaki yarda da magana na yanzu ai gashi kun gani.
Suna mota hanyar zuwa gidan sai masifa suke ya Amina dai shiru tayi mamaki ya cika mata zuciya halin nafisa ya bata tsoro yadda taciwa su mommy mutunci.
Ina gani wani irin zama na keyi a gidan dasu ga yan uwan ta tab a gidan niko ni kadai babu ko abokin hira a tare dani.
Sun iso gidan basu yi mamakin ganin gidan hakana ba gyara ba don yawan mutanen dake ciki zaune ba masu moriya bane.
Don sun dade da sanin halin su ba yauba don haka yanayin da suka samu gidan bai basu mamaki ba.
Part dina yana rufe kamar kullun nan suka nufa ina jin an kwankwasa muna zaune tare da maryam muna hira jin motsin kofan nace da maryam ko sune suka iso maryam ne ta bude kofan sune a tsaye.
Da murana na mike na tare su ina masu sannu da zuwa duk na rude da ganin su in gaida wanan in gaida waccen suna karba min.
Idanuwan su na akaina sai da suka zauna ne na shiga kitchen maryam ta biyo ni abin sha muka fara gabatar masu sai abinci ya biyo baya.
Bayan na gama gabatae masune mommy tace sallah zasu fara kafin su zauna cin abinci din dakin na yi masu jagora suka shiga ana suka fara gabatar da alwala da sallah daya bayan daya.
Bayan su idar ne suka zauna cin abinci yar gurin Faiza ce dauke a hannu na ina mata wasa naji sun sako zancen rashin mutuncin da Nafisa tayi masu a asibiti.
Murmushi nayi ina sauraren abinda suke fadi maryam ce tace ikon Allah ina laifi wanda yazo ya gaida kai gari ya gari haka.
Ni shi yasa ban daukan wanan matar a cikin masu hankali Fauziya tace wai haka kuke fama da ita da wanan bakin halin nata .
Nidai murmushin karfin hali nayi mata ba tare da nayi magana ba haka yasa suka san akwai matsala boye masu dai nake yi a hakan.
Anty amarya dake zuba abinci tace ni ai mamaki ya hana ni magana mata kamar tana jirace damu haka na dauka yanzu fa ta canza.
A wurin ku wanan yake abin mamaki inji mommy tace ni da na zauna nan da iyan bawa ai mu muka ga abu a lokacin bata da yarda ko kadan ga bakin zargi da sheri.
Ya Amina tace ai yau mun ga inda ake kishi a filin wai muna dangin mayu kuma ikon Allah bai karewa a duniya wallahi kishi haka harda na hauka.
Anty ina kika sani ai muma haka tai muna shekaran jiya da muka je gaida ita wallahi baki ga irin wullakancin da tai muna ba a gaban abokan ta.
Kamar dai yadda tai muna ke nan inji Faiza tace yau ai munga mamaki wallahi Fauziya tace ai bari ya AA din ya dawo wallahi zan fada mai idan sha,anin nafisa ya sake tashi kada ya kara neman mu a ciki.
Mommy tace ai ba, a haka ba don ta mukeyi ba don dan uwan ku muke yi yasan kuma muna mashi ai don gashi ya kira yana fadin abinda ya samay ta.
Ba gashi mun zo ba ko bamu samu taron arziki a gurin ta ba bagashi yanzun mun samu anan ba dadin auren ke nan ai da yanzu ina muka san zamu dosa idan ba khadija a gidan.
Anty Amarya tace yanzu ai na kara fahintar manufar yaya na jajirce ma karin auren shi yanzu kin ga ai zaman khadija gidan mudai yai muna rana.
Sai zuwa yamma sosai ya shigo gidan don da su niyar su su juya a ranan su koma kaduna rashin dasowan shi da wuri yasa dole su kwana.
Ya shigo muna zaune a falo ana hira bayan na dora masu girkin dare maryam tana taimaka min don kusan aikin itace mai yin shi.
Zama yayi suna gaisawa yana tambayan su gajiyan hanya da mutanen gida suka amsa da lafiya yace ashe har kun baro asibitin na buga akace min baku can.
Ai dole mu barcan yaya AA mu da bamu ko zauna ba aka tare mu da rashin mutunci da hauka a asibitin wai munzo leken asirine ba zuwan girma da arziki ne ya kawo mu ba.
Haba dai Fauziya nafa sanki da daukan zafi akan dan abu karami ina jin ya fadi haka nace uhmm na mike daga inda nake.
Bina yayi da ido ina dauke da yarinyar a hannu na taci gaba da fada mashi abinda ya faru dasu da nafisa a asibitin.
Wani irin zafi da kunyan su mommy yaji na kokarin da suke mai amma Nafisa tana gwace mai wai shi yaya zaiyi da Nafisa ne a rayuwan shi yake tambayan kanshi.
Mommy ne ta katse shi tana fadin kada wanan abin ya damay ka mudai domin Allah muka zo da kuma kai in ma tayi ne don wata manufa nata tayi karya.
Yace hakane mommy kuyi hakkuri don Allah kuyi hakkuri Nafisa bata da mutunci idan ta tashi halin ta.
Ai tayi da masu yi wallahi sai ta rena kan ta watarana a wurin mu don dai ni ba kyaleta zanyi ba wallahi kallon ta yayi ya girgiza kai.
Ya mike yana fadin barin dan shiga ciki in watsa ruwa in fito lokacin na fito daga kitchen din ina fadin akawo abinci ne yanzu.
Ya dan juyo yana fadin bari har zuwa dare yanzu hutu kawai nake so anty tace da ka dawo da wuri babangida da yau zamu juya gida.
Juyowa yayi yana fadin anty munyi magana da Abba na fada mai yayi hakkuri sai gobe ku dawo saboda yanayin hanyar yanzu.
Ya fadin haka ya fice daga dakin nima kitchen na koma wurin gurki bayan na kammala hadawa na dawo wurin su ina fadin amma zaku shiga kasuwa gobe kafin ku wuce .
Mommy tace dani bamu son dare yai muna a hanya banjin zamu shiga kasuwan nan sai anty Faiza tace mommy don Allah mu dan shiga ko a gurguje mana bamu rasa abin saye a can.
Har lokacin ban samu kebewa da yar uwata ba fita nayi zuwa wurin shi na samu baya dakin na dawo part din na samay su.
Mommy mace mai fahinta tace kuje daki khadija Amina zata baki sako acan nace to mommy tashi mukayi zuwa dakin.
Anan muka samu kebewa da ya Amina din tambayan farko data yi min shi ne Khadija haka kike fama da wanan matar haka, ?
Nace to yaya zanyi ya Amina tunda haka daddy daku kuka zabar min yi kada kice haka khadija muna taya ki da addua a kulun wallahi.
Yanzu yaya yanayin zaman naku yake a gidan nace da dama ya Amina tace komai dai yai sauki a bangaren ki dashi har yanzu ko murmushi nayi mata tare da kama hannun yarinyar dake hannuna.
Nace yayi ke nan amma a yadda na fahince shi komai a tsorace yake yin shi kamar hanyanzu ita Nafisan bata fahinci yana kawai gareni ba don yawan lafazin ta a kullun shine haks zamu zauna sai kallo a tsakanin mu.
Dan dariya tayi tana fadin wawiya ai haka yafi sauki don tana ganewa ba kyale ku zatayi ba wani shirin zata sake kuma.
Nace na fada maki yar maryam ne ta samo min taimakon da abinda tayi muna ya karye ai kila da har yanzun ba abinda ke shiga tsakanina dashi.
Tace ai naso ace ba,a taro muka zo ba da naje gidan nata nace ko yanzu zaki iya zuwa sai mu tafi da daren nan ai anty wayayiyar mace ce bazata nuna wani abu ba sai ku ce kunzo gaida ita ne.
Gaskiya ya kamata inje in mata godiya kuma in ganta don wanan matar takai wallahi nace ai sai ma kin ganta zaki san takai.
Idan munyi sallah sai mu tafi ai ba wani nisa ne sosai da mu ba ci gaba da bani shawara tayi har lokacin sallah yayi muka mike zuwa sallah.
Ina idar da sallah na dauki waya na kirashi ina sheda mai zancen fitar mu din yace kai yakamata dai in sama maki mota haka khadija barin nemo driver da zai kaiku yanzu.
Driver din yazo na fada ma su mommy ina son su dan raka Ya Amina gidan su maryam su gaisa kowan su bai ki ba suka shirya muka fito nan falo ina rufe kofan part dina muka samu su Samiha zaune gaba dayan su sai yanyaka ce dake asibiti bata gurin.
Nan suka samu ganin Ihisan suka tsaya suna tambayan lafiyan yarinyar tare da dan taba ta duk da ran buzayen bai so haka ba.
Wurin shi na haura sama na na sallamay shi na fito muka fita Fauziya ce ke fadi bayan fitar mu daga gidan take cewa yanzu khadija har yanzu wanan taron na nan maku haka a gidan nan.
Maryam tace ai ma sai abinda ya karu wallahi motan biyu ya tanadar ma fitan namu.
Mun kai gidan maryam ta riga fita taima maigadi magana ya bude kofan muka shiga da motacin mu.
Mun shiga gidan anty hauwa suna babban falon su a lokacin ganin mu tare da jamma,a yasa ta dan yin fara,a tana taron mu.
Bayan gaisawa ne maryam ta fara gabatar da su ya Amina a gurin ta dasu mommy sai da ta kalli ya Amina da kyau tace mata kanwa dai tafi ki kyau duk da akwai kama gare ku.
Dariya mukayi falon tace ma mommy amma sai nake ganin kamar na sanki a baya mommy tace ba abin mamaki bane hakan.
Kila mun taba haduwa a wani guri a can baya tace sai nake ganin kamar a federal school na maiduguri na sanki ko ?
Mommy tace kwarai kuwa don can nagama tace kwarai kuwa don nima acan na kare sai dai ban zato mate muke daku don kamar muna gaban ku da shekara daya.
Sai lokacin mommy ta tuna tace sister hauwa black jos tace kwarai kuwa nice nan suka fara hiran yaushe rabo a tsakanin su tana tambayan mommy yan kadunan da ta sani tana bata labarin su.
Maryam tace yanzun dai ashe mommy muka rako wurin sister ta sanun sannu har aka dauko hiran Nafisa nan anty hauwa je basu labarin kungiyar su nafisa din a gari .
Tace ai sai matar da bata san ciwon kanta bane take shiga wanan kungiya ko last week kafin wanan abin ya faru mun hade dasu a wani buki.
Sun ganin na gansu sai dai ba dama su shiga harkana don kar ta san kar dani dasu kuma har yanzu ina ganin basu san nasan ita khadija ba.
Tace aike khadija baki san kan wa yan nan buzaye bane don har yanzu da sauran kurciya a tare dake da sannu dai zamu kai can insha Allahu Nafisan may can don Allah.
Da ita dasu madam din aini duk a tafin hannuna nake kallon su maganin shegiya koku a gare ku dangin miji ku nuna mata idan tana iskancin ta kunsan asakin ta ai basu kaunar a tuna masu asalin na gida don yanzu sun waye.
Basu sha mamakin anty hauwa ba sai da zasu wuce ta bisu da abun arziki na irin kayan da take sayarwa nan suka mutu da mamakin ta.
Zamu fitane take fadin ida na samu lokaci tana son ganina nace to anty zan zo idan Allah yarda mukai mata godiya muka bar gidan.
Ko da muka dawo baya gidan yana asibiti wurin nafisa yaje ya dubata a lokacin tare da maryam muka dawo don tace ina da baki zata taimaka min da aiki da safe.
Suna zama ledan da taba kowa suka shiga budewa atamfofine masu kyau da tsada na mommy ne super daga ciki sai hiranta sukeyi suna yaba kirkin ta.
Daki na shiga na watsa ruwa kafin dare yayi sosai sha daya da rabi kamar kullun ya dawo daga asibitin .
Waya ya bugo min don bakin da ke akwai a shiyan nawa yana fada min in kawo mai abinci cikin shiri na fita na barsu a part din.
Ledan da ya dawo masu dashi ya bani in kai masu bayan na gama jera mai abincin na samu suna ta hira na aje masu ledan tare da fada masu sakon shi ban dade ba nayi ma maryam signal da ido na zan tafi tace mu tashi lafiya.
Ina fita ta rufe part din na samu ya gama cin abinci yana zaune saman kujera yana duban laptop din shi na shigo sai da na shiga ban daki na yi lalura na fito.
Ban tsaya ba na haye saman gadon don a gaskiya na gaji sosai ranan ban dade da kwanciya ba ya rufe laptop din ya hawo yana fadin ina ganin gobe za a sallamo nafisa don taki yarda ta zauna acan yadda suka bukata.
Allah ya kaimu lafiya nace yaci gaba da fadin don Allah Deedar abinda nake so dake shine ki kawar da idon ki akan nafisa da duk wani iya shegen da takeyi a gidan nan .
Don ita ba ciwon kanta ta sani ba bazata damu da abunda hakan zai iya haifa ma rayuwan ta ba don naga cikin bai damay ta ba.
Ni dai ina sauraren shi banyi magana ba don abinsu tsoro ma ya fara bani yanzu yace banji kinyi magana ba mana ?
Nace may zan ce yanzu kuma may zance tunda na fahinci maganan ka kamar nice mai takakan ta ba ita ba.
Yace ba haka nake nufi ba nayi maki magana ne don nasan ke zaki iya fahintar manufa akan haka idan tayi taga baki biye mata ai bari zatayi dole gyara kwanciya na nayi ina juya mashi baya.
Shiru yayi yana tunanen yanzun kuma may ye laifin shi daga fadin gaskiya nayi fushi kokatin rugumoni yakeyi na koma mai kamar dutse.
Har yai abinda zaiyi ya gama ban muda mai ba naji ya mike ya shiga bandaki ya yi wanka ya fito nima mikewa nayi zuwa bandakin na watso ruwa na wanke najasan dake jikina.
A can asibiti kuma bayan sun gama rigima da Nafisa yafito duban yanyala tayi tana fadin dole gobe ki shirya zuwa gida wurin Fatumay don karbo min sakon da aka hada min.
Yanyala ta kalleta tace gobe goben nan kallon tayi a wullakance tana fadin koba zaki je bane in nemi wani ?
Da sauri yanyala ta amsa da Allah ya kaimu don tasan kwanan wasan don ko su ba dadin ta suke ji ba kwadiyi ne kawai irin nasu da son jin dadin rayuwa.
Waya ta dauka tana kirsn madam tare da fada mata yadda suka kwashe da AA din tace idan ba kinyi da gaske ba Nafisa samad na gab da juya maki baya.
Ba komai kuma zai kawo haka ba sai yadda baki da hakkuri akan komai ke baki iya hade magana a cikin ki.
Ai na fada maki bai kamata kiyi wa yan uwanshi da kishiyoyin mahaifiyar shi haka ba namiji fa duk yadda kake ganin ka kama kafan shi idan ka taba yan uwanshi ba kyale ka zaiyi ba.
Ai duk yadda kike ganin kin kama shi kada ki yarda ki nuna yan uwan shi basu da mutunci a gurin ki don zai ji abin har cikin ranshi.
Balle Samad da hsr yanzu ba gama kamashi a hannu kikayi ba yadda kike so ni wanan mijin naki har tsoro yake bani wani lokaci mutum kamar dutse haka anayi kamar ba ayi.
Ni dai ina ganin ko zama da wanan kishiyar taki kamar dai boyon kurwa yake muna wallahi.
Nafisa tace madam kin fi kowa sanin abinda nake kashewa akan samad duk rabin samuna agurin shi akan shi yake zuwa.
Ni wanan fannin banda matsala don nasan shirin da nayi masu ai shiya nake son komawa gida kada ina nan abin yazo ya karye ya lalaba ya taushe yar iska kin san rana da hauka zan maki.
Don wanan zuman na samad sai ni nasan kan lasan abina badai wata mace tazo ta lasa man ba.
Madam tace sai ko fati ko don itama ta rigaki lasawa tace ko ta lasa ta manta kalar zakin shi don shegiya warin jaba na sakar mata bashi ba zuwa kusa da ita.
Haka sukai ta shirmay su na surkule basu san a lokacin har zuman ya fara fita kaina ba don banda jimiri a wanan fanin ko kadan yanzu don dole nake daurewa saboda hudubar mutaneba kaina ko yaushe.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Ga Allah na dogara shine mai komai mai kowa ubangiji ya sada mu da rahamomin sa masu albarka duniya da rahira.
Barkan mu da safiyan jumma ubangiji yasa muga haske a rayuwan mu ta yau da kullun.
Washe gari na samu har maryam ta gama hada abin karyawa jira kawai take ya kara sulala ta sauke na shigo.
Kitchen din na fara zuwa don jin motsinta danayi nan tana gani na ta dan sakar min murmushi tare da fadin amarya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login