Showing 66001 words to 69000 words out of 95984 words

Chapter 23 - Mijin Marigayiyya Complete Sakina Yazid

18 Sep 2025

9703

yana kan kofar dakinta kamar dai ta zata dakinta yake nufi bata gyara ba, yace ‘Ba fa dakinki nake nufi ba, dakina nake nufi tunda ai a nan zamu kwana.’

‘Oh,..’ sai kuma ta dan sunkuyar da kai kamar dai ta kasa fadin abinda take son fada ne. ya kurbi shayi ya bita da kallo yana jira ta karasa fadin abinda ta fara fada.

‘Gaskiya mu kwana a dakina, in ya so duk ranar kwana kai sai ka dinga zuwa dakina muna kwana.’

Da mamaki yake kallonta yana dariyar yake ‘Khadeeja a ina kika taba jin miji ya bi matarsa dakinta kawai saboda su biyu ne? shike nan yanzu duk wacce take da kwana nine zan je dakinta kenan?’

Ta dan bata rai ‘Nifa ba haka nace ba, ita idan tana so ta dinga zuwa dakinka bani da matsala da hakan amma ni dai sai ka dinga zuwa dakina.’
PAGE 172
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Dariya ma maganar tata taso ta bashi; tunda yake bai taba jin inda maigida yake bin dakin matansa ba sai dai a inda bashi da dakin saboda kankantar gidan ko kuma agidan haya. Amma ya za ayi yana da gida kamar wannan ga dakinsa da parlor dinsa amma ace shine zai dinga bin mace dakinta? Allah ma dai yasa Khadeeja wasa kawai takeyi.

‘Tunda kike don Allah kin taba jin inda aka ce maigida kamar wannan yana bin matansa daki saboda kwana madadin su suje dakinsa?’ Ya tambayeta yana nuna gidan, sannan ya cigaba ‘Kuma ma a wanne karatun aka biya miki haka bayan ga yanda kika taso kika ga ana yi?’

Ta kalleshi ta marairaice da fuska tana cewa ‘Don Allah ka bari mana, na ga dakin nawa ma duk gidanka ne ai meye don ka kwana a ciki. Itama Najan idan tana bukatar hakan ba sai kaje dakinta ka kwana ba?’

‘Oh, nine ma zan dinga binku ina kai muku kwanan kenan?’

‘To meye a ciki, abu ne fa wanda ya zo a tarihi ma.’

Ya dan zaro ido yana kallonta ‘Wanne tarihin Khadeeja? In ce ko dai tarihin tsumburbura ne?’

Ta kula dai so yake ya raina mata hankali, kuma idan bata yi da gaske ba so yake ta dinga zuwa dakinsa kwana. ita kuma gaskiya bata jin zata iya kwanciya gadon da ya kwanta da wata matar ko da kuwa ba Naja din bace. Gara kawai ya dinga zuwa dakinta. Ta kara bata fuska tace ‘To a islamiyya dai tunda ake buya mana sirah sai dai ace Annabi SAW ya je dakin Aisha, ko yaje dakin Hafsa da sauransu, duk bayanan da aka yi mana sun nuna shi yake zuwa dakin kowacce. Kuma tunda dai auren nan shi ake kwaikwayo SAW ai ba zai zama matsala ba idan an kwaikwayi wannan din ma.’

Bude baki yayi kawai yana kallonta; ya rasa yanda aka yi Khadeeja take lale shi haka har take samun damar gaya masa duk maganar da ta ga dama. Ya jijjiga kai yace ‘To idan nace ba zan zo ba fa sai dai ke ki zo dakin nawa?’

Tayi murmushinta wanda yake kara bashi mamaki; kana cikin magana da ita fuska murtuke sai kuma ta koma murmushi har kaga kamar da zuciyarta take murmushin, haka ma kuma idan tana walwala lokaci guda zata sha kunu ka zata kamar bata taba murmushi ba.
PAGE 173
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Muryarta ce ta katse masa tunanin tana cewa ‘Na san ma ba zaka ce hakan ba, kai da gidanka. Abinda ko a parlor ka kwana babu wanda zai nuna maka yatsa balle don ka kwana a dakin matarka?’

Binta kawai yake da kallo yana jijjiga kai, yace ‘Toh tsarani Khadeeja.’

Tayi dariya tana mikewa tsaye tana cewa ‘To ina laifi, yaushe rabon da a tsaraka.’

Kasa magana yayi kawai ya dinga binta da kallo har ta gama kwashe kwanukan. Bukatar ta yakeyi saboda shi kansa ya san yayi kewarta, don haka ma baya son yaja rigima a wannan daren da yake son ya huce gajiyarsa. Gashi sai kaiwa da kawowa takeyi tana kwashe kwanuka tana juya jikinta kamar da gayya, ya ma rasa me zai ce mata.

Bayan ta gama kwashe kwanukan ta dafa kafadarsa tace ‘Sai ka shigo.’

Bata ko saurari amsarshi ba wuce dakinta ta barshi a nan.

Sai yau ya tabbatar Khadeeja ta raina shi; tunda yake bai taba ganin matar da idan tayi niyyar abu sai tayi shi ba ko da tsiya ko da tsiya-tsiya sai Khadeeja. Anya kuwa ba wani abu Khadeeja tayi masa ba; idan taga dama ta gwada masa taurin kai da fitan idan kuma taga dama ta mayar da shi kamar wabi sakarai tayi masa wayo? Amma dai gaskiya ba zai juri binta dakinta ba dole ta hakura tayi yanda aka saba wato duk mai kwana ta bi miji dakinsa.

Babu yanda ya iya da yake shine yake da bukatarta dole ya tashi ya bita dakinta; kafin yaje ma bacci ya riga ya kwasheta. Don haka sai da ya tasheta ta sake lallabata sannan ya sami biyan bukatarsa.

………..
Washegari ya kama ranar asabar ce don haka yara basu da makaranta; ko da ya dawo daga masallaci a kan dadduma ya sami Khadeeja a dakinta tana azkar, bayan ta idar ta gaisheshi sannan tace ‘Mantawa fa nayi jiya ban gaya maka yau ne bikin su Fatin Baba Sani wanda na nuna maka invitation din last week.’

Ya gyara pillow ya kashingide a kan gadon yana cewa ‘Ok, Allah ya sanya alkhairi. Ai in sha Allahu nima zani daurin aure don Baffa da kansa ya turo min kati.’

‘Ok. Ni sai wajen azahar zan tafi don ka ga ban je yawon arba’in ba sai na hada gaba daya, idan na kwana biyu a gidan Mommy ranar litinin sai na dawo.’
PAGE 174
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ya dan bata fuska ‘Kuma shine har kwana biyu? Ai na zata a gidan bikin zaki ga duk wani wanda ya kamata kije masa yawon.’

Tayi ‘yar dariya sanna tace ‘Kada fa ka manta bikin na dangin Baffa ne, ‘yan uwan Mommy su kuma ai sai dai naje musu gida yawon arba’n din ko? Hajiya Nana dama ban kai mata baby ba ga su Anti Halima da Baba Usman. Ka ga yau a gidan biki zan wuni, gobe kuma tun safe zamu fara da Nabila; dama zamu kai musu katin bikinta tunda ka ga an fara rabo duk da dai bikin saura sati uku.’

‘Uhm, sai kun dawo.’

‘Mun dawo kuma? Ni kadai fa zan tafi, Hafsa kawai zan dauka saboda Hammad.’

Ya tashi zaune yana fuskantarta ‘Na zata ke da yara zaki tafi kamar yanda kuka saba.’

Ta jijjiga kai tana dariya ‘Haba dai, yawon arba’in din na kwashi yara har hudu? Dama saboda babu mai kula da su ne yanzu kuma ka ga Antinsu tana nan. Ni kadai zan tafi.’

Duk yanda ya so ta tafi da yaran nan haka ya hakura ya kyaleta domin ta ci alwashin ba zata sake tafiya da su danginta ba tunda yanzu suna da uwar dakin da zasu dinga kawowa gulma.

A kan lokaci ta gama abincin safe, sai dai da yake yana nan babu yanda ta iya haka ta jera a dining table din parlor dinsa. Dankalin bature ta soya da ragowar sauce din jiya da aka ci abincin dare sannan kuma da soyayyen kwai. Kowa a plate dinsa ta zuba masa har shi Mustaphan ta saka sauce a gefe da kuma soyayyen kwai. Nashi ta fara ajiye masa tare da na Shukra sannan ta juya ta koma kitchen din.

Tana shigewa kitchen din ya dubi Afaf yace ‘Jeki kasa ki kirwo Antinki ta zo muyi breakfast.’

Nan da na ta mike ta fice, ya dubi Habib ya mike yana shirin ya bi Khadeeja kitchen ya karbo nashi abincin yace ‘Shiga parlor din Anti ka daukowa kujerar dinin guda daya a kara.’

Don haka yabi bayan Khadeejan. A hanya ta hadu da shi ta riko plate biyu, tana kokarin mika masa yace ‘Abba ne yace na daukowa Anti Naja kujera tare za ayi breakfast din da ita.’
PAGE 175
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Kafin ta gama fahimtar abinda ya fada ya wuceta ya nufi dining; tana karasowa ta ajiye farantan hannunta daya a gaban Nasreen ta zagayo da dayan zata ajiye a kujerar da take kusa da Mustaphan a daidai lokacin da Afaf ta shigo tare da Naja suna tafe suna hira. Kafin tayi magana ta zauna a kujerar da take kusa da Mustapha daga damansa a daidai lokacin da Khadeejan take shirin ajiye nata abincin a wajen. Tayi cak ta dauke farantin da take niyyar ajiyewa ta dubi Habib tace ‘Yaya kaje kitchen ka dauko naka abincin ke kuma Afaf ungo wannan ni sai na dauko wani.’

Cike da fara’a Naja tace ‘Ina kwana Umman Hammad.’

Itama nan da nan ta saki fara’a ‘Lafiya kalau amarya ba kya laifi, ya gajiya.’

‘Alhamdulillah. Sannu da aiki.’

‘Yauwa.’

Har cikin ransa yaji dadin yanda suka gaisa, haka yake son iyalansa ko da dai idan baya nan ba zasu hadu suyi hira ba to idan yana nan a zauna duka kamar haka a ci abinci tare; ya dubi Khadeeja yace ‘Yauwa itama ki taho mata da abincin ko?’

‘Ok.’ Ta amsa a gajarce sanna ta juya ta nufi kitchen dinta.

Kafn ta karasa kitchen din zuciyarta ta gama tunzura; Mustapha so yake yayi mata dole kenan? Ta gaya masa ba zata yi abinci da matarsa ba amma shine zai saka a kirawota harda zama a kujerarta. Lokacin da ita Najan take girki ai bai taba kiran Khadeejan yace tazo suci abinci ba shine sai yanzu don ya tabbatar mata Naja itace matar da yake kauna shine zai ce ta bata abinci.

Nan take ta juye ragowar dankalin wanda dama ba yawa ne da shi ba ta ajiye ne saboda Shukra, ta hada da wanda da ta zubawa Afaf ta zuba sauce da kwai. Ta hada shayinta mai kauri ta dauka ta wuce dakinta ta bar Hafsa a kitchen tana cin nata abincin.

Shiru Khadeeja bata fito ba, kowa yana ta cin abinci yayinda Naja take shan shayinta wanda ta hada. Shirun yayi yawa ya dubi Habib yace ‘Je ka dubo ko Antinka dankalin ta tsaya soyawa?’

Bai dade da shiga ba ya dawo yace ‘Abba bata kitchen din, tana dakinta kuma ta kulle kofar.’ Ya zauna ya cigaba da cin abincinsa ba tare da wata damuwa ba.
PAGE 176
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ajiye fork din dake hannunsa yayi yayi shiru saboda takaici; mantawa ma yayi ya bawa Khadeeja mukullin dakinta saboda a da yayi alkawarin ba zai sake bata mukullin dakinta ba saboda yanda take kulle kanta a ciki tayi burus da kowa.

Ya ture kwanonsa ya mike, itama Naja ta mike a lokacin. Ya kalli plate dinsa; ya riga ya ci da yawa sannan kuma sauran duk ya dame da sauce. Cike da damuwa ya cewa Naja ‘Ko wannan zaki ci naje na dubo.’

‘No, kada ka damu. Ku ci abincinku akwai bread a kasa zan je na ci.’ Ta juya ta fice daga parlor din ba tare da ta surareshi ba.

A fusace ya nufi dakin Khadija, tuna kafin ya fara buga kofar ya kirawo sunanta. Ba tare da bata lokacin ba ta amsa sannan ta taso ta bude masa kofar, ko a fuska bata nuna masa ta san tayi laifi. Ya shige cikin daki ya kalli abincin da take ci a gefen dadduma yace ‘Ya zaki taho nan ki kama cin abinci ki bar mutane? Kuma kina ji nace ki bata abincin itama.’

Duk yanda ta so abi maganar a hankali bai samu ba, domin yanda yayi mata wannan tambayar da isa da gadara take taji duk wata kara da zata iya yi masa ta bushe. Ta kalleshi ta kawar da kai sanna ta wuceshi ta koma ta zauna a gaban abincinta inda ta taso sannan tace ‘Gani nayi kun cike table din, abincin kuma babu tunda ni ban soya dankali da ita ba. Me kake so na bata?’

‘Ai tun jiya nace ki dinga saka abincin a can don kowa ya ci kuma kika amsa ko? Me yasa ne kike so ki dinga raina ni a gaban mutane? Saboda me nace ki bata abinci ba zaki bata ba zaki shigo nan ki bar mutane?’

Ta kula dai duk wani zille-zille ba zai yi mata ba, ta kalleshi suka hada ido tayi murmushin yake mai dauke da takaici sannan tace ‘Kwana kusan talatin tayi a gidan nan tana girki bata taba bani ba, kuma tare kuke cin abinci kai da ita da yara baka taba cewa a kirawoni naci abinci ba; ko da yake ko ka kirawoni ma ba ci zan yiba tunda nima na iya girkawa. Kayi hakuri ba zan hada girki da matarka ba itama kar ta hada dani, duk wanda ya girka yaci shi da maigida da yara kawai.’
PAGE 177
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ta mika hannunta ta dauki fork a kan plate din da yake gabanta ta fara wasa da shi tana kokarin tokare takaicin da yake taso mata yana neman ya sakata kuka.

‘Wai ke me yasa ban isa na gaya miki magana kiji bane Khadija? Ko..’

‘Ita da ka gaya mata ai ta ji har ta bani abincin, ko da yake ita ka dauka mutum shi yasa kake nema mata abinda zata ci. Ni da babu wanda ya damu da rayuwata ina nan kake fita ka siyo muku abinci ka sakata a gaba ita da yaranka ku cinye ba tare da ko rabona an bani ba. Ban yi magana ba, shine kuma yanzu za ace ni zan bata abinci; to ta cigaba da jirana taga idan zata ci abinci.’ Ta gyara zama ta jingina da bango ta kawar da kai.

Ya rasa abinda zai gaya mata saboda tabbas ya san duk abinda ta fada gaskiya ne, sai dai a wancan lokacin ai laifi tayi masa na kin amincewa ta kula da yara don haka bai ga dalilin da zai sa ya bata abincin da ya siyo ba bayan taki ta girka. Ba tare ya ce mata komai ba ya fice daga dakin don a yanda ya san Khadija da taurin kai sai dai ya datse igiyar auren nan amma ba zata yi abinda yake so ba. Sai dai tabbas idan ta cigaba da gwada masa taurin kai irin wannan zai datse igiyar auren ya huta, taje can gidansu ta cigaba da taurin kan.

………..
Haka ya karasa shiryawa zuciyarsa babu dadi, don ko dakin Najan ma bai shiga ba suka fice tare da Habib suka tafi daurin aure.

Yana ficewa itama ta gama shiryawa, ta kulle dakinta da parlor dinta gaba daya. Ta hada mukullanta da wanda ta cire daga jikin nashi keys din duka ta jefa a jaka don bata so ko shi ya bude mata waje idan bata nan. Ta goya Hammad ta tasa Hafsa a gaba, suna saukowa kasa ta shiga parlor din Naja inda ta jiyo hayaniyar yaran, ta dubeta da fara’a tace ‘To Anti ni na fita, zan je gidanmu ne in sha Allahu zan kwana biyu. Sai ranar litnin zan dawo.’

Ta juyo ta yi mata wani kallo na raina sanna tace ‘A dawo lafiya.’
Shukra ta tashi da gudu ta kama hannunta tace ‘Anti gidan Mommy zaki je?’

Ta shafa kanta ‘Can zan je Shukra, sai ranar Monday zan dawo.’

Ta langabe kai tana cewa ‘Kai Anti ina son zuwa fa, kwana biyu ban je wajen Anti nabila ba fa.’
PAGE 178
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

‘Ai kin ga Monday akwai school ko? Shi yasa ba zan tafi dake ba. Amma idan zan koma ranar da babu makaranta zan tafi dake kin ji.’

Haka ta tsaya ta lallabata sannan ta wuce.

000000
Haka rayuwarsu ta cigaba; duk yanda ya so Khadeeja ta dinga binshi dakinsa gaba daya taki. Don haka bashi da zabi duk daren da yake bukatarta sai dai ya bita dakinta su kwana, idan bai je ba sai dai kawai ta leka dakin nasa tace masa sai da safe. Sau da dama ya sha kyaleta yaga ko zata biyo shi amma da zarar ta shiga dakin tace masa sai da safe sai tayi ficewarta. Da farko duk ranar kwananta idan bai ya bukatarta yayi kwanciyarsa a dakinsa haka yake kwana shi kadai, amma tunda Naja ta gane sai ta dinga bibiya; idan ta sameshi shi kadai sai tayi kwanciyarta a nan da uzirin laulayi. A zatonsu Khadeeja bata sani ba; sai dai ita din ta zabi tayi shirune tunda ta san yana yin hakan ne don ta hakura ta koma kwana dakinsa. Ita kuma har ga Allah gani take yi babu yanda za ayi ko wa take aure ta kwana gadon da yake kwana da wata matar; musamman Naja wadda bata tsanar wata mace kamar ita ba.
……..

Tunda Khadeeja ta dawo daga gida kuma sai laulayi ya saka Naja a gaba. Haka zata wuni jikinta babu kwari, abinci kuwa to idan dai itace ta dafa ba zata iya ci ba dole sai dai ya siyo mata wanda zata ci.

Yau Khadeeja take fita daga girki don haka a wajenta shi da yara suka ci abincin rana. Ragowar abincin ranan shi ta diba ta zuba a flask ta ajiye musu ita da Hafsa saboda ta huta shiga kitchen da daddare.

Tana zaune a parlor tana bawa Hammad nono ya shigo parlor din, bayan ta amsa sallamarsa ya zauna kusa da ita. Sai da ya gama kame-kamensa yace ‘Da-Allah kiyi abincin dare gaba daya saboda Naja bata da lafiya, kin san na gaya miki ciki ne da ita kuma yana bata wahala.’

Ko da dai bata zata abinda ya zo fada kenan ba amma tana jiran wannan din ma domin tu tuni yara suka gaya mata Najan bata da lafiya kuma ta fahimci menene ciwon. Ta cire Hammad daga nono ta saka shi a kafada tana cewa ‘Ai kuwa ka ga yau ba girki zan yi ba ga ragowar abincin rana can shi na ajiye zamu ci da daddare. Allah ya bata lafiya.’
PAGE 179
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ya sake bata rai ‘Khadeeja, da-Allah ki bari. Yarinyar nan bata da lafiya ko abincin ma ita bata iya ci, kuma ba ita nace ki yiwa girki ba. Ni da yara zaki girkawa, idan ta sami lafiya zata karbi girkinta.’

Ta kwantar da Hammad a gefenta sannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login