Showing 27001 words to 30000 words out of 30186 words
Chapter 10 - Wani Gari Horror Novel [www.arewahausanovels.com.ng]
yaci gaba da kallon cikin mirror din still tana nan haryanzun kuma matsowa takeyi wajensa wanda shikawai akan iska yaga tana tafiya kuma abinda yakara bashi mamaki ganin bayansa a cikin wani daji suke amma duk lokacin daya waiwaya saiya ganshi a dakinsa..Dab dashi ta matso cikin sanyin murya tafara magana saidai bayajin abinda take cewa kalmar karshe kawai yaji "dama nace zakazo gareni masoyina inasonka" sama ko kasa ya nemeta baigantaba....
Saiyanzun yagane wace kwarai itane yarinyar daya hadu da ita a kauye...kenan aljana ce? amma meyasa take bibiyansa...jikinsa a matukar sanyaye ya kwanta bayan yayi addu'a....
~*
Next page ta bude saidai kafin tace komai wani guard ya shigo da sauri durkusawa yayi akan gwiwansa bayan ya sunkuyar da kansa cikin girmama yace "Akwai matsala yake shugabata wani babban al'amari yafaru a safiyar yau din nan domin kuwa an wayi gari duk ruwan dake kogin gabas ya kafe ga mutane can hankalinsu a tashe saboda duk ciki shine yafi kowanne yawan kifaye dakuma ruwa."
Gaba dayan su mikewa sukayi wata hanya sukabi sai gasu a wani waje lekowa Nimueh tayi ganin jama'arta awajen amma kallo daya zakayi musu kagane cewa suna cikin tashin hankali da damuwa yawancin su kuka sukeyi kanta ta dafe cikin damuwa ta kali guards din ta "afada musu gani nan fitowa yanzun zamuje temple domin yin addu'a" tana gama fadar hakan takoma cikin gidan suma su Lady Catrina bin bayanta sukayi...
Queen Nimueh Lady Catrina ne suka fito amma yanzun sun sanja kaya zuwa wasu kalar daban kallon su Hassy tayi tace zasuje su dawo sukam kansu kadai suka daga saboda mamaki inbanda ma bata tayaya zaka kirkira abu da hannunka kuma sannna ace shine abin bautarka?
Merapati tace "Mithian ke mene abin bauta dinki?" shiru tayi batace komi ba ganin hakan yasa suma duk yin shiru.
A hankali Hassy tace "I'm missing home...bansan awani hali mum take ba bansan yanda Abbah zaiji ba idan har yasamu labarin batan muba" kuka tafara a hankali Merapati ce ta matsa kusa da ita hannunta takama saikuma tayi hugging dinta tana rarrashinta ita kanta Basma daurewa kawai tayi....
~*
Mom din Hassy zaune tana kallon news innalillahi kawai take maimaitawa ganin abinda ke faruwa daidai lokacin Abbansu yashigo parlourn jin tana salati yasashi tsayawa yace "Aaa Mum din su mene lafiya kuwa menene yafaru? TV take nuna masa saboda sam takasa magana zama yayi bayan ya maida hankalinsa kan TV din news ne akan annobar data shigo garin ga mutane nan duk sunkoma zombies saikuma wasu irin halittu daban daban suma kuka tafara sosai take nadama ya rufeta akan abinda takema Hassy kallon Abbah tayi cikin kuka tace " Kira Principal din school din tasu Allah yasa abin bai shafe su ba" shikansa jikinsa yayi sanyi da kyar ya ciro phone din yayi dialing number din...
Tana zaune ta buga tagumi ga duk staffs din nan a zaune saboda ganin irin abinda ke faruwa yasata tura driver domin ya dauko su Merapati amma saiyazo mata da labarin daya daga mata hankali nacewa baiga kowa ba awajen kuma alamu sun nuna bawai tafiya sukayi ba saboda akwai sauran kayansu anan saidai babu alamun student ko daya awajen....
Wannna dalilin yasa ta tattaro duka teacher's din domin asan abinyi inda wasu sukace akai report police station wasu kuma sukace aa abari dai ayi bincike a sirri saboda wannan babban case ne daidai lokacin phone dinta tafara kara gaban tane yafadi ganin cewa Abban Hassy ne ke kira dagawa tayi hankali tashe bayan sun gaisa nan yake tambyanta "amma su abin bai shafe suba ko saboda yanzun yake gani a news..." Hamdala tayi aranta da dukkan alamu baisamu labarin batan students din ba murynta ta gyara tafara magana "abin bai shafe mu bayanzun haka duk wasu students an tattara su waje daya da niyartama kowa tatafi gidansu amma aka hanata saboda fita waje a irin wannan yanayin da ake ciki abu ne mai hadarin gaske karya damu yarinyarsa tana cikin koshin lafiya saboda ansa security sosai...." Hamdala yayi sannan sukayi sallama gaba daya staffs din sun zuba mata ido lalle mata sun kware a komi dagowa tayi tace "mene kuka zubamin ido haka? wannna karyan danayi bani kadai ba harku ma zata taimaka yanzun dai menene abin yi?"
~*
"Oh my gosh" tace tana dafe kanta zama tayi a gefen bed din taci gaba da cewa "guy's mene abin yi? kunsan dai bazamuci gaba da zama anan ba har karshen rayuwan mu yakamata mu nemo mafita I'm tired of this place...we can't just stay here forever dole mukoma gida nasan hankalin iyayen mu yatashi ni bama wannan ba shin inasu Basma suke?me zamu fadama Pc idan munkoma school?"
Kallon su tayi ganin basu ce komai ba cikin bacin rai tace "mene hakan wai saikace bada mutane nake magana ba? Stop staring at me and open your fucking mouths! we need a plan on how to go out of this shitty place! Because I’m so fucking tired of being trapped in here!" tsaki taja sai kuma ta zauna ranta a matukar bace, Nasir ne yace "mekikeso muce kin riga dakin sani muma bamuda amsa din baki ai....koban fada miki ba kinsan cewa akwai zombies nasani dakyar idan zamu fita daga nan a raye saboda..." Hannu tadaga masa a zafafe Ruky tace "you shut up please! I don’t wanna hear your damn explanation,sam sam bakinka baya fadan alkairi tsskk"
@NM__🦋♥️
[27/01, 4:05 pm] Ablerh Authoress: Title: WANI GARI (The beginning of a new world)
Description: What happens when you somehow end up in a "New world? And what does it feel like to suddenly be a stranger in the world you thought you knew?
Merapati Hassy And Basma, both students one day a gate Into a different dimension opens to them as they find themselves in a different world,a world where mysteries and enchanted magic happens...How will they get home? What will happen to these girls along the way? Will they even be able to survive being in a world that is completely different from their own?
Tags #dimension#parallelworld#zombiesapocalypses#disappearance#journey#vampires#wonderland#magic#cursed#doppelgänger
~*
Episode 17: Sleeping Beauty.
^*^
Kallon su tayi ganin basu ce komai ba cikin bacin rai tace "mene hakan wai saikace bada mutane nake magana ba? Stop staring at me and open your fucking mouths we need a plan on how to go out of this shitty place! Because I’m so fucking tired of being trapped in here!" tsaki taja sai kuma ta zauna ranta a matukar bace, Nasir ne yace "mekikeso muce kin riga dakin sani muma bamuda amsa din baki ai....koban fada miki ba kinsan cewa akwai zombies nasani dakyar idan zamu fita daga nan a raye saboda..." Hannu tadaga masa a zafafe Ruky tace "you shut up please! I don’t wanna hear your damn explanation,sam sam bakinka baya fadan alkairi tssk! Saidai idan kaine bazaka fita a raye ba amma nasani we can make it!Yanzun dai abu nafarko dazamu farayi shine samun makaman dazamu kare kanmu dashi saboda dole mufita daga wannan wajen and let me tell you about zombies they are not like us cause they're dead already.To kill zombies,you need to destroy their brains,when their brain dead they can't do anything...wannan itane hanya mafi saukin kashe su indai ba brain din sune yadaina aiki ba to bazasu taba kyalemu ba secondly zombies are afraid of fire,indai kanason tsira da rayuwanka dole kasamo fireworks saboda bazasu iya zuwa inda kake ba,sannan main weakness dinsu shine stupidity,zombies have no intelligence,so they can be easily fooled..zombies cannot walk fast mu kuma da wannan damar zamuyi amfani wajen tsira da rayuwan mu...lastly try not to make any sounds saboda duk inda sukaji sounds sai sunje wajen koda kuwa ace nisan wajen yakai 100kilometers, ta wannan hanyan ne kadai zamu kauce sharrin su...hope I made myself clear?" tana kallonsu Adam ne yace "inada tambaya tayaya akayi duk kikasan wannan Ruky tayaya akayi kikasan abubuwa akan zombies haka?" Mikewa tayi saida taje wajen bag dinta kayanta tafara tattarawa tace "cause I'm watching zombies movies that's why I know lots about them but remember this isn't a movie, or kdrama this is real it is happening to us right here in this hospital we need to be very careful.... "
~*
“Oh lord" tace a hankali kallon kanta take a madubi cikeda mamaki ganin yanda skin dinta ya sanja color ita dai tasani jikinta ba haka yake ba amma yanzun saiwani glowing yake and her eyes suma sun sanja color zuwa golden color to kenan dama idan mutum yayi rashin lafiya haka yake zama? Anya kuwa aikuma ba yau ne tafara yin rashin lafiya ba....Itadai tasani tun ranan nan a station wata mata tasa bakinta a wuyanta tundaga nan bata kara sanin abinda ke faruwa ba yau tsawon two weeks kenan saida tayi kwana goma a asibiti amma meyasa meyasa tunda tadawo gida abubuwa suke sanja mata? cigaba tayi da kallon kanta ganin yanda takara kyau da haske tsallen murna tayi amma ga mamakinta saigani tayi tayi sama sosai cikin tsoro ta sauko kasan lalle akwai abinda ke damunta babu ta yanda zata iya wannan tsallen...Knocking aka fara wanda hakan shiya tsaida tunanin datakeyi, zuwa tayi ta bude kofan Maid ce cikin girmama tace "Hajiya tace ki sauko ga breakfast can yana jiranki..."
"Tell her I don’t wanna eattt!" daga haka ta rufe kofan..
Zama tayi a gefen gado gaskiya dole akwai abinda ke damunta komawa tayi gaban mirror din taci gaba da kallon kanta again knocking aka karayi "God meyasa mutane bazasu barni na huta ba?" tace ranta a bace zuwa tayi ta bude tana cewa "I said I don’t wanna eatt!!" Shiru tayi ganin Friend dinta ce tsaye itama kallonta take kamar wadda taga sabon halitta tace "Amara mezan gani haka? Mene yasamu idonki? And your skin is glowing wow that's really cute you just look Ah...may...zing Amara...mene sirrin? don na lura tunda kika kwanta a asibiti kikayi wani kyau.." Itakam takasa magana saboda ita kanta ta lura akwai sauyi a tattare da ita cikin sanyin murya tace "come inside we really need to talk!" Hannunta taja zuwa cikin bedroom din.
~*
"I just want to go home,and I want to see my family again...am sick of being alone..I need my family, I really missed my daddy, I wanted to hug him again..." she can't control herself right now kawai saitafara kuka..."Oh no don't cry babe please I'm here for you,I'll comfort you in the difficulty and painful times, and I will never leave you alone!!" Merapati tace bayan ta zauna a kusa da ita kanta ta kwantar akan lap dinta sosai take kuka ganin hakan yasa Basma zuwa ta kira Nimueh itama hankalinta yatashi ganin yanda Hassy ke kuka zama tayi tsawon minti daya saikuma ta mike kallon su tayi tace su biyo ta Merapati ce takama Hassy suka bi bayanta harda Mithian ma, wani bangare suka bi daban wanda tunda sukazo gidan basu taba zuwa ba babban daki ne saikuma gunki kala kala na dragon's manya da kanana saikuma wata matattakala a karshen wajen wani babban kasko ne saman shi wani mulmulallen dutse ne amma yanada haske sosai wanda ya haska kusan rabin dakin wani ruwa ta dauko acikin wata karamar butar zinare zubawa tafarayi akan dutsen, ruwan maimakon ya zube saima shigewa dayakeyi cikin dutsen saida ta zuba rabi sannan ta maida butar mazauninta nan da nan hasken yafara zama color daban daban red blue pink purple white black orange brown duk wani color dakuka sani saida yakoma sannan a hankali wata kofa ta bayyana ajikin dutsen nan da nan wasu irin sparks suka fara fitowa saikuma dutsen yafara zagayawa da sauri sauri bayan yayi sama sosai....a hankali komi ya dawo normal saidai abin mamaki tamkar tv haka suke kallon jama'ar garin su sosai hankulansu yatashi ganin yanda garin nasu yazama....Ita kanta Nimueh ta firgita da ganin abinda ke faruwa nan take Basma Merapati suma suka fara kukan....
Hannunta tanuna dutsen wani green din haske yafito nan da nan komi yakoma yanda yake juyawa sukayi suka koma masaukinsu gaba daya kuka suke inda su Mithian Nimueh,Catrina suke rarrashin su....
Yau kwana daya da ganin abinda ke faruwa a duniyar tasu gashi bazasu iya komawa ba saboda yanzun ba lokacin fita daga duniyar bane ba, kallo daya zakayi musu ka tabbatar suna cikin damuwa da tashin hankali sannan bangare guda Basma akwai maganan datakeso suyi da Merapati...
Kamar kodayaushe suna dinning area don cin lunch duk da bawani sosai suke ci ba saboda damuwan da suke tattare da ita...
Su kansu su Mithian sun damu ganin yanda suke cikin damuwa sam yanzun basa hira saidai kowa tayi shiru gara ma Merapati tanayima Hassy hira duk da bata cika bata answer ba..Mithian ce ta debo abinci a hannunta ta watsawa Basma, da mamaki take kallonta ita kuma tayi mata gwalo ganin hakan yasa itama Basma ta debo ta watsa mata because she understand why she did it she wants to lighten up their mood...Catrina ta debo ta watsawa Merapati ita kuma ta watsawa Hassy...kafin cikar 15seconds gaba dayan su sun fara watsawa kowa Wasa suke tamkar wasu kananun yara saida suka bata komai na wajen sannan suka daina.
Nimueh ta kalle su cikin murmishi "ina tunanin yau zamu fita kuga gari kusha iska na tabbata damuwar datake ranku zata rage sosai don haka kowa taje ta shirya ku wanke jikinku.."
Tana gama cewa hakan ta mike wani part ta nufa daban, ganin hakan yasa su Hassy zuwa su shirya suma har suka dawo Nimueh bata dawo ba...kuma abin mamaki kaf wajen da suka bata dazun an gyara tsab tsab, zama sukayi suna jiranta ba a dauki lokaci ba saigata ta fito jikinta sanye da white and blue din kaya saikuma karamar dragon a samanta “wow" Basma tace kallon su tayi tace "ku taho akwai inda zamuje"
Wani bangare daban sukaje na cikin masarautar anan suka ga dragons kala kala awajen guda uku tasa guard ya fito dasu Queen Nimueh Lady Catrina suka hau guda daya Basma Princess Mithian suka hau guda daya inda Hassy da Merapati suka hau guda daya.....Nan take suka fara tafiya akan iska saikuma suka shiga can cikin sararin samaniya.
Basu wani dade suna tafiya ba suka gansu asaman gajimare inda agabansu wata babbar masarauta ta bayyana amma kuma wani circle ya zagayeta sannan ga dragons nan kala daban daban suna zagaye wajen kallon su Drakaina tayi tace "anan wajen Nainah take duk da har yanzun bata farfado daga dogon baccin da aka sata ba lalle dole ku kula da inda zaku taka dakuma abinda zaku taba saboda wajen yanada matukar hadarin gaske"
A hankali dragon din suke saukowa tamkar walkiya haka suke shige cikin circle din saikuma gasu a gaban masarautar....Bayan sun sauko Merapati takama hannun Hassy tundaga wajen ginin mutum zaigane cewa lalle wajen yatara abubuwan mamaki da al'ajabi mutane ne manya da yara amma gaba daya sun kame jikinsu baya motsi kuma sun zama light brown wasu ma kamar aiki sukeyi amma a hakan suka kame wato jikinsu kamar tabo kamar kuma kasa...
Kallon su tayi "duk abinda kuka gani karku tabashi domin hakan zai iya janyo wata matsalan daban" tana gama fadar hakan tafara tafiya suma binta sukayi zuwa ainahin cikin gidan.
Tafiya suke cikeda kulawa saboda gudun janyo matsala nan take Basma tayi misplacing kafarta da sauri Queen Nimueh ta juyo "kowa ya tsaya a inda yake kada wanda ya motsa sabod.."kafin ta karasa aka fara zubo musu kibiya nan Mithian,Drakaina suka fara using da magic dinsu da kyar suka samu aka daina sannan takara cewa "this is just the beginning, you must be very careful idan kuma ba haka ba we will all died here saboda ba ko ina bane magic zai taimake mu ba.." Hannunta ta nuna zuwa kan wani kasko take wuta takama nan take duk wani kaskon wuta yakawo.
Haka suka ci gaba da tafiya zuwa cikin gidan sanann suna mamakin yanda gidan ya kasance da duhu gaba daya ginin yayi bakin kirin tamkar wani bangare na garin Drakaina kuma duk inda suka wuce akwai mutane,macizai,halittu daban daban amma gaba daya basa motsi wani babban gunkin maciji suka fara hangowa Mace ce akan throne amma kuma kanta gaba daya na macizai ne sune a matsayin gashinta saikuma kafafunta suma irin na maciji amma kuma yayi kama da kafar mermaid tana zaune amma itama bata motsi kamar sauran dai....
Wani babban daki ta bude amma shi baiyi bakin ba mutum zai iya cewa ana rayuwa a ciki ganin komi tsab ga lu'ulu'u inda suka karama dakin haske...Makeken gado ne na alfarma irin na sarauta wanda bakowane yake iya mallakar saba acikin sarakan harsai wanda ya isa kuma yakai wata kyakykyawar budurwace kwance akan gadon kanta da crown mai shape din maciji tunda su Merapati suke basu taba ganin mace mai kyau da kwarjini kamar wannan ba a hankali Hassy tace "Nainah ko? Gaskiya ne sai yanzun na yadda da zancenki dakikace she's the most beautiful princess in the world..yes you're right she's damn beautiful...."
Basma tace "what a sleeping beauty! Saina tuno wannan cartoon din buh ita only a true love kiss can wake her up..." tana maganar tana smiling, ganin yanda suke kallonta yasa ta jin kunya "you are such a baby Basma" Merapati tease her.
Sai kuma suka maida kallon su kan Nainah
Tana kwance hannunta daya akan daya jikinta sanye dawasu kaya na alfarma saikuma rabin jikinta rufe da wani irin bargo wanda da gashin dawisu akayi shi,duk wanda bai saniba zaiyi tunanin bacci take lalle tsafi gaskiyar mai shi kalleta tsab da ita alhalin tafi shekaru dubu ahakan? tabbas duk wanda bai shiga duniya ba yabar kallon abubuwan mamaki Hassy tace aranta..
Drakaina tace "ga Nainah the serpent wanda akasa bacci kuma kune kadai zaku iya tasota saidai ni kaina bansan tayaya ba harsai nagama karanta muku labarinta" Basma tace "nufinki baki taba karantawa ba?" Kanta ta gyada tace "kwarai kuwa bantaba karantawa ba kuma ka'ida ne duk wanda yake mulkin Drakaina yasan tarihin Nainah amma ni?" smile tayi taci gaba da cewa "sam bantaba sha’awar karanta labarin ba saboda a lokacin ma muna cikin tashin hankali shiyasa na yanke shawaran bazan taba karantawa ba harsai kunzo sannan....kuma wannan wajen babu mai iya shigowa a yanzun harsai mutum shi jinin Drakaina ne...kuyi sani