Showing 21001 words to 24000 words out of 30186 words
Chapter 8 - Wani Gari Horror Novel [www.arewahausanovels.com.ng]
saboda fitsarin dayayi duk yagama bata masa jiki.."
Karfe 2:30 nadare agogon dakin yabuga kuma adaidai wannan lokacin ne yafara mafarkin wani dajine mai duhuwa yaganshi a ciki babu komi a cikin dajin sai wasu irin tsuntsaye wanda girmansu yawuce misali. kamar daga sama ya hangota tana nufoshi cikin wani irin yanayi wanda shi a zahirin gaskiya baiga tana taka kafafuntaba kawai yaga tana tahowa gareshi kafin cikar minti daya ta iso wajensa kamar koda yaushe,tana isowa tafasa wata razanniyar kara sannan tafadi kasa tana wani irin kuka,,,saiyaga takoma MACIJIYA Amma wannan lokacin rabinta mutum rabinta macijiya, cikin wata murya mai dadin sauraro tafara magana "Shin kanaso nazama ajalinka ko? meyasa kaki yarda da bukatata" cikin rashin tsoro yayi yunkirin bata amsa. Saurin matsawa tayi dab dashi hannunta tasa ta rike masa makwogaro take idanunta yasanja color zuwa bakin kirin saikuma kwayar idon tazama yellow cikin wata murya marar dadin sauraro tafara magana "kada kayi tunanin don inasonka shi yasa kake ganin bazan iya kashe kaba,,,kasani yanzun nan Zan kashe Ka kowa ya huta shake masa wuya tayi da karfi, yafara kakarin mutuwa idanunsa sukayi jaah saboda tsabar azaba...dogon harshenta ta fito dashi tafara bin fuskanshi tana lashewa...Cikin wani irin yanayi yafarka gaba daya gumi yagama rufeshi dafe kanshi yayi sam yakasa gane dalilin sa na yin wannan kalar mafarkin meyasa yarinyan takeson ganin bayanshi? shin wani laifi ya aikata mata ne? Shi dai a iyakar saninshi komai kama da ita baitaba gani ba..
Asalin sunan sa Umar baban sa kuma Khalil a wancan lokacin yana daga cikin wadanda ake sa ran bama sarautar Drakaina Su uku iyayen su haifa saidai shi musulmine saboda mamanshi ba yar kasar bace ba wanda a lokacin auren nasu ansha rigima saboda ganin babanshi zai auri wanda bata bautama gunki Nova....Dakyar dai akayi auren kuma sunyi yarjeniya akan cewa bazasu takura ma yaransu ba duk addinin da suke so shi zasu bi....Hakan ce takasance lokacin data haifi Khalil yaron yataso cikeda hazaka da nutsuwa kuma sai hankalinsa yafi karkata kan bautama Allah daya lokacin dasuka girma ya auri wata a cikin gidan take itama maisuna...Elena itama dai haka suka sake yarjeniya akan bazasu takurama yaransu ba duk addinin da sukeso shi zasuyi....Bayan ta haifi Umar shima yazabi addinin babanshi wanda hakan ba karamin batama ran sarkin wancan lokacin yayi ba.......yataso cikin so da kauna kowa a cikin Masarautar son shi yakeyi duk da wani lokacin yanason yin magana akan meyasa suke bautawa abinda suka kirkira da hannun su? Amma babanshi ya hanashi shikam yadauki kudurin koba yau ba saiyayi magana...Ranan daya cika shekara 25 a duniya tundaga ranan yafara mafarki da ita wanda duk iyakan tunanin sa baitaba ganin koda mai kama da itaba....
Nainah kam al'amarinta ya tsananta kullum saitasa Kakanta fitsari a wando daya gaji babanta yakira yace yadauketa sutafi gida Habu yaso sanin dalilin,, Amma fir Baban Suwaiba yaki fada masa yace shi kawai yagaji da rigimarta kullum sai an raba fada d ita.
Tunda Nainah takoma gidan babanta abubuwa da dama sun faru ciki harda auren da babanta yakara. Ya auri wata bazawara mai suna Hajjo,sam batada mutumci ko kadan irin matan nan ne wanda suka gama yawo a duniya...yau kwananta uku da tarewa. Lokacin data tare da darene washegari da safe cikin isa taje ta taso Nainah waitayi mata aikin gida itakam tace baza ta iyaba, hayaniyarsu ce ta tada Habu daga baccin dayake, cikin sauri yafitoh yana tambayar "mene yafaru da wannan sanyin safiyar ake hayaniya haka?" Hajjo tace "yo wannan yar taka wai baza ya yimun aikiba" cikin bacin rai yace.. "Haba Hajjo da Nainah nawa take dudu shekaranta bakwai amma kice tayi miki aiki ae wannan rashin tausayine" cikin daga murya take cewa "ah lalle Habu!" tana magana tana tafa hannu "to wannan abin bazai yiwuba ace da wannan katuwar yarinyan a gida amma ni zanyi girki da shara? Wato saidai ta nemi waje ta zauna kenan inyi mata komi to wannan abin sam sam bazan yadda dashi ba yau ni naga lukutar masifa da sassafe" lol.
tana maganan kamar ta rufeta da duka, Habu kam takaicine yahanashi magana daki yakoma yana mai nadamar aurenta....sam batada tarbiya...
~*
Cikin nuna isa da gadara Hajjo tace "kee,Nainah badake nakeba magana ba" cikin tsananin tsoro tafito,tulu tabata tace taje rafi ta deno mata ruwa. jiki ba kwari tadauka tulun tana share kwallah,dakyar ta iya debo ruwan saboda bata saba ba Bayan tadawo tasata wanke-wanke da shara kafin tagama, tagama jigata dakyar ta shige daki domin ta huta.
Darana ma haka tasha aiki,abin mamaki Babanta kam Kodamuwa baiyiba sam baya magana wani lokacin ma har sa baki yake idan tana mata fada, Hajjo tamaida Nainah baiwarta duk wani aiki itane takeyi tun bata saba ba harta saba kullum tasan aikinta duk tarame ta fita hayyacinta kallo daya zakayi mata kagane cewa tana cikin matsala. Ko abinci bata ci sosai...hakan yakara sawa tayi rama sosai.
"Ni'ima.! Nainah!" Hajjo takirata cikin bacin rai tana huci kamar wata zakanya , dasauri ta karaso jikinta duk rawa yake saboda wani irin tsoronta takeji yanzun "wato dan iskanci kinaji ina kiranki shine kikayimn shiru koh" Cikin in'ina tace "uhm uhm banjiba shiyasa kiyi hakuri" rankwashi ta zuba mata sannan tarike kunnenta cikin fada take maganar "duk lokacin dana kara kiranki baki amsaba sainaci ubanki shegiya mayya,kitashi kikaimin nika kafin na zauneki anan" cikin sauri ta mike tadauka kwaryan tafita tana sharan kwallah.
Tana fita suka hadu da Habu nan take yakara bata ranshi yaja tsaki yayi shigewarsa cikin gidan.
Nainah kam tana can wajen nika sai can dare tadawo saboda layin dake wajen...bayan ta ajiye nikan taji muryan Hajjo a bayanta cikin tsoro taje wajenta nan Hajjo ta rufeta da duka,,tanayi tana masifa "taje ta zauna kamar wadda ta aika wata duniyar..."
Sosai take kuka tarasa abinda dake mata dadi haka ta rarrafa tashiga dakin datake kwana.wani tunani tafara lalle yazama dole ta nemo mafita idan kuwa ba haka ba zata rasa rayuwanta a banza...
Washe gari dasafe kamar kullum Hajjo tadauko kasko ta zuba wani garin magani aciki ta fito tsakar gida dashi, saida ta tabbatar ko'ina yasamu sannan ta ajiye kaskon, Sannan ta kira Nainah domin tayi mata aikin data saba.
Kwanaki sunja yanzun haka Nainah shekaranta takwas kullum da irin sabon wahalan datakesha a wajen Hajjo, Habu kam yafita harkanta. gaba daya yamanta yanada wata diya wai ita Nainah saboda ko kallonta yayi wani irin bacin rai ne yake rufeshi jiyake tamkar yakasheta kowa ya huta....
Yauma kamar kullum Hajjo ce rike da kasko amma kana ganinta kasan bata cikin hayyacinta sai gumi take sharewa duk ta hargitsa dakin. Leka can,bude nan haka take fama tun karfe 6na safe haryanzun sha biyu na rana tana aikin abu daya. kamar daga sama tajiyo muryan Nainah tana cewa "maganin kike nema koh" dawata irin murya maiban tsoro, cikin tsurewa tace "a,a,,,ah ba magani nake nemaba." kutt,ta hadiye miyau. kana ganinta kaga marar gaskiya Wata irin dariya Nainah tafara can kuma tayi shiru ta zubawa Hajjo ido saikuma tafashe da kuka irin na jarirai,tuni jikin Hajjo yafara kyarma dama tasan wannan ranan tana nan zuwa.
Bayan Nainah tagama dariyan saikuma ta hade rai, tafara magana cikin murya kala-kala sannan tace "kinsan nasan komi amma nafison kifada da bakinki" Cikin tashin hankali Hajjo tafara magana "dama,..dama... Uhm.... Dama lokacin dana hadu da babanki sai kawata jummai (kawar hajjo) tace yakamata naje wajen boka,,saboda babanki yana sonki sosae gara kafin na shigo na mallakeshi. Muka shirya sai wani kauye bangaren yamma da Drakaina mukaje dakyar mukaga bokan saboda tsabar yawan mutanen. muna shiga yafara wata irin dariya sannan ya murtuke fuska. Bayan mungama yimasa bayani saiyace tun farkon shigowan mu yasan komi akwai aiki babba agabanki,saboda wannan yarinyar MACIJIYA Ce" Cikin tsananin firgice ta dubeshi sannan tace boka "bangane ba kamar ya macijiya ce" Yace "kwarai kuwa amma nakasa gano komi akanta kawai abu daya nasani macijiya ce mai hadarin gaske.kuma tabbas baza ta bari ki auri babantaba" "To boka yaya Zanyi..?" Ta tambaya, "akwai wani garin magani dazan baki kullum da safe kinayin turare dashi shikadaine hanyan dazaki bi domin macijiyar batason warin maganin,amma fa duk ranan dabakiyiba kisani bazaki kara kwana a duniya ba, saikuma yabani wani kullin daban wanda da shine zan mallake Habu ko kallonki zaiji baison yi." Cikin kuka Hajjo tagama bawa Nainah Labarin Kuka take mai cikeda nadama tana rokon Nainah ta yafe mata. Kafin tagama rufe bakinta Nainah tayi kasa nan tadawo katuwar macijiya wanda saboda girmanta ta kusa cika dakin gaba daya...nannadeta tafarayi harsaida ta nade ta duka.....Sannan ta fito da harshenta take tafara zuke duk wani energy na jikinta......saikuma tafara sarin hajjo har a waje biyar take ta fadi kasa ba rai..gashi kuma jikinta yayi fari fat duk ta yamutse....,,,,, A hankali takeyin kasa harta dawo ainahin siffarta....sannan ta fice daga dakin ta bace bat.
@NM__🦋♥️
[27/01, 4:05 pm] Ablerh Authoress: Title: WANI GARI (The beginning of a new world)
Description: What happens when you somehow end up in a "New world? And what does it feel like to suddenly be a stranger in the world you thought you knew?
Merapati Hassy And Basma, both students one day a gate Into a different dimension opens to them as they find themselves in a different world,a world where mysteries and enchanted magic happens...How will they get home? What will happen to these girls along the way? Will they even be able to survive being in a world that is completely different from their own?
Tags #dimension#parallelworld#zombiesapocalypses#disappearance#journey#vampires#wonderland#magic#cursed#doppelgänger
~*
Episode 14: Nainah 2.
Nainah data bace a dakinta ta bayyana kwanciya tayi take bacci ya dauketa...Habu dama tundazun baya gidan sai yanzun yadawo
Da sallama yashigo gidan amma shiru ba a amsaba "Hajjo! Hajjo!!" Yafara kiran sunanta amma babu alamun zata amsa. A fili yace "yanzun haka ta fice yawon data saba ace mace kullum tana yawo bazata zauna a gidan taba."
Dakin yashiga gabansane yafadi ganin Hajjo kwance bakinta nafitar da wani irin farin ruwa,sannan gaba daya ta sanja kala kamar ba ita ba jikinta ma yayi fari fat ya yamushe cikin tashin hankli yafara kiran sunan "Nainah" wanda cikin bacci taji kiran da sauri tafito "Na'am baba lafiya kuwa" cikin tashin hankali yake magana "menene ya faru? Meyasamu Hajjo?"
Cikin damuwa tace "Baba nima bansaniba dazun dai najiyo ihunta"
Baice komiba yasa kai yafice daga dakin Nainah ajiyan zuciya tayi bayanta dafe kirjinta itama tafice da sauri.
Gidansu Hajjo yaje yasanar dasu Hajjo ta rasu,babanta kamar yayi hauka saboda kaf cikin yaranshi yafison Hajjo saboda tana bashi kudi sosai.. Komawa yayi cikin gida ya sanar da iyayenta mata cewa Hajjo lokaci yayi...nan gidan ya rikice da koke koke...Kafin karamin lokaci mutuwan Hajjo ta tsara ko ina a kauyen...
Bayan sun iso gidan dakinta suka Shiga cak baban Hajjo ya tsaya domin kallo daya yayi mata yagane cewa dafin macijine yayi sanadiyar mutuwar ta,baice komiba haka akayi mata wanka aka kaita gidanta na Gsky.
Shikam mamaki yakeyi garin yaya hakan tafaru? Kara matsawa yayi yana kallon jikinta sosai a firgice ya mike saboda mamakin abinda yagani ba wani abu ne ya bashi mamaki ba illa ganin irin dafin macijin wanda a kaf fadin duniya duk wani masananin sirrin macizai yasan cewa wannan macijin yanada daga cikin mafi hadari domin yawancin su ma ba ainahin macizai bane ba iska ce take shiga jikinsu wanda hakan zaisa suna sanja siffa zuwa duk abinda sukeso.
Bayan kwana Arba'in da rasuwan Hajjo babanta yakira Habu saboda yanason suyi magana ta fahimta lokacin dayaje yana zaune akan buzu na fata a kofar gida gaisuwa sukayi sannan yafara cewa
"Hakika nasan zakayi mamakin wannan kiran danayi maka abinda yasa nakiraka saboda na shaida maka Hajjo macijine yasa mata dafi kuma shine sanadin mutuwanta...saidai bansa ta ina macijin ya shigo ba" yadanyi jim yana kallon Habu kuma yana karantar fuskarshi
Cikin alamun rashin fahimta yace "kamarya banganeba
a ina tasamu dafin maciji,,?"
Baban Hajjo Yace
"Kasan dai nidin tsohon mafarucine kuma nasan kowani kalar dabba tacikin daji kallo daya nayima farin ruwan da Hajjo take fitarwa nagane dafin macijine,sannan kuma ga jikinta daya sanja color alamu sun nuna macijin saida ya zuke duk wani jinin jikinta sannan ya sareta.."
Kallon fuskar Habu yake saikuma yaci gaba da cewa "kuma alamu sun nuna cewa macijin agidanka yake saboda naji warinsa amma bansan ainahin inda yake ba kuma irin wannan macijin yanada matukar hadari kuma ina zargin yarka Nainah shawarata itace ka...." kafin Ya karasa fadan abinda zai fada Habu ya dakatar dashi ta hanyar daga masa hannu "nagode" kadai yace yayi ficewarsa daga gidan.
"Tabbas mutanen garin nan basa kaunata nida ya ta Nainah basuda burin daya wuce su daurawa Nainah sharri yakamata nadauka mataki bazan zauna ake yima yata irin wannan kazafin ba" Duk cikin zuciyanshi yake wannan zancen.
Da sallama yashiga cikin gidan Nainah ta amsa tana mai yimasa sannu da zuwa, ya amsa cikin kulawa duk saiyaji tausayinta yakamashi yarinya karama akeson kalawa irin wannan sharrin? shikam baisan dalilin dayasa ake yi mata sharriba. Wata zuciyan tace saboda kaf garin nan babu mai kyau dinta..
"Baba nakawo ma abinci" muryan Nainah ce ta katseshi daga tunanin dayake,yace "eh Ni'imatullah kawomin"
murmishi tayi harsaida dimple dinta ya lotsa tanason Babanta Yakira ta da wannan sunan.
~*
Lokaci yaja yanzu Nainah Shekaranta goma sha shida a duniya sosai kyau dinta yakara fitowa wanda mutane sukan cemata anya kuwa ke mutum ce? Duk lokacin data fito waje domin zuwa aika to fa ranan mutane basa iya aikin komi saboda har layi akeyi maza da mata yara da manya domin kawai suga murmishinta Her smile is like summer moonlight-beautiful and magical, with a fire that could melt the night.She can kill with her smile, she can wound with her eyes,and her skin is as white as snow, she's damn beautiful and hot....Duk lokacin data fita sai ansamu wanda suke jika jikinsu da miyau wannan dalilin yasa babanta yahanata fita.... (Jajaja I laughed in Spanish),,
Sai yanzu babanta yake shirin kara wani auren.
Shirye-shiryen biki ya kankama Habu har fenti yakara yima gidansu duk da cewa gidan kasa ne kuma kasar baka ce yarinyar dazai aura acikin garin Drakaina take akasuwa suka hadu wajen kasuwancin sa soyayya mai karfi ta shiga tsakaninsu.
Yau juma'a aka daura auren Habu da Amaryansa Sadiya.
Saiwashe gari aka kawo masa amaryansa, bayan yan kawo amarya sunzo Habu yayi komi wanda duk wani ango yakeyi.
Sannan yan kai amarya suka tafi akabar amarya da ango kawai...Wanda duk abinda ke faruwa Nainah ko lekowa batayi ba..
Bandaki yaje domin yayi alwala bayan ya idar yashigo dakin.
maimakon yaga sadiya kan gado saiyaga wata katuwar macijiya wanda saura kadan ta cika gadon gaba daya, wani irin faduwa gabansa yayi yanason yayi addu'a amma sam bakinsa kamar ansa dan makulli an rufe masa bakin.
Aebaigama tsorata ba saida yaga macijiyan ta taso tana tafiya irinta mutane tana nufowa gareshi sannan kuma tana fito da dogon harshenta... kafin takaraso yafadi kasa sumamme
Labulen dakin na daga amma maimakon naga tsakar gidan Habu sainaga wata irin Hadaddiyar fada tunda nake bantaba ganin irin fadar ba iyakar tsaruwa fadar ta hadu Ko ina ya wadatu da haske kamar ba dareba.
Wata kofa muka nufa tafiya muke amma ba alamun munkusa bayan kamar minti talatin mukazo wani gini,macizai ne kala-kala awajen, sannan gawani babban gunkin maciji nan wanda kasanshi duk macizai masu girman gaske can na hango Sadiya wani maciji ya nannade ta babu alamun tanada rai, Nainah wata dariya tafara saikuma tayi girgiza gaba daya ta bace bat saidai wani bakin hayaki wanda a cikin hayakin fuskantane kawai ake gani cikin wata irin murya tafara cewa "wannan shine hukuncin duk wadda ta auri babana"
Habu kam sanyi asubane yafarkan dashi yana farkawa yaga Sadiya kan gadon amma fuskanta yana kallon bango take ransa yabaci yaji tsanarta sosai aranshi wato shi zata rainama wayau kenan..wani bakin ciki yakeji...yanajin dama ya shake ta kowa ya huta gaban gadon yaje ya sharara mata mari yace "Don ubanki tashi ki kwashe kayanki nasakeki saki uku" amma me? ji yayi tamkar dutse yataba gashi hannunsa yaji ciwo...
Cak yatsaya sakamakon tozali da yayi da bakin abu yana fita daga bakinta,cikin tashin hankali yakare mata kallo tabbas bata motsi wata irin zufa ce take ketomasa shikam meke damunsa haka? meyasa duk lokacin dayayi aure baya samun nutsuwa saidai tashin hankli.?meyasa duk matar daya aura take mutuwa? A matukar sanyaye yafice daga dakin.
Keken doki yahau yaje Drakaina yasanar da iyayenta tarasu bakin ciki tashin hankali al'ajabi duk sunganshi a wannan ranan,
Nan aka kira wani mai maganin gargajiya saboda a gano dalilin dayasa take fitar da bakin ruwa din nan...maganar dai dayace macijine yayi ajalinta.
wasa-wasa saida ya auri mata Biyar duk suna rasuwa dalilin dayasa kenan mutanen kauyen suka daina bashi auren "ya." Kuma duk wani mai magani cewa suke Nainah ce take ajalin duk matan dayake aure amma haryanzun yaki yadda da hakan shi kawai gani yakeyi hassada ake masa ganin irin kyawun datake dashi....
Kara bude wani page din tayi da niyan cigaba da karanto musu labarin Nainah Merapati ce tayi saurin katse ta tace "Lokacin sallan magrib ya gabato kibari zuwa anjima idan mukayi sallan saikici gaba da bamu labarin." Hassy tace "abinda zance kenan kika rigani" Basma tace "tunda nike bantaba jin labari mai cikeda al’ajabi kamar wannan ba lalle Nainah tanada abin mamaki nikawai so nike nasan dalilinta na kashe duk wanda ya auri babanta."
Mikewa sukayi alwala sukayi sannan suka gabatar da sallan magrib wanda Princess Mithian, Queen Nimueh, Lady Catrina baki bude suke kallon su saboda tunda suke basu taba ganin ana bauta haka ba,, (in case of confusion basu san addinin islam ba sai a labari kawai, basu taba ganin yanda ake sallah ba cause yanzun babu abinda suke bautama idan ba Gunki Nova ba)
Bayan sun idar sunyi addu'o'i sannan suka dawo wajen suka zauna da mamaki suke kallon su ganin yanda suke kallon su kamar yau suka fara ganin su Basma tace “what's wrong?"
Lady Catrina tace "kawai muna mamaki ne shin wannan wani irin addini ne haka? Saboda mu duk fadin nahiyar nan babu masu bauta irin taku sama da shekaru dari biyu gunki nova muke bautama saikuma masu bautama wuta da taurari.." Smile tayi tace "karki damu lokaci na