Showing 24001 words to 27000 words out of 30186 words
Chapter 9 - Wani Gari Horror Novel [www.arewahausanovels.com.ng]
nan zuwa zanyi miki bayanin komi.." Kallon Queen Nimueh tayi tace "my lady we are waiting for you..." She just smiled and said "don't worry dear but before I continue the story,I have something to show you follow me" mikewa sukayi dukansu sukabi bayanta....basu dade suna tafiya ba suka tsinci kansu a wani babban garden wanda tunda su Merapati suke basu taba ganin garden mai kyau din wannan ba wajen saboda hasken shi kamar safiya ne sannan daga can sama akwai moon blue color wanda hakan shiya karama wajen kyau da haske sannan ga flowers nan kuma duk bayan 10seconds suke sanja color ga Rose's nan masu kyau kala kala duk wani abu dake cikin garden din yana motsi don wasu flowers din ma har heart shape sukeyi kuma suna fesawa mutum wani irin ruwa mai kamshi..."Wow" kawai suke cewa saikuma daga can gefe wata shimfida ce ta alfarma inda aka zuba kayan motsa baki kala kala dakuma abinci suma kala kala nunasu tayi da hannunta take wani green din haske yafito ya shiga jikinsu atare suka fara tafiya akan iska.... sama sukayi kadan yanda zasufi ganin garden din da kyau...Hassy hannunta tasa ta rufe bakinta saboda yanda garden din ya hadu ga wasu irin sparks lights suna fita daga jikin kowace flower wanda hakan yasa wajen kara shining.....The place is very beautiful, amazing,breathtaking and magical...Sannan ga karamin kogi mai haske sosai wanda a cikinsa wasu kalan kifaye ne masu kyau kala daban daban hakama jikinsu colors ne masu haske da kyau....
In a slow motion suke saukowa har suka gama sauka a kasa wajen shimfidar suka nufa dukansu zama sukayi sannan suka fara cin abincin....
Yanda suke hira dakuma wasa da dariya mutum zaiyi tunanin sun saba sun san juna tunda can...
Bayan sungama komawa sukayi cikin gidan Hassy ce ta kwanta bayan ta dafe kanta tace "oh my gosh...I am very tired" Merapati ce ta matsa kusa da ita tafara yimata massage ganin hakan yasa itama Basma zuwa ta farayi mata.....
Dagowa tayi tace "thank you babes " Bayan tayi musu wink*
Mithian,Nimueh,Catrina cikin birgewa suke kallon su saboda suna kula da junan su sosai duk da wani lokacin suna fada......
@N__M🦋♥️
[27/01, 4:05 pm] Ablerh Authoress: Title: WANI GARI (The beginning of a new world)
Description: What happens when you somehow end up in a "New world? And what does it feel like to suddenly be a stranger in the world you thought you knew?
Merapati Hassy And Basma, both students one day a gate Into a different dimension opens to them as they find themselves in a different world,a world where mysteries and enchanted magic happens...How will they get home? What will happen to these girls along the way? Will they even be able to survive being in a world that is completely different from their own?
Tags #dimension#parallelworld#zombiesapocalypses#disappearance#journey#vampires#wonderland#magic#cursed#doppelgänger
~*
Episode 15: Friends
Washe gari bayan sungama breakfast sunyi wanka Basma ta kalli Queen Nimueh "yaushe zaki karasa mana labarin?" Hassy tace "eh gaskiya kuwa don ni na matsu naji karshen labarin." Merapati ce tadawo kusa da Hassy tazauna dab da ita sannna ta daura kanta a kafadarta tace "wallahi nima haka please kici gaba yanzun tunda bama komai we are all free now"
Mikewe Catrina tayi ta dauko book din ta ajiye agabanta sannna itakuma Drakaina tafara budo shafin har tazo daidai inda suka tsaya sannna tafara karantowa a fili kamar haka....
~*
"Al'amarin Nainah kuwa sai cigaba yake ko cikin kawayenta idan akayi musu koh fada da ita Toh daga ranan sunanka gawa,Ko makaranta duk malamin daya daketa shima saita kasheshi. Tun Abin baya damun Habu haryafara damunsa yanzu m shima yafara yadda da maganar mutanen gari cewa Nainah Macijiya Ce,saidai bashida hujjar hakan kuma bata nuna masa wata alamar ita din Macijiya Ce Shidai Abu daya yasani duk wanda yayi mata laifi washegari za aga mutum ya mutu. shawara ya yanke akan zaije ya tambayeta tafada masa gaskiya idan ita din da gaske macijiyace"
"Nainah! Nainah!!"
"Na'am Babana"
"Zo nan inason muyi magana"
Da sallama ta shiga dakin tace "Dada Gani" Kallon tsaf yayi mata sannan yafara cewa "Nainah!...hakika banjin dadin yanda mutanen kauyen nan sukeyi miki sharri da kazafi suna cewa ke macijiya ce.,kinsani kaf fadin kauyen nan bakida wanda yafini inason kifadamn gaskiyan lamarin! meyasa kike kashe mutane? meyasa duk wanda kukayi fada sai ya mutu washe gari? kuma dagaske ke macijiyace?"
kuka tafara sannan tace "Duk duniya banida kamarka inason farin cikinka fiye danawa yakai babana kayi sani cewa niba Macijiya Bace ba kawai sunayiman sharri saboda surabani dakai sannan kuma duk wanda kaga ya mutu kwanan sane yakare bantaba kashe kowa ba kuma bazan iya kashe kowa ba" ta karasa maganan tana kara fashewa da kuka, take tsananin tausayinta yakara kamashi tabbas da alamun gaskiya a maganganunta tayaya zatake kashe masa duk matar daya aura alhalin tanason ganin farin cikinsa,akwai dai wanda yake binsa da sharri shine ake makalawa diyarsa kuma gudan jininsa cikin kulawa yace "yi hakuri kinji yar baba nidama nasani mutanen garin nan basa kaunata tunda harsuke dora mki irin wannan sharrin" Goge Hawayenta tayi ta kalleshi "Baba Dan Allah kayi hakuri banson kana damuwa da maganan mutanen garin nan saboda ina tsoron wani ciwon yakamaka kai kadai nake gani zuciyata tayimin sanyi idan narasaka bansan yaya rayuwata zata kasance ba a cikin garin nan saboda sam basa sona basa kaunatah" takara fashewa da kuka nan yaci gaba da rarrashinta dakyar tayi shiru
~*
"Haba Umar wannan wace irin rayuwace ka zabawa kanka kai kullum cikin tunani duk kabi ka rame nayi nayi kafadamin abinda dake damunka amma ka ki fadamin ko?" tunda tafara maganar ya zuba mata ido cikin alamun damuwa yace "Ummieh babu abinda yake damuna" hannu ta daga masa "banason wani dogon zance idan babanka yadawo zanfada masa tunda shi kana tsoronshi zaka iya fada masa abinda ke damunka" mikewa tayi ta barshi nan zaune.
Bayan kamar awa uku Abbanshi yadawo bayan ya huta yaci abinci suna zaune a babban parlourn su wanda yaji kayan alatu irin na gidan sarauta ga maids nan sunata aiki kallon su Ummieh tayi tace "ku ba mu waje" atare suka durkusa sannan suka fice daga parlourn.
"Yawwa dama inason magana dakai" tana kallon Abban nashi "toh inajinki" "dama maganar Umar ce,yaron nan akwai abinda ke damunsa amma sam yaki fadaman,,Duk ya rame kamar bashiba"
"Kiramin shi" Kawai yace,tashi tayi takirashi bayan kamar 5mns ya iso,guri nasamu ya zauna sannan yace "Abba gani"
"Umar?" yakira sunanshi,"Umar meke damunka Umminka taceman kwana biyu ta rasa gane kanka? Shin akwai abinda ke faruwane wanda bamu sani ba?"
"Abba babu abinda yake damuna fa" kallon tsab yayi masa yace "idan ma wani abu kake boyewa wata rana za muji kuma zamu gani" Ummieh ta kalle shi "yanzu iyakan abinda zaka ce kenan? baza kasashi a gaba yafadama damuwarsa ba.nifah duk na damu”
Smile yayi yace "haba yazakice haka tunda yace babu abinda yake damunsa shikenan,tunda aishi ba yaro bane ba kuma bazamu takura masa ba kibarshi wata rana dakansa zaizo yafadama abinda ke damunsa.." Shidai umar bashida bakin magana yana jinsu,can yace "Abba zankoma ciki inason anjima naje gidansu Fadeel,"
"to kakula dakanka"
Ummin sa kuma tace "ka gaisawummin fadeel din" ya amsa da "toh" sannan yamike yakoma dakinsa.
Fadeel Abokin Umar ne tunsuna yara sun shaku sosae shima musulmi ne kamar Umar din kuma ta dalilinsa ya musulunta yanzun haka har Ummin Fadeel din sun muslinta
Lokacin daya isa gidansu Fadeel sauka yayi daga kan keken dokin sannan yafitoh direct cikin gidan ya shiga a parlour yatarar da Ammin Fadeel gaisheta yayi Itakuma tana tambayrsa yan gidan,,,,yace duk suna lafiya ummieh ma tace nagaisheki,ina amsawa tace yaje fadeel din yana dakinsa to yace sannan yatashi ya nufi dakin fadeel dn.
Da sallama yashiga dakin kwance ya ganshi da alamu yayi nisa a tunanin dayake "Fadeel!fadeel.!" Yakira sunanshi firgit yatashi ganin Umar ne yasashi ajiyan zuciya, “ya friend ashe kaine wallahi nadauka Ammi ce,." Hannu yamika masa suka gaisa kowa yana tambayar kowa ya aiki. Fadeel yace "gara dakazo wallahi ina cikin damuwa Umar"
"meke damunka.?"
Fadeel yace "Wallahi Abbane da rigima dole sainaje kauyensu kuma fa babu kowa nashi acan saboda anyi zaman mutumci da kakannina shine zanje nagaishesu" dariya Umar yake yace "shikenan saika samo mata acan koh,? shikam Fadeel abin ne yabata masa rai yace "Aa ka manta surika zanyi ba mata ba" wata dariyan Umar yakara kwashewa da ita yace "ai duk daya yaushe zan raka ka?" yakarasa maganan yana daga masa gira. Fadeel Yace "Aesaikaxo kakaini koh.?" Umar ne yataso yazo kusa dashi sannan "yace kaga friend dawasa nake yaushe zakaje? inason na raka ka saboda inason zuwa kauyen, dama nagaji da zama a cikin Draikana din nan" Wata harara Fadeel yayi masa sannan yace "ba rana,don banason zuwa" dakyar Umar yashawo kan Fadeel akan ranan asabar zasuje daga nan yayi masa sallama har bakin kofa yarakashi sannan yadawo cikin gidan. Umar kam lokacin daya koma gida ana kiran sallar magrib masallaci yawuce duk anan cikin gidan yake a wancan lokacin...baidawoba saida akayi isha abinci kawai yaci ya wuce dakinsa saboda yau yagaji sosae,saida yayi wanka sannan yakwanta.
Can cikin dare kamar dai kullum yau ma yafara mafarkin daya saba amma wannan karon yasha banban dana kullum domin suna zaune cikin wani lambu mai kyau ga ya'yan itatuwa da furanni masu kyau da kamshi fuskanta fal fara'a tana sanye cikin wata hadaddiyar doguwan riga maroon color wadda tayi dai-dai da skin dinta hakan yasa kyawunta yakara fitowa bayan ta iso ta zauna a kujeran dake kusa dashi tanayi masa wani rikitaccen murmishi, wanda duk lokacin datayi smile hasken hakoranta har kashe ido sukeyi cikin murynta mai kamada busar sarewa tafara magana "Yakai masoyina kuma abin alfaharina hakika ina cikin farin ciki marar misaltuwa domin ka kusa zuwa gareni." Yace "Hakika kinyi babban kuskure dahar kike tunanin zan zama masoyinki babu wadda na tsana kamarki kiyi sani cewa..." kafin yakarasa ta daka masa wata irin tsawa wanda bakinta har fitar da hayaki yake kuma idonta sunfara sanja color ganin tana kokarin rasa control kawai saita bace bat..Wani irin gurnani yafara ji daga bayansa mutuwar tsaye yayi ganin wata irin katuwar macijiya a bayansa kafin yayi wani yunkuri tuni macijiyar tafara hadiyeshi....daidai wannan lokacin ya farka yana mai nadamar kwanciyarshi baccin Toilet yanufa yadauro alwala yana mai kaiwa ubangiji kukanshi akan ya saukaka masa abinda ke damunsa.
~*
Habu zaune abin duniya yayi masa yawa saboda wani abu da Nainah ta tsiro kullum idan dare yayi baya kuma ganinta saikuma gobe da safe wannan abun yana damunshi. gashi jiya sunyi fada da yar gidan maigari yanzu haka yarinyan ta rasu itakuma Nainah hukuma sunkamata tanacan hannunsu. mutanen gari sunyi kokarin nuna masu ilar kama Nainah amma sunki, Adaren da suka kamata mutum dayane ya tsira gaba dayansu su biyar duk sun mutu.
Itakuma ba agantaba ko ina anyi cigija amma babu alamarta. abubuwa sunyima Habu yawa yarasa inda zai sa kansa yaji sanyi mutanen gari kowa yafita harkansa,duk inda yaje saidai kaga ana gudunsa...yanzun haka ko kasuwa yaje ba a siyan kayansa wata tsohuwa ce kadai take siya kuma kullum duka take siyewa wanda hakan ba karamin mamaki yake bashi ba kuma baitaba ganin fuskanta ba...
Yau takama asabar ranan dasu Fadeel zasu je kauyen su Nainah hakanan gaban Umar yaketa faduwa baisan daliliba,kuma duk jikinsa yayi masa nauyi. dakyar da tambaya suka iso kauyen kafin su iso cikin kauyen cikin ciyayin dake gefen hanya suka ga alamun ana daga musu hannu cikin sauri Fadeel yace a tsaya da tafiyan kallon Umar yayi yace "mutsaya mutaimaka masa koh" shikam tsaki yaja yace "duk yanda kagani." Murmishi Fadeel yayi sannan yafita yana zuwa gabansa yafadi cikin tashin hankli yake kiran "Umar....!!!"
@N__M🦋♥️
[27/01, 4:05 pm] Ablerh Authoress: Title: WANI GARI (The beginning of a new world)
Description: What happens when you somehow end up in a "New world? And what does it feel like to suddenly be a stranger in the world you thought you knew?
Merapati Hassy And Basma, both students one day a gate Into a different dimension opens to them as they find themselves in a different world,a world where mysteries and enchanted magic happens...How will they get home? What will happen to these girls along the way? Will they even be able to survive being in a world that is completely different from their own?
Tags #dimension#parallelworld#zombiesapocalypses#disappearance#journey#vampires#wonderland#magic#cursed#doppelgänger
~*
Episode 16: The News.
Cikin tashin hankali yaci gaba da kiran sunan Umar da sauri yafito wanda shikansa a lokacin ji yayi tamkar umarni ake basa akan yafito din yana karasawa wajen idanun sa yasauka akanta saidai baya ganin fuskan ta saboda ta juya can, kallon Fadeel yayi yace "to yanzun yaya zamuyi da ita?bamusan wace ba gaskiya bazamu taimak..." kafin yakarasa ta juyo da fuskan saidai haryanzun baya ganin ta saboda fuskanta duk jini ya rufe rabin... Fadeel yace "kawai mutaimaka mata inaga a cikin kauyen take itama" kamata sukayi sukasata a bayan keken dokin sannan sukaci gaba da tafiya...
Lokacin dasuka isa kauyen gidan mai unguwa suka tambaya aka nuna musu gashi mutanen garin sai kallon su sukeyi ganin cewa yanayin shigar su ta banbanta datasu komi da komi ma ba iri daya bane ba saboda ba sosai ake ganin yan gidan sarautar Drakaina ba...shi yasa suka zama abin kallo a wajensu shikam Fadeel duk ya tsargu kara jan tsaki yayi saboda sam bayason takura bare kuma ayita kallonsa...
Bayan anyi musu sallama dashi yace su shigo gaisawa sukayi kallon su yayi yace "daga ina kuke? Meya kawoku wannan kauyen namu don kallo daya za ayi muku a gane cewa daga gidan sarauta ko attajirai kuke" don shi bai gane suba Fadeel ne yayi masa kwatancen kakanninsa cikin fara’a suka kara gaisawa sannan suka ce a hanya sun hadu da wata yarinya wataqilan a nan take mikewa sukayi atare suka fita gaban sane yafadi saboda kallo daya yayi mata yagane cewa Nainah ce salati yafara saikuma ya tsaya da tafiyan kallon su yayi yace "kuyi gaggawar sauketa daga kan keken dokin saboda wannna yarinyar dakuke gani muguwa ce kuma macijiya ce duk wanda tsautsayi yafada akansa baya kara koda kwana daya yanzun haka ba a fi kwanaki ba takashemin yata saboda kawai sunyi cacar baki bama ita kadai ba hatta uwarta saida ta kashe kuma duk matar da babanta ya aura a ranan take mutuwa.."
Baki bude suke kallon sa Fadeel ne yafara dariya saboda shi a ganinsa duk karya ne kokuma tsatsuniya ce kawai dagowa yayi yace "haba dai tayaya zata zama macijiya? wace shaida kukeda ita dahar zaku iya kulla mata wannan sharrin? yanzun dai ba wannan ba bani magani nasa mata saboda ta zubar da jini sosai" kanshi kawai ya daga cikeda takaici yakoma cikin gidan baidade ba yafito hannun sa rikeda wata jaka ta fata mikama Fadeel yayi bayan sun fito da ita shikuwa Umar cikin keken dokin ya shiga inda anan Fadeel yafara goge mata duk jinin daya bata mata fuska tasbihi yake aranshi saboda ganin irin kyawun datake dashi... Aransa yace "lalle nasamu matar aure."
Duk wani ciwo saida yabi yasa mata magani amma baigama sa mata ba yaga duk inda yasa maganin yana cirewa dakanshi kuma babu ko alamun ta tabajin ciwo da sauri ya mike daga gabanta tunda yake baitaba ganin irin hakan tafaru ba amma tayaya? dama akwai irin wadannan mutanen wanda sunajin ciwo atake yake warkewa?tabbas akwai kamshin gaskiya a maganar mai unguwa koda ace ita ba macijiya bace ba akwai wani abun al’ajabi atareda ita juyowa yayi ganin mai unguwa yana mishi kallon "ai na fada maka" yasashi mazewa kawai yana sosa keya yace "yanzun ka yadda da abinda nafada maka? Ko haryanzun kana tantama?” kansa ya girgiza yace "dama akwai yan baiwa irin su ai."
Wajen Umar yaje yace masa yazo yaga wani abun mamaki fitowa yayi saidai sama ko kasa basu gantaba Fadeel har hanya ya duba amma babu koda mai kama da ita but how is that possible?who is she? definitely there is something wrong with her...she's not a normal person, tunanin dayakeyi kenan aransa...
Basu wani dade ba suka ce zasu tafi a hanyan su ta komawa bayan sun bar kauyen suka fara hango wani farin haske yana matsowa inda suke tsayawa sukayi da tafiyan saboda babu ta inda zasu iya wuce wa hasken ne yaci gaba da matsowa haryazo dab dasu kyakykyawar budurwace sanye da fararen kaya saboda tsananin hasken kayan shiyasa suke hango hasken tundaga nesa..baki bude suke kallonta tunda suke basu taba ganin mace mai kyau kamar wannan ba shikuwa Umar yayi nisa a tunaninsa tabbas yasan wannan fuskar amma kuma a ina? kwata kwata yakasa tuno inda yasanta hakan yasa shima maida hankalinsa kanta yazuba mata ido...
Cikin hadaddan greek dinta tafara magana "ThĂ©lo aplĂłs na sas efcharistĂso, pou me voithĂsate, sas efcharistĂł polĂ˝! kai tha sas plirĂłso pĂso, párte aftĂł to koutĂ pou tha sas voithĂsei mia mĂ©ra.....means (I just want to thank you,for helping me, thank you very much! and I will pay you back, take this box it will help you one day.)"
Bayan ta mika masa wata karamar akwati mai kyau dakyar ya amsa saboda ya shagala da kallonta dakuma yanda take magana da greek tamkar dama can yaren saboda ita akayisa....
"her voice is so cute, and her accent was damn amazing when she is talking in greek.."
*Oo I'm in love with you Nainah*wink
Yana amsa ta bace bat da sauri sukabar wajen gaba dayansu a mugun tsorace suke...babu tantama aljana ce suka hadu da ita gashi kuma ko sunan ta basu sani ba sannan kyau dinta ya wuce misali....
Yau kwanansu biyu dakomawa gida shikam Fadeel jiyake kamar ya bude akwatin yaga mene a ciki amma kuma wani bangare na zuciyansa yana gargadinsa akan hakan wataqilan haryanzun akwai sauran lokaci..da wannan tunanin yake hakura kuma a yanzun yagama yadda cewa sonta yake yakamu dason aljana.
Umar ma duk hankalinsa baya jikinsa kawai burinsa ya tuno inda yasanta amma yakasa tamkar wanda aka wanke ma brain kuma duk lokacin daya tsananta tunani take wani irin ciwon kai ke kamasa wanda harsaiyaji kamar zai rasa ransa...Yanzun haka yana gaban mirror kansa yake kallo ta cikin mirror din yafara hango wata mata jikinta tasa wata black abaya amma kuma lokacin daya waiwaya baiga komi ba juyowa yayi