Showing 12001 words to 15000 words out of 30186 words
Chapter 5 - Wani Gari Horror Novel [www.arewahausanovels.com.ng]
din.
kowa bag dinsa ya dauka sannan suka nufi cikin dajin.
Basu wani dade suna tafiya ba sukaga gidan shiga sukayi bayan sun kunna torch saboda wajen yanada duhu sosai.
Bin ko ina suke suna dubawa gashi gidan babban gida ne, ci gaba da duba ko ina sukeyi amma basu gansu ba.
Wani babban daki suka gani budewa sukayi saidai gaba daya wasu irin halittu ne tamkar mutane amma kuma jikinsu yayi bakin kirin su kansu baza su iya tantancewa ba bi suke a hankali suna duba ko ina wani mai suna Abduljalal ne yataka wani abu mai tsini nan da nan jinin sa yafara zuba ganin hakan yasa su kamoshi suka fice daga gidan,bayan sun rufe gidan.
Direct wajen tents din suka tafi.
Abinda basu saniba akwai wata a cikin su Leemah ashe ita zamewa tayi tabi wata hanya daban sukam sam basu lura da itaba ganin yanda Abduljalal yaji ciwo....
Jin kamshin jinin yasa wannan konannun zombies din fara hade jikinsu cikin karamin lokaci gaba daya sun dawo ainahin siffarsu ta zombies kuma a lokacin babu abinda suke so sama da son shan jinin mutane.
Leemah tana tafiya nan tafara jin motsi a bayanta juyowa tayi ta haska amma bataga komai ba cigaba tayi da tafiya still bata daina jin gurnanin ba cikin tsoro ta juyo da niyan komawa jitayi an kama hannunta nan take yasa bakinsa ya cijeta,dama hannunta akwai torch nan ta hau buga masa a kai take yafadi awajen da balain gudu itama ta fice daga gidan tana mai mamakin menene ya cijeta haka? Saboda ita sam bata taba kawowa akwai wata halitta a gidan ba,gashi kuma torch dinta ta mutu lokacin hakan yasa bataga komai ba.
Bayan ta fito nan ta duba inda aka cijeta din,wajen yayi bakin kirin ga wani irin blood black yana fitowa tacikin wajen, karamin handkerchief tadauko daga bag dinta ta daure wajen.
Tana komawa tent din su ta shige saboda sam batajin dadin jikinta,,
~*
15mns later
Tent partner dintane ta shigo ganinta kwance cikin matsanancin hali yasata fita da gudu su Ruky ta fadama gaba daya kanta sukayi suna mata sannu kanta kawai ta iya dagawa saboda ita kadai tasan metakeji gashi color din idonta yafara sanja color Nasir Mukhtar Nasir shine yayi mata allura saboda jikinta yayi zafi sosai fita sukayi domin bacci yafara dauketa.
_2:00am_
Partner dinta bacci takeyi hankali kwance kuma sai akayi rashin sa'a dayar da suke sharing tent tare bata nan sunacan tent din su Merapati itadasu Ruky anan zasu kwana tamkar a mafarki tafara jin wani irin sauti bude idonta tayi,ganin Leemah durkushe acan gefe tana wani kalar amai da sauri ta mike domin taimaka mata saidai lokacin dataga yanda kamanninta suka sanja hakan yasata sakin wata irin kara Leemah kam batayi wani tunani ba takamo ta sannan tasa bakinta a wuyanta....daidai lokacin su Ruky suka iso tent din in shock suke kallonta ganin yanda take shan jinin partner dinta gaba dayansu firgicewa sukayi cikin sauri suka dauki bags dinsu sannan suka nufi cikin dajin da gudu.
Wannan gidan dai suka kara komawa anasu ganin nan ne kadai zasu samu su tsira da rayuwansu, saidai ga mamakin su yanzun gidan babu duhu gaba daya bulbs din sunkawo sai a sannan suka lura da cewa asibiti ne shiga sukayi bayan sun rufe kofar shiga ainahin cikin hospital din.
Nan ma ko ina fess tamkar yau aka bude hospital din,jikinsu yagama basu cewa akwai wani abu a cikin hospital din saidai basu san mene ba ganin hakan yasa Ruky cewa "mu bar hospital din nan" juyawa sukayi amma abin mamaki babu kofan da suka shigo sama ko kasa basu gantaba.
Kowa yarasa abin cewa nan fa aka hau kallon kallo,kuma kallo daya zakayi musu kagane cewa a tsorace suke tattarawa sukayi suka shige female ward dakin yanada girma sosai ga patient bed's nan masu yawa kowanensu yasamu bed daya suka kwanta amma babu alamun bacci a idon su kowa tunani yake wace irin masifa suka kawo kansu?
Washe gari da suka tashi duk wannan hasken babu hospital din yakoma asalin yanda yake take hankulan su yakara tashi sudai sun san cewa ba mafarki sukayi ba jiya gaba daya hospital din da haske tayaya hakan tafaru? Kallonsu Ruky tayi cikin sanyin murya take magana "You already know what is going on,we must be very careful. This place isn't safe and secure...from now on we will be together.... Kar wanda yabar dakin nan duk da cewa bamusan ainahin abinda ke faruwa ba amma alamomi dayawa sun nuna cewa wajen nan akwai hadari...."
~*
Leemah kuwa bayan tagama shan jinin partner dinta itama cikin karamin lokaci takoma zombies din a tare suka bar cikin dajin su kansu basu san inda zasuje ba a yanzun babu abinda sukeso irin shan jinin mutum daidai lokacin suka iso bakin titi,wata karamar mota ce ta tsaya a gabansu sam bai lura da yanayin su ba fitowa yayi yana tambayarsu shin zai iya taimakon su? Sai a lokacin ya lura da yanda kamanninsu suka sanja kafin yayi wani abu harta kamo hannunsa tasa bakinta hakama leemah itama bakinta tasa a kafanshi wani karfe ya dauko a motanshi ya buga musu da sauri ya shige motan.
_8:30am_
*TRAIN STATION*
Tsaye take jikinta sanye da wata black gown bin mutanen wajen take da kallo take idonta ya sanja color yakoma dark red,She felt her fangs coming out,ready to bite human. Right now she is hungry,hungry for blood, for a flesh to taste,for a body to consume... Kalle kalle tafara wani irin kamshi tafaraji tunda take bata taba jin dadin kamshin jini ba sai yanzun juyawa tayi idonta yasauka akan wata yarinya bazata wuce 18yrs ba binta take da kallo she's looking straight at her flesh,ganin hankalin mutane baya kanta kowa harkan gabansshi yakeyi yasata zuwa dab da ita Without a doubt she grab her close,and put her mouth on her neck,and starts sucking her blood. Kuma daidai lokacin ne wanda su leemah suka ciza yakaraso wajen cikin mawuyacin hali faduwa yayi awajen jama'ah sukayo kanshi ana tambayarshi lafiya? nakusa dashi yakamo ya yage cikin shi yanacin naman wajen,ganin hakan yasa sauran mutane kokarin guduwa amma a kalla saida ya ciza mutane sama da goma,,,,kafin cikar 2hrs gaba daya yan station din sun zama zombies take gari ya rikice mutane suka kulle kansu a gidaje domin tsira da rayuwan su.
~*
_@Hospital_
"Gaskiya bazan zauna ina gani na rasa rayuwata a banza ba komine zai faru saidai yafaru amma saina nemo hanyan fita daga nan" cewar Abdul, wanda tun dazun yake musu mita akan cewa shifah saiya fita sukuma sun hanashi Ruky ce taja tsaki cikin bacin rai take magana "Kagafa Abdul naga sokake ka rainama mutane wayau don kawai kaga ana lallaba ka daga yanzun babu wanda zai kara hanaka fita Allah yabada sa'a," tana gama fadar hakan takoma kan bed tazauna ganin hakan yasa sauran ma komawa suka zauna akabar Abdul kadai tsaye baiyi tunanin komai ba yadauki bag dinsa sannan ya fice daga dakin.
Saida yayi tafiya mai nisa amma baiga alamun kofa ba juyowa yayi da nufin yakoma inda su Ruky suke amma me cak ya tsaya sakamakon tozali da yayi da wani irin kare(dog) gaba daya jikinsa ya sanja kama, jikinsa babu gashi ko daya kuma rabin naman jikinsa duk babu wajen yayi wani irin abu tsoro bakinsa wasu irin zago zago hakora ne,sannan harshen sa yazama kalar abin tsoro sosai,,,, ga wani irin gurnani mai firgitarwa yana fitowa daga karen hatta color din idanunsa sun sanja sunkoma yellow and black, Juyawa yayi da niyan komawa ta baya nan ma arba yayi da karnukan su wajen biyar kuma gaba dayan su duk rabin jikinsu babu..wani irin tsoro ne yakamashi tunda yake bai taba ganin abu mai firgitarwa kamar wadannan karnukanba,,,Atake sukayo tsalle suka hau cin naman jikinsa wata irin kara yasaki wanda har sauran students din saida suka jiyo ihun nashi...
~*
"Yanzun mene abin yi? Ni damuwa tama inasu Merapati suka shiga?"
Zaynab tace tana kallon su.
Suna shirin bata answer suka farajin motsi a jikin kofa...mikewa sukayi a hankali suka leka window din zombies ne su wajen 30 gaba daya sunzama abin tsoro don wasu ma fuskansu babu tsoka kuma jikinsu duk yazama ash while others have yellow colored skin... Idonsu ma kadai abin tsoro ne wasu nasu yakoma greenish blue,greenish black,orange,while others has yellow green eyes.
"Shhh" Nasir frightened voice said, "don't make any sounds,keep quite, if they hear you, they will hunt you" alamu yayi musu akan su koma baya gaba daya a tsorace suke zama sukayi kowa da abinda ke ransu....
Duniya ta rikice yayinda zombies suka shiga cikin garin sosai yawancin rabin garin sunkoma zombies kuma bi suke ko ina duk inda sukaji kamshin jini saisunje mutum ko a cikin me yake sai sun shiga,yanzun kuma saiga tashin hankalin dayafi na zombies domin kuwa wasu irin halittu ne suka fara bayyana wanda har mutune suke tunanin gara suje zombies su cije su akan wannan halittun su gansu saboda su direct suke kashe mutum su dai wadannan hallitun sunada siffar mutane amma kuma ta bangare guda suna kama da bat,saboda sunada fuka fukai masu tsini hannun su ma wasu irin farce ne masu tsayin gaske bakinsu kuma manyan hakora ne (fangs) wanda idan suka saka bakinsu a wuyan mutum take suke rabashi da gangar jikin.....!!!
@NM__🦋♥️
[27/01, 4:05 pm] Ablerh Authoress: Title: WANI GARI (The beginning of a new world)
Description: What happens when you somehow end up in a "New world? And what does it feel like to suddenly be a stranger in the world you thought you knew?
Merapati Hassy And Basma, both students one day a gate Into a different dimension opens to them as they find themselves in a different world,a world where mysteries and enchanted magic happens...How will they get home? What will happen to these girls along the way? Will they even be able to survive being in a world that is completely different from their own?
Tags #dimension#parallelworld#zombiesapocalypses#disappearance#journey#vampires#wonderland#magic#cursed#doppelgänger
~*
Episode 9: The Gatekeeper.
Dedicated To Merapati🦋
Basma Hassy zaune suna duba abu cikin phone din Basma, Merapati ta shigo kallo daya tayi musu take kunyan Basma yakamata saboda yanda ta fada mata maganganu a lokacin.
Mikewa sukayi a tare Hassy tace "lafiya naganki a haka?"
Basma ta matso ta kamata bayanta zaunar da ita sannan ta zuba mata ruwa a cup ta mika mata amsa tayi saida tasha rabi ta ajiye cup din a gefe kallon Basma tayi her voice is so slow "I’m so sorry Basma,,at first I don’t trust you buh now I agree with you! we are in a different world." In shock suke kallonta "What do you mean?" Hassy asked as she took a seat next to her....
Merapati looked at her "Um I mean I saw myself, amma kuma bani bace ba but it was me"
Gaba daya shiru sukayi saboda sun tabbata cewa Merapati taga Sheenaz.
Basma tace "sai yanzun nagane abinda kike nufi kuma dama abinda mukeso kigani kenan ta hakan ne kadai zaki yadda cewa ba a duniyar mu muke ba muna wata duniya ce daban wanda mu kanmu bamu san ta yaya kokuma ta ina mukazo ba,,,kuma bamu san ta ina zamu koma ba,Kuma na tabbata yanzun kingane komai bakya bukatar wani karin bayanin! Yanzun abu uku ne a gabanmu na farko kota halin yaya ne karki bari masu hotel din nan suke ganinki saboda komai zai iya faruwa idan har suka gano bakene ainahin Madam din su ba...Abu na biyu dole ne musan hanyan daza mubi domin komawa duniyar mu sai kuma abu na karshe wanda shine yafi kowanne hadari kada mu nuna wata alama cewa ba anan duniyar muke ba cause people
are dangerous now we must be very careful...." Maida kallon ta tayi kan Merapati taci gaba da cewa "karki damu kanki muma farko haka muka shiga rudani a lokacin da mukaganta sunanta Sheenaz"
Kallonta suke gaba daya jikinsu yayi sanyi Hassy tace "dama hakan tana faruwa? do you think there is a different world like ours, and they live as we do?"
"Yes, there are different worlds and in them there are different beings who live just like we do, just like you see in this world..There are different species and each species has its own way of life. One day I will tell you how a bee lives....you will see how it lives I am sure you will be amazed.." Basma continue with her explanation......
~*
Yau kwanan su 20 cif a sabuwar duniyar dabasu san tayaya sukaje ba,kuma tundaga ranan Merapati komai irin na Sheenaz takeyi wanda hakan yasa ba a ganeta.
Suna zaune kowacce da tunanin datakeyi knocking akafara a kofan kallon kallo aka shiga saboda indai ba order sukayi ba babu mai shigo musu daki kuma yanzun lokacin Lunch baiyi ba bare suce sunyi order,Hassy ce taje ta bude kofan wata mata tagani sanye da black abaya saikuma face inta data sa nikab...Hassy looks at her,her face was full of surprise "who are you?what are you doing here? what do you need from us?"
She just smile and say "please let me in i need to talk to you, and it's an important issue trust me."
Juyowa tayi ta kalli su Basma kanta tayi nod alamun tabarta ta shigo....
Cikin nutsuwa take takowa harta iso cikin parlourn kallonsu take daya bayan daya akan Merapati ta sauke idanunta saikuma ta cire nikab din baki bude suke kallonta Merapati kuwa mutuwan zaune tayi zuciyanta yana bugawa da karfi ganin tsananin kamar ta da Sheenaz, komai da komai iri daya ne hatta tsawon su da hasken fatarsu, gefe guda kuma a tsorace suke ganin yanda suka shiga tashin hankali yasata sakin murmishi tace "ku kwantar da hankalinku banzo da niyan cutar kuba,nazo nan ne da niyan taimakon ku saboda nariga dana sani cewa ku baki ne a wannan duniyar tamu.... I know you don't exist in this world" Mamakin su yakaru to wai tayaya ma tasan cewa su baki ne a wannan duniyar?
Zama tayi a daya daga cikin kujerun taci gaba da cewa "nasan kuna mamaki ta yanda akayi nasan ku baki ne ko? because I am the gatekeeper and no one can enter or leave without my knowledge! Tun ranan da kuka shigo nasani saidai a lokacin ina busy sosai shiyasa banbi ta kan lamarin ku ba, sannan principal din mu takira Dad dina tanayi masa complain akan cewa ta ganni a wata school din daban wanda nikuma nasan bana zuwa wata school idan ba wadda Dad yasani ba tundaga nan nafara tunanin akwai abinda ke faruwa...Saikuma Manager dina(Hotel Manager) yakirani yana bani hakuri akan abinda yafaru nan ma nakara tabbatar wa something's wrong saikuma kwatsam na hadu da Hassy Wanda harna bigeta nakaita hospital shima tundaga nan na kara yadda akwai abinda yafaru saboda yanda take kallona tamkar ta sanni saikuma naji ta kirani da suna Merapati....and ranan dana fara ganinki I was surprised when I saw you" she pointed at Merapati..."Tun farkon shigowata Park din naganki amma ke baki ganni ba shiyasa nabarki kikayi magana da fiancé dina saboda in tabbatar da cewa you’re me, cuz I know ta wani bangaren zamu iyayin abu iri daya ,sai gashi yazo yayimin complain akan cewa abinda nayi masa a park sam baiji dadi ba...and I was surprised yanda kikayi treating din fiancé na exactly haka nakeyi mishi duk lokacin da muka samu matsala! Jiya kuma ina zaune Manager yakirani akan cewa zaman da nikeyi a hotel bashida amfani gara nakoma gida don ya tabbatar da ace Dad dina yana gari bazan zauna a hotel tsawon kwanaki ba...Tundaga jin bayaninsa nagane kene wadda nagani a Park...kuma dama inason haduwa dake amma bansan ta ina zanfara ba Shiyasa yau na shirya domin zuwa nasa meku sannan kuma lokaci yayi dazaku koma gida ina nufin ainahin duniyar ku."
Basma ta kalleta "amma tayaya kike ganin zamu iya komawa duniyar mu?"
Smile tayi tace "Three days before the rise of a blue moon"
"Wait I dont understand,can you explain it?" Merapati ask her.
She keep smiling and talking at the same time "Normally blue moons come only about every two or three years...you guy's are very lucky nan da kwana biyu zaku koma duniyarku."
Hassy tace "yanzun a misali idan naje wata duniyar daban dole saina jira blue moon sannan zan iya komawa ainahin duniyar mu? Like saina jira shekarun fitowar blue moon?"
Kanta ta gyada "aa gaskiya tunda ko wace duniya yanayin yanda suke rayuwa daban ba lalle bane ace komai zai zama iri daya." Basma ta sake jefo mata tambaya "kintaba zuwa wata duniyar ne bayan wannan?"
Murmishi takarayi taci gaba da cewa "gaskiya bantaba zuwa ba tunda ana gargadin mu akan mu kula da inda muke zuwa...Some places are very dangerous."
"Amma tayaya kika zama gate keeper? Naga bakida wasu shekaru" she just smiled and said "maybe I'm among the luckiest one's..."
~*
Tundaga ranan komai tare sukeyi Basma Hassy Merapati Da Sheenaz sun shaku sosai har sunajin bazasu iya rabuwa da itaba tanada matukar kirki gata mace mai son jama'ah don yanzun haka ma suna tare a hotel din duk da Sheenaz taso suje gidan su amma sunki saboda suna ganin hakan kamar zai haifar da wata mtsalan daban..
Kuma a gobe suke shirin komawa duniyan su...dukkan su suna zaune shiru sam basason rabuwa da Sheenaz itama haka don jitakeyi kamar ta bisu su tafi tare amma hakan bazai taba yiwuwa ba ita kadai Allah yabama iyayenta..
Kamar wancan karon tafiyan 8hrs sukayi sannan suka iso wajen, tent aka hada musu sannan Sheenaz ta sallami masu hada tent din shiga sukayi dukansu shiru sukayi saboda aihinin rabuwa da juna....
_1:00am_
Hasken farin wata ne yafito sosai wanda ko allura ce ta fadi mutum zai iya ganinta saboda tsananin haske da girman moon din...Cikin dajin suka shiga daidai wajen dasuka tsinci kansu suka koma...Hugging dinta sukayi gaba daya kuka sukeyi sam basason rabuwa. Bayan sungama bankwana Sheenaz tafara fadan wasu magic words take wata irin iska mai karfi tafara kadawa cikin karamin lokaci suka daina ganin komai walkiya aka fara cikin second's komi yakoma daidai....Wani irin kuka ta Sheenaz takeyi mai tsuma zuciya!
Lokacin dasuka bude idonsu a wannan wajen katangar suka tsinci kansu. Hamdala sukayi Merapati tafara duba inda Sheenaz ta kwatanta mata wanda ta nan ne kadai zasu iya komawa ainahin duniyar su...Ganin da gaske dai komawa zasuyi yasa Hassy cewa "Ku tsaya..." Juyowa sukayi suna kallonta